Featured Create an Ad

Makalu

Blogs » Rayuwa da Zamantakewa » Ire-iren matsaloli da ake samu da dangin miji da yadda za a kauce fadawa cikinsu

Ire-iren matsaloli da ake samu da dangin miji da yadda za a kauce fadawa cikinsu

 • Dangin miji mutane ne da ke da muhimmanci kuma suke taka muhimmiyar rawa a zamantakewar aure ta ya mace.

  Da yawan mata kan ci karo da kalubale daga wannan bangare na dangin miji. Har ta kai wasu matan babbar fargabar su bai wuce a ce suna fuskantar matsala da dangin mijinsu ba, duk yanda namiji ya kai ga son mace, kaso mafi yawa daga cikin mazaje ba su yarda da cin mutunci ko wulakanta danginsu ba. 

  Sai dai wani bangaren matan na ganin dangin miji a matsayin mutane masu takura da sa ido a kan al’amuran gidan matar dan uwansu wanda yasa da yawan mata kan shiga damuwa da ka iya jefa rayuwar aurensu cikin wani yanayi.

  Ya zama wajibi mace ta karanci su waye dangin mijinta don ta san yanda za ta zauna dasu, duk da cewar ba su take aure ba, kamar yadda take da ikon mijinta haka suma akwai hakkin yan uwantaka a tsakanin su.

  Wasu bangaren dangin mijin ke kawo matsala inda wani bangaren kuma ita matar ce ke da matsala.

  A matsayin ki na mace dole ki taya mijinki son yan uwansa matukar kina son zama lafiya da shi da kuma su, ki samu kwanciyar hankali a rayuwar aurenki.

  Daga lokacin da kika yi aure ki sa a ranki cewa ba wai kin yi aure don farantawa mijinki ba, a’a kin yi ne don ki koyi zama da dangin mijinki. Ki kuma kulla kyakkyawar alaka tsakanin ki da su.

  Zamu tattauna game da irin matsalolin da ake samu da dangin miji da kuma yanda za a yi don warware su.

  • Dangin miji masu nuna isa, mulki da iko akan mijinki

  Akwai dangin mijin da daga ke har mijin ki zasu nuna suna da iko mai karfi a kan ku, abun bai tsaya akan mijinki da yake dan uwansu ba, har ke. Sai abinda suka ce za a yi shi za a yi, ba ki isa ki nuna cewa hakan ba dai-dai bane, mijinki ma ba zai dauka ba, komi da yan uwanshi suka yi shine dai-dai. 

  Irin wannan matsalar na nan birjik a cikin gidajenmu.

  Idan irin wannan matsalar gare ki, farko abinda za ki fara dubawa shine, shin minene tushen matsalar? Shin dangin mijin ki na tsoron kar ki kwace masu dan uwa ne?

  Duk wadannan basu rasa nasaba da dalilin matsalar. 

  Daga zarar kin gano bakin zaren ya wajaba ki zauna da mijinki don tattaunawa. Ki nuna masa muhimmancin yan uwansa da kuma na ki muhimmancin da kuma bambancin hakkunanku da ke kan shi.

  Kar ki matsa akan cewa komi ke ce a kan gaba, duk abinda ya shafi abinda zai yi na kyautatawa dangin shi ki bar shi yayi da kansa kar ya wakilta ki, sai dai idan ke din ce za ki yi. Ganin cewa komi ta hannunki yake shigowa zasu yi tsammanin cewa ke ce ke tsarawa mijinki iya kyautatawar da zai masu, hakan kuma na saurin haddasa husuma a tsakani.

  • Dangin miji masu shiga harkokin da suka shafi aurenku

  Kowadanne ma’aurata suna da na su matsaloli da ba a rasa ba, sai dai mi? Ba matsaloli bane na a zo a gani ba, amma sai ki ga dangin mijinki na shiga cikin harkokin da bai kamata su shiga ba, a gefe guda kuma su dauki wadannan matsaloli da girma, wanda sai ku rasa ma ta inda za ku gyara abun ya daidaita. 

  Hanya ma fi sauki a nan ita ce, ya zama duk wani abu da ya shafi auren ku ya tsaya a wajenku kadai sai in ba yanda za ku yi sannan iyaye su shigo ciki. Kar ku yarda sirrinku ya fito waje.

