Makalu

Jalaluddeen Junaid: Babi na daya

 • Da sunan allah mai rahma mai jin ķai. tsira da amincin Allah su tabbata ga shugaban halittah Annabi Muhammad SAW.

  Masoyana a duk inda kuke ina mika saķon gaisuwa agareku. ķaunarku a gareni da ķarfafa min gwiwar da kukene ya sanya nake a inda nake yanzu. ba abunda zance sai dai ince Allah yabar so da k'auna.

  Masu karatu sai kun yi haķuri da wannan doguwar tafiyar da zamuyi , wannan littafin ba kamar sauran littafai na ba ne. ya ďan banbanta dasauran. dafatar zaku bani haďin kai.

  Wannan labarin k'agagge ne, idan yazo daidai da rayuwar wani ko wata akasi aka samu. ba'a yi shi don cin zarafin kowa ba.

  *********

  Tankwashe ķafafunsa yayi tareda nannaďe hannayen rigarsa. Yafara kwasar best delicious. Kamar yanda ya laķaba masa. Tinda ya fara kai lomar fari yake gyaďa kai alamar daďi kenan. Sai jinjina kai yake bai tsayaba saida ya kusa cinyewa sannan ya ďago fuskarsa.

  Fari ne ba can sosai ba, ya nada doguwar fuska mai ďauke da dogon hanci yanda kasan biro, bakinsa daidai shi, idon sa manya irin golden eyes ďin nan , masu ďauke ďa zara zaran gashi eyelashes kenan, eyebrow ďin sa mai yawa kwance lub.
  Kai dagani kasan zaiyi gashi, yanda fuskarsa take ďauke ďa siririn saje tin daga kansa har zuwa gemunsa ataķaice dai ya haďu.

  Wannan shi ake kira handsome.

  Ruwan paro ya buďa ya shanye ķaramar gorar ruwan yayi hamdala ga Allah, tareda faďan ( Allahamdu lillahil-ladhi at'amani hadha wa razaķanihi min ghairi haulin minni wa lah ķuwwatin )

  Zaķin muryarsa baiyi kama dana bahaushe ba , sautin muryarsa kamar balarabe, wata kila hakan yana da nasaba da furta kalmomin larabci da yayi.

  Tashi yayi yana fuskantar matar da take kan kujera.
  "Hajiya zan shiga ciki in rage kayan jikina. Zan iya kaiwa 4 sannan infito, akwai wasu takardun da nakeson cikawa."

  Wacca yakira da Hajiya tayi murmushi tace "bakomai kaje kayi aikinka nima kwanciyar zanyi in huta, Allah yayi maka albarka yaķara haske acikin rayuwar ka" farin ciki marar misaltuwa ya bayyana a fuskarsa. Ameen ya allahu nagode mamana (sakillahu fil janna)

  Tsayuwarsa ta tabbatar da tsayinsa, dogo ne sosai, irin tsayin da guntun mutum sai ya ďaga kai sama zai iya hango fuskarsa.

  Da sallama ya shiga ďakinsa. hakan ya zame masa al'ada dikda ba kowa a d'akin, Sanyin Ac da ķamshin tirare ke tashi acikin ķayataccen ďa kin, komai na ďakin fari ne kamar ba'a amfani da ďakin yanda naga komai fes sabo.
  Hakan yana nuni da cewa mamallakin ďa kin mai tsabta ne.

  Takalminsa yafara ajiyewa gurinda aka musu tanadin zama wato shoe drawer. Ya buďe wardrop ya cire doguwar rigar da take ajikinsa ya ajiyeta, brown jallabiya yaďauko yasaka bayan ya cire wandon rigar.
  komai da tsarinsa.

  Kai tsaye toilet yawuce. Inda yayi mixing warm water da cool daidai yanda zai ishesa wanka.

  D'aure da farin towel yafito d'aya a hannun sa yana tsane jikinsa, k'amshi ya gauraye d'akin.

  Bin kowane sassa na jikinsa yake da ingantattun mayuka yana feshi jikinsa da tiraruka masu k'amshi da dad'i.

  Bayan yagama ya kishingiďa kan wata lumtsatstsiyar kujera. Yajawo system d'in shi yana dubawa.

  ******

  "Saudah muba ķananun yara bane, da zamu tsaya b'ata lokacin juna. Nida ke dikanmu mun mallaki hankulan kanmu, bai kamata muna wasa da lokacin da yake tsadadde a rayuwar mu ba"

  Wacca aka kira da sauda ta sauke gauron nunfashi.

  "Haka ne sir. Yanzu ya kake gani za'ayi?

  "Ke zan tambaya" ya fad'a batareda ya d'ago ya kalleta ba, idonsa na kan wayarsa da yake danna.

  "Uhm uhm ni bansan ya za'ayi ba, kaine yakamata ka kawo mana mafita"

  Zaman glasses d'in sa ya gyara yace "alright tinda bakida solution ni zan wuce."

  Bai jira amsar ta ba ya kunna motar sa zai tashi.

