Makalu

Hukunce-hukuncen zakkar fidda kai

 • Ma'anar zakkar fidda kai:

  Sadaka ce wacce ake bayar da ita sakamakon kammala azumin watan Ramadan.

  An shar'anta zakkar ne a shekara ta biyu bayan hijirar Annabi sallallahu alaihi wa sallam daga Makkah zuwa Madinah, a shekarar da aka wajabta azumin watan Ramadan.

  Hukuncin zakkar fidda kai:

  Fitar da zakkar fidda kai wajibi ne ga dukkan musulmi, namiji da mace, babba da yaro, 'da ko bawa.

  An karbo daga Abdullahi Bin Umar (Allah Ya yarda da shi) ya ce:

  «فرض رسول الله صلى الله عليه وسلم زكاة الفطر صاعًا من تمر، أو صاعًا من شعير على العبد والحر، والذكر والأنثى، والصغير والكبير من المسلمين، وأمر بها أن تؤدى قبل خروج الناس إلى الصلاة».

  Ma'ana: "Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya wajabta zakkar fidda kai, sa'i daya na dabino, ko sa'i daya na sha'ir, akan bawa da da, namiji da mace, da kuma  babba da yaro daga cikin musulmai. Kuma ya yi umurni da a bayar da zakkar kafin mutane su fito zuwa sallar idi". Buhari da Muslim ne suka rawaito hadisin.

  Hikimar wajabta zakkar fidda kai:

  An wajabta zakkar fiddai kai saboda wasu hikimomi kamar haka:

  1. Tsarkake mai azumi daga yasasshen zance da kuma batsa.
  2. Saboda ciyar da miskinai da talakawa abinci a ranar Sallah, don kar su fita rokon mutane abinci a ranar sallah.
  3. Don godiya ga Allah Madaukakin sarki saboda kamala azumin Ramadan.

  An karbo daga Abdullahi Bin Abbas (Allah Ya yarda da shi) ya ce:

  "فرض رسول الله - صلى الله عليه وسلم - زكاة الفطر طهرة للصائم من اللغو والرفث، وطعمة للمساكين".

  Ma'ana: "Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya farlanta zakkar fidda kai don ta zama tsarkaka ga mai azumi daga yasasshen zance da batsa, kuma abinci ne ga miskinai". Abu Dawud da Ibn Majah ne suka rawaito shi.

  Malamai sun hadu kan cewa zakkar fidda kai wajibi ne. Ibnul Munzir yace: "Kuma sun yi ijma'i akan zakkar fidda kai farilla ne".

  Mai karatu na iya duba wannan makala da ta yi bayani akan falalar azumin watan Ramadan

  Wadanda zakkar fidda kai ke wajaba akan su:

  Zakkar fidda kai yana wajaba ne akan dukkan musulmi, namiji ko mace, babba ko yaro, da ko bawa. Saboda Hadisin Ibn Umar wanda ya gabata.

  Magidanci zai fitar da na shi da na matan sa da 'ya'yan shi da duk wanda suke karkashin sa.

  Mustahabbi ne fitarwa jaririn da ke ciki, saboda an rawaito Sayyidina Usman (Allah Ya yarda da shi) ya kasance yana fitarwa jariri.

  Sharuddan wajabcin zakkar fidda kai:

  Zakkar fidda kai tana wajaba ne da sharudda guda biyu:

  1. Zakkar tana wajaba ne akan musulmi, bata wajaba akan kafuri. Allah Y ace:

  «وما منعهم أن تقبل منهم نفقاتهم إلا أنهم كفروا بالله وبرسوله»

  Ma'ana: "Kuma babu abin da ya hana a karbi ciyarwarsu daga gare su face domin su, sun kafirta da Allah da Manzon sa". Suratut Tauba, aya ta 54

  Haka nan Hadisin Ibn Umar (Allah Ya yarda da shi) wanda ya gabata, ya nuna cewa zakkar na wajaba ne akan musulmi kadai.

  2. Tana wajaba ne akan wanda yake da abinda zai ci a ranar sallah da daren wannan ranar, kuma ya samu rara akan hakan.

  Lokacin da ake bayar da zakkar fidda kai:

  Zakkar fidda kai tana wajaba ne da zaran rana ta fadi a ranar karshe na watan Ramadan. Duk wanda ya mutu kafin faduwar rana, to bata wajaba akan sa ba.

  Duk wanda aka haifa kafin faduwar rana, ko ya musulunta kafin faduwar ta, to zakkar fidda kai ta wajaba akan sa.

  Lokacin da ya fi shine fitar da ita ranar idi, daga fitowar alfijir zuwa kafin a tafi masallacin idi. Saboda ya zo a hadisin Ibn Umar (Allah Ya yarda da shi), ya ce:

  «وأمر بها أن تؤدى قبل خروج الناس إلى الصلاة».

  Ma'ana: "Kuma (Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya yi umurnin a fitar da ita kafin mutane su tafi wurin sallar idi". Bukari da Muslim ne suka rawaito hadisin.

  Baya halatta a jinkirta fitar da zakkar zuwa bayan sallar idi. Duk wanda ya jinkirta ta zuwa bayan salar idi, to zai sa ta zama sadaka, kamar yadda ya zo a Hadisin Ibn Abbas (Allah Ya yarda da shi), ya ce:

  "فمن أداها قبل الصلاة، فهي زكاة مقبولة، ومن أداها بعد الصلاة، فهي صدقة من الصدقات".

  Ma'ana: "Duk wanda ya bayar da ita kafin sallar idi, to wannan zakkah ce karbabbiya. Wanda kuma ya bayar da ita bayan sallah, to sadaka ce daga cikin sadakoki".

