Makalu

Blogs » Addini da Tarbiyya » Muhimman bayanai daga cikin falalar watan Ramadan

Muhimman bayanai daga cikin falalar watan Ramadan

 • Bismillahi rahmanir Rahim

  Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Mai girma da daukaka. Salati da sallama su kara tabbata ga Manzon Allah, da iyalansa da sahabansa baki daya.

  Allah Madaukakin Sarkin Ya yiwa bayinsa ni'imomi masu yawa wadanda basu kirguwa, ni'imomin basu gushe ba suna kwarara ga bayin Allah a kowani lokaci. Haka nan Allah bai gushe ba yana kwarara nau'uka daban-daban na alkhairai kuma ya baiwa bayinsa damar yin ayyukan aikhairi, ta yadda zai tsarkake su daga zunubai. Muna godiya ga Allah kan wadannan ni'imoni da ya mana.

  Lalle ne daga cikin ni'imomin da Allah Ya yiwa bayinsa, Ya sanya musu lokaci mai tarin falala don yin ibada, ayyukan alheri sukan yawaita a cikin sa, ana kankare zunubai, ana ninnika lada, rahamar Allah tana sauka a cikinsa, ana girmama sadaka da kyauta a cikin sa. Daga cikin mafi daraja da falala da albarka shi ne lokacin watan Ramadan mai albarka, wanda Allah yace: "Watan Ramadan ne wanda aka saukar da Al-Kur'ani a cikinsa, yana shiriya ne ga mutane da hujjoji bayyanannu daga shiriya da rarrabewa (tsakanin karya da gaskiya)". Suratul Bakarah, aya ta 185.

  Watan alkhairi, watan rahama da yafiya da yantarwa daga wuta, watan kyauta da karamci da alheri da kyautatawa.

  Ku duba wannan makala da ta yi bayani akan abubuwan da Musulmi ya kamata ya yi don shigowar watan Ramadan.

  Hakika Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya kasance yana yiwa sahabbansa albishir da zuwan wannan wata mai girma da daraja, kuma yana kwadaitar da su akan dagewa da ayyuka kyawawa na farillai da nafilfilu, kamar sallah, da sadaka, da kyautatawa, da hakuri akan yiwa Allah biyayya, da shagaltuwa da azumi a wuninsa, da sallolin nafila a darensa, da kuma shagala a lokatansa masu albarka da zikiri da tasbihi da hailala da karatun Al-Kur'ani da sauran ayyukan alheri.

  An karbo daga Anas Bin Malik (Allah ya yarda da shi) yace:  Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: "Wannan watan Ramadan ne, hakika ya zo muku, ana bude kofofin Aljanna, kuma ana kulle kofofin wuta, kuma ana daure shaidanu". Haka nan Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) a wani hadisin ya ce: "Ramadan wata mai albarka, ana bude kofofin aljanna, kuma ana rufe kofofin sa'ir (wuta), kuma ana daure shaidanu. Kuma wani mai shela (Mala'ika) zai yi shela: Ya kai mai son alheri, kusanto, ya kai mai son sharri, ka kame".

  Haka nan kuma Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: "Duk wanda ya azumci watan Ramadan yana mai imani da neman lada, to an gafarta masa abinda ya gabata na zunubansa". Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi. Kuma ya ce: "Duk wanda yayi tsayuwar Ramadan (Sallah Tsarawihi) yana mai imani da neman lada, to an gafarta masa abinda ya gabata na zunubansa". Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi. Haka kuma yace: "Duk wanda yayi tsayuwar dare lailatul kadiri, yana mai imani da neman lada, to an gafarta masa abinda ya gabata na zunubansa". Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.

  Hakika Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya siffanta watan Ramadan da cewa watan albarka, kuma haka yake gaskiya watan albarkan ne, duk lokutan watan masu albarka ne, ayyukan da ake yi a cikin watan masu albarka ne, ladan da ake samu mai albarka ne, kuma gashi a cikin watan akwai daren lailatul kadiri wanda ya fi daren watanni dubu (1,000). Daga cikin albarkar watan; ana ninninka ladan ayyuka, ana bude kofofin gidan aljanna, ana kulle kofofin wuta, kuma ana daure shedanu da kuma kangararru daga cikin aljanu, kuma Allah yana yawaita yanta bayi daga wuta a cikin watan.

  Ya kai dau uwa mai albarka! Lalle yana daga mafi girman asara da tabewa, mutum ya riski watan Ramadan mai albarka, kuma bai samu aka gafarta masa zunubansa ba, kuma bai samu aka shafe masa kura-kuransa ba, saboda sakacin sa da kuma rashin komawa ga Allah da tuba zuwa gare shi.

