Featured Create an Ad

Makalu

Blogs » Kagaggun Labarai » So Sartse: Babi na Daya

So Sartse: Babi na Daya

 • Bismillahir rahmanir rahim.

  Free book ne daga farko har ?arshe kamar yadda na ?aukar wa readers al?awari Insha Allah.

  ?agaggen labari ne ban yi shi dan wata ko wani ba, sai dan ya fa?akar da al'umma ya kuma nisha?antar dasu. Allah yasa zamu amfana da abin da ke cikinsa. Ameen.

  *********

  MAIDUGURI

  Garin Allah ya waye duk kan al'umma sukan ta shi domin fara gudanar da al'amuran yau da kullun, musamman Mata da suke cikin kitchen dan ha?a karin kumallon safe, Ma'aikata na ?o?arin shirin fita aiki, Yara suna ?o?arin shirin tafiya makaranta. Da misalin ?arfe takwas na safe Mubeena ce ke saukowa daga matakalar bene cikin natsuwa, sanye take cikin riga da siket na atamfa, ta sanya dogan hijab mai hannu brown color, tana sanye da takalmi flat shoe rataye da handbag a kafa?arta, fuskarta shafe da powder sai kwalli data sanya a dara-daran idonta wanda ya ?ara fidda kyawunsu, ta shafa lips stick ka?an a bakinta yana she?i, ?amshin turarenta ya gauraye falonsu yayin data kai ga saukowa, ta samu Mami da Baba zaune bisa Cushing mai mazaunin mutum biyu, tunda ta sauko suke binta da kallo fuskarsu ?auke da murmushi.

  "Mubeena har kin shirya kin fito? Kin karya kuwa? ina kika baro Hafsa? fatan ta tashi daga barcin asarar data saba kar tasa kiyi latti"

  Cewar Mami cike da murmushi a fuskarta tana duban Mubeena.

  "Mami zan karya a office, na tada Hafsat da kyar ta tashi, na dai baro ta tana sanya kaya, ina gudun kar na yi latti dan yau ina da shirin da zan gabatar da ?arfe tara na safen nan"

  "Kinga yi tafiyarki karta ?ata miki lokaci, in ta fito sai ta hau napep" cewar Mami.

  "A'a Hajiya ki bari su tafi tare, kinsan Hafsat sai ana ha?uri da halinta, Mubeena yi ha?uri ki jirata Insha Allah ba zaki yi latti ba" cewar Baba yana ?ar dariya.

  "Tom Baba bari na jirata, yanzu ma takwas da kwata da ?an sauran lokaci. Ina tausaya mata ne dan samun abun hawa da safen nan akwai wuya kuma..."

  "To ki tafi mana ?in sai me, Baba nima ya kamata a siya min mota na huta da ?orafin Anty Beena"

  Cewar Hafsat lokacin da ta sauko daga matakala, ta katse maganar Mubeena.

  "Kin ci gidanku na ce, daga saukowarki zaki fara da rashin kunya ko? maza zo ki wuce kan in ?ata miki rai"

  Baba ya ce da fa?a cikin harshen kanuri.

  Turo baki Hafsat ta yi tana gunguni rai a ?ace, ta rasa me yasa su Baba ke nuna banbanci tsakaninta da Mubeena, cikin ?aure fuska ta gaishe su, suka amsa ba yabo ba fallasa. Baba ya ciro ku?i a aljihunsa na gaba ya ?irga dubu biyar ya mi?awa Mubeena.

  "Mubeena ga shi, dubu uku kisa mai a mota dubu biyu ki ri?e na abinci, dan nasan zaki iya kaiwa yamma baki dawo ba"

  "Ke kuma Hafsat ga dubu biyu nan ki ri?e"

  Mubeena ta amsa tana godiya sai ta yiwa musu sallama ta wuce, Hafsat kuma ta tsaya akan sai Baba ya ?ara mata ku?i zata siya handout.

