Makalu

Yadda ma’urata ya kamata su bullowa matsalolin rashin lafiya idan sun taso a rayuwar aure

 • Matsalar rashin lafiya matsala ce babba da ke taka muhimmiyar rawa wajen hargitsa zamantakewa da rayuwar iyali. Ba abu bane da mutum daya zai boye ma kansa ba tare da sanin aboki ko abokiyar zama ba. Saboda matsala ce babba da take bukatar shawara, tattaunawa a tsakanin juna. 

  Mafi yawa kunya, tsoro da kuma fargaba kan sa ma’aurata su kasa furta abinda ke damunsu, musamman idan aka yi katari da ma’auratan da ke fama da matsalar fahimtar juna. Sai ya zamo abinda ka iya jawo barazana ga rayuwar aurensu.

  A duk inda aure ya kullu a na fatan akwai fahimtar juna, so da kaunar juna da kuma tausayi a tsakani.

  Wadannan ababe kan taimaka matuka gaya wajen ganin an samu kyakkyawar mu’amala a tsakanin juna, hakan zai ba kowane bangare damar fadin lalurar da ke tattare da shi/ita ba tare da wata fargaba ba. 

  A duk inda ma’aurata suka samu wata matsala ta rashin lafiya a tsakanin su babban abu a nan shine su cire tsoro da fargaba, su tunkari juna da maganar don ganin an samu fahimtar juna. Hakan zai taimaka wajen warware matsalolinsu. 

  A wannan makala ta mu za mu tattauna a kan yanda ya kamata ma’aurata su bullowa lamarin, a gefe guda kuma mun yi tattaunawar sirri da wasu daga cikin ma’aurata maza da mata da ke fama da wata lalura wadda ta shafi lafiyar su.

  Mun ji ta bakin su da irin yanayin da suka shiga da abokan zaman su har da irin kalubalen da suka fuskanta.

  • Fahimtar juna

  A duk inda ma’aurata suke ana tunanin akwai fahimtar juna a tsakanin su, ta hakan a duk lokacin da daya ya shiga wata matsala ko dumuwa daya zai fahimci halin da yake ciki. A kowane irin yanayin kana iya karantar dan uwanka. 

  Babban kuskuren da wasu ma’auratan kan yi a duk lokacin da suke dauke da wata lalurar shine rashin sanin yanda za su bullowa abokan rayuwar su. Kamar yanda na ambata a farko wasu tsoro da kunya kan same su a lokacin. Matukar ka/kin fahimci da wa ka/ki ke zaune, mutum zai san yanda zai bullowa lamarin, tunda akwai kyakkyawar fahimtar juna a tsakani.

  Anan dole a lura da irin yanayin da mutum ke ciki, shin farin ciki ne ko akasin haka. Kowace mace ko namiji sun san lokacin da ya kamata su sako magana mai muhimmanci, irin wannan lokacin za a iya kawo zancen rashin lafiya ga miji ko mata don samun maslaha. Domin a irin wannan lokacin aka fi bada hankali yanda za a fahimci ina zancen ya dosa.

  Daga zarar kun fahimci juna akan matsalar rashin lafiya da daya daga cikinku ke fama da ita, babban abinda ya kamata ku yi shine zuwa ganin likita domin a san musabbabin cutar da hanyoyin kariya da za a bi don ganin daya bai cutar da daya ba. 

  A duk lokacin da lalura ta rashin lafiya ta samu daya daga cikin ma’aurata, dole a samu daya daga cikin da zai zama mai jajircewa don ganin an san ina matsalar take don ya zama kowane bangaren an samu kariya. 

  Kamar yanda mu ka tattauna da wata baiwar Allah a kan matsalar ciwon sanyi da take fama shi.