  Ya halatta a fitar da zakkar fidda kai kwana daya ko kwana biyu kafin ranar sallah. Saboda Sahabbai sun kasance suna yin haka kamar yadda ibn Umar (Allag Ya yarda da shi) ya ce:

  «وكانوا –أي الصحابة- يعطون قبل الفطر بيوم أو يومين»

  Ma'ana: "Kuma (Sahabbai) sun kasance suna bada ita kafin sallah da kwana daya ko biyu". Buhari ne ya rawaito shi.

  Kuna iya duba makamancin wannan makala da ya yi sharhi akan hukunce-hukuncen shiga ittikafi.

  Wani nau'in abinci ne ake bayarwa?

  Ana bayar da irin nau'in abincin da mafi rinjayen mutanen gari suke ci, kamar dabino ko alkama ko zabib ko shinkafa ko masara ko gero ko dawa, da sauransu.

  An karbo daga Abu Sa'id Al-Khudri (Allah Ya yarda da shi) yace:

  «كنا نخرج زكاة الفطر صاعًا من طعام، أو صاعًا من شعير، أو صاعًا من تمر، أو صاعًا من أقط، أو صاعًا من زبيب».

  Ma'ana: "Mun kasance muna fitar da zakkar fidda kai sa'i daya na abinci, ko sa'i daya na sha'ir, ko sa'i daya na dabino, ko sa'i daya na cukui (shine nonon da ya bushe; ana girki da shi), ko sa'i daya na zabib". Buhari da Muslim ne suka rawaito wannan hadisi.

  Gwargwadon abinda ake fitarwa:

  Ana fitar da sa'i daya na abinci, wanda shine mudun Annabi sallallahu alaihi wa sallam. Sa'i yana daidai da cikin tafuka biyu sau hudu na matsaikacin mutum, ko kuma kusan nauyin kilogiram uku.

  Wadanda ake baiwa zakkar fidda kai:

  Ana bada zakkar ne ga miskinai da fakirai. Saboda hadisin Ibn Abbas (Allah Ya yarda da shi) wanda yake cewa:

  "فرض رسول الله - صلى الله عليه وسلم - زكاة الفطر طهرة للصائم من اللغو والرفث، وطعمة للمساكين".

  Ma'ana: "Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya farlanta zakkar fidda kai don ta zama tsarkaka ga mai azumi daga yasasshen zance da batsa, kuma abinci ne ga miskinai". Abu Dawud da Ibn Majah ne suka rawaito shi.

  Sa'an nan ya halatta a bayar da zakkar ga mabukaci guda daya, ko a rarraba ta ga sama da mutum daya. Amma abinda ya fi shine a bada ita ga dangi na kusa wadanda ciyar da su bai wajaba akan mai zakkar ba.

  Shin ya halatta a bada kudi madadin abinci?

  Malamai sun yi sabani kan hukuncin bada kudi a madadin abinci.

  Akwai malaman da suka tafi akan ba laifi in an bayar da kudi ko kima idan akwai bukatar haka.

  Amma magana mafi rinjaye ta malamai itace: ba ya halatta a bada kima ko kudi. Ibn 'Kudamah yace: "Bada kima (a zakkar fidda kai) ba zai wadatar ba, saboda karkata ne daga ya zo a nassi (hadisi)".

  Mai karatu na iya duba wata makalar da ta yi karin bayani akan zakkar ta fidda kai. Allah ne Masani.

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Yadda ake hada KFC chicken

  Posted Thu at 10:11 AM

  Assalamu Alaikum, barka da sake saduwa a cikin shirin girke-girken Bakandamiya tare da ni mai gabatar muku da shirin. A yau in sha Allah zan nuna mana yadda ake hada KFC chicken. Abubuwan hadawa Kaza Flour Man gyada Bread crumbs ko cornflakes Kwai Maggi ...

 • Yadda ake hada egg masala

  Posted Thu at 9:57 AM

  Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa a cikin shirin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau na zo mana da yadda za a hada egg masala a saukake. Abubuwan hadawa Dankalin turawa Albasa Carrots Maggi Mangyada Kwai Yadda ake hadawa Farko za ki wanke dankal...

 • Jini Baya Maganin Kishirwa: Babi na Uku

  Posted Jan 12

  Ku latsa nan don karanta babi na biyu. Sakinah ta share hawayen da ke zuba kan kuncinta kafin ta ce. "Insha Allahu Umma zan yi aiki da dukkan abin da ki ka umarce ni da shi da yardar Allah, ba zan taɓa baki kunya ba". "Yauwa Sakinah Allah ya yi miki albarka". "Amin"...

 • Yadda ake baked awara

  Posted Jan 11

  Barka da sake saduwa a cikin shirin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau na zo maku da sabon girki wato yadda za ku hada baked awara. Abubuwan hadawa Awara Kwai Carrots Seasoning Cooked minced meat Muffin tray Albasa Yadda ake hadawa Farko za ki yanka a...

 • Bayanan masana game da ingantattun hanyoyin ƙayyade iyali

  Posted Jan 8

  Mene ne ƙayyade iyali? Ƙayyade iyali ko tazarar iyali ko kuma family planning a Turance wani mataki ne da ma'aurata kan dauka don hana mace daukan ciki domin rage yawan haihuwa akai-akai, ko ƙayyade yawan ‘ya’ya da za ta haifa ko dai ma don wasu dalilai na ...

 • Ma'aurata: Babi na Biyu

  Posted Jan 8

  Idan baku karanta babi na daya ba to ku latsa nan don karantawa. Ana kiran sallah asuba ta farka daga bacci addu'an tashi daga bacci tayi kafin tayi miƙa tana salati ga Annabi S.A.W kai dubanta tayi a gefen da Fahad yake kwance tayi, har yanzu yana nan yana bacci kamar...

View All