Makalu

Sabbin Makalu

View All

Ra'ayoyin maza da mata game da zuwa aikin mace bayan ta yi aure

 • A kwanakin baya na ga wani tattaunawa a social media game da zuwa aiki ga mata, musammam matan aure da kuma mata masu yara. Abinda na lura shi ne yawanci mazaje ba su fiya son matansu na zuwa aiki ba duk da cewa yawancin mazan na so a ce matansu sun yi karatu sosai kuma sun waye da sanin abubuwan rayuwa. Domin kowani namiji ya yi imanin cewa ta hakan ne za ta kasance uwa ta kwarai ga ‘ya’yanta ta hanyar ba su kulawa a wajen karatunsu da tarbiyarsu. Amma kuma idan ka duba daya bangaren na gefen matan su kansu za ka tarar yawanci mata, kusan zan iya cewa kashi casa’in cikin dari na mata, suna da burin bayan sun kare karatu su yi aiki ko kuma su yi wata sana’a na su na kansu wadda zai taimaka musu wajen dogaro da kansu. Sannan a bangaren maza, kamar yadda na fada da farko, kusan zan iya ikirarin cewa kashi hamsin cikin dari ba su son matansu su je aiki musamman aikin da zai fidda su a gida kullum. To wannan abu a gaskiya ya jima yana ci min tuwo a kwarya, mene ya sa mu mata muke son fita mu yi aiki, su kuma mazajenmu ba su fiya son hakan ba? Saboda haka na dan yi wani kwarya-kwaryan bincike game da wannan lamari hakan ya sa na zakulo wasu daga cikin dalilai da hakan ke faruwa ta bangaren mata da mazan kansu.

  A wannan makala zamu yi kokarin ganin dalilai da ke sa mata son zuwa aiki ko rike wata sana’a ta daban, ko da kuwa mazajensu na kokarin wajen biya musu dukkan bukatunsu na kudi. Sannan za mu ga dalilan da ke sa wasu mazan ba su fiya son ganin matansu na zuwa aikin ba.

  Ga hanyoyi da na bi na samo wadannan dalilai; na gudanar da bincike son jin ra’ayi a taskar Bakandamiya, sannan na bi tattaunawa daban-daban a social media akan wannnan maudu’i a groups da pages daban-daban na Facebook da Twitter. Wasu groups din mata zalla wasu kuma groups da suka hada kowa da kowa.

  Ga kadan daga cikin dalilan da ke sa mata son zuwa aiki ko dogaro da kansu.

  1. Domin biyan bukatunsu na yau da kullum

  A matsayinmu na mutane dukkaninmu muna da bukatu wadda suka kebanta da kawunan mu kawai. Kuma dukkan dan adam kan yi kokarin samo hanyar biyan wadannan bukatun. To a wajen mata da dama zuwa aiki ko rike sana’arsu na ba su daman cimma wannan buri na su.

  2. Domin kula da iyayensu

  Duk da na kwarai idan yana tasowa daya daga cikin burukansa shi ne ya zama wani abu a rayuwa domin ya sami abinda zai farantawa iyayensa rai ko da kuwa iyayen suna da rufin asirinsu. Wannnan dalili ya sa da yawa daga cikin mata ko da sun yi aure hankalinsu ba zai natsu ba sai sun ga su ma suna taimakon iyayen. Ta hanyar aiki ne ko sana’a wannan buri na su zai iya cika.

  3. Domin tallafawa mazajensu:

  Duk da cewa a addinance da al’adace namiji shi ke da hakkin ci da ciyarwa da tufatarwa da sauran bukatu na gida, amma wani lokacin abubuwa kan yiwa namijin yawa har daukan wadannan dawainiya kan zama wahala. Wannan dalili ya sa wani lokaci dole mace ta ji lalle tana bukatan taimakawa ta hanyar kawo na ta gudumawar a gida. Kuma aiki ko sana’a shi ke ba da wannan dama.

  4. Domin shiga a dama da su

  Dan adam tunda Allah Ya yi shi, shi mutum ne mai son shiga a dama da shi a duk bangare na rayuwa. Kowa na son a ce shi ma a na yi da shi a harkokin rayuwa. Saboda wannnan dalili wasu matan su ke son yin aiki ko sana’a; "wance na yi, kawata ce, ko wance na yi ‘yar uwata ce ai dole ni ma sai na yi!” A kwai mata da yawa masu yin aiki domin fita tsara da kuma gasa da sauran ‘yanuwansu mata.

  5. Domin tanadin ko-ta-kwana

  Na san mata da dama wadanda rayuwarsu da ta ‘ya’yansu ta koma halin kaka-ni-kayi a sabili da rabuwa da ko kuma mutuwar mazajensu. Domin dama can miji shi ke yin komai a gidansa, idan mutuwa ta zo ko kuma rabuwa ya samu sai ka ga an bar mace a halin ha’ula’i ta koma ba yadda za ta yi da ita da ‘ya’yanta. Wannnan dalili ya sa mata da yawa yanzu sun farga ba su yadda su zauna sai abinda miji ya yi ba; suna fita aiki ne domin gudun ko ta kwana.

