Makalu

Da Iyayena

 • Tsaye nake ina kallon saman rufin ɗakinmu, na shiga tunanin yadda muka kwana cikin saukar ruwan sama, kasantuwar muna cikin yanayi na marka-marka, har zuwa gabanin sallar asubahi kafin ya tsagaita. Ruwan da ya ƙare akanmu, ɗakin da muke ciki kwanon ya buɓɓule ruwa ko'ina yake zuba ya jiƙa duka shinfiɗarmu, a tsugune muka kwana wasu kuma a tsaye, a haka muka kasance har garin Allah ya waye ya yi tangaras, sanyi ya gama ratsa duk illahirin sassan jikinmu, in da sabo mun riga mun saba da wannan rayuwa mai cike da ruɗani, haka muka fito daga cikin ɗakin tsamo-tsamo kowa ya kama gabansa babu wanda ya yi yunƙurin yin sallar asubahi ko neman sanya tufafi.

  Zama na yi akan dakalin dake gefen ɗakinmu, na yi tagumi hannu bibbiyu, tun ina ɗan shekara bakwai ban san ya duniya take ba ban san ina na dosa ba amma da garin Allah ya waye abu biyu nake fara tunani. 

  'Shin ta wace hanya zan samu abin karin kumallo?'

  Har kawo iyanzu da shekaruna ya kai sha biyar tunanina kenan, sai kuma tunanin Iyayena da kullum yake cika min zuciya.

  "Shin anya iyayena suna kaunata kuwa?"

  Tambayar da ba ni da amsarta, wasu siraran hawaye ne suka sauka a kuncina, na sanya hannu na goge, sai na kuma tambayar zuciyata.

  'Shin ta wace hanya zan samu kuɗin da zan ciyar da kaina?'

  Domin a irin wannan lokaci ba lallai na samu abincin kalaci a gidajen mutane ba, musamman da unguwar ta kasance na talakawa suma rayuwar suke hannu baka-hannu kwarya. Ɓangaren unguwannin masu hannu da shuni kuwa, a irin wannan lokaci ba kasafai suke ta shi barci da wuri ba, musamman yau da ta kasance ranar hutun ƙarshen mako.

  "Ni Ashiru yaushe zan zama cikakken ɗa mai ƴanci kamar yadda sauran ƴaƴa suke zaune a gaban Iyayensu cikin gata?"

  Na tambayi kaina a fili, *DA IYAYENA*, na zama tamkar maraya wulaƙantacce a idon duniya, banda sauran gata, ni ke kula da tarbiyyata da abincina, ina nan ina gararamba a wata duniyar da babu dangin iya ba na Baba, domin biɗar abin da zan sanyawa bakin salatina, sabulun wanki da sutura, babu mai kula da lafiyata, na ci ko na sha babu mai tambayata, kuma  Iyayena suna raye, suna can wata duniya ina nan ina garari a wata nahiya mai cike da rudani.

  "Ko ta yaya zan mayar da hankalina na yi karatu cikina babu yaɓa, yaushe Iyayena zasu waiwayeni susan halin da nake ciki?"

  Na tambayi kaina a fili babu amsa. Shi kansa Malam Tanimu in mun samu abun amfani amshewa yake yi, mun yi masa yawa babu yadda zai iya kulawa da tarbiyyar mu, kuma kullun rana sai an kawo sabbin yara ƙanana don yin karatun Allo, ba kuma ya fasa karɓansu. Iyayenmu sun kawomu Almajiranci sun yasar wa duniya ta raine mu, basa waiwayenmu balle susan halin da muke ciki. 

  Na sauke gauron numfashi, na miƙe tsaye domin zama bai ganni ba da hutun jaki da kaya a kai, na wuce dan samawa kaina mafita kafin cikina ya soma ƙugin yunwa, sannan ƙarfe goma na safe muna da darasu, in ban dawo kan lokaci ba, na ci baƙin duka wurin manyan Almajirai masu kula da mu.

