Featured Create an Ad

Makalu

Blogs » Harshe da Adabi » Kwatanci tsakanin wa?ar ‘Tabban Ha?i?an’ da wa?ar ‘Lalura’ na Shehu Usmanu ?anfodiyo

Kwatanci tsakanin wa?ar ‘Tabban Ha?i?an’ da wa?ar ‘Lalura’ na Shehu Usmanu ?anfodiyo

 • Tsakure

  Wa?ar Lalura da kuma Tabban Ha?i?an tamkar ?anjuma ne da ?anjummai. Dalilai da yawa sun nuna hakan, musamman idan aka yi la’akari da cewa dukkaninsu an gina su ne kan jigon wa’azi. Sannan baki ?ayansu wallafar Shehu Usmanu ?anfodiyo ne. baya ga kamanceceniya ta wa?annan ?angarori, baitoci da dama a cikin wa?o?in biyu tagwaye ne ta fuskar abin da suke jan hankali zuwa gare shi. Sai dai bayan wannan kamanceceniya, aikin ya kawo bambance-bambance tsakanin wa?o?in biyu. Baya ga haka, aikin ya kawo shawarwari game da yanda wa?o?in biyu za su kasance masu amfanarwa ga ?alibai da ma sauran al’umma baki ?aya. ?aya daga cikin wa?annan hanyoyi shi ne nazartar wa?o?in tare da gane sa?onnin da suka ?unsa, ba sauraro ko karatu domin nisha?i ba kawai.

  Na

  Abu-Ubaida SANI

  Department of Educational Foundations

  Usmanu Danfodiyo University, Sokoto

  Phone No. 08133529736

  Email Adress: abuubaidasani5@gmail.com

  da

  Mansur Abdullahi

  Department of Hausa Studies

  College of Education, Ikere-Ekiti

  Phone No: 08034402746

  1.0 Gabatarwa

  Babban yun?urin aikin nan shi ne fito da bambanci da kuma kamanceceniya da ke tsakanin Wa?ar Lalura da kuma Tabban Ha?i?an. Aikin ya kawo ta?aitaccen tarihin marubucin wa?o?in na asali (Shehu Usmanu ?anfodiyo). Baya ga haka, aikin ya kawo ta?aitaccen tarihin Isa ?an Shehu da kuma Nana Asma’u a matsayin masu hannu wajen fassara wa?o?in daga Fillanci zuwa Hausa, tare kuma da yi musu tahamisi. Wato Shehu Usman a matsayin wanda ya wallafa wa?o?in biyu, Nana Asma’u ta fassara Tabban Ha?i?an sannan Isan Kware ya yi mata tahamisi. A ?aya ?angaren kuma, Isan Kware ne ya fassara wa?ar Lalura daga Fillanci zuwa Hausa, sannan ya yi mata Tahamisi. [1]

  Aikin ya shafi wa?a ne, sannan rubutacciyar wa?a ba wa?ar baka ba. Masana da dama sun ba da ma’anar wa?a kamar haka:

  Wa?a wani furuci ne (lafazi ko sa?o) cikin azanci da ake aiwatarwa ta hanyar rerawa da daidaitattun kalmomi cikin wani tsari ko ?a’ida da kuma yin amfani da dabaru ko salon armashi. (?angambo, a cikin Habibu, 2001).

  Ha?i?a wa?o?i suna taka muhimmiyar rawa wurin fa?akarwa tare da wa’azantarwa ga al’umma. Ba za a ta?a mantawa da gudummuwar rubutattun wa?o?i ba a lokacin jihadin jaddada addinin Musulunci ?ar?ashin jagoranci Shehu Usmanu ?anfodiyo (Yahya, 1987; Zurmi, 2006).

  1.2 Rubutacciyar wa?a

  Masana da dama sun kawo ma’anar rubutacciyar wa?a. Wasu masanan a rubuce-rubucensu suna bambancewa tsakanin wa?a, da rubutacciyar wa?a da kuma wa?ar baka. Wasu kuma suna kawo ma’anar wa?ar ne kawai a dun?ule ba tare da bambancewa ko rabewa ba. [2] Habibu, 2001 ya rawaito Yahya yana cewa:

  Rubutacciyar wa?a magana ce mai ?unshe da sa?o a rubuce, da ta shafi za?en kalmomi da tsara su cikin tsarin da ba lallai sai sun dace da maganar yau da kullun ba. Wannan tsari yana bu?atar karin sauti da amsa-amo. (Yahya a cikin Habibu, 2001)

  1.1.1 Ta?aitaccen tarihin rubutacciyar wa?a

  Masana da marubuta da dama sun kawo tarihin samuwar rubutattun wa?o?i a ayyukan rubuce-rubuce daban-daban da suka yi [3]. Sai dai wannan aikin zai kawo tarihin ne a ta?aice.