  Ko da mijin ki ya bata mi ki rai kar ki kuskura ki nuna a gaban su ta yanda har zasu iya tsoma bakinsu a ciki.

  A duk lokacin da kuke kusa da su, kar ki bari fada ko wata gardama na hada ki da miji. Rayuwar aurenku ya zamo yana da sirrin, ta hakan za ku samu saukin shigowar su cikin rayuwar aurenku, saboda ba ku basu damar da zasu tsoma bakinsu a ciki ba.

  Ku karanta irin kuskuren da ma’aura ke yi bas u sani ba.

  • Dangin mijina na saurin yanke mun hukunci da tsangwama ta

  Duk irin wannan na faruwa a tsakanin dangin miji da matar dan uwansu.

  Iyaye da yan uwa kan so kasantuwar abu mai kyau ga nasu. Sai dai a duk lokacin da mace ta yi aure, a kan samu yan kura-kurai kasancewar ta sabuwa a irin wannan fannin kafin ta saba. 

  Sai ya zamo ta bangaren dangin miji sai wasu su ga sam wannan ba ta dace da dan uwarsu ba, ko kuma ba irin matar da suke so bace ga dan uwansu. Daga nan zasu fara tsangwamar matar saboda ta saba ma tsarinsu.  Sai ya zamo duk wani motsinta a tafin hannunsu yake, komi za ta yi a wajensu to ba ta iya ba.

  Duk wata matsala da za ta bullo, su fa a wajen su ke ce musabbabi.

  Zama da irin wadannan dangin miji na bukatar gogewa da wayewa, dole ta karkashin kasa za ki rika bullo mu su, matukar ki na son zaman lafiya ki kuma zauna da mijin ki. 

  Duk abinda zasu yi kar ki rike shi a ranki, ki yi magana da mijinki saboda zaman shi kike yi, amma su din ma wasu bangare ne na aurenki. Idan ta kama ku zauna da su a yi sulhu. Sannan ki kyautata musu tamkar na ki yan uwan, ki basu kulawar da ta dace. Ita zuciya na son mai kyautata ma ta.

  • Dangin mijina sun cika takura da bin mijina

  Akwai dangin mijin da a koda yaushe basu rabo da gidanki, kullum maganar sun zo ganin dan uwansu ne. Ba ki iya raba yan uwa. Sai dai idan zuwan da suke ya wuce shari’a har ya zamo takura tsakanin ki da mijinki akwai irin mataki na hikima da za ki iya dauka saboda mafi yawan lokutta yana tare da yan uwansa, ba ki isa kiyi korafin cewa baida lokacin ki ba.

  Wasu lokuttan ma har ta kai su kan nuna kishinsu akan ki, saboda suna ganin dan uwansu ya fifita ki sama da su, har ya zamanto cewa su na fadar yafi son ki a kan su.

  A irin wannan yanayin fada da su bai taso ba, a bu ne da za a bi shi a hankali saboda yan uwan shi ne, sun cancanci so da mutuntawa daga wajen shi. Za ki jawo su a jiki, ya zama akwai wasa da dariya a tsakaninku, ki kuma saki jikin ki dasu ta yanda babu kyara babu tsangwama, a daya bangare kuma ki kama mutuncinki. Ki nuna mu su irin son da dan uwansu ke mu su da kuranta irin yanda yake maganar su. Hakan zai sa ke ma su saki jiki da ke, su na masu yakinin cewa ba kwace mu su dan uwa za ki yi ba.

  • Dangin mijina basu girmama sirrina

  Duk lokacin da su ka ga damar zuwa gidan ku zuwa suke ba tare da sun sanar da ku ba, su a ganin su ai gidan dan uwansu ne su ma su na da iko a kan shi. Za su iya zuwa a duk sanda suka so, su tafi a lokacin da su ka so. Wanda hakan kan shiga hakkin ki, musamman a lokuttan da ki ka fi bukatar kasancewa da mijinki. 