  An rawaito daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), ya ce: Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: "Jibril (A.S) ya zo mini, ya ce: Ya Muhammad! Wanda duk ya riski daya daga cikin mahaifansa, ya mutu ya shiga wuta, Allah Ya la'ance shi. Ka ce: Amin, sai na ce: Amin. Yace: Ya Muhammad! Duk wanda ya riski watan Ramadan kuma ya mutu ba'a gafarta masa ba, ya shiga wuta, Allah Ya la'ance shi. Ka ce: Amin, sai na ce: Amin. Yace: wanda aka ambace ka a wurin sa kuma bai maka salati ba, sai ya mutu ya shiga wuta, Allah Ya la'ance shi. Ka ce: Amin, sai na ce: Amin". Imam At-Tabarani ne ya rawaito shi.

  Haka kuma Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya siffanta wannan wata mai albarka da cewa watan hakuri. An karbo daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) ya ce: "Azumin watan hakuri, da azumin kwana uku a kowani wata, azumin shekara". Imam Ahmad ne ya raawaito shi.

  Hakuri kashi uku ne: Hakuri akan yiwa Allah biyayya, hakuri akan barin abinda Allah ya haramta, da kuma hakuri akan kaddarar Allah da take samun bawa. Dukkan su suna haduwa a azumi. Saboda akwai hakurin akan yiwa Allah biyayya, da kuma hakuri akan barin sabawa Allah, da kuma hakuri akan kaddarar Allah wacce take samun mai azumi na yunwa da kishin ruwa da sauransu. Kuma hakurin da mai azumi yake yi ibada ne, zai samu lada mai yawa a wurin Allah Madaukakin Sarki, saboda Allah zai bashi lada ba tare da ya kirga ba. Allah Ya ce: "Masu hakuri kawai Allah yake cika wa ladan su ba tare da wani lissafi ba". Suratuz Zumar, aya ta 10.

  Ga wani karin bayani na kadan daga cikin falalar watan Ramadan.

  Lalle watan Ramadan wata ne da ake samun riba mai yawa. Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya kasance yana dagewa da yin ayyukan ibada fiye da wanin wannan watan, ya kan kebe kansa don yawaita ayyukan ibada. Kuma ya kan koma masallaci a kwanaki goman karshe na Ramadan don yin itikafi. An karbo daga Nana Aisha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: "Lalle Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya kasance yana yin itikafin kwanaki goman karshe na Ramadan, har Allah ya karbi rayuwarsa. Sa'an nan matansa sukan yi itikafi bayansa". Buhari da Muslim ne suka rawaito shi.

  Kuna iya duba hukunce-hukunce da suka shafi ittikafi.

  Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya sa kasance mai yawan kyauta. Kuma ya fi yin kyauta a watan Ramadan. An karbo daga Ibn Abbas (R.A), yace: Manzon Allah ya kasance ya fi kowa kyauta, kuma kyautarsa ta fi yawaita a watan Ramadan; lokacin da mala'ika Jibrilu yake haduwa da shi, kuma Jibrilu ya kan hadu da shi a cikin kowani dare, sai yayi bitar Al-Kur'ani tare da shi. Lalle Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya fi iska mai kadawa yin alheri". Buhari da Muslim ne suka rawaito shi.

  Haka nan magabata na kwarai sun kasance suna baiwa watan Ramadan kulawa ta musamman, domin suna dakatar da komai, su shagala da ayyukan ibada, da yawan nafilfilun dare. Imam Az-Zuhri (Allah Ya masa rahama) yace: "Idan Ramadan ya shigo, to abinda na sani kawai shine karatun al-kur'ani da ciyar da abinci". Haka halin magabata yake a cikin watan Ramadan; a wurin su wata ne na azumi da nafilfilu  da karatun Al-Kur'ani da zikiri da kyautatawa bayin Allah da kuma ciyar da abinci.

  Wajibi ne mu fiskanci wannan wata mai albarka ta hanyar tuba ga Allah madaukakin sarki, da kuma yin farin cikin da shigowar watan, da kuma dagewa da shagaltuwa da yiwa Allah biyayya da neman kusanci zuwa gare shi ta hanyar kyawawan ayyuka, da kuma yawan ambaton Allah, da kuma nesantar ayyukan da Allah ya haramta, kamar zalunci da karya da yaudara da gulma da rada da zagi da cin mutumcin mutane da sauran abubawan da Allah ya haramta. Hadisi ya tabbata daga Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: "Duk wanda bai bar zancen karya ba, da aiki da shi ba, to Allah baya da bukatar ya barin cinsa da shansa".

  Daga karshe, muna rokon Allah madaukakin sarki Ya karba mana azumin mu da sallalinmu da sauran ayyukan mu, Ya sa muna cin yantattu a wannan wata mai albarka, Ya bamu albarkar dake cikin watan.

  Wa sallallahu ala nabiyyina Muhammad, wa ala alihi wa sahbihi wa sallam.

Comments

1 comment