  "Hafast bana son wannan ba?in halin da ki ka hudo da shi Mubeena ?ar uwarki ce fa, amma ki rasa wacce zaki kishi sai da ita, tun wuri ki sauya hali kafin na sanya ?afar wando ?aya dake. Maza ki bace min da gani kanna sa?a miki sha-sha-sha kawai, kuma bari Hamman ku Hafiz ya dawo saina fa?a masa"

  Cewar Mami fuska ?aure, Hasat ta fita tana kukan shgawa?a tare da buga ?afa a dole ranta ya ?aci.

  Mai gadi ya bu?ewa Mubeena gate ta fitar da mota ya kulle gate, ta yi parking tana jiran fitowar Hafsat, ta jin gina bayanta jikin kujera ta sauke glass ?in motar ta sha?i iskar gari, ta soma kallon Mutane masu wucewa a motocinsu da ?ai-?ai ku masu tafiya a ?afa kasantuwar unguwar ce new GRA ta masa hannu da shuni, babu cikowar Mutane kowa na harkan dake gabansa. Wani Saurayi ta hango nesa ka?an daga tsallaken gidansu, zaune yake a ?ar?ashin wata bishiya, yana sanya cikin ?ananun kaya T-shirt fara da wando jins blue, sai tarin suma a kansa a du?un?une ba gyara, ga ?aramin gana mazgo a gefensa idonsa ya ramba?a kwalli, kallonsa take cike da tausayi sabo da tarin dau?ar da ta hango a jikinsa wanda bai ?oye tsantsar kyawunsa ba, ga wata hamma da yake ta saki yana hangame baki harda gutun hawaye da yaje fita a idonsa, hakan yasa ta soma tunanin ba?o ne ba?auye kuma yana cikin jin yunwa, ta da?e tana kallonsa ta na nazarinsa shi kuma ga duk kan alamu bai san da tana kallonsa ba. Hafsat ce ta fito daga gida ta bu?e ?ofar gefe ta zauna, Mubeena ta kalleta a nutse.

  "Little ya dai kin gama rikicin?"

  Ha?e fuska ta yi tana cin Magani, hakan ya bawa Mubeena dariya sai ta tayar da motar suka fara tafiya. Mubeena haka nan taji tana son ?ara kallon fuskar wannan ba?on, tazo gab da zata gifta shi sai ta kalli ?angaren da yake zaune, tsaraf suka ha?a ido sai ta yi sauri ta mai da kallonta kan hanya, ba?on ya cigaba da kallon motarsu har suka fice a layin.

  Wucewar su ba jimawa Baba ya fito a mota da nufin zai tafi wurin aiki, har ya gota wannan ba?on sai ya ja burki ya tsaya yasa hannu ya kira shi, cikin sanyin jiki ya mi?e ya ?auki jakar gana mazgo ?insa ya nufi motar Baba, kafin ya ?araso Baba ya ?are masa kallo yana tantance yanayinsa.

  "Bawon Allah lafiya ka zauna a nan? akwai babban hatsari zamanka a wannan unguwa saboda muna da security. Tun a daren jiya na wuce na ganka, sannan da Asubahi da zani masallahi na ?ara ganinka, hakan ya tabbatar min da a nan wurin ka kwana, lallai ka hanzarta ka tafi"

  Saurayin ya yi rau-rau da ido kamar zai fidda kwalla, damuwa ya bayyana ?arara a cikin kwayar idonunsa.

  "Alhaji ni ba?one daga ?aramar hukumar Gaji~Garna, nazo wurin ?an uwana ne da ya yi min alkawarin zai sama min aiki a nan, sai dai na yi ta kiransa wayarsa baya shiga, kwana na biyu a garin nan ina ta galantoyi amma bansan ina na nufa ba, ku?in guzurina ya ?are banda inda zani bansan kowa ba, kusan tun jiya da rana rabona da abinci"

  Ya ?arasa maganar yana matsar kwalla. Baba ya yi matu?ar tausaya masa sai ya sauke ajiyar zuciya.

  "bawon Allah ya sunan ka?"

  "suna na Mansoor Khalid"

  Ya ba shi amsa a gaggauce.

  Baba ya girgiza kai sai ya ciro wayarsa ya danna number mai gadi, bugu biyu ya ?auka.