  6. Domin cikan burinsu na rayuwa

  Wasu mata tunda suka taso suna da burin da yake ransu da suke so su cimma a aikace ko sana’ance. Wasu tun farkon fari so suke su zama likitoci, wasu malaman makarata ko jami’a, ma’aikatan banki da ma sauran aikace-aikace daban-daban. Saboda haka yin karatu har izuwa aikinsu buri ne da kaman an haife su da shi, idan ba su samu cikan wannan burin na su ba za su kasance a cikin rashin farin ciki.

  7. Domin hadakan dalilai masu yawa

  Wasu kuma matan suna aiki ne saboda dalilai masu yawa - kama daga dalilan biyan bukatunsu har izuwa dalilai kamar tattalin ko-ta-kwana da sauran dalilai da dama.

  Dalilian da ya sa wasu mazan ba sa son matansu su rika zuwa aiki

  Kamar yadda mata ke da dalilansu na son zuwa aiki haka suma wasu mazan ke da dalilansu na rashin son matansu su rika zuwa aiki. Ga wasu daga cikinsu:

  1. Saboda da suna bukatan matansu su zauna domin kula da iyali

  Kula da gida da iyali wani abu ne da idan muka maida hankali akansa muka yi shi tsakani da Allah, amfaninsa ya fi duk wani abinda zamu zama a rayuwa. A addinance da kuma al’adun duk yawancin mutanen duniya, mace ita ta fi cancanta ta tsaya ta kula da gida. To saboda wannan dalili ya sa wasu mazajen sun fi son su ga matansu na gida suna kula da yara da kuma sauran harkoki da ya shafi gida. Domin kar a samu rabuwan hankali wajen kula da wannnan bangare mai muhimmanci da kuma zuwa wurin aiki. Duk da cewa wasu matan suna iya hadawa kuma su yi nasara a kowannensu amma a gaskiyar maganar hada aiki da kula da iyali gagarumin aiki ne.

  2. Domin ba su son su ga matan su na hulda da wasu mazan a waje

  Wasu kuwa saboda ba su son suna ganin matansu na hulda da maza wadanda ba muharramansu ba a waje. Wannan dalili ya sa maza da yawa suke kyamatar aikin mata. Kuma idan ka duba anan, duk da cewa ba a taru aka zama daya ba, akwai bata garin mata wadanda ba su kama kansu idan sun fita aiki sam.

  3. Suna tsoron raini a yayin da ita mace ta kasance ta mallaki abin kanta

  Wasu mazan sun yi imani cewa idan mace ta zamana zata iya yiwa kanta komai to ba za su iya da ita ba. Duk da cewa akwai matan da ke ganin nasara na wajen aiki ko sana’a kamar gidan aljannah ce, amma kuma akwai da yawa sun san muhimmanci da darajar mazajensu kuma suna basu wannan girma da darajar din ko da kuwa sun kai kololuwar mataki ne a wajen aikinsu.

  4. Dalili na son juya (control) mace

  Wasu kuma mazan dalilin su shi ne su ga suna juya mace ta ko ta ina, ba su son ta samu wani ‘yanci ko wani katabus da zata iya zartar da wani abu na karan kanta.

  Mafita domin samun iyali mai nagarta da adalci

  Na yi imani cewa duk wata matsala ta na da maslaha idan mutane da ke cikinta suna da niyyar samun wannan maslaha. Ga wasu daga cikin maslaha da a gani na ya kamata mata da maza su bi ko su kula da su domin kowa ya samu abinda ya ke ko ta ke so. Ga su kamar haka:

  1. Aure ibada ne

  Yana da kyau mace da namiji su sani cewa aure ibada ne da suke yi domin samun rabo daga wajen Allah. Kuma kamar ko wani aikin ibada, aure kan zo da na shi bukatun da ka’idoji wadanda wani lokacin ba lallai ba ne su yi mana daidai da son ranmu. Sanin wannan da kuma aiki da sanin zai kawo maslaha mai yawa ko da mace na aiki ko ba ta aiki za ta san yadda za ta tafiyar da al’amuranta na yau da kullum a gidanta ko a wajen aiki.

  Sannan a bangaren namiji kuma shi ma ya sani wannan ibada akwai hakkoki da ya ba shi kuma ya bawa ita ma matan na ta, sannan akwai wasu iyakoki da ya ke da su. Tallafawa mace da ba ta kwarin gwuiwa suna da ga cikin aikin ibada sai dai idan aikin sabawa Allah ne ta ke yi.