  Tafiya nake ban san ina na dosa ba, kusan hankalina baya jikina, a haka har na isa wata unguwa ta ƙun-ƙun Talakawa, na hangi yara a bakin wani kwazazzabon rafi, da sauri na isa gurin na taras da wasu yaran suna ciki suna tsamar yashi, wani guntun murmushi na saki dan tsantsar murnar samun mafita da na yi a nan take, sai na cire rigar jikina na aje akan wani dakalin wani gida dake gefen rafin, na naɗe ƙafar wandona naje na shiga cikin rafin na soma tsintar kayan tsaɓi, danginsu gwangwani, ƙarfe da sauran kayayyaki da ake samu a cikin kwatami ko rafi na tsaɓi. Lokuta da dama wayon da nake yi kenan a cikin unguwanni, dan samun tsaɓi na siyar na samu kuɗin siyan abinci, sabulu da ƴan ƙananun abubuwa da zan iya siyawa kaina.

  Minti biyar da shigata na soma tsince-tsince, tsautsayi baya wuce ranarsa, banyi aune ba na taka wata kwalba ta shige min cikin ƙafata ta yi min mugun yanka, a gigice na tsandara wani irin ihu saboda tsabar azaba dana ji ya ratsa kwanyata, ihun da ya gigita yaran da suke tsamar yashi suka saki cebur suka arce a guje, cikin hanzari na tsuguna na kai hannuna wurin tafin ƙafata na fincike kwalban da ƙarfi, jini kawai yake fita wanda har ya fara sauya kalar ruwan rafin daga in da nake tsaye, cikin hanzari na fito daga kwazazzabon rafin na je na zauna a dakalin dana aje rigata, hawaye ya gama wanke fuskata, na ɗago ƙafata ina kallon yadda na yanke, hankalina ya yi matuƙar tashi, na kuma ɓarkewa da sabon kuka wiwi, na tsorata sosai musamman yadda naga jini yana fitowa daga gurin yankar, duk na ɓata jikina, rigata na ɗauka na ɗaure ƙafata, minti biyar baya na ji wani irin sanyi yana ratsani, zazzaɓi yana barazanar rufeni wanda na ta allaƙa shi da tsabar firgicewa ce.

  Wani Dattijo ne na hango yana tafiya a nutse har ya wuce ni sai ya tsaya, yana kallona cike da tausayawa, ya shiga tambaya ta.

  "Kai yaro me ya sameka jikinka duk jini haka?"

  "Yankewa na yi da kwalba a cikin rafi naje tsintar tsaɓi"

  Na ba shi amsa cikin rawar murya a gaggauce.

  "Subhanallahi! yaro meyasa ba kwa tausayin kanku, haka kawai ku jawowa Iyayayenku masifa a yadda muke fama da wannan rayuwa na halin babu, yanzu ina gidanku yake?"

  "Ba ni da gida a nan sai..."

  Na ba shi amsa ina shasshekar kuka.

  "To ina Iyayanka suke ko sun rasu ne?"

  Dattijon ya katse ni da tambaya cikin ɗaga murya.

  "Da Iyayena, amma basa tare da ni, ni Almajiri ne"

  "Wace Makaranta kake?"

  "Makarantar Malam Tanimu na kan kwana"

  Dattijon ya girgiza kansa cike da tausayawa ba tare da ya ce komai ba, ya juya ya tsayar da wani ɗan acaba ya matsa kusa da shi ya yi masa kwantance, ban san yadda suka yi ba, Dattijon ya dawo gareni ya umarceni da na miƙe ya taimaka min har zuwa gurin ɗan acaba na hau mashin kana ya ce.

  "Ka kai shi chemist ɗin Nuhu dake kan hanya, ina biye da ku a baya"

  Ɗan acaba ya amsa da to, ni dai ban iya cewa komai ba saboda ni kaɗai na san irin azabar da nake sha, a haka muka wuce ina makyarkyatar sanyi. Da isarmu ɗan acaba ya taimaka mini muka shiga cikin chemist ɗin Nuhu na zauna bisa benci, ɗan acaba ya yi masa bayani ina jinsu ban iya tankawa ba, Nuhu ya kwance rigar dana ɗaure ƙafata yana ɗigar jini ya shiga duba inda na yanke, tunda naga yana girgiza kai nasan ba ƙaramin rauni na yi ba.

  "Subhanallahi! wannan yankar ya shigar ciki sosai"

  Ban iya cewa komai ba saboda tsananin azabar da yake ratsa kwanyata, kuma hakan ya yi dai-dai da isowar Dattijon nan, ya gaisa sa Nuhu ya shiga koro masa bayanin abin da ya faru, cikin jimami Nuhu ya ce.