  "Ka fito waje ka sameni ina jira ka"

  Bai jira amsarsa ba ya kashe wayar. Minti biyu sai ga mai gadi ya ?araso.

  "Yalla?ai gani"

  "Yauwa Buba, wannan Saurayin nake so ka ba shi masauki a ?akinka kafin zuwa yamma na dawo, ka shiga wurin Hajiya ka amso masa abinci, yanzu zan kirata a waya na sanar mata, zaku iya wuce wa"

  "Nagode, nagode Alhaji, Allah ya ji?an mahaifa ya ?ara bu?i"

  Cewar Mansoor ya ?arasa maganar yana hawaye, Baba ya amsa Ameen a zuciyarsa ya kunna mortarsa ya wuce. Mansoor ya bi bayan motar Baba da kallo yana yaba karamcinsa a ransa, ya rungume gana mazgo ?insa ya bi bayan mai gadi suka shiga cikin gidan.

  Baba ya tafi yana jin-jina halin rayuwa, ya tuno da irin wahalar rayuwa da ya sha a baya kafin ya tsinci kansa a cikin wannan daular, a kullun yaga na ?asa da shi koya ga wani yana cikin talauci yakan zubda kwalla ya yiwa Allah godiya bisa ni'imonin da ya yi masa da yin Addu'a ga wanda yayi silar arzikinsa, shiyasa ya kasance mai jin ?ai ga duk na ?asa da shi musamman ba?o, domin shima ta wannan tushen ya samu kafar arzikinsa, bai gajiyawa wurin sanya dariya a fuskokin mutanen da suke cikin ?uncin talauci.

  "Allah ka bamu Arziki daga halaliyarmu ka haramta mana cin haram ko ha??in waninmu, ka bamu ikon ri?e amanar kanmu da amanar wanin mu. Ameen"

  Cewar Baba a fili ya yin da ya dawo daga gajeran tunanin sa, a haka ya isa kamfaninsa yana mai nazarin rayuwa.

  ****** ******

  Mubeena ta sauke Hafsat a makaranta ta wuce wurin aiki, tana isa ta yi parking tabi hanyar da zai sada ta da babban ofis ?insu da yake ?auke da mutane goma a ciki Maza da Mata, table da kujeru ne kusan goma a ciki ko wanne ?auke da computer tv tare da takardu masu yawa, aiki suke ba kama hanun yaro, Mubeena ta shiga da sallama duk suka amsa tare da mi?a musu gaisuwa, Fanna ce ta saki aikinta ta iso wurin Mubeena da sauri.

  "Oyoyo ?awata hajiyar latti yau ma halan Hafsat ce ta saki kika makara?"

  Cewar Fanna tana murmushi tare da kama hannun Mubeena alamar gaisuwa.

  "Uhum ai zancen gizo bai wuce da ?o?i lamarin Hafsat sai ha?uri, bari na isa ?akin gabatar da shirina, halan Dr. Faisal ya iso?"

  "Aiko tun ?azu yazo, ki hanzarta ki shiga ki kimtsa kafin director yazo ya fara masifarsa duk da dai ke ta gaban goshinsa ce"

  "Uhum haka dai kika ce"

  Cewar Mubeena sai ta wuce tana murmushi, jaka ta ajiye saman table ?inta ta fita ta shiga ?akin kimtsawa ta shirya, kafin ta isa ?akin da zata gabatar da shirin ta na kiwon lafiya, wanda take yinsa kai tsaye a duk ranar monday da ?arfe tara na safe tare da gayyato likitoci dan zantawa dasu. Ta gaisa da Dr. Faisal ?arfe tare dai-dai aka ?aura musu cemara ta fara gabatar da shirinta cike da natsuwa da bayanai masu gamsarwa.

  Sai ?arfe goma ta ?are shirin tana fitowa Fanna ta jata zuwa restaurant dake kallon office ?insu dan su ci abinci.