  “Tunda na fahimci ina dauke da cutar ciwon sanyi, nayi ta kokari wajen shan magungunan asibitin dana gargajiya amma abin babu wani cigaba, da ya tafi kwana biyu sai ya dawo.  Haka dai na daure na je asibiti, bayan gwaje-gwaje da aka yi, likita ya ba ni shawarar in koma gida mu zo tare da mijina don ko ni an bani magani an magance cutar, ta yiwu shi yana da ita don haka tawa cutar dawowa za ta yi. Sai da ya kai wata guda kafin in samu karfin gwuiwar fada ma sa lalurar da ke damuna, da yake mutum ne mai fahimta ya amince mu koma asibiti tare don neman lafiyar mu. Mu ka je aka yi duk gwaje-gwaje da za a yi, a ka ba mu magunguna. Yanzu haka dai duk babu mai dauke da wannan cuta a cikin mu saboda tare mu ka nemi magani”.

  Kuna iya duba wannan makala da ta yi bincike akan kayan mata a kasar Hausa.

  • Jin tsoro da kunya

  Wadannan ababe guda biyu na daya daga cikin dalilan da kan sa wasu ma’auratan kasa tunkarar junan su. Wasu su na tsoron kar a guje su ne, inda wasu kuma kunya da tsoron ne su ka taru a waje daya.

  Babban abinda ake so shine a duk inda ma’aurata suke babu maganar tsoro da kunya musamman a kan abinda ya shafi lafiyar daya daga cikin su. 

  Kunya kan cutar da mutum a irin wannan yanayi na lalura bare idan aka yi dace da miji ko mata mara kula.

  Sai ma’aurata sun cire tsoro da kunya wajen tattauna matsalolin da suka shafi lafiyar su, domin samun ingantaccen zama mai cike da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

  Daga inda aka ce yau daya daga cikin ma’auratan ba lafiya, kwanciyar hankali zai yi karanci a cikin wannan zamantakewar, amma daga zarar an gano bakin zaren za a samu rangwame.

  Allah ne ya halicci cuta kuma ya halicci maganinta, don haka babu dalilin da zai sa mutum ya boye cuta a cikin sa ba tareda sun zauna don ganin yanda za a bolluwa ita wannan cutar ba. A duk lokacin da ka ke cikin wata matsala ka tattauna ta da wani, za ka ji a cikin zuciyar ka tamkar an rage ma wani kaso mai yawa na daga cikin abinda ke damunka, saboda mi? Saboda wannan matsalar da damuwar da mutum ke ciki ya cire ta daga cikin zuciya ta hanyar yin magana, ba kamar wanda zai bar maganar a ran shi ba tare da ya tattauna ta ba.

  A kullum a na kira da ma’aurata su kasance mafi kusa da juna, su zama tamkar abokan juna, hakan zai sa su kara kusantar juna yanda ko wata lalura na damun daya, dayan ba zai ji kunya ko tsoron tunkarar daya ba.

  • Karfafawa da tsaya ma juna

  A duk lokacin da wata lalura ta samu daya daga cikin ku, babban abinda ya kamata ku yi shine a karfafa ma juna gwuiwa, nuna kyama da hantara ba abinda yake haifarwa sai dan da na sani. A irin wannan lokacin ba abinda mutum yafi bukata sama da lallashi da kulawa ta musamman. Hakan na taimakawa wajen rage radadin ciwo da mutum ke ciki, ko da kuwa ba samun sauki, za a samu rangwame a dalilin wannan kyautatawa da ake ma mutum.

  Amma daga lokacin da mutum ya kamu da wata lalura a ka nuna kyama a gare shi, ko rashin kulawa a gaba ba zai so ya fadi cewa yana dauke da cuta ba, irin hakan ke sa wasu boye cututtukan da ke damun su har sai abu ya kai matakin da zai wahalar magantuwa.

  Kamar yadda naji ta bakin wani bawan Allah da matar shi ke fama da lalurar sankarar mama.

  “Matata ta dade ta na mun korafin cewa tana yawan jin kullutu a mamanta, na kan fada ma ta cewa ba wani abu bane. Ban mantawa akwai lokacin da nace ma ta ta cika raki, abu karami sai ta maida shi babba. Ba tare da na ji ta bakinta ba. A lokuta da dama ta kan ji ciwo sosai a wajen, ba ta samu kwarin gwuiwar zuwa asibiti a duba lafiyarta ba, sai da wata rana ta wayi gari da kurji a wajen wanda ya dau ruwa, ya zamo bata iya komi saboda azabar ciwo. A dalilin hakan yasa ta je asibiti inda aka tabbatar tana dauke da sankarar mama. Sakaci na da rashin daukar maganar matata ya jawo min asara babba saboda har ta kai sai da aka yanke ma ta mama guda daya. Na san akwai magidanta ire-ire na da basu dauki maganar matansu a bakin komi ba. Shi ciwo tun yana karami ake tarbar sa. Na yi danasani marar iyaka”.