  2. Kula da iyali hakki ne da ya ke kan kowa; mace da kuma miji

  Lallai ya kamata mu sani kula da iyali aiki ne na hadin kai da mata da miji domin samun nasara da nagartar iyali. Aiki ne da kowa ya kamata ya saka hannunsa dumu-dumu a ciki. A bangaren mace, idan aikinki zai hanaki bawa iyalinki lokaci da gudumawar da yakamata, to lallai yana da kyau ki yi nazari a kai sosai ki dauki matakin da zai kai ku gaci duka. Alhamdulillahi yanzu zamani ya kawo mu, mutum na iya aiki daga gida. A gani na idan kula da iyalinki ya kai ga haka mai zai sa ba za ki gwada ba.  Sannan a bangaren namiji kuma shi ne, ka kasance kana jagorancin gidanka da adalci, ka taimakawa matarka ta cimma burinta na rayuwa a cikin halin da take kula da gidanka. Idan har ta samu cikan burinta to gida zai yi dadi kuma da yardan Allah za ku tayar da zuri’a mai nagarta.

  3. Yarjejeniya kafin ayi aure

  Wasu matsaloli da ake samu su ne ba a yin yarjejeniya kafin aure. Idan mace na aiki ko tana son ta yi aiki bayan aurenta to dole ne mijin da zata aura ya sani kuma ya amince kafin aure. Yin haka zai sa dukkanin ma'aurata su shirya kuma su tsara yadda za a yi. Idan aka yi hakan, to da yardan Allah aiki ba zai kawo cikas a rayuwar iyalinku ba

  4. Taimakawa juna wajen ganin kowa ya samu abinda ya ke so daidai gwargwado

  Aure bai zama karshen cika burin juna ba. Ya kamata miji da mata su shiga aure da zuciyar sadaukarwa. Idan zuwa aiki zai dan rage lokaci da matarka ta ke baka a gida ka taimaka mata ta hanyar hakuri da kuma saka hannu wajen da ta gaza domin ta sami sauki wajen cikan burinta. Na tabbata duk macen da mijinta ya kasance mai taimakonta wajen cikan burinta to lallai za ta dauke shi tamkar mahaifi. Domin duk abinda ya ke so shi za ta yi, sai dai idan ita ba macen kwarai ba ce. To haka abin ya ke a gefen namiji ma idan matarsa ta kasance mai goyon bayansa a al’amuransa.

  Babu wani hanyar samun control a kan mata kaman wannan hanyar.

  5. Sanin cewa a rayuwa ba wanda ya hada komai da komai kamar yadda ya ke so

  Da aure ko ba aure ba mu samun dari bisa dari na abinda muke so a rayuwa. Idan ma’aurata suka fahimci hakan to dole wani lokacin su yi hakuri wajen rashin samun wani abinda suke so. Wani lokacin dole ma’aurata su hakura da wani abinda su ke so domin ci gaban iyalinsu.

  6. Abinda ya yi wa wasu magani ba lallai ne ya yi wa wasu ba

  Ma’aurata su yi koyi da rayuwan kwarai na wasu amma ba lallai ne komai da suka gani ya musu amfani ba. Saboda haka ma’aurata su fito da na su customized solution din na matsalarsu, kar su dogara da abinda ya yi wa abokansu ko ma iyayensu aiki. Saboda haka maganar aikin mace ma, ku nemi mafita da ya yi daidai da matsalarku da kuma bukatun iyalinku.

  Kammalawa

  A karshe ina son na jawo hankalin ma’aurata da su sani cewa duk inda aka ga zaman aure ya yi kyau to lallai akwai fahimtar juna da kuma sadaukarwa mai yawa a ciki. Raini da jiji da kai ba sa kawo ‘yanci a aure. Danniya ba ya kawo iko a aure. Tausayi, da sadaukarwa, da taimakawa juna, da kuma selflessness su ke kawo nasara mai dorewa a rayuwar aure. Allah Ya mana jagora akan al’amuaranmu na yau da kullum da ma rayuwar aurenmu, amin.

  Kuna iya duba wata makalata da na dan yi kwarya-kwaryar bincike akan yadda za a shawo kan matsalar da duba wayar miji ke janyowa a gidan aure.

  Hakkin mallakar hoto (photo credit): nohat.cc

Comments

6 comments
 • Auwalu Masha Allah,
  Duk da yakamata in ce wani abu amma bayanan sun isa su gamsar da duk mai bukatar neman haske a kan wannan turka-turkar bisa yadda mashahuriyar marubuciyar ta fidda kalkala da madda a makalar ga shi kuma abin da ya fi birgewa a matsayin ta na...  more
 • Rahmatu Lawan Godiya na ke Mal. Auwal. Allah Ya sa mu dace.
 • Muhammad Zaharaddin A gaskiya rayuwar yau ce ta canza al'adunmu Hakan yasa da Dama Basu Barin matansu suyi aiki,
 • Nura Ahmad Menene al'adun namu da suka canza Muhammad? Ina ganin mu ne dai muka canza ba al'adu ba.