  Masana suna ?iyasi ne kawai na lokacin da aka fara samar da rubutattun wa?o?in Hausa. Babban linzamin wannan ?iyasi shi ne, kasancewar ba a fara samun rubutattun wa?o?in Hausa ba sai da Hausawa suka koyi karatu da rubutu. Wannan ya faru ne bayan sun kar?i addinin Musulunci. Wannan ne ya sa rubutattun wa?o?in farko suka fi mayar da hankali kan fa?akarwar addini da ilmantarwa da kuma wa’azantarwa, da ma sauran jigogi da suka shafi addinin Musulunci (Habibu, 2001).

  Duk da akwai masana da suke ganin cewa addinin Musulunci ya shigo ?asar Hausa tun kafin ?arni na goma sha hu?u, [4] ba a samu wata hujja da take nuna samuwar rubutattun wa?o?i a wancan lokaci ba. Hasali ma an samu ?ur?ushin rubutattun wa?o?in da suka fi da?ewa ne wa?anda aka yi a ?arni na goma sha bakwai. Wa?annan ?ur?ushin wa?o?i da aka ?iyasta samuwarsu za su iya kasancewa tun a ?arni na goma sha bakwai (17). Wa?o?in sun ha?a da, Shi’ir Hausa da Jamuya na wani malami mai suna Shekh Ahmad Tila. Sai dai ba a tantance ko wane ne malamin ba. Bayan wa?annan akwai wasu wa?o?i na Wali ?an Marina da kuma Wali ?an Masani, wa?anda aka tabbatar sun samu tun ?arni na goma sha bakwai (17) (Habibu, 2001).

  Daga ?arni na sha takwas zuwa na sha tara kuma, (musamman lokacin jihadi), marubuta da dama sun rubuta wa?o?i domin fa?akarwa da kuma kiran al’umma (Birnin-Tudu, 2002) [5].

  1.2 Tarihin mawallafan 'Tabban Ha?i?an' da wa?ar 'Lalura'

  Dalilin da aka ce ‘mawallafa’ ba ‘mawallafi’ ba shi ne kasancewar sa hannun wasu daban bayan asalin marubucin wa?o?in, ma’ana fassararta da kuma yi mata tahamisi. Aikin zai kawo tarihinsu a ta?aice domin ya zama tubalin ginin bayanai game da wa?o?in biyu.

  1.2.1 Shehu Usmanu ?anfodiyo

  Shehu Usmanu ?anfodiyo ya fito ne daga tsatson Fulani. Sun yo hijira zuwa ?asar Hausa ne daga Futa Toro. An haife shi a shekarar 1754 a Maratta ta ?asar Gobir. Sai dai ya tashi ne a ?egel a sakamakon hijirar da iyayensa suka yi daga Maratta zuwa ?egel. Sannan a ?egel ne ya fara koyarwa da kuma wa’azi, wanda hakan ne ya kai shi ga martabar da ya samu a rayuwa (Yahya, 1987).

  Shehu ya fara karatu ne a wurin babansa. Bayan nan kuma ya yi a wurin baffansa mai suna Shekh Jibril Umar. Bayan wani lokaci kuma sai shi da sahabbansa suka fara tafiya ?auyukan Gobir da Zamfara da kuma Kabi domin koyarwa da kuma kira zuwa ga Musulunci. Ya wallafa littattafai da dama sannan ya rubuta wa?o?i. Abubuwan da ba za a ta?a mantawa ba game da Shehu Usmanu ?anfodiyo, sun ha?a da ?imbin rubuce-rubucensa da kuma kasancewarsa jagoran jihadin ?aukaka addinin Musulunci (Yahya, 1987; Birnin-Tudu, 2002).

  Shehu Usmanu ?anfodiyo ya rasu a shekarar 1817, lokacin yana da shekaru sittin da uku a duniya. Ya rasu ne a Sakkwato shekaru biyu da komawrsa nan (Sakkwato) daga Sifawa (Yahya, 1987).

