Makalu

Sabbin Makalu

View All

Yawaitar binciken wayar miji: Dacewa ko rashin dacewa?

 • A wannan zamani matsalolin da suke cikin aure musamman anan Arewacin Najeriya abin ba a cewa komai idan muka lura da ire-iren labarai da suke yawo yau da kullum a kafofin sada zumunta, wato social media. Duk lokacin da ka shiga social media idan yau baka ga labarin wata ta soki mijinta da wuka ba to gobe za ka ji yadda wata ta ci amanar mijinta ko kuma wacce mijinta ya mata duka har ya farfasa mata jiki. Abubuwa gasu nan dai kaca-kaca ko ta ina. A kwai dalilai iri-iri da ake dangana wadannan yawan matsalolin da su. Daya daga cikin dalilan da ke gaba-gaba wadda ake ta mahawara akai shi ne lamarinnan na duba wayar miji a sace da yawancin mata ke yi. Muhawarar shine wasu na ganin ya kamata mace ta iya duba wayar mijinta duk lokacin da ta ga dama wasu kuwa cewa suke bai dace ba domin mijin ai shima yana da daman sirri.

  Gaskiya magana shine mata da yawa na binciken wayoyin mazajensu a boye ba wai kawai a nan Arewa ba, abu ne da yawan mata duk duniya ke yi. A wani bincike da aka yi, wadda na karanta kwanakin baya, an samu cewa duk inda ka samu mata hudu to daya daga cikinsu na aikata wannan bincike na wayar miji a asirce, kimanin kashi 25% kenan cikin mata. Tirkashi! Duk da cewa wannan bincike ya nuna su ma mazan wasunsu na bincika wayoyin matayensu a boyen, to amma dai na matan ya fi yawa kamar yadda wannan bincike ya tabbatar.

  To amma abin tambaya anan shine, wannan bincike na waya da ma’aurata kan yi wa junansu a boye, musamman mata, wani maslaha ya ke kawowa ga al’umma ko ince auratayyarsu? Kusan kowa ya sani wannan binciken na karewa ne akan gano wani abinda kan iya bata zaman auren, inda zargi da rashin yadda ke shiga tsakani, ko kuma wani lokacin har ya kai ga rabuwar auren. To meye amfaninsa ke nan? Kuma menene maslaha?

  A gani na, duk da cewa wannan zamani ya zo mana da ci gaba mai yawa musamman a harkar social media da ma Internet gaba daya, amma wadannan ci gaban da aka samu din kuma sune ke gaba-gaban fitinun wanna zamani, musamman idan mutane ba sa amfani da su ta hanyar da ya dace. Da shike cikin al’adar dan adam ne idan ya samu dama sai ya zake, ya sa maza da dama suna amfani da wayoyinsu wajen yin alaku da basu cancanta ba. Wani lokacin ba wai kawai mazan ba har matan ma wasu suna yi. Saboda haka wannan ta’ada ya haifar da rashin yarda tsakanin ma’aurata da dama a wannan zamani.

  Yana da kyau daga mazanmu har matanmu mu sani aure dai ibada ne ba wai zama ne na haka kawai ba. Kuma zaman aure ana yin sa ne bi sa amana da soyayya da hakuri da juna, sannan kuma da sadaukarwa. Kuma hakki ne ga kowa daga mace har da namiji su ga cewa sun kare darajar aurensu.

  Kuna iya karanta wannan makala da ta yi bayani akan alfanu da kuma rashin alfanun abota da wasu a waje.

  Wannan matsala na biciken waya ya kashe aure da yawa ya kuma saka aure masu dimbin yawa cikin halin ka-ka-ni-ka-yi kamar yadda na fada a baya.

  To amma abin tambayar anan shine wai mene ne dalilin da mata ke nacin yin wannan dabi’a na bincika wayoyin mazajensu ba tare da saninsu ba? Amsar da kusan kowa ya sani shi ne rashin yarda. Kusan kuma kullum hali ne da mazan ke yi ke jawo hakan. Yawanci suna zargin mazan nasu na wani abu na daban da su basu sani ba. Yawanci kuwa baya rasa alaka da zargin da suke yiwa mazajen nasu na ma’amala da wasu matan a waje na daban. Kuma tabbas maza da yawa suna cikin wannan rukuni. Amma duk da haka, a gani na, wannan dabi’a bai dace ba sam. Ga dalilai na kamar haka.

