Makalu

Sabbin Makalu

View All

Bayanai game da cutar gyambon kafa (Venous leg ulcer)

 • Gyambon kafa ciwo ne da ya ke yawan kama mutane da dama asabili da dalilai masu yawa. Yana da matukar muhimmanci mara lafiya ya je asibiti a yi masa kwaji don yama san wani irin gyambo kafan ne ke damun sa kafin a fara shan magani. Rashin sanin hakan kan jawo matsaloli marasa kyau in har aka fara jinyar wani gyambo da bashi ke damun mara lafiyar ba.

  Ire-iren gyambon kafa wadanda sukafi yawa sun hada da; venous (wato wadda ya shafi jijiyoyin da ke kai jini cikin zuciya). Wannan irin gyambon kafa na faruwa ne saboda rashin aiki da su wadannan jijiyoyin ba su yi sosai, yanayin da aka fi sani a Turance da suna venous insufficiency. Sai kuma arterial leg ulcer, wadda ke faruwa saboda nakasun wannan jijiyoyi na arteris (wato jijiyoyin da ke fidda jini daga zuciya), sai kuma ta dalilin irin cutannan na rheumatism, da kuma ta dalilin cutar diabetes. Har’ila yana iya faruwa ta dalilin haduwar matsalolin jijiyoyin arteris da kuma jijiyoyin veins a lokaci guda.

  Cikin duk wadannan irin gyambon kafa, wanda ya fi yawaita cikin mutane shine na farko da muka ambata, wato, venous leg ulcer. A kiyasi da hukumar yada bayanai da suka shafi lafiya ta kasar Birtaniya, ta nuna cewa a kasar ta Birtaniya, kashi casa’in (90%) cikin masu fama da ciwon gyambon kafa, suna fama ne da venous leg ulcer. Da yardan Allah a wannan makala, zamu mai da hankali ne akan shi wannan irin gyambon kafa, tare da kawo bayanai game da abinda ke haddasa shi da kuma hanyoyin da za a bi don guje masa.

  Jan hankali: Manufar wannan makala shine a taimakawa al’umma wajen fadakar da su don samun ilimi akan wannan matsala ta venous leg ulcer. Ko kadan baya zama a madadin zuwa asibiti. A duk lokacin da mutum ya samu kan shi cikin matsala na rashin lafiya, to a garzaya zuwa wajen likita don gano asalin abinda ke faruwa.

  Abubuwan da kan jefa mutum a hadarin kamuwa da venous leg ulcer

  A kwai abubuwa da dama da kan jefa mutum cikin hatsarin kamuwa da wannan cuta.

  1. Kiba (obesity) na iya haifar da matsala a jijiyoyi, wanda ta hanyar ciwon hawar jini, za a iya kamuwa da irin wannan gyambon kafa.
  2. Rashin motsa jiki na tsawon lokaci a dalilin watakila cuta mai shanye gabbai (stroke) ko kuma ta dalilin wani ciwo na daban. Hakan kan haifar da matsala ga wannan jijiyoyin da za su iya haifar da gyambon.
  3. Sannan matsalar nan da ake kira da Deep vein thrombosis (DVT) kan iya toshe wadannan jijiyoyi din ta yadda zai rage haurawar jini zuwa zuciya.
  4. Sannan kuma fiye da rabin masu fama da chronic venous insufficiency suna da tarihin hadarin da ya shafi kafa. Wannan ya nuna cewa hadari a kafa kan haifar da wannan cutar.
  5. Haka zalika, yadda mutum ke tafi da rayuwarsa ma kan haifar da wannan matsala. Abubuwa kamar shan taba ko kuma wata sana’a da kan sa mutum ya rika tsayuwa mai tsayi (dadewa a tsaye) da makamantansu duk na iya jefa mutum cikin hatsarin kamuwa da wannan cuta.

  Duk wadannan matsalolin da muka lissafo a sama kan iya kawo tangarda ga yadda jini ke gudu (flow) musamman a kafan mutum (lower legs). Gudu da jini kan yi daga kafa zuwa zuciya ya danganta ne da nagartar passive valve na cikin jijiyan (veins) wadda kan hana dawowar jini ta kafa (lower legs) saboda nauyi da kuma karfin canji da ake samu a cikin vascular system na mutum. Samun nakasun wannan system din kan haifar da chronic venous hypertension, abin nan da ake cewa long-term increase in ambulatory venous pressure. Shi wannan chronic venous hypertension kan haifar da matsuwa (stretching) ga jijiyoyin (venous) da kuma capillary walls a wurin da matsalar ta shafa wadda hakan kan baiwa duk wani abu mai ruwa-ruwa damar yoyo (leaking) zuwa interstitial tissue. Wanna yoyo din sai ya aibunta naman jikin mutum, wato tissue, kuma a karshe sai matsalar ta zama venous leg ulcer.

  Duba: Yadda za a rage sugar a cikin jini ba tare da shan magani ba

  Alamun dake nuna kamuwa da venous leg ulcer

  Marasa lafiya masu dauke da chronic venous hypertension na fama da ciwon kafa (limb) wadda ake samun saukin shi ta hanyar daga kafar sama kadan (elevation). Samun saukin wannan ciwo ko radadi ta hanyar dagawa na nuni da cewa wanna matsalace ta venous leg ulcer ko da yake ba ko wani mutum ba ne kan yi nuni da wannan alamun.

  Wani alamu kuma shine irin kumburin nan da ake kira pitting edema. Shi wannan kumburi na faruwa ne saboda yoyon ruwa (fluid) daga jijiyoyi (veins) ke yi kuma ya yadu a naman jikin mutum da ke wannan wurin. Wannan yanayin kan tsananta ne gwargwadon tsawon lokacin da ya dauka, amma akan samu sauki yayin da aka kwanta a gado kamar kwanciyar bacci.