  1.2.2 Nana Asma’u

  Nana Asma’u ita ce ?iyar da ta fi sanuwa a cikin ‘ya’yan Shehu Usmanu ?anfodiyo. An haife ta a shekarar 1792 a ?egel, wato bayan dawowar Shehu daga Zamfara inda ya yi wa’azin tsawon shekaru biyar. Ta auri Usman Gi?a?o wanda aka fi sani da Waziri Gi?a?o. Nana Asma’u ta rubuta wa?o?i da dama, sannan ta fassara wasu zuwa harshen Hausa, wa?anda Shehu ?anfodiyo ya rubuta. ?aya daga cikin wa?o?in da ta fassara ita ce Wa?ar ‘Tabban Ha?i?an’ ta Shehu Usmanu ?anfodiyo. Daga cikin wa?o?in da ta rubuta akwai Kiran Amada da Gwadaben Gaskiya da wa?ansu daban-daban da ta rubuta cikin harshen Hausa da Fillanci (Yahya, 1987).

  Bayan rubutun wa?o?inta, ?aya daga cikin abubuwan da za a tuna Nana Asma’u da shi, shi ne kasancewarta jagorar ‘Yan Taru. Wato ?ungiyar fafutukar ilimantar da mata. wadda ta yi ?o?arin ha?a kan mata tare da ilmantar da su. Nana Asma’u ta rasu a shekarar 1817 (Yahya, 1987).

  1.2.3 Isa ?an Shehu

  An haifi Isa ?an Shehu a shekarar 1870, wato watanni ka?an bayan rasuwar mahaifinsa (Shehu Usmanu ?anfodiyo). Yarsa (Nana Asma’u) ita ce ta ri?e shi har zuwa girmansa. Wasu masana suna ganin cewa, wannan ne ya sanya masa sha’awar rubuta wa?a, saboda Nana Asma’u marubuciyar wa?a ce (Muhammad, 1986; Yahya, 1987).

  Isan Kware shi ne ?an auta a wurin Shehu. Ana masa la?abi da Isan Kware ne saboda na?a shi da aka yi Sarkin Yamman Kware. Wanda ya na?a shi, shi ne Sultan na wancan lokaci, wato Muhammadu Bello. Isah ya fassara wa?o?in Shehu da ma na Nana Asma’u da dama zuwa Hausa. Baya ga haka, ya yi tahamisin wa?o?i da dama, ?aya daga ciki ita ce ‘Tabban Ha?i?an’ ta Shehu ?anfodiyo (Yahya, 1987).

  Yahya (1987) ya ce, akwai kokonto game da ta?amaimai ranar rasuwarsa. Sai dai ya ce, ?angambo ya rawaito Junaidu yana cewa, Isan Kware ya rasu ne a shekarar zuwa 1970. Sai dai wasu masana sunan ganin bai kai wannan lokaci ba.

  1.3 Tsokaci kan 'Tabban Ha?i?an' da wa?ar 'Lalura'

  Wa?ar ‘Tabban Ha?i?an’ ce ta fara samuwa kafin ‘Wa?ar Lalura’. ?anfodiyo ya rubuta wa?ar ne da Fillanci. Bayan wani lokaci sai Nana Asma’u ta fassara ta zuwa harshen Hausa. Daga ?arshe kuma Isan Kware ya yi mata tahamisi. Wa?ar ta kasance mai tsauri sosai, kusan babu sassauci a cikinta ko ka?an. Za a iya lura da hakan yayin da aka dubi baitocin wa?ar, wato yadda suke tabbatar da shiga wuta ga masu aikata wasu zunubai (wa?anda aka zayyano a cikin wa?ar) ba tare da kawo uzuri ba (Birniwa, 2016). Ga misalin ?aya daga cikin irin wa?anan baitoci:

  Masu cin kura kasuwa duk akwai su,

  Wansu keri su kai su samo bukinsu,

  Wansu na nan ina fa?a ma kamassu,

  Masu cin dukiya ta baital wasunsu,

              Su wuta kan ci gobe tabban ha?i?an.

  A ?aya ?angaren kuma, ?anfodiyo ya rubuta ‘Wa?ar Lalura’ ne sakamakon koke da sahabbansa suka yi game da tsauri na wa?ar ‘Tabban Ha?i?an’. Saboda haka ne ?anfodiyo ya yi takwararta (Wa?ar Lalura). A ciki ya nuna cewa, akwai lalura game da duka hukuncin da ya shafi kowane laifi. Misali, a baitin sama da aka kawo, an yi nunin hukuncin wuta ga masu cin dukiyar da ba ta halarta ba gare su, kai tsaye ba tare da sassauci ba. Akwai takwaran wannan baiti a ‘Wa?ar lalura inda aka nuna akwai sassaucin hukunci idan dai akwai lalura. Ga misali daga cikin wa?ar:

  Ka jiya min abinga dut na fa?a ma,

  Kada ka bar ko guda karanta ka kama,

  Shaihu yac ce ri?e batun mai karama,

  Dukiyaj jangali da gado ku koma,

              Har ta ya?i wuta halam shi larura.