  "Baba ina ga sai kun dangana zuwa babban asibiti saboda yankar ya shiga ciki sosai kuma ya zubar da jini"

  "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, yaro ka taimaka ka ɗanyi masa wani abu, a yanzu haka daga ni sai naira ɗari biyu, nima taimakonsa na yi, in yaso sai nasa ɗan acaba ya kai shi can makarantar su"

  Nuhu ya jinjina lamarin ya ɗago kai ya kalle ni cike da tsantsar tasauyi.

  "Shi kenan bari na yi masa allurar kashe zafi dana tetanus"

  "Yauwa nagode Allah ya yi maka albarka, kai ma ka yi taimakon musulunci"

  Nan Nuhu ya yi duk taimakon da zai iya min, ina kallonsu ni ka ɗai nasan azabar dana ke sha, yaƙi taɓa ƙafata a cewarsa babu abin da zai iya min a kai iya ka allura da magani daya bani, nan take na ji tashin zuciya, a sannan ne yake tambaya ta ko na ci abinci? bayan ya gama allurar, na girgiza masa kai alamar a'a.

  "Subhanallahi ai da banyi maka allurar ba sai ka ci wani abu. Baba a sama masa abinci ya ci, sai ka bar kuɗinka ka siya masa abincin, na yi masa komai a kyauta"

  Ya ƙare maganarsa yana duban wannan Dattijo. 

  "Nagode sosai Allah ya ƙara rufa maka asiri duniya da lahira"

  Cewar Dattijo cike da tsantsar farin ciki, haka ya taimaka min na miƙe tsaye muka fito ina ɗingishi ya azani bisa mashin, ya miƙawa ɗan atsaba ɗari biyu.

  "Ka cire naira ɗari, sai ka tsaya a hanya ka siya masa ɗan wake a rumfar Jimmala sai ka wuce da shi makarantar Malam Tanimu ka yi masa bayani"

  Ɗan acaba ya amsa yana godiya, na ɗago kai na kalli wannan Dattijon na ce cikin rawar murya.

  "Baba nagode Allah ya saka da alkhairi"

  "Babu komai yaro Allah ya baka lafiya"

  Na ce Amin kana ɗan acaba ya wuce dani ina kukan zucci.

  ******

  Bayan mun isa makarantarmu ɗan acaba ya tsaya ya saukeni ya taimaka min zuwa kan dakali na zauna ina nishi, ya hango malaminmu cikin wata baranda ya isa wurinsa ya risina suka gaisa ya shiga ba shi labarin komai kamar yadda Dattijo ya umarce shi, malaminmu ya yi masa godiya ya wuce. Malam ya taso ya tawo inda nake zaune tare da wani babban Almajiri mai suna Sani, suka tsaya a kai na.

  "Dan ubanka ina ka je ka ji wannan ciwon?"

  Sani ya jefa min tambaya wanda ya hautsina min ciki, saboda ina tsananin tsoronsa, na kasa ba shi amsa ina rawar baki.

  "Kaga ja irin yaro, ba tambayarka ake ba ka yi shuru?"

  Cewar Malam yana daka min tsawa, kuka na fara yii ban iya furta komai ba, wani wawan mari Sani ya sakar min sai da na ga taurari biyu, ban gama dawowa hayyacina ba ya dunƙule hannu ya sakar min ƙola a kai, a zabure na dafe kaina na saki gigitaccen ihu saboda raɗaɗin azabar daya ratsa kwakwalwata.

  "Uban wa zaka yiwa kuka, ko wani ya aike ka? Ai jiki magayi kuma ka sani sisina ba zai yi ciwo ba, ubanka zan kira yanzu ya zo ya ɗauke ka ya kai ka asibiti, sha sha shan yaro"

  Malam ya faɗa a hasale yana tusa hannu a aljihun rigarsa yana lalubar wayar nakia ɗin sa, ya ciro ya lalubo number Mahaifina ya danna wajen kira, bugu ɗaya ya ɗauka suka gaisa ya shaida masa halin dana ke ciki, ban san amsar da babana ya ba shi ba na ji dai Malam yana faɗar.

