Makalu

Sabbin Makalu

View All

Takaitattun bayanai kan hukunce-hukuncen zakkan fidda kai

 • Fadin Ibn Baaz cewa zakkan fidda kai dai zakka ce da ta rataya a kan wuyan kowani Musulmi, na miji ko mace, yaro ko baba, ‘yantacce ko bawa.  (Fatawa 14/197).

  Me ake bayarwa a matsayin zakkan fidda kai?

  Ibn Baaz ya ce: A na bayar da sa’a (gwargwadon cikin tafin hannu hudu) na abinci, kamar dabino, Sannan kuma da duk wani abinci da aka fi ci a wurin da mutum ya ke da zama kamar shinkafa, masara, dawa da sauransu.

  Menene mudun zakkan wato kwatankwacin awon da ake bayarwa?

  Ibn Baaz ya ce: Ana bada sa’a daya ne na abincin da ake ci a kasa, gwargwadin kilo uku ke nan. (al-Fataawaa 14-203)

  Yaushe ne ake bada zakkar (a wani lokaci)?

  Ibn Baaz ya ce: Ana bayarwa ne a ranakun 28 ko 29 ko 30 na watan Ramadan sannan kuma za’a iya badawa a daren salla ko safiyan sallar kafin sallan idi.
  (al-Fataawaa 14/32-33)

  Menene dalilin da ya sa ake bayar da zakkan fidda kai?

  Ibn ‘uthaymiin ya ce: Ana bayarwa ne don a nuna godiya ga Allah (SWT) na bawa mutum daman ganin kammaluwan azumi da kuma ganin karshen watan Ramadan. (al-Fataawaa 18/257).

  Su wa ake bawa zakkan fidda kai?

  Ibn ‘uthaymiin ya ce: Ana bada wannnan zakka ga talaka ne kawai. (al-Fataawaa 18/259).

  Menene hukuncin wadda ya sa ‘ya’yansa ko wani can daban bayar da zakkan a madadinsa?

  Ba laifi in mutum ya sa ‘ya’yansa su bayar da zakkan a madadinsa in lokacin bayarwa ya yi ko da a wannan lokaci ya na wani kasan na daban don aiki ne. (al-Fataawaa 18/262).

  Shin a kwai laifi in talaka ya sa wani ya karba masa zakkan daga wani wuri?

  Ibn ‘uthaymiin ya ce: Babu laifi a yin hakan. (al-Fataawaa 18/268)

  Shin a kwai wani kalma ko addu’a da mutum zai ce in ya zo bada zakkan?

  Babu wani shaida na cewa ga wani addu’a da mutum ya kamata ya yi in ya zo bada zakkan. (al-Lajnah ad-Daa’imah 9/387)

  Shin mutum na iya bada kudi (gwargwadon mudun zakkan da zai bayar) a madadin abinci a matsayin zakkan fidda kansa?

  Ba ya halatta mutum ya bada kudi a madadin zakkan fidda kai a fadin maluma da dama saboda yin hakan ya sabawa fadin annabin Allah da sahabansa game da shi zakka din (al-Fataawaa 14/32).

  Ibn ‘Uthaymiin ya ce: Bayar da kudi baya wadatarwa saboda an ce a bayar da abinci ne ba kudi ba (al-Fataawaa 18/265).

  Shin mutum na iya ba da zakkan fidda kai a wani kasa daban ba inda mai bayarwa ke da zama ba?

  Sunna dai ita ce mutum ya bayar a kasar da ya ke da zama don ya taimaka wajen wadatar da talakawan da ke kusa da shi ba wa su can a nesa ba. (al-Fataawaa 14/213).

  A ina ake bayar da zakkan fidda kan?

  Ibn ‘Uthaymiin ya ce : Ana bayar da zakkan fidda kai ne a wurin da mutum ya ke a lokacin da aka kammala azumi (wato lokacin karshen watan Ramadan) ko da kuwa wannan wurin ko kasan na nesa da kasan mai bayarwan na asali ne.

  Shin ana bayar da zakkan a madadin dan da ke ciki?

  Ibn ‘Uthaymiin ya ce: Ba lallai ba ne a bayar a madadin dan da ke ciki amma an kwadaitar ainun da yin hakan (al-Fataawa 18/263).

  Shin akwai laifi in an bayar da zakkan ga ma’aikata wadda ba musulmai ba?

  Ibn ‘Uthaymiin ya ce: Ba ya halatta a bawa wani daban da ba talaka musulmi ba (al-Fataawaa 18/285).

  Shin za’a iya rabawa mutane da yawa zakkan mutum daya ko ko lallai sai dai a bawa mutum daya zakkan mutum guda?

  A kan iya rabawa mutane da yawa zakkkan mutum daya sannan kuma za’a iya bawa mutum guda na mutum daya, duk wadda aka yi babu laifi (al-Lajnah ad-Daa’imah 9/377).

  Ya ya hukuncin wadda ya karbi zakkan kuma ya je ya saida shi?

  In har mutumin ya cancanci samun wannan zakka (wato talaka ne musulmi), to ba laifi don ya sayar (al-Lajnah ad-Daa’imah 9/380).

  Ya ya jinkirin bayar da zakkan ya ke sai bayan sallan idi ba tare da uzuri ba?

  Ibn ‘Uthaymiin ya ce: Jinkirin bayarwa har sai bayan sallan idi haramun ne sannan baya biyan bukatan wannan zakkan (wato baya zamantowa zakkatul fitr) (al-Fataawaa 18/266).

  Allah Ya sa mu dace sannan kuma Ya zamanto majibincin al'amuranmu. Ya ba mu ladan ayyukanmu na kwarai sannan ya gafarta mana zunubanmu, Amin. Za a iya duba: Garabasar ranar arafa da sauransu.

Comments

1 comment