  1.4 Kamanceceniya tsakanin ‘Tabban Ha?i?an’ da wa?ar 'Lalura’

  Akwai kamanceceniya tsakanin ‘Tabban Ha?i?an’ da kuma ‘Wa?ar Lalura’. Wannan kamanceceniya ta shafi sigogin wa?o?in biyu, da zubi da tsarinsu da ma tarihin rubuta su. Saboda haka, za  a iya raba wa?annan kamaceceniya ta fuskoki kamar haka:

  1.4.1 Tarihin rubutun wa?o?in

  Ha?i?a idan aka bi tarihin wa?o?in biyu za a tarar cewa suna da tushe ?aya. Dalili kuwa shi ne, dukkaninsu biyu, marubucinsu shi ne Shehu Usmanu ?anfodiyo. An bayyana hakan a cikin baitocin wa?o?in biyu na kammalawa. Ga yanda abin yake:

  A wa?ar ‘Tabban Ha?i?an’ an ce:

  Shehu na yaf fa wa?i wa?a ta asali,

  Nana Hausance taf fa maishe ta badali,

  Isa tahmisi yay yi kau ya halili,

  Ya yi Hausance kun ji shi ko dalili,

              Wa’azu na don ku ji shi tabban ha?i?an.

  A takwararta ma an tabbatar da Shehu ne ya rubuta ta, misali:

  Shehu asalinta Isa na bi ma baya,

  Don fa lada ta samu har dud da shirya,

  Niy yi Hausance don darajjassu manya,

  Nan da can in gane shi in samu tariya,

              Don darajassu sun bi sunna larura.

   1.4.1.1 Fassara

  Fassarar da aka yi wa duka wa?o?in biyu shi ma yana mazaunin wata kamanceceniya a tsakaninsu. Dukkannin wa?o?in biyu, Shehu ya rubuta su ne da Fillanci, sai daga baya aka fassara su zuwa Hausa. A cikin wa?o?in akwai baitoci da ke tabbatar da fassara wa?o?in aka yi. Idan aka duba misalin da aka bayar a sama na ‘Tabban Ha?i?an’, za a ga inda aka kawo cewa Nana Asma’u ce ta fassara wa?ar. Misali:

  Nana Hausance taf fa maishe ta badali,”

  A ?aya ?angaren ma, Wa?ar Larura an rubuta ta ne da Fillanci, sai daga baya ne aka fassara ta zuwa Hausa. Misali:

  Na gama kuma zaton da niy yo na khairu,

  Shaihu Fillance yay yi to ka ji Baharu,

  Taulafina garai iyaka na daharu,

  She?ara lajju shekaran nan ta Huru,

              Cana Aljanna yo ?ida don larura.

  1.4.1.2 Tahamisi

  ‘Wa?ar Larura’ da ‘Tabban Ha?i?an’ duka an yi musu tahamisi. Kasancewar tahamisin da aka yi wa wa?o?in biyu na zaman wata kamanceceniya tsakanin wa?o?in biyu (Birniwa, 2016).

  1.4.2 Jigo

  Wa?o?in guda biyu sun kasance suna da jigon wa’azi. Akwai baitoci da dama da suke nuni da hakan a cikin wa?o?in guda biyu. Wasu daga cikin hani da aka kawo koyarwa ne daga Al?ur’ani mai tsarki, wasu kuma daga cikin hadisan Manzon Allah (S.A.W.). A cikin wa?ar Tabban Ha?i?an an fa?a ?arara cewa:

  Kun jiya wa’azu na da?a ‘yan uwana,

  An fa tasshe ku duk zumai dag ga kwana,

  Don ku kau tuba kun jiya muminina,

  Duk fa?in nan da anka yo gaskiya na,

              Sai fa rahama da ceto tabban ha?i?an.

  A ?aya ?angaren ma, ‘Wa?ar Lalura’ tana da jigon wa’azi ne. baitocin wa?ar da dama suna nuni da hakan. Misali:

  Ka jiya min abinga dut na fa?a ma,

  Kada ka bar ko guda karanta ka kama,

  Shaihu yac ce ri?e batun mai karama,

  Dukiya jangali da gado ku koma,

              Har ta ya?i wuta halam shi larura.

