Featured Create an Ad

Makalu

Blogs » Kagaggun Labarai » Nadamar Da Na Yi: Babi na daya

Nadamar Da Na Yi: Babi na daya

 • Da sunan Allah mai Rahama mai jink'ai ina godiya ga Allah subhanahu wata'ala Allah ka sa yanda na fara rubuta littafin nan lafiya, na gama shi lafiya amin.

  Gargadi

  Wannan littafin nawa k'irk'irarre ne banyi shi dan cikin fuska wani ko wata ba na yishine dan ilimantarwa ha?i da nishadantarwa, ban yarda wani ko wata su ?auki koda kalma ?aya daga cikinshi da niyyar su juya min littafi, in ba tare da izinina ba, duk wanda yayi haka to ban yafe ba.

  Godiya

  Godiya ta musamman ga k'ungiya mai albarka na gaishe ku *NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION* Allah ya k'ara basira da ha?in kanmu amin ya Allah.

  Jinjina

  Jinjina. dole nayi maki jinjina masoyiya ta gaskiya, hak'ika kin wuce k'awa aminiya sai dai na k'iraki 'yar uwa domin kin taka rawar gani sosai a zamana dake, ke 'yar uwa ce ta gaskiya ina alfahari dake HAUWA SHEHU ALIYU* ( JIDDAH ALIYU) idan nace ina da kamarki a duniyar nan nayi k'arya saboda irin so da kauna da kika nuna min hak'ika *BANDA KAMARKI*

  *********

  Parlour ne na gani na fa?a wanda ya ke ?auke da lausa_lausan kujeru, k'ayatuwar parlourn kawai zai tabbatar maka da gidan wani attajirin mai ku?i ne. Parlourn tsit yake baka jin motsin komi sai sautin kuka k'asa_k'asa. Zaune yake akan kujera ya ?aura k'afa ?aya kan ?aya, yayinda fuskarsa na kan wadda taketa faman kuka kanta a k'asa yake sai dai hawaye kawai dake sauka akan hannayen ta. K'afarshi ya sauke k'asa ya g?ara zamanshi kafin ya sauke ajiyar zuciya ya ce.

  "Fatima kada kiga ina maki fa?a kiyi tunanin kamar bana sonki ne a'a ina maki fa?a ne kawai dan irin son da nake maki, nasan bazaki gane hakan ba sai bayan ba raina, ni ina son na gina maki rayuwa mai inganci, kada ki manta ke ?aya mahaifiyarki ta haifa, shiyasa na zab'a maki miji da kaina, saboda na tabbata Faruq yaron kirki ne. Fatima a matsayina na mahaifinki ki ?aure ki amshi Faruq a matsayin mijin auranki, idan kika yi min haka kin gama min komi a rayuwa please."

  A hankali ta ?ago jajayin idannunta ta dubi mahaifn nata da duk hankalinshi na kanta cikin muryar kuka ta ce.

  "Dad I know Dad kana sona fiye da tunanina but Dad bani da burin da nakeso irin na k'yautata maka...Amma sai dai hakan ba mai yuwa ba ne, bazan iya hana abinda zuciyata ke so ba rabani da Musaddik tamkar rabani da rayuwata ne Allah na gani bazan iya auran Yaya Far....."

  Marin da ya wanka matane ya sa ta ha?e sauran maganar da ke bakin ta. Tashi tsaye tayi cikin zabura, da tsoron ganin fuskar mahaifin nata ta sauya lokaci ?aya.

  "Thanks Fatima da irin sakayar da kika nuna min a matsayina na mahaifinki wanda nasha wahalar tarbiyarta dake tun bakisan abinda duniya ke ciki ba, to bari kiji dak'yau no one can stop this marriage and it’s my final answer, zaki iya fitar min daga ?aki."

  Hannu yasa ya nuna mata hanyar fita da gudu tabar parlour ta nufi ?akinta tana kuka, kan gado ta fa?a ta saki wani kuka mai sauti. Wayarta ta jawo da sauri jikinta na rawa ta danna wata number mai ?auke da sunan *NOOR HAYYAT* ringing ?aya aka daga, tamkar dama jiran k'iran nata ake. Daga b'angaran da ta k'ira naji ya wani sauke ajiyar zuciya mai sauti.