  Ankle flare shima wani alamu ne na venous leg ulcer. Shi wannan ankle flare wani yanayi ne da ke sa fatan kusa da dunduniyar (ankle) kafar mutum ya yi kamar ruwan kasa-kasa, kamar wadda wuta ya kona shi.

  Mafi yawan lokaci, venous leg ulcer yana faruwa ne a tsakanin ciki da wajen dunduniyar kafar mutum sannan kuma yana faruwa ne a hankali.

  Yawa-yawan lokaci, gyanbon venous leg ulcer za a ganshi babu alamun ya shiga jiki haka sosai (shallow in appearance) sannan za a ga alamun dan gari-gari haka nan na fitowa a wurin. Sannan kuma yana da dan danshi-danshi saboda ruwan da ke cikin jikin mutum na wannan gefen na dan fita a wurin.

  Yadda ake gwajin gano cutar (diagnosis)

  Ana duba tarihin lafiyar mutum (clinical history), da kuma gwaje-gwaje kamar; su visual assessment (gwajin lafiyan ido) da su laboratory tests don gano ko akwai wasu matsalolin na daban domin a dauki mataki da wuri. Rashin yin cikakken gwaje-gwaje (clinical assessment) kan haifar da nakasu wajen jinyar shi wannan cuta na venous leg ulcer.

  Masana sun tabbatar da cewa, yana da matukar muhimmanci a yi wa mara lafiya abinnan da ake kira da suna  Doppler measurement  na dunduniya (ankle/brachial) pressure index (ABPI) domin watakila ko mara lafiyar na dauke da cuta na jijiyar arteries, wato arterial disease a Turance.

  Hanyoyin da za a bi don gaggauta warkewar cutar

  Kamar yadda kowa ya sani ne shan taba sigari na haifar da cututtuka da dama, hakannan kuma game da wannan ciwo ya kan kara tsananinsa. Sannan kuma shan taba na rage yadda mutum ke daukar (absorption) vitamin C cikin jikinsa, wadda ake bukatar shi don samun sinadarin protein da kuma samar da abinnan da ake kira collagen. Saboda haka, barin shan taba, ba wai kawai rage hadarin kamuwa da cutar leg ulcer ya ke yi ba, harma yana taimakawa wajen samun sauki da wuri ga mai fama da wannan cutar. A dalilin haka, idan mai fama da venous leg ulcer ya bar shan taba zai yi gaggawan warkewa.

  Ana bukatar daidaito wajen cin abinci wato balanced diet a Turance. Shi balanced diet nan ana bukatarsa ne don warkar da gyambo da wuri. Ana bukatar sinadarin protein don gina jiki (building tissue), sannan sinadarin carbohydrates don samun karfi da kuzari (energy), da kuma sinadarin oil da vitamins duk ana bukatarsu kafin balanced diet ya samu.

  Baicin balanced diet, ana bukatar mara lafiya mai kiba (obese) da ya yi kokarin rage kiban don taimakawa kansa wajen samun sauki da wuri.

  Amfani da bandage (bandeji) da ake kira compression bandaging or hosiery na daga cikin abubuwa masu muhimmanci a jinyar venous leg ulcer. Amma yana da kyau a tabbatar cewa wannan mara lafiya, cutar venous leg ulcer ne da shi domin wannan bandaging yana da hadari game da ciwon arterial leg ulcer. Shi wannan compression bandaging yana taimakawa gudun jini a cikin jijiyoyi (veins) na mutum. Kuma a tabbatar kwararru ne a asibiti za su sakawa mara lafiya compression bandaging. Sannan sai an duba tarihin lafiyar mai dauke da wannan cutar sosai kafin a saka mi shi wannan compression bandage din.

  Kamar yadda muka yi bayani a baya, dalilin da ke kawo cutar venous leg ulcer shine rashin gudun (flow) jini a kafafun mutum yadda ya kamata. Saboda haka, idan a kwai wani abu guda da mutum zai iya bi, ba wai kawai daga kafa ba (elevation) lokacin da ake zaune a kan kujera, to zai yi kyau, ma’ana, zai taimaka gaya wajen gudun jini zuwa zuciya.

  Karanta: Amfani 10 na kayan kamshi spices ga lafiyar bil adam

  Da fatan wannan makala zai taimaka wajen ba wa mutane daman sanin wannan cuta na venous leg ulcer, da kuma sani hanyar da za a bi don kariya daga shiga hadarin kamuwa da shi. Kuma dadin dadawa, ya taimakawa masu fama da shi wajen samun sauki da wuri. Da yardan Allah, in aka bi hanyar da ya dace wajen kula da gyambon, da kuma taimakon malaman jinya, za a shawon kan wannan cutar har ya warke.

  Jan hankali: Asalin wannan makala an rubuta shi ne da harshen Turanci a taskar Penprofile, mu kuma a Bakandamiya muka fassara muku zuwa harshen Hausa. Mai karatu na iya karanta na Turancin ta hanyar dannan wannan wuri.

  Kaman yadda ku ka sani, burinmu a Bakandamiya shine mu yada ingantaccen ilimi ga kowa da kowa, musamman ga masu amfani da harshen Hausa, saboda haka muke kokarin kawo muku makalu masu inganci don karuwarku da al’umma baki daya. Kar ku manta, za ku iya duba daruruwan makalunmu akan maudu’ai daban-daban na ilimi a sashin makalunmu.

Comments

1 comment