  1.4.3 Zubi da tsari

  Zubi da tsarin wa?o?in biyu ma na nuni da kamanceceniyar da ke tsakanin wa?o?in biyu. Sun yi kamance da juna a fuskar amsa amo babba da ?arami. Kowa ce wa?a tana da uwar goyon amsa amo wato kalma ?aya ce sukutum kowa ne baiti yake ?arewa da shi a matsayin amsa-amo, wato tabban hai?an da lalura. Kuma kowaccensu tana da ?aramin amsa-amo a kowane baiti. Wato kowane baiti yana da irin tasa ga?ar da yake ?arewa da ita. Baya ga wannan, ga bisa dukkan alamu kowacensu tana hawa karin Aruli na wa?o?in Larabci. Sannan kowace na da mabu?i da marufi da ?irgen lokacin wallafa na Ramzi da ambaton sunan mawallafi mai fassara da mai tahamisi. Sannan a karon farko suna da zubin tagwai. Bayan wani lokaci ne kuma aka yi musu tahamisi. Kenan a nan sun yi kamance ta ?angaren zubi da tsarinsu.

  1.4.2 Salo

  Salon wa?o?in biyu yana ?ara dan?on kamanceceniya da ke tsakaninsu. Hasali ma dai, zamani da yanayi da ma sauran abubuwan da suka shafi rayuwar marubuci na yin tasiri a cikin wa?arsa [6] (Muhammad, 1986). Wannan ya sa dole a samu kamanceceniya ta ?angaren salon wa?o?in biyu, domin kuwa duka mutum ?aya ne ya rubuta su.

  1.4.2.1 Salon wasa da kalma

  A duka wa?o?in guda biyu an yi wasa da kalma. Misali a wa?ar Tabban Ha?i?an ana cewa:

  Masu iko su mai da himma su kyauta,

  Kun jiya masu ji da?a kada ku ?ata,

  Ba ?a tsangini garin bi?owab bu?ata,

  Masu matsuwat talakka ko don sarauta,

              Su ka matsuwa ga gobe tabban ha?i?an.

  A sha?ara ta biyu an kawo jiya, sannan aka ce masu ji. Wannan wasa da kalma ne kamar yadda aka jero cikin ?ango ?aya. Sannan a ?ango na hu?u aka ce: “Masu matsuwat talakka ko don sarauta.” A nan matsuwa na nufin takurawa ko musgunawa. A ?angon ?arshe na baitin kuma sai aka ce: “Su ka matsuwa ga gobe tabban ha?i?an.´A nan kuma kalmar matsuwa tana nufin u?uba ta ranar gobe kiyama.

  A ‘Wa?ar Lalura’ ma akwai wurin da aka yi wasa da kalma. Misali:

  Dubi aikinka aikata yo ma Allah,

  Kowane kaj jiya da aikin jahala,

  An fa?i ka jiya bi addin ka lela.

  Maslaha an aje guda kankamala,

           Dai bu?ata guda tana kan larura.

  A ?angon farko an yi amfani da kalmar aiki sau biyu, inda aka ce; “Dubi aikinka aikata yo ma Allah.” A ?ango na uku ma an maimaita kalmar: “Kowane kaj jiya da aikin jahala. A wa?annan ?angogi aiki na nufin bautar Ubangiji Ma?aukaki.

  1.4.2.2 Salon aron kalma

  Akwai wuraren da aka yi aron kalma a cikin duka wa?o?in biyu. Misali a Tabban Ha?i?an ana cewa:

  Wanda duk ya zamo yana shina son salama

  Nan da can gobe sai shi bar yin zalama,

  Kwa? ?i foron ga dut shina yin nadama,

  Wanda yaz zam fa hakimi yay yi rahama,

              Shi ka tsira ga gobe tabban ha?i?an.

  Kalmar salama wadda ta fito a ?angon farko kalamr Larabci ce. Asalinta a Larabci shi ne salamatun, wanda ke nufin aminci ko tsira. Kalmar zalama kuwa asalinta a Larabci shi ne az-zulmu, wanda ke nufin zalunci. Asalin kalmar nadama kuwa a Larabci shi ne an-nadamu, wana ke nufin da-na-sani. Sannan kalmar rahama, asalinta a Larabci shi ne ar-rahma.

  A cikin ‘Wa?ar Lalura’ ma akwai baitoci da suke ?auke da aron kalmomi. Misali:

  Bari ?asak kufru kar ka zamna yi ?aura,

  Wanda bai tashi duk shina cim ma sharra,

  Don zaman nan cikinsa shi ag garura,

  Ba halat na ba fun musulmi shi barra,

              Sai zama dole na shikai kan larura.

  A nan, kalmar kufru ta samo asali ne daga Larabci wato al-kufrun. Kalmar na nufin duk wani wanda bai kar?i addinin Musulunci ba. kalamr sharra kamar yadda ta zo a ?ango na biyu ta samo asali ne daga kalmar Larabci ta sharrun. Kalmar tana nufin abin ?i ko a she sharri/sheri. Kalmar halat ma daga Larabci aka aro ta. Asalin kalmar ita ce al-halal, wanda ke nufin abin da aka amincewa. Kalamar musulmi ma an aro ta ne daga Larabci. Asalinta shi ne al-muslim, wanda ke nufin duk wani mabiyin addinin musulunci.