  "Amincin Allah ya tabbata agareki yake sarauniyar matan duk duniya, haba tawa ina kika shige ne? ko kinsan zuciyata zata iya tarwatsewa a duk lokacin da na rasa wannan muryar taki mai da?i kamar sarewa, banida wani buri da ya wuce injini kusa dake, a kullum ina rukon Allah ya nuna min lokakacin da zamu zama miji da mata, Sahiba lafiya naji kinyi shiru?"

  Tunda ya fara magana Fatima ta lumshe idonta bata bu?e ba sai yanzu da ta saki sabon kuka.

  "Ya salam haba *SANYIN IDANIYATA* wa ya tab'a minke? wallahi ko waye sai yaga b'acin raina dan ban hadaki da kowa ba!"

  Kuka ta k'ara fashewa dashi muryarta na rawa ta fara magana.

  "Musaddik na shiga uku! Dad naso ya tarwatsa min zuciya, ba susan cewa rabani da kai tamkar rasa rayuta...."

  "Dakata Teema! ban gane abinda kike fa?i ba."

  "Musaddik Dad yace zai aurar dani ga ?an d'an uwansa Yaya Faruq..."
  Wata irin tsawa yayi tamkar tana kusa dashi

  "What Faruq? No!!! dear dat impossible taya Dad zai raba anta da jini!? ko yasan rabamu babban kuskure ne. Ba komi Sahiba nasan ba komi yasa Dad yatsaneni ba dan kawai ya ga ni makaho ne ba ido shiyasa yake son rabamu, amma ki sani duk ranar da aka rabamu to daga ranar zan sha guba na mutu kowa ya hut..."
  Da sauri ta daga murya cikin sautin kuka

  "Na shiga uku haba Musaddik me yasa zaka fa?i haka ko ka manta zuciyata tamkar kitse ce Idan tanajin wannan kalaman naka zata iya narkewa, duk duniya bani da wani farin ciki da ya wuce na ganni a ?akinka mun zama miji da mata a kullum mafarkina shine mukasance tare har abad..

  "Ai kam babu rana babu kuma lokaci indai akan wannan dan iskan yaron ne dan haka idan ma mafarki kike to ki farka dan gari ya waye."
  Cikin tsorata Fatima ta ?aga kai tana kallon mai magana."

  *******

  DEDICATED TO *BEEBAH LUV*

No Stickers to Show

X

Da Dumi-Dumin Su

 • Mon at 1:39 PM
  Posted by Bakandamiya
  Uwargida ba za ki yi dana sanin koyan yadda ake yoghurt in fruits ba. Domin kuwa kayan dadi ne sosai da sosai kuma cikin mituna kalilan za ki hada. Ba a ba yaro mai kiwiya!!! Wannan recipe yana daya daga cikin recipes da muka koyar a zauren Free Ramadhan Classes with Umyuman a nan Bakandamiya. Abu...
 • Hadin special salad nawa na musamman ne! Ga sauki ga dadi, uwargida sai kin gwada za ki bani labari! Wannan ma yana daya daga cikin recipes da muka koyar a Ramadan a shirin girke-girkenmu wadda aka gabatar a zauren Free Ramadhan Classes with Umyuman. Shin ko kin tuna gashin tsokar kaza da muka koya...
 • Red velvet cake, cake ne da mutane da dama suke so kuma kuma suke son ci. Saboda haka, akwai hanyoyi daban-daban na yin red velvet cake, ga yadda na ke nawa cake din na kawo muku. Wannan yana daya daga cikin recipes da muka koyar lokacin Ramadan anan Bakandimya. Domin ganin duk jerin recipes din da...
 • Bismillahi rahmanir Rahim Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad, da alayensa da sahabbansa baki daya. Lalle haduwar Idi da Jumma’a wani abu ne da ya saba faruwa lokaci zuwa lokaci. Hakan ya taba faruwa a zamanin Manzon Allah (S.A.W...
 • Lemun zaki ko orange juice lemu ne mai dadi da kuma tarin amfani a jiki. Ga yadda na ke lemun zaki na a gida. Da farko wannan recipe mun koyar da shi ne a shirinmu na Ramadan cikin zauren Free Ramadhan Classes with Umyuman. Shin yaya ki ke yin lemon zakinki? Ga yadda na ke nawa, ki gwada wannan!&nbs...
 • Bismillahi rahmanir Rahim Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Mai girma da daukaka. Salati da sallama su kara tabbata ga Manzon Allah, da iyalansa da Sahabansa. Mece ce layya? Layya ita ce: Abinda ake yankawa na dabbobin ni'ima (rakumi da shanu da rago da akuya) ranar idin babbar sallah, d...
View All