  "Sai ka zo ɗin Allah ya kawo ka lafiya"

  Daga haka suka yi sallama ya sauke wayar, bai cemin uffan ba ya wuce yana gyara babban rigarsa, Sani ya rufa masa baya.

  ******

  Haka na kwana cikin azaba babu wanda ya damu dani, na zama abin kyama cikin ƴan uwana Almajirai, duk sunƙi kwanciya kusa dani saboda warin da ƙafata ta fara yi, ba komai a cikina tun ɗan wake dana ci da safe ban ƙara cin abinci ba, har zuwa wayewar gari. Haka na rarrafo na fito daga ɗakinmu dan bana iya taka ƙafar saboda ta kubbura sosai, na zauna bisa dakali ina mai da numfashi, babu sallah balle na samu halin yin wanka, a yanayin dana ke ciki dabba ta fini daraja, dan ita in aka turke ta guri guda ana bata abinci da ruwa, ni kuwa ba ni da wannnan gatan. In da mutum yana iya fidda kukan jini lallai dana fidda saboda irin azabar dana sha a rayuwata, da kuma wuya tana kisa dana jima a barzahu. Haka na kwanta bisa dakalin ina fidda numfashi da kyar yunwa ta gama galabaitar da ni, ga jikina da ya yi mugun zafi mutuwa kawai nake jira ta ɗaukeni, tun ina jin hayaniyar mutune har komai ya ɗauke min ɗif kamar an ɗauke wutar lantarki, ban kuma sanin duniyar dana ke ciki ba sai da na farka na ganni bisa kan gadon asibiti, an ɗaura min ruwa ga ƙafa ta lulluɓe da bandeji.

  Na juya fuskata gefe ina kallon mutanan dake kai na, naga Malam tare da Mahaifina sai Sani, duk suna tsaye sunyi jugum-jugum da tsammanin farkawata. Siririn hawaye ya shiga gangarowa a kunci na, yanzu na fahimci cewar suma na yi aka kawoni asibiti, ashe har Mahaifina ya zo bana cikin hayyacina. Mahaifina ya matso jikin gadon yana cewa.

  "Sannu Ashiru ya jikin naka?"

  Na kau da kaina fege ina nishin kuka, kwata-kwata bana son ganin fuskarsa, a yanzu ina tantamar anya ba shi ne asalin mahaifina? sakamakon irin yadda ya ɗaukeni ya kawoni karatun Almajiranci babu wata kulawa ta iyaye an maisheni mara galihu. Kuka mai sauti na ɓarke da shi sosai, wanda yajawo hankalin mutanan dake cukin ɗakin, na shiga cewa.

  "Ni nasan ba ni da sauran gata dan bani da kowa a duniya, dan Allah Baba ka ɗaukeni ka kai ni gurin asalin iyayena ko ƙila zan samu gata a gunsu"

  "Kai dan ubanka ni kake gayawa haka? kana cikin hankali na kuwa?"

  Cewar Babana cikin masifa.

  "Ai Mal. Hadi na gaya maka Ashiru ya zama ɗan iska, baya tsayawa ya yi karatu sai yawo da rashin ji"

  Cewar Malam yana gayawa Babana haka. Na ɗago jajayen idona ina kallon Malam cike da mamakin ƙaryar daya shinfiɗa a kai na.

  "Mal. Tanimu ta yaya zaka barshi yana wannan rayuwa, ku riƙa hukunta shi da kyau. Wannan shi ne kaɗai gatan da zan iya baka, in zaka tsaya ka yi karatu to, in kuma iskanci ka zaɓarwa kanka to ka sani sai dai ka sauya wani uban ba dai ni ba"

  "Baba anya kana tausayina?"

  Sani ne ya gwaɓe min baki yana sababin faɗa, wasu mata da suka shigo dubiya ɗaya ta matso kusa damu.

  "Bai kamata ka bigeshi ba, ka sani ko raɗaɗin ciwo ya sanya shi faɗar haka? ya kamata ku yi masa uzuri"

  Matar ta ce tana jan kujera ta zauna a gefen gadona, tana ƙare min kallo cike da tausuyi. 

