Makalu

Sabbin Makalu

View All

Sakamakon bincike game da matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi a Najeriya

 • Matsalar shaye-shayen miyagun gwayoyi matsala ce da kusan kowa da kowa na iya tabbarwa akwai shi a cikin al’umma musamman mu a Najeriya. Idan wani baya sha a gidanku, ko cikin danginku to kuwa lallai ba za a rasa masu yi ba a unguwarku ba. To amma duk da haka a kullu yaumin sai dai a yi ta maganar, amma sai ka ga ba wani kwakwkwarar mataki na zahiri da mutum zai ce ga shi ana dauka don shawo kan lamarin tun daga bangaren gwamnati, wacce hakkin nauyin jama’a ya doru akan ta, har izuwa kan iyalai, wadda duk wata tabarbarewa kan faro ne daga nan.

  Anan Najeriya misali, ba da jimawaba a shafin sada zumunta ta Twitter, wani ma’abocin amfani da kafar ya sako wani sakamakon da aka wallafa akan wani bincike da aka gabatar mai taken, Drug Use in Nigeria 2018, wadda aka wallafa a shafin yanar gizo na ofishin da ke kula da miyagun kwayoyi da laifuka na Majalisar Dinkin Duniya, wato United Nations Office on Drugs and Crime (UNODC). Shi wannan sakamakon binciken ya kunshi bayanai masu muhimmanci da ya kamata duk wani dan kasa mai hankali ya maida hankali a kai.

  Abin kaico da takaici wai a maimakon ‘yan Najeriya su fara tattaunawa da kawo dabarun yadda za a shawo kan wannan matsala sai kawai aka shiga muhawara akan gaskiya ko rashin gaskiyar rahoton binciken. Duk da cewa wannan bincike an gunadanar da shi ne a shekara 2018, amma na tabbatar sakamakon har a yau kusan hak ya ke, sai ma abinda ya karu. Ni a gani na, lokaci ya yi da ya kamata matasanmu su maida hankali da saka karfi akan muhawara da zai ficcemu domin a gudu tare a tsira tare!

  Mai karatu na iya duba wannan makala da ta kawo illolin shaye-shaye da kuma hanyoyin magance su.

  Da farko dai yana da kyau a sani cewar, wannan bincike an yi shi ne a karkashin jagorancin Federal Ministry of Health da kuma National Bureau of Statistics (NBS) tare da Centre for Research and Information on Substance Abuse (CRISA) na Najeriya. A yayin da ofishin kula da miyagun kwayoyi da laifuka ta Majalisar Dinkin Duniya ta bada taimako irin na kwarewa wato technical support kenan a Turance. Sannan kuma kungiyar Hadakan Turai wato European Union (EU) su suka dauki nauyi don taimakawa Najeriya yaki da matsalar miyagun kwayoyi. An yi wannan bincike ne a duk fadin kasannan. Kusan ba’a taba bincike mai fadi ba akan matsalar miyagun kwayoyi a Najeriy kamar wannan.

  Wannan binciken ya bankado abubuwa da dama da ya kamata musamman mahukunta su maida hankali akai. Wasu daga cikin abubuwan da aka gano sun hada da:

  1. Akwai karuwar masu amfani da miyagun kwayoyi fiye da yadda ya ke a shekarun baya a Najeriya.
  2. Daga cikin masu amfani da miyagun kwayoyin, idan ka samu mutum uku maza to na hudunsu mace ce.