  A duk lokacin da daya daga cikin ma’aurata ke fama da lalura, babbar shawara a nan ita ce su je asibiti tare, su zauna a gaban likita don bayanin da likita zai yi ya amfani kowane daga cikinsu. Watakila akwai abubuwan da mai fama da lalurar zai yi wanda sai da taimakon bangare daya za a cimma nasara. Sannan hakan zai kara tausayi da kuma karin kulawa a tsakanin juna.

   Abun taimako da ka raina kana ganin ba wani abu bane, sai ya zamo shine taimakon da aboki/abokiyar rayuwar ka/ki ke bukata a wannan lokacin na rashin lafiya.

  A duk inda matsalar rashin lafiya take a tsakanin ma’aurata a na bukatar a zauna a tattauna wannan lalura domin samun mafita gaba daya. A duk inda aka ce a rayuwar aure akwai mai lalurar rashin lafiya, akan samu nakasu a ciki. Dole a jajirce wajen ganin an samo bakin zaren.

  Ku karanta wannan makala da ta yi bayani akan irin kura-kuran da ma’aurata ke yi ba suna ni ba.

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Jini Baya Maganin Kishirwa: Babi na Uku

  Posted Jan 12

  Ku latsa nan don karanta babi na biyu. Sakinah ta share hawayen da ke zuba kan kuncinta kafin ta ce. "Insha Allahu Umma zan yi aiki da dukkan abin da ki ka umarce ni da shi da yardar Allah, ba zan taɓa baki kunya ba". "Yauwa Sakinah Allah ya yi miki albarka". "Amin"...

 • Yadda ake baked awara

  Posted Jan 11

  Barka da sake saduwa a cikin shirin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau na zo maku da sabon girki wato yadda za ku hada baked awara. Abubuwan hadawa Awara Kwai Carrots Seasoning Cooked minced meat Muffin tray Albasa Yadda ake hadawa Farko za ki yanka a...

 • Bayanan masana game da ingantattun hanyoyin ƙayyade iyali

  Posted Jan 8

  Mene ne ƙayyade iyali? Ƙayyade iyali ko tazarar iyali ko kuma family planning a Turance wani mataki ne da ma'aurata kan dauka don hana mace daukan ciki domin rage yawan haihuwa akai-akai, ko ƙayyade yawan ‘ya’ya da za ta haifa ko dai ma don wasu dalilai na ...

 • Ma'aurata: Babi na Biyu

  Posted Jan 8

  Idan baku karanta babi na daya ba to ku latsa nan don karantawa. Ana kiran sallah asuba ta farka daga bacci addu'an tashi daga bacci tayi kafin tayi miƙa tana salati ga Annabi S.A.W kai dubanta tayi a gefen da Fahad yake kwance tayi, har yanzu yana nan yana bacci kamar...

 • Burina a shekarar 2020: Saurare na ya fi magana ta yawa

  Posted Jan 4

  Masana sun ce daga cikin abubuwan da suka sa dan Adam yin galaba a kan sauran halittu shi ne yadda yake iya hada kai. Don mutum shi kadai ba zai iya gwada karfi da zaki ko giwa ba. Amma idan ya hada karfi da sauran ‘yan uwansa babu kalubalen da ba za su iya t...

 • Yadda ma’urata ya kamata su bullowa matsalolin rashin lafiya idan sun taso a rayuwar aure

  Posted December 31, 2019

  Matsalar rashin lafiya matsala ce babba da ke taka muhimmiyar rawa wajen hargitsa zamantakewa da rayuwar iyali. Ba abu bane da mutum daya zai boye ma kansa ba tare da sanin aboki ko abokiyar zama ba. Saboda matsala ce babba da take bukatar shawara, tattaunawa a tsakanin...

View All