  "Ai Hajiya yaron nan ɗan iska ne, baya jin magana baki ga rashin kunya yakewa Babansa ba"

  Cewar Malam cike da jin haushi. Hajiyar ta yi murmushi ta kalleni.

  "Ya sunan ka?" 

  "Ashiru"

  Na bata amsa.

  "Meyasa kakewa Baban ka rashin kunya, anya kana so ka yi albarka kuwa?"

  Na fashe da kuka mai tsanani.

  "Hajiya zaki iya aika ɗanki Almajiranci tun yana ɗan shekara bakwai, baki san cinsa ba da shansa ba, ɗanki ya koma tamkar marayan da ba yi da Uba da Uwa, kin sakarwa duniya ta ba shi tarbiyya?

  To wannan shi ne abin da Mahaifina ya min, ina ce a kawai Almajiran da iyayensu suka basu kulawa tare da yawan kawo musu ziyara, sannan Malaminsu yana kulawa dasu sosai tare da basu abinci mai kyau,  to ni wannan gatan na rasa"

  Haka na cigaba da bata labarin rayuwar da nake ciki, tun da na fara sanin ciwon kaina har zuwa yau dana farka na ganni a asibiti, kuka nake kamar raina zai fita duk mutanan ɗakin sai da suka taya ni kokawa, ƙarar fanka ne kawai ke tashi tare da sautin kukana. Hajiya ta goge kwallarta ta kasa cewa komai, sai da na ɗauki minti goma ina kuka kafin Hajiya ta shiga lallashina da kyar na iya yin shuru ina mai da numfashi. Hajiyar ta juya tana kallon Mahaifina da ya yi shuru kamar ruwa ya cinye shi, Mal. Tanimu sai zare ido yake saboda yaji kunya sosai, Sani kuma sunkuyar da kai ya yi ƙasa yana muzurai duk sun kasa ƙaryata zance na.

  "Ni sunana Hajiya Zainab, mataimakiyar shugabar ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam na jihar Kaduna, mun kawo ziyara wannan asibitin Dutse domin mu bada tallafi ga gajiyayyu. A gaskiya jikina ya yi sanyi. Ya kamata iyaye mu sani, ƴaƴanmu amana ce da Allah ya danƙa mana, kuma a ranar gobe ƙiyama sai mun amsa tambayoyi game da yadda muka riƙe su. ƴaƴanmu sune manyan gobe, muddun muka tauye rayuwarsu tun suna ƙanana, tofa gaba mu ne za muyu kuka dasu, yadda muka basu tarbiyya haka suma zasu bawa nasu ƴaƴa da ƙannensu tarbiyya, mu riƙa sara muna duban bakin gatari. Kai kuma Malam a gaskiya akwai gyara a lamarinka, Malamai nawa ne suke kula da tarbiyyar Almajirai, yaro harya girma hannunsu gwanin sha'awa, saboda basa haɗama suna amsar adadin wanda zasu iya ne, sannan a gidansu ana dafa abinci da za a rabawa yara su ci. Meyasa kai ba zaka zama irinsu ba?

  Dan Allah mu gyara mu tuna cewa duk abin da muke yi Allah yana ganinmu kuma akwai ranar da zamu tsaya a gabansa mu amsa duk abin da muka aikata walau alkhairi ko sharri. Dan haka ni na ɗauki alƙawarin zan sanar da manyanmu domin ku samu tallafin da za a yiwa kamarantar ku gyara da kuma sadakar abinci".

  Haka Hajiya ta yi ta jero bayani, daga ƙarshe ta ɗauki nauyin karatun boko na, ta ciro kuɗi masu kauri ta bani kyauta, ta amsa number Mal. Tanimu da alƙawarin zata kira shi, haka suka yi mata godiya sosai kafin suka tafi.

  Sati na ɗaya a asibitin dutse aka sallame ni, Mahaifina ya wuce da ni garinmu Birnin Gwari dan na ƙarasa jinya ta a can.