  Hakkin mallakar hoto (photo credit): UNODC

  1. Ire-iren sinadarai da masu shan kwayoyin suka fi amfani da su, sun hada da cannabis wadda ya fi kowanne yawan masu amfani da shi, sai mabi da shi mai suna opioids da kuma magungunan mura masu dauke da sinadarai irin su codeine da makamantansu.
  2. An gano cewa, duk daya daga cikin mutane bakwai masu shekaru da ke tsakanin sha biyar zuwa sittin da hudu (15-64) a Najeriya ya taba amfani da miyagun kwayoyi (wadda ba giya ba kuma ba taba ba, sannan kuma ba don magani ba) a shekarar da ta gabata.
  3. Amma yawancin mutanen da aka samu suna ta’ammali da miyagun kwayoyin suna masu shekaru ne daga ashirin da biyar zuwa shekaru talatin da tara (25-39).
  4. Kiyasin yawaitan masu ta’ammali da miyagun kwayoyin a cikin maza ya kama kashi 21% wadda hakan ke nufin akalla mutane miliyan goma da dubu dari takwas da hamsin ke nan. Sannan a bangaren mata kuma, a kalla mutane miliyan uku ne da dubu dari hudu da talatin wadda hakan ya yi daidai da 7% a cikin masu mu’amala da wadannan kwayoyin. A kasar gaba daya kuma ya kama kiyasin miliyan sha hudu da dubu dari uku (14,300,000) ke nan, wadda ya yi daidai da kashi 14.4% na jama’ar kasar baki daya
  5. Masu amfani da miyagun kwayoyin sun fi yawa a bageren kudancin kasar nan fiye da arewacin kasar.
  6. An yi kiyasin kusan mutane dubu dari uku da saba’in da shida (376,000) ne a cikin masu ta’ammali da miyagun kwayoyin ke cikin hatsari sosai a duk fadin kasan.
  7. Sannan a kowani mutum biyar da ke cikin hatsarin, an tarar daya daga cikinsu na amfani ne da nau’in allura wajen mu’alama da kwayoyin. Kenan a kwai mutane da yawansu ya kai 80,000 wadanda suka fada a cikin wannan nau’in.
  8. Haka zalika, wannan bincike ya gano cewa, mata sunfi shiga hatsarin shiga mu’amala ta saduwa na barkate, wato high risk of sexual behavior a Turance, fiye da takwarorinsu maza. Wannan ya karawa matan shiga hatsarin kamuwa da cututtuka kamar su cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV/AID.
  9. Bugu da kari, wannan bincike ya gano cewa tsadar jinya da kuma rashin yawaitar kafafen yin jinya hada da tsangwama da mutane kan nuna wa masu fama da matsalar shaye-shayen duk sun taimaka wajen hana wa’yanda ke bukatar taimako cikinsu samun taimakon da ya kamata.
  10. Sannan wannan bincike ya gano cewa da yawa daga cikin masu wannan dabi’a akan same su da aikata laifuka kamar su sace-sace, sana’ar karuwanci da makamantansu.
  11. Sannan dadin dadawa masu wannan dabi’a na kawo matsaloli da dama a cikin iyalansu, kamar kawo tashin-tashina a cikin iyalan da kuma watsi da ‘ya’yansu ga masu ‘ya’ya da dai abubuwa munana daban-daban da kan iya watsa iyali.

  Dubi wannan hoton:

  Hakkin mallakar hoto (photo credit): UNODC

  Wannan kadan kenan daga cikin abuwawan da wannan bincike ya gano.

  Binciken ya yi bayanai ko kuma ince ya kawo wasu shawarwari da ya kamata a dauka don ganin an shawo kan wannan matsalar. Don karanta cikakken bayani game da wanna bincike latsa wannan wuri.

  Kuna iya karanta: Illolin shan miyagun kwayoyi ga matan aure

  Jan hankali:

  A maimakon mai da hankali ga nuna wa juna yatsa da banbance-banbance, yana da kyau mu sani cewa duk abinda ka gani ga wane gobe gareka yake zuwa.

