Rubutu

Blogs » Addini da Tarbiyya » Hukunce-hukuncen shan azumi da biyan sa

Hukunce-hukuncen shan azumi da biyan sa

 • Bismillahi rahmanir Rahim

  Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Mai girma da daukaka. Salati da sallama su kara tabbata ga Manzon Allah, da iyalansa da sahabansa baki daya.

  Mutane sun kasu kashi uku game da wajabtuwar azumi:

  Kashi na farko: Marasa uzuri (masu lafiya, mazauna gida), ya wajaba su yi azumi a cikin watan Ramadan. Bai halatta su jinkirta shi ba.

  Allah Ya ce: "To duk wanda ya halarta daga gare ku a watan, sai ya azumce shi, kuma wanda ya kasance majinyaci ko kuwa kan tafiya, sai ya biya adadi daga wasu kwanuka na dabam". Suratul Bakara, aya ta 185.

  Kashi na biyu: Masu uzuri (mara lafiya, da matafiyi, da mai ciki, da mai shayarwa, da mace mai haila ko jinin biki, da sauransu), wadannan ya halatta su sha azumi, sannan su biyan bayan sallah, idan uzurin ya gushe.

  Allah Yace: "Kuma wanda ya kasance majinyaci ko kuwa kan tafiya, sai ya biya adadi daga wasu kwanuka na dabam". Suratul Bakara, aya ta 185.

  Kashi na uku: Wadanda ba zasu iya yin azumi ba, kuma ba zasu iya biya ba, sune kamar tsoho futuk da kuma mara lafiyan da ba'a tsammanin warkewar sa. Wadannan Allah ya musu rangwame, sai ya wajabta musu ciyar da miskini maimakon yin azumi, zasu ciyar da sa'i ga kowani wunin azumi.

  Allah Ya ce: "Kuma a kan wadanda suke yin sa da wahala akwai fansa; ciyar da matalauci". Suratul Bakara, aya ta 184. Abdullahi Bin Abbas (R.A.) ya ce: "(Ayar tana Magana ne) a kan tsoho da tsohuwa wadanda ba zasu iya yin azumi ba, zasu ciyar ga kowani wuni miskini guda daya". Bukhari ne ya rawaito shi.

  Haka nan mara lafiya wanda ba'a tsammanin warkewar sa, zai dauki hukuncin tsoho, zai ciyar da miskini a kowace rana daga ranakun azumi.

  Amma wanda ya sha azumi saboda wani uzuri mai gushewa, kamar matafiyi ko mara lafiya wanda ake tsammanin warkewar sa, da kuma mai ciki da mai shayarwa idan suka ji tsoro akan kan su ko jaririn su, da kuma mai haila da mai biki, toh duk wadannan ya wajaba akan su su rama azumin bayan sallah, gwargwadon yawan kwanakin da suka sha.

  Allah Ya ce: "Kuma wanda ya kasance majinyaci ko kuwa kan tafiya, sai ya biya adadi daga wasu kwanuka na dabam". Suratul Bakara, aya ta 185.

  Kuna iya duba wannan makala da ta kawo hukunce-hukuncen azumi da suka kebanci mata.

  Sai uzurin da yake halatta shan azumi:

  Na farko: Rashin lafiya; duk wanda ya kasance bai da lafiya, ba zai iya yin azumi ba, to shari'a ta rangwanta masa ya sha azumi.

  Na biyu: Tafiya; duk tafiyar da ta kai a mata kasaru, to ya halatta a sha azumi.

  Shan azumi ga mara lafiya wanda yake cutuwa da yin azumi, da kuma matafiyi wanda kasaru ta halatta a gare shi, sunnah ne. Saboda fadin Allah Maduakikin Sarki: "Sai ya biya adadi daga wasu kwanuka na dabam". Ma'ana: zai sha, kuma ya biya adadin kwanakin da ya sha.

  Kuma Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya kasance idan aka bashi zabi tsakanin abubuwa guda biyu, ya kan zabi mafi sauki daga cikin su. Haka nan ya tabbata a sahihul Bukhari da Muslim, Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) yace: "Baya daga da'a (biyayya), yin azumi a halin tafiya". Ma'ana: Idan ya zama azumin yana wahalar da ku, kuma kun ji tsoron cutuwa. Idan matafiyi yayi azumi ko mara lafiya wanda azumi yake wahalarda  shi ya yi azumi, toh azumin su ya inganta, amma abin ki ne aikata hakan.

  Na uku: Mai haila ko biki; mai haila da mai biki haramun ne su yi azumi a lokacin jinin haila ko biki, kuma koda sun yi, to azumin bai inganta ba.

  Na hudu: Mai ciki da mai shayarwa idan suka ji tsoron cutuwa ka kan su, ko ga jaririn su, ya halatta su sha azumi. Kuma ya wajaba a gare su su biya azumi a wasu kwanaki na daban bayan sallah.

  Shin idan cutarwar akan jaririn su ne, zasu ciyar kari akan ramakon azumi? Akwai sabani tsakanin malamai. Amma Magana mafi rinjaye ba zasu ciyar ba.

  Na biyar: Wanda zai kubutar da wani; ya wajaba ga wanda ya bukaci ya sha azumi don tseratar da wani ga halaka, kamar wanda zai nitse a ruwa da makamantan haka.

  Ku duba kashi biyar na daga kura-kuran masu yin azumi.

