Makalu

Sabbin Makalu

View All

Yadda za a cire sinadarai masu guba da ake samu a rigakafi

 • A yayin da alluran rigafi ya zame mana abin dogaro don kare iyalanmu da kuma mu kanmu daga cuttuka da dama, haka nan kuma ya haifar mana da rudani masu dinbin yawa.  Wasu na ganin yin alluran bai da wani alfanu sai dai illa a inda suke ganin yana nakasa  yaro ko mutum har karshen rayuwarsa.  Amma wasu kuwa gani suke ba haka abin yake ba, akasari ma, a nasu ganin, ai taimakonmu Turawa suke yi wajen ganin sun inganta lafiyar ‘ya’yan namu wajen ganin basu kamu da wasu cututtuka ba.  A wani bangaren kuma, wasu ko a tsaka-tsakiya suke a wannan mahawarar.

  Ko ma menene ra’ayin mutum a wannan lamari, yana da kyau a fahimci irin kayan hadin wadannan magunguna na rigakafi. Wasu daga cikin sinadaran da ake hada magungunan sun hada da:  formaldehyde, aluminum, thimerosal (a mercury-based preservative), antibiotics, 2-Phenoxyethoanol, FD&C Yellow #6 dye, and monkey kidney cells. (yawancin wadannan sinadarai, sinadarai ne masu dauke da karafuna)

  Ba wai cikin magungunan rigakafi kawai ba har a mazaununmu da wajajen da muke gudanar da al’amuran mu na yau da kullum mu kan yi kacibis da sinadarai masu dauke da karafuna. Irin wadannan abubuwan sun hada da: Gurbataccen iska, da robobi (plastics) da aluminum irin su aluminum foil da makamantansu, da baturan motoci da na fitilu (flashlight) har ma a cikin abincin mu da muke ci yau da kullum.

  Hulda da sinadarai masu dauke da karafuna kamar su mercury, aluminum, copper, cadmium, nickel, arsenic, da lead zai iya haifar da yanayin nan da ake kira “heavy metal toxicity,” yanayi ne da ke da illa kwarai ga lafiyan dan adam wadda ka iya haifar da cututtuka da dama ciki harda cutar kansa.

  Alamun heavy metal toxicity sun hada da:

  1. Mutuwar jiki, mutum ya rika jin kamar an yi masa duka
  2. Ciwon kai mai tsanani (Migraines)
  3. Ciwon gabobi (join pain)
  4. Rashin samun natsuwa a kwakwalwa (brain fog), wadda ke haifar da mantuwa da rashin natsuwa
  5. Wahala wajen zagawa/kashi  (constipation) da dai sauran matsaloli da suka danganci digestion
  6. Rashin iya bacci sosai
  7. Yawaitan Yeast da bacteria
  8. Eczema da cututtukan da suka shafi fata

  Wanda ya kamata ya cire sinadarai masu guba a jikinsa

  Wadanda suka kamata su cire sinadarai masu cutarwa a jikinsu, sun hada da:

  1. Mutanen da suka taba yin rigakafi
  2. Wadanda suke fama da abubuwan da muka lissafa a saman nan
  3. Masu fama da auto-immune disorders
  4. Masu tarihin cutar mantuwa a zuri’ansu (dementia)
  5. Yara masu fama da cutan autism ko ADD/DHD

  Hanyoyi mafi sauki na cire sinadarai masu guba a jiki

  Bisa ga shawarar masana lafiya, yana da kyau  kafin mutum ya fara kokarin cire wadannan sinadarai ya san ya ya jikinshi ke sarrafa su ainihin sinadaran, wato toxic din.

  Mutum na iya tambayan kansa wadannan tambayoyi kamar haka:  Shin kana hada zufa ne sosai?  Sannan kana zagawa/yin kashi  ko wani rana ne?

  Idan amsoshinka sun kasance a’a,  to yana da kyau ka  wanke cikinka tukuna (digestive tract cleanse) kafin cire wadannan sinadarai don samun ingantaccen sakamako.  Rashin wankin cikin na iya overloading organs na mutum kamar su hanta (liver), da tsaifa (pancreas) da hanji (colon).