  A gani na a matsayinmu na ‘yan kasa, kamata ya yi mu mai da hankali ga bayanai masu muhimmanci da wannan bincike ya kunsa. Kar ku manta duk da cewa abu ne da kusan dukkanninmu zamu iya shaidawa, wannan bincike ya nuna mana cewa:

  Yawan matasa da ke ma’amala da miyagun kwayoyin ya kai wani matsayi. Sanin kowa ne wannan na nufi ko yana nuni lallai akwai matsala da matasanmu ke ciki. Suna bukatar taimako.To tambayar anan shine, mene ne mutum zai yi a matsayin sa na taimakawa wa’yanda ke bukatan taimako kafin su fada cikin wannan hali. Ta ya ya za ka/ki taimakawa wadanda ke cikin wannan hali da ke kusa da kai/ke don karesu daga halaka.

  Sannan kuma yadda wannan bincike ya nuna yawan mata da ke mu’ala da miyagun kwayoyi abin tsoro ne. Me ke faruwa? Ganin cewa mata suke renon yara, su basu tarbiya – ana sa ran wadannan yara za su girma su zama ginshikin al’umma. To ina muka dosa a al'ummance? Yau an wayi gari kaso da dama cikin iyayensu na fadawa cikin wannan lamari na shaye-shaye, lallai abin dubawa ne da gaggawa. Lallai wannan lamari ne da ke bukatar kowa da kowa don ceton al’umma.

  Haka zalika, wannan bincike ya nuna duk da cewa babu isassun kafafen taimakon masu fama da wannan matsala, amma tsangwama da suke fuskanta daga wajen jama’a na daga cikin abinda ke hana masu bukatan taimako nema taimakon da ya kamata su samu. Wannan tsangwama ba karamar illa ba ce ga kokarin shawo kan wannan lamari.

  Hakki ne akan mutane, kama daga iyaye da ‘yan uwa har izuwa mutane unguwa su taimakawa mutanen da ke fama da wannan matsala don ceto su. Domin ceton su ceton kai ne gaba daya. Kasancewarsu ba ‘ya’yanmu ba ko ba danginmu ba ba zai kubutar da mu daga cikin hatsarin wannan halayyar ta su ta shaye-shayen za ta haifar ba. Saboda haka taimakonsu yi wa kai ne. Duk wadda ya taimaki wani kuma Allah zai taimake shi.

  Abu na gaba da na ke son jawo hankalinmu musamman mu ‘yan arewacin kasarnan, akan al’adar rashin yin magana idan an ga ba daidai ba musamman idan ya shafe mu ko wani na mu. Saboda kunyar kar a ce namu ya lalace sai mu gwammaci mu yi shiru. Yin shiru har abada ba zai kawo mana maslaha ba. Don haka a yi kokari da zarar an ga wani abu a yi magana don taro matsalar akan lokaci tun kafin ya fi karfi.

  Har ila yau, wani abu kuma mai muhimmanci da ya kamata a maida hankali akai shi ne kokarin rage zaman banza a tsakanin matasanmu. Dole ne mu mai da hankularmu wajen samarwa kawunanmu aikin yi ba jiran sai gwamnati ta ba mu aikin yi ba. Sannan kuma iyaye da yayyu da kuma duk wadda ke da fada a ji a cikin al’umma su zamanto masu cusa wa ‘ya’ya, da matasa ra’ayin dogaro da kai tun da wuri ba wai sai an kare karatu ba ko kuma sai yaro ya girma sosai ba. Malam Bahaushe ya ce, da zafi-zafi ake dukan karfe. Hakan zai taimaka ainun wajen rage yawan matasan da za su rika shiga damuwa har ya kai su ga fadawa harkar shaye-shaye.

  A karshe ina jawo hankali duk wadda ke da hakki a gwamnatance da a ji tsoron Allah a mai da hankali akan alkawari da aka yi na sauke nauyin jama’a da ke kanku. Wannan sakamakon bincike da aka yi yana hannunku. A tsaya tsakani da Allah a yi abinda ya dace. Allah Ya datardamu baki daya.

  Mai karatu na iya duba wani makalar da ta yi tahalili game da matsalar shaye-shaye a tsakanin matasa.

Comments

0 comments