  Yin hakan ba ya sa ki samo kan mijinki

  Da farko dai, ina son ‘yan uwana mata su gane cewa wannan ba shi zai kawo musu sauki ko tabbatarwa sun mallake mijinsu ba. Duk da cewa wannan “mallakar mijin” ina da matsala da ita. A gani na aure mai kyau ba mallaka ke kawo shi ba, gaskiya, rikon amana da mutunta juna su ne, yayinda mace da namiji kowa ke da ‘yanci a ciki.

  Sam wannan dabi’a baya kawo maslaha ko gyara. Kafin mata su min ca a ka, sam bana goyon bayan maza suje su ci karensu ba babbaka. Bana daya daga cikin masu goyon bayan namiji mai  wulakanta matarsa ko mai da ita ba kowa ba ta hanyar yin alaka da wasu mata can da bai cancanta ba a waje. Matarka abokiyar zamarka ce da ta cancanci mutuntawa, kuma namijin kwarai ya wuce nan.

  Ki sani cewa wannan dabi’a baya sa miji ya bar duk wani abinda ki ke gani ba kya so, sai dai ma ki tunzura shi ya koma yin abinda ya ga dama.

  Yana nuni da takurawa miji

  Wasu mata su daura wa kansu dabi’a ne na bin kwakwafin tsiya. To yan uwana mata kowa na bukatar lokacin kanshi da kuma dan sarari da ba wanda zai dame shi ko da kuwa ke matarsa ce. Ki zama mai bawa miji sarari da kuma uzuri ba don komai ba sabo da ke ma hakkin ki ne ya baki wannan damar. Wannan baya nufi don kin ba shi dan sarari zai je ne ya haukace da aikata abinda bai kamata ba. Kowa na son ‘yanci da sarari.

  Yana iya shafar lafiyarki

  Ke ma a wurinki wannan dabi’a ba kyau ne gare shi ba musamman ga lafiyarki. Idan  ki ka ce baki da aiki sai leke-leken wayar miji, to za ki kasance a kullu yaumin cikin bakin ciki da kuma rashin kwanciyar hankali. A maimakon ki maida hakali wajen yin abubuwa na ci gabanki, sai ki bi ki mamaye kan ki da wannan fitina. To meye amfanin a kullun ki kasance cikin zullumi da tunanin abinda ki ka gani ko za ki gani. Idan ki ka jima cikin wannan yanayi sai ki shiga depression ba ki sani ba. Kuma ko shakka babu shiga depression na da alaka da irin wasu matakai da mata ke dauka idan zamantakewa ta yi tsami.

  Karanta abinda ba shine ba cikin waya

  Sannan wani abu da yawa daga cikin mutane basu sani ba shine idan mutum ya ce zai rika duba messages na mutane ne, to tabbas wata rana za ka dau magana ko kuma wani abu da ki ka gani out of context ka hau ka zauna a kai alhali ba wai abinda ka ke zato ba ne. To haka abin yake a tsakanin mata da miji ma.

  Yana nuni da rashin aikin yi

  Kuma a gaskiya wannan dabi’a na nuni da rashin aikin yi da rashin sanin darajar kai. Rashin aikin yi mana. Idan ki ka zauna baki da wani abinda ke damunki a rai sai dai kawai miji da abinda yake yi ai wannan na nuni ne da rashin aikin yi. Kar a min rashin fahimta a nan, miji abin kula ne da mai da hankali, amma komai yana da iyaka. Komai ya yi yawa to ya zama wani abu na daban.

  Kuna iya duba wata makalar da ta yi sharhi akan manya-manyan kura-kurai da ma’aurata ke yi ba su sani ba.

  Gare ku maza

  Ga wasu shawarwari da na ke gani maza ya kamata su bi don rage wannan matsalar a gidajensu.

  Kwatanta gaskiya da adalci

  Shawara ta a gare ka maji shine, a matsayinka na shugaba a gidanka ya kamata ka tsaya tsayuwan daka wajen gina gidanka akan adalci da kuma zaman gaskiya. Duk wani yanayi da mata kan shiga a sabili da rashin gaskiya ne da babu a tsakani. Kuma a har kullum a gaskiya yawanci maza ke jawo wannan rashin gaskiyar.

  Tsoron Allah

  Maza su zamana masu tsoron Allah cikin mu’amalarsu da wasu a waje can, musamman wasu matan a waje. Ka sani duk wani abu da ka yi na nuni da darajar ko rashin darajar matarka ce. Na tabbatar kana son matarka ta kasance mai mutunci da daraja a idon duniya.