  Mutum ka iya wankin cikinsa ta hanyoyi kamar haka:

  1. Cin danyun ganyayyaki  masu kyau (organic vegetable) da kuma shan lemun ‘ya’yan itace (fruit juice ).
  2. Wankin hanta ta hanyar cin abinci kamar: Turmeric (kurkur), da milk thistle, da dandelion tea, cin abinci masu dauke da sinadarin potassium sosai kamar ayaba da fiya (avocado).

  Bayan an bi hanyoyin da muka ambato a samannan don wankin ciki, to yanzu sai mu ga hanyar da za a bi don a cire wadannan sinadarai masu guba a jiki. Ga su kamar haka:

  Fitarwa ta fata (through skin)

  1. Fitarwa ta hanyar wanka (bath): A zuba gishiri rabin kofi a cikin ruwa mai dumi na wankan ko na wanke kafar yaro. Sannan za a iya saka baking soda cokali biyu (2 tablespoon) a cikin ruwan (optional). In yaro nauyinsa ya kai 27 kg kuma, to a yi amfani da gishirin kofi guda cur. Sannan yaro  kuma da ke kasa da wata shida (under  6 month), to a sa gishirin kashi daya bisa hudun kofi  (¼ cup).  Amma a tabbatar wajen yin wankan yaro bai hadiye ruwan ba. Sannan cikin ruwan, a akan iya zuba detoxifying essential oil  kamar lavender, tea tree,  lemon  da makamantansu.
  2. Skin brushing (yin buroshi wa fata): A kan yi wannan brushin din ne kafin wanka. Mutum zai rika brushin din jikinsa ne a hankali har ya game jikin yana mai fuskantar zuciyarsa (direction of the heart).
  3. Tausa (massage). Latsa wannan don ganin yadda ake yin wannan Tausan.
  4. Ta hanyar hada zufa (sweating). Mutum kan iya hada zufa ta hanyar motsa jiki kamar yin dan guje-guje da makamantashi.

  Fitar da sinadaran ta digestive system

  1. Za a yi amfani da garin chlorella don fidda sinadarai masu guba a jiki. Sannan ana iya samun sa a matsayin capsule don a rika sha.
  2. Ganyen cilantro ma yana da matukar amfani wajen ciro sinadarai masu guba a jiki. Saboda haka za a iya lazimtar saka shi a cikin abinci a koda yaushe.
  3. Sannan za a iya juice na su veggies kamar su cucumber, da karas, da broccoli, da kabeji a hada da ‘yan kayan itace. A yi kokarin shan a kalla kofi daya a rana.
  4. Cin abinci da mai (oil) wadda ke dauke da omega 3 oil kamar su cod liver oil shi ma ya na taimakawa wajen cire wadannan sinadarai a jiki.
  5. Yawaita cin abinci mai vitamin C ko shan irin supplement dinnan na shi vitamin C din na taimakawa kwarai ainun.
  6. Cin tafarnuwa shima ya na da matukar amfani. Sannan da shan horsetail tea.

  Amma yana da kyau mai karatu ya sani, a lokacin da mutum yake kokarin bin wadannan hanyoyi don cire sinadarai masu guba a jikin shi ko na yaron shi, zai iya fama da yanayin rashin jin dadi kamar na gudawa, ko gajiya (fatigue), ko dai ma yanayi kamar na mura (flu). Amma wasu ma abin bai haifarmusu da komai a jiki, ya dai danganta ne da mutum-mutum.

  Wasu hanyoyin da za a bi don samun kariya daga wadannan sinadarai masu guba sun hada da:

  1. Yawan shan ruwa mai kyau da tsafta
  2. Rage shan soda drink, kamar su Coca kola da su Pepsi
  3. Yawan shekan iska mai tsafta (clean air)
  4. Samun bacci isasshe da kuma fita a rana
  5. Yin abinnan da ake kira earthing; wato cire takalma a ajiye kafa a kasa na dan wani lokaci

  Sau nawa mutum ya kamata ya cire sinadarai masu guba a jiki?

  Ya kamata a yi wannan treatment din na sati biyu. Sannan a maimaita ko wani bayan wata uku ko makamancin haka

  Dr Laura ce ta rubuto wannan bincike a shafinta, kuma ana iya latsa wannan wuri don samun karin bayani.

Comments

0 comments