  Wa?annan misalai da ma wasu da dama da za a samu a cikin baitocin wa?o?in suna nuni ne zuwa ga dangantaka ko kamanceceniya da ke tsakanin wa?o?in guda biyu.

  1.5 Bambance-bambance tsakanin ‘Tabban Ha?i?an’ da wa?ar 'Lalura’

  Ha?i?a duk da cewa akwai ala?a ko kamanceceniya tsakanin ‘Wa?ar Lalura’ da ‘Tabban Ha?i?an’, akwai kuma wurare da suka bambanta da juna. Wa?annan bambance-bambance za a iya karkasa su kamar haka:

  1.5.1 Tarihi

  Tarihin rubuta wa?o?in ya samar da kamanceceniya tsakaninsu ta wasu ?angarori. A ?angare guda kuma, tarihin ya samar da bambanci a tsakaninsu. Kamar yadda aka fa?a a sama, duka wa?o?in an fassara su ne daga harshen Fillanci. Bambancin a nan shi ne na wa?anda suka yi fassarar. Nana Asma’u ce ta fassara ‘Tabban Ha?i?an’, yayin da Isan Kware kuma ya fassara ‘Wa?ar lalura’. Akwai baitocin wa?ar da suke tabbatar da hakan. Ga nan abin da aka fa?a a ‘Tabban Ha?i?an’:

  Shehu na yaf fa wa?i wa?a ta asali,

  Nana Hausance taf fa maishe ta badali,

  Isa tahmisi yay yi kau ya halili,

  Ya yi Hausance kun ji shi ko dalili,

              Wa’azu na don ku ji shi tabban ha?i?an.

  A wa?ar 'Lalura’ kuma cewa aka yi:

  Shehu asalinta Isa na bi ma baya,

  Don fa lada ta samu har dud da shirya,

  Niy yi Hausance don darajjassu manya,

  Nan da can in gane shi in samu tariya,

              Don darajassu sun bi sunna larura.

   1.5.2 Salo

  Duk da cewa wa?o?in guda biyu suna da jigo guda, akwai bambanci tsakanin yadda aka isar da sa?onnin da ke cikin wa?o?in. ‘Tabban Ha?i?an’ dai ta kasance mai tsauri sosai. An lissafo laifuka sannan aka tabbatar da cewa mai irin wa?annan ayyuka wuta zai shiga. A ?aya ?angaren kuma, ‘Wa?ar Lalura’ tana da rangwame. Laifuka da dama da aka yi maganarsu, tare da nuna hukuncinsu a matsayin wuta, an nuna a cikin ‘Wa?ar Lalura’ cewa, wani dalili zai iya kawo rangwame a hukunci. Misali a ‘Tabban Ha?i?an’ ana cewa:

  Wansu ko sun bi sun tsaya inda haddi,

  Wadda Allahu yay yi sun yo jahadi,

  Wansu ba su bi su sun ?iya sun bi liddi,

  Masu yawon gari suna yin fasadi,

              Su ka yawon wuta fa tabban ha?i?an.

  A cikin ‘Wa?ar Lalura’ akwai takwaran wannan baiti. Sannan ya zo ne da nuni da cewa, akwai rangwame saboda lalura. Ga nan yadda baitin yake:

  Anniya kan ta nan akan aikatawa,

  Kowane za ka yi ka bar da?ilewa,

  Bari fululu da munkari jimre kewa,

  Maslaha aikata ?i banna da kowa,

              Tsari ibada ka san ta shi al larura.

  A wani baitin kuma na daban a cikin ‘Tabban Ha?i?an’, an tabbatar da wuta ga mai mulki ko babba da yake danne na ?asa da shi:

  In da?a ka zamo imamun mutane,

  To tsare alhakinsu balle ubanne,

  Ka ji kyauta da?a fa don kar ka ?one,

  Wanda yaz zam imamu don cin mutane,

              Shi wuta kan ci gobe tabban ha?i?an.

  A ‘Wa?ar Lalura’ akwai takwaran wannan baiti. A ciki ya zo da sassaucin zance. Ga baitin kamar haka:

  Wanda yab bi ka duk bar sa shi kuka,

  Masu iko kuna jiyawa ku falka,

  Kun ji Allah abin da yac ce ku ?auka,

  Bari  walakanta wajibi kway yi suka,

              Ha wuta Walla ha wuta sai larura.