  Sannan in sun zo, su din ga mi ki bincike kenan kama daga dakin ki, dakin shi, kicin, wayar ki da sauran su. Duk don su bincika su ga wani hali kike ciki. Ba ki da damar magana da mijinki sai sun sa ka ma ku baki a ciki. 

  Daga lokacin da ki ka fara fuskantar irin wannan halin daga dangin mijinki daga lokacin ne ya kamata ku taka ma abin birki.  Sirrinku na ku ne, babu bukatar wani daga cikin su ya sani, ko hatsaniya ku ke kar ku kuskura su sani, duk wani abu da zai basu fuskar son sanin sirrin da kuke boyewa kar ku nuna mu su. Duk wani abu da kika san zai sosa mu su rai ki guje mi shi.

  Sannan ta bangaren su, daga zarar kin lura suna son magana da dan uwansu to ki basu wuri, su yi duk maganar da za su yi ba tare da kin sa mu su baki a ciki ba. Hakan zai kawo zaman lafiya a tsakanin ku saboda sun san cewa su na da iko da dan uwansu suma, saboda zai zauna ya saurare su, ya ji matsalolinsu ba tare da kin ji sirrin su ba. 

  Mata su lura cewa ba koda yaushe bane mace za ta rika kai ma mijinta karar danginshi ba, a wasu lokuttan ke da kanki za ki yi maganin matsalar.

  Yadda kika amshi mijinki da hannu biyu duk da tarin nakasu da yake da shi, suma haka za ki rungume su dukkansu mutane ne masu ajizanci. Zasu yi ba dai-dai ba, zai kuma kasance ba zasu iya canzuwa a yanda kike so ba. 

  Kuna iya duba wannan makala da ta yi tahalili akan abubuwa guda 6 da duk mace ke bukatar sani kafin ta yi aure.

No Stickers to Show

X

Da Dumi-Dumin Su

 • Ku latsa nan don karanta labarin Saurin Fushi Na Kawo Da Na Sani. A wani ƙauye akwai wani mutum  ana kiran sa Abu Sabiru, ya kasance mai tsananin haƙuri da kawar da kai akan wasu al’amura. Dalilin da ya sa ma ake kiransa Abu Sabiru kenan. Yana zaune tare da matarsa kyakkyawar gaske ...
 • Ku latsa nan don karanta darasin rana ta uku. DARASI NA 1 Matakan rubutun gajeren labari A jiya mun yi bayani akan matakan da ake bi wajen tsara labari, yau kuma za mu bayani a takaice kan matakan da ake bi wajen rubuta ingantaccen labari. Waɗannan matakai ba tabbatattu ba ne, ma'ana ba wajibi ne...
 • Ku latsa nan don karanta babi na shida. Habeeb na kwance a kan doguwar kujera ya ji an murɗa handle ɗin ɗakinshi tare da turo ƙofar a hankali. A hankali ya buɗe idanunsa da suka yi nauyi sakamakon ciwon kan da yake fama da shi. "Fateemah" ya faɗa a ransa, lokacin da ya kai duba ga Jummai da ke ts...
 • Mon at 1:39 PM
  Posted by Bakandamiya
  Uwargida ba za ki yi dana sanin koyan yadda ake yoghurt in fruits ba. Domin kuwa kayan dadi ne sosai da sosai kuma cikin mituna kalilan za ki hada. Ba a ba yaro mai kiwiya!!! Wannan recipe yana daya daga cikin recipes da muka koyar a zauren Free Ramadhan Classes with Umyuman a nan Bakandamiya. Abu...
 • Hadin special salad nawa na musamman ne! Ga sauki ga dadi, uwargida sai kin gwada za ki bani labari! Wannan ma yana daya daga cikin recipes da muka koyar a Ramadan a shirin girke-girkenmu wadda aka gabatar a zauren Free Ramadhan Classes with Umyuman. Shin ko kin tuna gashin tsokar kaza da muka koya...
 • Red velvet cake, cake ne da mutane da dama suke so kuma kuma suke son ci. Saboda haka, akwai hanyoyi daban-daban na yin red velvet cake, ga yadda na ke nawa cake din na kawo muku. Wannan yana daya daga cikin recipes da muka koyar lokacin Ramadan anan Bakandimya. Domin ganin duk jerin recipes din da...
View All