  ******

  Watana guda a garinmu a lokacin na ji sauƙi sosai, na ga gata gurin iyayena musamman Mahaifiyata da tun farko da ta nuna rashin amincewarta a kai ni Almajiranci, lokacin da ta ganni tare da Mahaifina ya dawo dani har kuka ta yi ta tausaya min sosai, yanzu ga shi har wani ɗan ƙiba na yi da haske saboda kulawar dana samu a gunta. Haka Babana ya ɗaukeni ya dawo dani makaranta, na sha mamakin yadda aka soma gyarar makarantarmu, wanda na samu labarin cewar gwamnati ne ta ɗauki nauyin gyara mana, duk kuwa a sanadi na. Kwana biyu da dawowata na ga sauyi a gurin Mal  Tanimu sai jana a jikinsa yake, a ƴan zaman da na yi na kula da ya sauya halayyarsa, kullun kuma a gidansa sai an dafa mana abinci an raba mana, in bai ishemu ba ne sai mu yi bara.

  Cikin ƙanƙanin lokaci an kammala aikin gyarar makaranta, har kaya aka raba mana sadaka kala bibbiyu. Hajiya Zainab ta zo har makarantarmu ta ga aikin ta kuma gayawa Malam zancen boko data ce zata sanya ni, bai yi mata musu ba ya ce ya aminci amma a sanya ni makaranta nan cikin Rigasa saboda karatun Allo na. 

  *******

  Cikin watanni na zama mai cikakken ƴanci da gata, na tabbatar cewa *DA IYAYENA* a duniya, yanzu mahaifina yana zuwa duba ni a kai-a kai tare da ɗan kuɗin kashewa da kuma kyautar abinci da yake bawa Malam. Makarantar Mal. Tanimu ya yi fice sosai, yanzu da yawan makarantun Almajirai gwamnati ta gyarasu, Malamai sun ɗaura ɗamarar koyar da yara bisa gaskiya da riƙon amana.

  Ƙarshe...

  *Rahma ce*

  Read, Comment, Like

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Jini Baya Maganin Kishirwa: Babi na Uku

  Posted Jan 12

  Ku latsa nan don karanta babi na biyu. Sakinah ta share hawayen da ke zuba kan kuncinta kafin ta ce. "Insha Allahu Umma zan yi aiki da dukkan abin da ki ka umarce ni da shi da yardar Allah, ba zan taɓa baki kunya ba". "Yauwa Sakinah Allah ya yi miki albarka". "Amin"...

 • Yadda ake baked awara

  Posted Jan 11

  Barka da sake saduwa a cikin shirin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau na zo maku da sabon girki wato yadda za ku hada baked awara. Abubuwan hadawa Awara Kwai Carrots Seasoning Cooked minced meat Muffin tray Albasa Yadda ake hadawa Farko za ki yanka a...

 • Bayanan masana game da ingantattun hanyoyin ƙayyade iyali

  Posted Jan 8

  Mene ne ƙayyade iyali? Ƙayyade iyali ko tazarar iyali ko kuma family planning a Turance wani mataki ne da ma'aurata kan dauka don hana mace daukan ciki domin rage yawan haihuwa akai-akai, ko ƙayyade yawan ‘ya’ya da za ta haifa ko dai ma don wasu dalilai na ...

 • Ma'aurata: Babi na Biyu

  Posted Jan 8

  Idan baku karanta babi na daya ba to ku latsa nan don karantawa. Ana kiran sallah asuba ta farka daga bacci addu'an tashi daga bacci tayi kafin tayi miƙa tana salati ga Annabi S.A.W kai dubanta tayi a gefen da Fahad yake kwance tayi, har yanzu yana nan yana bacci kamar...

 • Burina a shekarar 2020: Saurare na ya fi magana ta yawa

  Posted Jan 4

  Masana sun ce daga cikin abubuwan da suka sa dan Adam yin galaba a kan sauran halittu shi ne yadda yake iya hada kai. Don mutum shi kadai ba zai iya gwada karfi da zaki ko giwa ba. Amma idan ya hada karfi da sauran ‘yan uwansa babu kalubalen da ba za su iya t...

 • Yadda ma’urata ya kamata su bullowa matsalolin rashin lafiya idan sun taso a rayuwar aure

  Posted December 31, 2019

  Matsalar rashin lafiya matsala ce babba da ke taka muhimmiyar rawa wajen hargitsa zamantakewa da rayuwar iyali. Ba abu bane da mutum daya zai boye ma kansa ba tare da sanin aboki ko abokiyar zama ba. Saboda matsala ce babba da take bukatar shawara, tattaunawa a tsakanin...

View All