  Ha?i?a a wa?annan misalai da ma wasu da dama da za a gani a cikin wa?o?in, ‘Wa?ar Lalura’ tana da sassaucin hukunci.

  Kammalawa

  Aikin ya kawo ma’anar wa?a da ma’anar rubutacciyar wa?a, sannan ta?aitaccen tarihin samuwar rubutacciyar wa?a. Baya ga haka aikin ya kawo tarihin mutane uku – a ta?aice – da ke da hannu cikin rubutun wa?o?in biyu. Daga nan sai aikin ya yi ta?aitaccen tsokaci kan wa?o?in guda biyu. Ha?i?a ‘Tabban Ha?i?an’ da ‘Wa?ar Lalura’ tamkar tagwaye suke. Baituka da dama daga cikin Tabban Ha?i?an na da takwara a cikin Wa?ar Lalura. Baya ga haka, jigon wa?o?in wa’azantarwa ne. A ?aya ?angaren kuma, akwai bambanci a tsakanin wa?o?in kamar ta wurin sassaucin da ke cikin ‘Wa?ar Lalura’ koma bayan ‘Tabban Ha?i?an’ da ke da tsauri sosai.

  Shawarwari

  1. Ya kamata ?alibai da sauran al’umma su tuna cewa, rubutattun wa?o?i suna ?auke da ?imbin darrussa, ba nisha?i kawai ba. A ri?a nazartar wa?o?i tare da gane sa?onnin cikinsu.
  2. Malaman wa?a su ?ara ?aimi wajen fayyace falsafar da ke cikin wa?a ga ?alibai tare da danganta sa?onnin wa?ar da rayuwar yau-da-kullum.
  3. Masana wa?a su ?ara ?aimi wajen nuna wa marubuta wa?a irin tasirin da wa?o?i suke da shi a cikin zukatan al’umma. Marubutan su ri?a karkata jigogin wa?o?insu zuwa ga abubuwan da za su kawo cigaban al’umma ba koma-baya ba.

  Manazarta

  Birnin-Tudu, S. Y. (2002). “Jigo da Salon Rubutattun Wa?o?in Fura’u na ?arni na Ashirin.” Kundin babban digiri na uku (Ph. D.) wanda aka gabatar a Sashen Harrunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu ?anfodiyo, Sakkwato.

  Birniwa, A. H. (2016). “ALH 302 (Varieties of Hausa Poetry) “ Darasin da aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu ?anfodiyo Sakkwato.

  Bunza, A. M. (1988). “Nason Kirari Cikin Rubutattun Wa?o?in Hausa na ?arni na 20.” Ma?alar da aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

  ?angambo, A. (1980). “Hausa Wa’azi Verse Fron CA 1800 to CA 1970: A Critical Study of Form, Content, Language and Style. A Ph. D. thesis submitted to the University of SOAS, London.

  Garba, B. (2011). “Tasirin Wa?ar Baka a Kan Rubutattun Wa?o?in Islamiya a Garin Sakkwato.” Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu ?anfodiyo Sakkwato.

  Gusau, S. M. (1993). Jagorar Nazarin Wa?ar Baka. Kaduna:  Fisbas Media Service.

  Habibu, L. (2001). “Bun?asar Rubutattun Wa?o?in Hausa a ?arni na Ashirin (20).” Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu ?anfodiyo Sakkwato.

  Muhammad, A. S. (1986). “Bambancin Wa?o?in Infiraji na Dakta Aliyu Namangi da Wa?o?in Isan Kware Autan Shehu Usmanu ?anfodiyo Wajen Salo da Zubi da Tsari. Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu ?anfodiyo Sakkwato.

  ?aura, H. I. (1994). “?awancen Salo a Tsakanin Rubutattun Wa?o?in Wa’azi da Madahu da Kuma Siyasa.” Kundin kammala digiri na biyu (M.A.) wanda a aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu ?anfodiyo, Sakkwato.

  Umar, G. (1986). “Mamman Yaro Hore da Wa?o?insa.” Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu ?anfodiyo Sakkwato.

  Yahya, A. B. (1987). “The Verse Category of Madahu With Special Reference To Theme, Style and the Background of Islamic Soures and Beliefs.” A Ph. D. thesis submitted to the Department of Nigerian Languages, Usmanu ?anfodiyo University, Sokoto.

  Yahya, A. B. (1996). Jigon Nazarin Wa?a. Kaduna: Fisbas Media Service.

  Zurmi, A. D. (2006). “Tsoratarwa a Cikin Wa?o?in Wa’azi na Nana Asma’u.” Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu ?anfodiyo Sakkwato.