  Hukunce-hukuncen biyan azumi:

  Duk wanda ya sha azumi a watan Ramadan saboda halataccen sababi, kamar uzuri na shari'a wanda ya halatta shan azumi, ko wani sababi haramtacce, to biya ya wajaba a gare shi. Saboda fadin Allah Madaukakin Sarki: "Sai ya biya adadi daga wasu kwanuka na dabam". Kuma mustahabbi ne ya gaggauta biya, saboda ya kubutar da kan shi.

  Kuma mustahabbi ne biyan azumin ya zama a jere, saboda biya yana madadin yi a lokacin sa ne. Idan bai gaggauta biya ba, to ya wajaba ya yi niyyar biya, kuma ya halatta ya jinkirta biyan, saboda lokacin biyan a yalwace yake. Saboda duk wajibin da lokacinsa yalwatacce ne, to ya halatta a jinkirta shi, tare da niyyar aikata shi. Kamar yadda ya halatta a rarraba shi, ta yadda zai biya azumin a rarrabe.

  Sai dai idan ya zama kwanakin da suka rage watan Sha'aban ya kare bai fi gwargwadon kwanakin da ya sha azumi ba, to a nan dole ne ya jeranta biyan azumin, saboda karancin lokaci.

  Haka nan, ba ya halatta jinkirta biyan azumin Rahamadan har zuwa bayan wani Ramadan ba tare da wani uzuri na shari'a ba, saboda fadin Nana Aisha (Allah Ya yarda da ita): "Yana kasancewa ana bi na azumin Ramadan, amma bana samun damar rama shi, sai a watan sha'aban, saboda aiki na kula da Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi". Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.

  Saboda haka, wannan hadisi yana nuna lalle lokacin biyan azumi lokaci ne yalwatacce, yana farawa ne daga bayan karamar sallah har zuwa gwargwadon yadda mai biya zai biya kwanakin da ya sha a watan sha'aban, a nan kam wajibi ne ya biya kafin shigowar sabon watan Ramadan.

  Idan Ya jinkirta biya har sabon Ramadan ya shigo bai biya bashin azumin da ake bin shi ba, to zai azumci Ramadan da ya shigo, ya kuma biya abinda yake kansa bayan Ramadan.

  Idan ya zama jinkirin biyan saboda wani uzuri ne da ya hana shi biya, to zai biya ne kadai. Amma idan kuma ya zama ba da uzuri ya jinkirta ba, to ya wajaba ya biya kuma ya ciyar da miskini ga kowace rana rabin sa'i, na abincin mutanen gari.

  Kuna iya karanta shar’antattu daga cikin ladubban mai yin azumi.

  Biyan azumi ga wanda ya mutu akwai bashin azumi a kan shi:

  Wanda ya mutu akwai bashin azumi akansa, to hukunci biya masa azumin ya bambanta da irin nau'in bashin azumin da yake kan sa.

  Azumin Ramadan

  Wanda ya mutu akwai bashin azumin Ramadan a kan shi, baya fita dayan hali biyu:

  Na farko: Ya mutu kafin ya samun damar biya, ko don saboda kurewar lokaci, ko kuma don uzurin rashin lafiya ko tafiya ko haila ko biki, wanda ya sa shi shan azumi, bai samu ya biya ba bayan sallah har ya mutu. To wannan babu komai a kan sa, kuma babu komai a kan magadan sa. Wannnan shine fadin mafi yawa daga cikin malamai.

  Na biyu: Ya mutu bayan ya samu damar biya, amma bai biya ba.

  Malamai sun yi sabani akan sa. Amma magana mafi rinjaye itace: Magadan sa zasu biya masa, saboda fadin Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi): "Wanda ya mutu akwai azumi akansa, to waliyyin sa zai masa azumin". Da kuma wani mutum ya tamabyi Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi); Ya Manzon Allah! Mahaifiya ta, ta rasu, kuma akwai azumin wata akan ta, zan iya biya mata? Sai yace: "Da ace ya kasance akwai bashi akan mahaifiyar ka, shin zaka biya mata?". Sai mutumin ya ce: Eh. Sai Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) yace: "Bashin Allah shi ya fi cancanta a biya".

  Azumin kaffara

  Idan kuma wanda ake bin shi azumin kaffara ne ya rasu, kamar kaffarar zihari ko azumin mai tamattu'i a hajji, to za'a ciyar masa ga kowani wuni miskini daya, ba za'a masa azumi ba. Kuma zai zama ciyarwar daga dukiyar sa ne, saboda shi azumi wakilci baya shigar sa, a raye ko bayan mutuwa, wannan ita ce maganar mafi yawa daga cikin malamai.

  Azumin bakance

  Idan kuma wanda ake bin shi azumin bakance ne ya rasu, to mustahabbi ne waliyyin sa (magajin sa) ya biya mishi azumin (Bakance shi ne mutum ya wajabtawa kansa abinda asali shari'a ba ta wajabta masa ba, misali kamar ya ce, idan Allah Ya bani nasari a jarabawa, zan yi azumi). Saboda abinda ya tabbata daga sahihai guda biyu (Bukhari da Muslim), wata mata ta zo wajen Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), sai ta ce: Lallai mahaifiya ta ta rasu, kuma akwai azumin bakance akan ta, shin zan iya yi mata azumin?  Sai Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: "Eh".

  Mai karatu na iya duba wannan makala da ta yi bayani akan hukunce-hukuncen ittikafi.

Comments

3 comments