  "Nima kin fara koya min halinki, sai in fito daga gida ba tare da na ci komai ba, nasan ko babu tambaya baki karya ba"

  Cewar Fanna. Murmushi kawai Mubeena ta yi mata dan da yawan lokuta magana bai cike damunta ba. Fanna ?awarta ce tun a makarantar sakandiri wanda suka ci burin yin karatun Mass communication a nan university of Maiduguri. Cikin ikon Allah suka samu aiki a NTA tv Maiduguri a lokaci guda, sunyi bautar ?asa a nan sabo da kwazonsu sosai aka ?auke su aiki. Fanna jin shurun Mubeena yasa ta yi shuru dan tasan ba lallai ta bata amsa ba, tunda ba yau tasan halinta na miskilanci ba.

  ***** *****

  Sai bayan la'asar Mubeena ta dawo gida, wanka ta fara yi ta gabatar da sallah kafin ta fito falo sanye da ?ananun kaya riga da wando ta yane kanta da ?aramin gyale, ta samu Mami zaune bisa cushing tana ?irga ku?i, Mubeena ta zauna tana yatsine fuska saboda irin ?ugin da cikin ta ke mata sabo da yunwa.

  "Mami mai aka girka ne yau dan da yunwa na dawo"

  Mami tana jinta bata tanka mata ba sabo da hankalinta yana kan ku?in da take ?irgawa.

  "Da?ina da ke Mami in aka zo kan lamarin ku?i gaba ?aya ki ke bada imaninki a kansu, na yi magana kin ji ni amma kin kasa bani amsa"

  "Ubanki na ce, in ban natsu na ?irgasu da kyau ba ai ban nuna musu soyayyar da ya dace ba, sannan kinsan hanyar kitchen meyasa baki je kin duba ba"

  Ta yi maganar cikin masifa.

  "Uhum kai Mami daga magana to ki yi ha?uri, ina Hafsat ban ji ?uriyarta ba"

  "Oho mata har yanzu bata dawo daga makarantar ba"

  "Amma Mami gaskiya kina nuna sakaci akan Hafsat, ya kamata kina tsawatar mata"

  "Kin ga Beena wallahi zan ci miki mutunci maza ta shi ki bani guri, tun ?azu sai ?atar dani kike ?irgan ku?in nan. Sannan ke da Hafsat ku ba Yara bane, iya tarbiyya na baku banga dalilin da zai sa na ri?a damunka kaina akan ku ba, ai kuna da hankali ba zan zauna ina mitar abu guda ba. Kuma ki tashi ki duba min miyata a kitchen karta ?one, Bintu ta?i dawowa daga cewa tafiyar kwana uku ga shi har kwana bakwai yau"

  "Uhum ai Mami da ke da Hafsat kuke koran ma'aikatan gidan nan, ke yawan mita da ?orafi ga fa?a, ita kuma Hafsat wula?antasu take, ga shi nan ko driver bamu da shi sun tafi, masu aiki kusan uku kenan suka gudu"

  Ta ?are maganar tana nufar kitchen. Taki Mami ta yi ta cigaba da abin da take yi. Murmushi Mubeena ta yi ta wuce kitchen tana tunanin hali irin na Maminsu, mugun son ku?inta har yana bata tsoro sam bata kulawa da su, tana kaffa-kaffa da ku?i kamar tana yunwarsu kuma dai-dai gwargwado Allah ya rufa musu asiri sosai suna da arzikinsu. Ta duba mata miyar ta fito ri?e da plate ?auke da jelof ?in taliya wanda yaji kayan lanbu tare da gorar swan, ta samu cushing ta zauna ta soma ci.

  Hafsat ne ta shigo ko sallama babu ta yiwa Mami sannu da gida tana niman haurawa saman matakalar bene.

  "Ke ya zaki shigo mana falo kamar gidan kafurai, kuma daga ina kike? Ina tunanin yau ?arfe biyu kuke ta shi lectures me kika tsaya yi a makarantar?" cewar Mebeena fuska ?aure.

  "Ban sani ba, Malama ki daina sawa rayuwata ido kin ji, kuma da kike maganar daga ina nake to daga yawon tazubar nake, rayuwarki ko tawa?" sai ta ja tsaki ta wuce tana ?ananan magana.