  Footnotes

  [1] Sai dai akwai wa?anda suke kallon cewa, Abdullahi Mai Bo?inga shi ne ya yi wa Wa?ar Lalura tahamisi, ba Isan Kware ba (Birniwa, 2016). Sai dai ko ma yaya abin yake, ya tabbata cewa an fassara wa?ar ne daga Fillanci zuwa Hausa sannan daga baya aka mata tahamisi.

  [2] Masana da marubuta wa?anda suka yi tsokaci kan ma’anar wa?a sun ha?a da: Gusau, 1993; ?aura, 1994; Yahya, 1996; Bunza, 1988; Habibu, 2001; Zurmi, 2006.

  [3] Daga cikinsu wa?anda suka kawo tarihin samuwar rubutacciyar wa?a akwai Habibu, 2001, da kuma musamman Birnin-Tudu, 2002 inda ya yi ?o?arin tattaro bayanai sosai game da tarihin samuwa da bun?asar rubutacciyar wa?a.

  [4] Wasu na ganin cewa addinin Musulunci ya shigo ?asar Hausa tun ?arni na goma sha biyu. Wasu ma sun ce tun ?arni na bakwai (Habibu, 2001). Amma akwai tabbacin Musulunci ya shigo ?asar Hausa tun zamanin sarkin Kano Ali Yaji. Wato shekarar 1349 zuwa 1385 (Birnin-Tudu, 2002).

  [5] Bayan an yi nasarar jihadi, Musulunci ya yi ?arfi, rubutattun wa?o?i sun ci gaba da bun?asa har aka shiga ?arni na ashirin. Bayan nan ne kuma jigogin wa?o?in suka bun?asa, suka wuce iya na addini kawai, suka shafi na duniyaci (Birnin-Tudu, 2002).

  [6] Saboda haka ne ma ake iya hasashen yanayin mawa?i da yadda rayuwarsa take ta hanyar nazartar wa?o?insa kawai. Sannan wannan na ?aya daga cikin abubuwan da suka bambanta wa?o?i daga ?arni zuwa ?arni. Dalili kuwa shi ne, kowane ?arni na zuwa da abin da ke jan hankalin marubuta wa?o?in, sannan yana tasiri kan tunaninsu.

No Stickers to Show

X

Da Dumi-Dumin Su

 • Ku latsa nan don karanta labarin Saurin Fushi Na Kawo Da Na Sani. A wani Æ™auye akwai wani mutum  ana kiran sa Abu Sabiru, ya kasance mai tsananin haÆ™uri da kawar da kai akan wasu al’amura. Dalilin da ya sa ma ake kiransa Abu Sabiru kenan. Yana zaune tare da matarsa kyakkyawar gaske ...
 • Ku latsa nan don karanta darasin rana ta uku. DARASI NA 1 Matakan rubutun gajeren labari A jiya mun yi bayani akan matakan da ake bi wajen tsara labari, yau kuma za mu bayani a takaice kan matakan da ake bi wajen rubuta ingantaccen labari. WaÉ—annan matakai ba tabbatattu ba ne, ma'ana ba wajibi ne...
 • Ku latsa nan don karanta babi na shida. Habeeb na kwance a kan doguwar kujera ya ji an murÉ—a handle É—in É—akinshi tare da turo Æ™ofar a hankali. A hankali ya buÉ—e idanunsa da suka yi nauyi sakamakon ciwon kan da yake fama da shi. "Fateemah" ya faÉ—a a ransa, lokacin da ya kai duba ga Jummai da ke ts...
 • Uwargida ba za ki yi dana sanin koyan yadda ake yoghurt in fruits ba. Domin kuwa kayan dadi ne sosai da sosai kuma cikin mituna kalilan za ki hada. Ba a ba yaro mai kiwiya!!! Wannan recipe yana daya daga cikin recipes da muka koyar a zauren Free Ramadhan Classes with Umyuman a nan Bakandamiya. Abu...
 • Hadin special salad nawa na musamman ne! Ga sauki ga dadi, uwargida sai kin gwada za ki bani labari! Wannan ma yana daya daga cikin recipes da muka koyar a Ramadan a shirin girke-girkenmu wadda aka gabatar a zauren Free Ramadhan Classes with Umyuman. Shin ko kin tuna gashin tsokar kaza da muka koya...
 • Red velvet cake, cake ne da mutane da dama suke so kuma kuma suke son ci. Saboda haka, akwai hanyoyi daban-daban na yin red velvet cake, ga yadda na ke nawa cake din na kawo muku. Wannan yana daya daga cikin recipes da muka koyar lokacin Ramadan anan Bakandimya. Domin ganin duk jerin recipes din da...
View All