  Ku sani matayennan da kuka auro amana ne a gare ku. Kuma duniya juyi juyi ne idan yau ku ne ku ke yi ba daidai ba ga ‘ya’yan wasu ko kannen wasu can. Wata rana ‘ya’yanku ne suke wannan matsayi ko kannenku.

  Shawarwari ga ‘yanuwa mata tare da hanyoyin fita daga cikin wannan fitina

  Zama ayi magana idan anga wani abu

  Idan ki na da wani abu da ki ke ganin baki yadda da shi ba game da mijinki, kamata ya yi a zauna cikin tsanaki da kwanciyar hankali a yi maganar. Aure zama ne na gaskiya. Ki nuna mi shi rashin jin dadinki cikin hikima kuma ke ma ki saurari inda ya ke da matsala game da ke idan ya nuna damuwarsa. Idan duka ku ka saurari juna da yardan Allah sai kin ga sauki.

  Fahimtar mijinki

  Na san akwai mata da yawa da ke korafin mazajensu ba su saurarensu, musamman anan Arewacin kasarnan, kuma lallai hakan ba daidai ba ne sam. Amma wani lokacin rashin sanin yadda za a bullowa lamarin ne. Yana da kyau ki fahimci yadda mijinki ya ke. Wannan zai ba ki damar sanin yadda za ki shawo kan duk wata matsala da ka iya tasowa. Kuma za ki fahimci yadda za ki yi magana da shi.

  Ki zamana kina da abin yi

  Ki maida hankali wajen gina kanki. A zamanin yanzu ba wai sai mutum ya fita waje ba zai nemi ilimi ko sana’a. Internet ya bawa kowa dama, idan har kina da data da ki ke amfani don sada zumunci a What’sApp ko Facebook, to me zai sa ba za ki yi amfani da wannan damar ba wajen neman ilimi da karuwar kanki wanda zai amfane ki da kuma al’umma baki daya. Neman ilimi ba wai yana nufin sai ankara wani degree ba ne, a’a ilimin karuwa na rayuwa akan topics daban-daban.

  Za ki iya yin registering a free online courses ko ma na kudi idan kina da dama, ko kuma su Youtube dinnan. A kwai irinsu Udemy, da Coursera, da su Khan Academy da makamantansu. Idan aka maida hankali a kwai abubuwa da yawa na karuwa a Internet. Kin ga wannan zai rage miki shiga wani damuwa sosai. Idan ma baki san inda za ki fara ba, kawai ki tuna abinda ki ke son karuwa akai sai ki yi googling, duk abinda ki ke so za ki samu a google.

  Ki kama sana’a

  Baicin karuwan ilimi da ake iya samu a Internet, akwai sana’o’i da dama da za ki iya yi idan kina da wani kwarewa akan wani abu. Misali wani abu mai kyau da na ga mata na yi yanzu shine koyar da girki a Whats’App, to ke ma za ki iya fara wani abu makamancin hakan. Ko kuma kin yi karatu, misali degree amma ba aikin yi, za ki iya karantarwa a irin su Udemy, idan kin san field na ki sosai, da makamatasu.

  Za ki yi mamaki irin alherin da za ki samu idan kin dage kuma kin yi hakuri. Ko kuma ma ki fita ki je ki koyi sana’a na hannu, ya fi zaman haka nan.

  Akwai websites da dama da suke bawa mutane masu skills daban-daban ba da services na su ga masu bukata don su samu kudi. Misali ire-iren wadannan websites din shine Fiverr da Udemy da muka fada a sama.

  Karkata hankali wajen tarbiyar yara

  Saka hankali sosai wajen tarbiyar yara ga mai yara ba karamin dabara ba ne. A maimakon tada hankali da sa hancinki ko ta ina, mai zai sa ba za ki mai da hankalinki sosai akan ‘ya’yan da Allah Ya baki amana ba? Na san hakkin tarbiyar ba a wuyanki ke daya ya ke ba, to amma da aikin da ba zai amfane ki ba ai gwara ki yi ta faman tarbiyar – ladanki tun daga duniya har lahira.

  A karshe ina fatan waddanan shawarwari za su taimaka wajen kawo mana sauki da maslaha a cikin zamantakewarmu na aure da a yau ya shiga wani hali. Allah Ubangiji Ya mana jagora.

Comments

2 comments