  Mubeena ta girgiza kai ta aje plate ?in abincin ta bi bayan Hafsat, ta sameta tana cire kaya da alamun wanka zata shiga.

  "Hafsat don Allah karki jefa rayuwarki cikin hatsari yana da kyau ki gane ke Mace ce mai daraja wacce Allah ya karramata, ji yadda kika shigo gida kamar..."

  "Kamar ina warin najasa ko? to abun nayi sai me jikinki ko nawa naga dai rayuwar da kowa ya za?a zai iyi yinsa a gidan nan"

  Cewar Hafsat a tsawace ta katse Mubeena cikin maganarta.

  Sakin baki Mubeena ta yi, tana kallonta cike da mamaki, bata ta?a tunanin lamarin Hafsat ya kai nan ba, sam bata ganin girmanta a matsayinta na Yayarta, ta raina ta bata jin kunyar fa?a mata duk abin da yazo bakinta, Mami tana sane kuma bata cika tsawatar mata ba, yanzu ma ga shi a gabanta suka fara magana amma sabo da hankalinta na kan ku?i bata tanka musu ba.

  "Malama ki fita min a ?aki ki kama kanki, kuma kar ki fasa ?ulla min sharrin a wurin Hamma Hafiz da Baba, wallahi zan ?auki mataki akan ki"

  Cewar Hafsat ta ja tsaki ta shige toilet tana kar ka?a jiki, Mubeena ta bita da kallon mamaki sai ta juya jiki a sanyaye ta bar ?akin.

  ********

  Rahma ce

No Stickers to Show

X

Da Dumi-Dumin Su

 • Ku latsa nan don karanta labarin Saurin Fushi Na Kawo Da Na Sani. A wani ƙauye akwai wani mutum  ana kiran sa Abu Sabiru, ya kasance mai tsananin haƙuri da kawar da kai akan wasu al’amura. Dalilin da ya sa ma ake kiransa Abu Sabiru kenan. Yana zaune tare da matarsa kyakkyawar gaske ...
 • Ku latsa nan don karanta darasin rana ta uku. DARASI NA 1 Matakan rubutun gajeren labari A jiya mun yi bayani akan matakan da ake bi wajen tsara labari, yau kuma za mu bayani a takaice kan matakan da ake bi wajen rubuta ingantaccen labari. Waɗannan matakai ba tabbatattu ba ne, ma'ana ba wajibi ne...
 • Ku latsa nan don karanta babi na shida. Habeeb na kwance a kan doguwar kujera ya ji an murɗa handle ɗin ɗakinshi tare da turo ƙofar a hankali. A hankali ya buɗe idanunsa da suka yi nauyi sakamakon ciwon kan da yake fama da shi. "Fateemah" ya faɗa a ransa, lokacin da ya kai duba ga Jummai da ke ts...
 • Mon at 1:39 PM
  Posted by Bakandamiya
  Uwargida ba za ki yi dana sanin koyan yadda ake yoghurt in fruits ba. Domin kuwa kayan dadi ne sosai da sosai kuma cikin mituna kalilan za ki hada. Ba a ba yaro mai kiwiya!!! Wannan recipe yana daya daga cikin recipes da muka koyar a zauren Free Ramadhan Classes with Umyuman a nan Bakandamiya. Abu...
 • Hadin special salad nawa na musamman ne! Ga sauki ga dadi, uwargida sai kin gwada za ki bani labari! Wannan ma yana daya daga cikin recipes da muka koyar a Ramadan a shirin girke-girkenmu wadda aka gabatar a zauren Free Ramadhan Classes with Umyuman. Shin ko kin tuna gashin tsokar kaza da muka koya...
 • Red velvet cake, cake ne da mutane da dama suke so kuma kuma suke son ci. Saboda haka, akwai hanyoyi daban-daban na yin red velvet cake, ga yadda na ke nawa cake din na kawo muku. Wannan yana daya daga cikin recipes da muka koyar lokacin Ramadan anan Bakandimya. Domin ganin duk jerin recipes din da...
View All