  Sanin idan bata fitaba zai iya ficewa gidan da ita yasanya ta saurin bud'e murfin motar ta fita. Dikda haka saida ya d'an bigeta batareda yadamu da abunda yayi ba.

  Zuciyar ta ta dafe dake fitarda wani zafi mai kama da gobarar wuta.

  Ta dafe bango tana fitarda iska abakinta.

  Sir bazai canza ba, yana bamu wahala , tasani sarai yana sonta amma bazai iya furta mata kalmar datayi kama da ra'ayi ba bare so, shine kuma yake neman ta zubar da nata makaman ajin ta tunkaresa da kalmar k'auna.

  Anya kuwa hakan zata yuyu. Toh idan kuma ya canza ra'ayi fa? Tasan hakan ba k'aramin aikinsa bane, cire mutum aransa shi yafi komai sauk'i, musamman idan mutumin zai bashi wahala ko b'ata lokaci abunda yafi bawa muhimmanci kenan a rayuwar sa.

  Qira'ar sudais ya kunna. Suratul Ibrahim yana bin karatun yana tuk'insa a hankali, cikin k'warewa da k'asaita.

  Zuwan sa gida keda wuya tafara damunsa da waya tin yana jure sauraren k'arar wayar har ya kasheta gaba ďaya.

  Saudah najin wayarsa switch off tasan ba ķaramin fushi yayi ba, wanda dakyar zata samo kanshi.

  Zuciyar ta ce ta azalzaleta akan ta tura masa sak'on ban hak'uri. Ko zai sauko daga dokin fushin da ya hau.

  Ba b'ata lokaci tafara rubuta masa sak'o.

  "Dear sir, How can I begin to say I`m sorry
  I didn’t mean to upset you. I hope that you can forgive me
  I’m sorry sir"

  Da safe ya bud'e wayar tashi ya riski cincirindun sak'onnin mata da maza harda MTN.

  Yayi tsaki tareda yin delete all na messages d'in.

  Yana tsaka ga gogewa wayar Saudah ya shigo.

  "Ya akayi?
  Kalmar da ya fara da ita kenan.

  "Sir please.....shhhh yayi saurin dakatar da ita.

  "Karki samun ciyon kai yanzu na tashi. Bakya buk'atar sake karanto miki ďabi'una , kinsani sarai yana daga abunda na tsana maida hannun agogo baya, abunda akayi jiya, dazu ya wuce agurina , na yanzu ne abun dubawa"

  "Shikenan sir. Amma ya kamata ka dena fushin nan dani, zuciyata tanada rauni bazata jure ababe makamantan wannan ba"

  "Ya kamata ki koyi juriyar, da taurin zuciya. Idan bakida abun fad'a inada abunyi"

  Kafun ya katse wayar tayi saurin cewa "na samo mana mafita sir."

  "Wannan zancen ba yanzu ba" amsar daya bata kenan.

  Dif ya katse wayar.

  Wata ajiyar zuciya tayi. tayi lamo kan katifa tana tariyo lokutan da suka shuďe musu atare batareda wani muhimmin cigaba ba.

  Wata zuciyar ke bata shawarar mezai hana ki tunkaresa da maganar so, tinda kin tabbatar yana son ki.

  Wata zuciyar kuma tace mata ina hakan bazai yuba ni mace ce at least inada aji da kunya na ýa mace.

  Toh amma sir zai iya sub'uce mini , samun irinsa abune mai wahalan gaske a wannan zamanin.

  ******

  Oyoyo Abbana!

  Oyoyo my son!

  "Ya school d'in?

  "Abba komai well kaga naci kyautar wanda yafi kowa tsabta da nutsuwa a primary school d'in mu"

  "Wow masha Allah my son. Haka nakeso ka cigaba da k'ok'ari, kayiwa malamai biyayya kamar ni, kayi dik abunda akace kabar wanda ba'a so, banda wasa da abokai, ayita karatun lessons, insha allahu zaka zamo."

  "Insha Allah abba zanyi me kace. Abba saukeni inje in gaida Anti"

  Da murnarsa yasame y'ar dattijuwar da bata wuce shekaru 45 ba. Ya duk'a har ķasa ya gaida ita.

  "Sannu da gida anti" murmushi mai girma tasaki mai cikeda k'aunar yaron tace "Sannun ka da zuwa yaron kirki. Maza kaje kayi alwala ankusa tada sallah"

  Atare da abban nasa suka wuce masallaci. Wanda yaza memusu al'ada aduk lokutan sallah.

  *****

  Sir. Aka fad'a tareda k'amewa ķam irin na wanda ake bawa girma.

  Ya cigaba da magana hannunsa na kan forehead d'in sa.

  "Sir. Ga Alhaji gadalima yazo belling yaran sa. Ya shigo mana station harda karnukan sa da wasu taķadaran karuwai."

  "What! Ya faďa tareda juyowa da ķarfi"

  Lion voice d'in shi yakusan firgita ni. Cikar zati da kamala nashi ya đimautani. Kwarjininsa kuwa ruđani yayi.

  "I'm coming"

  Amsar daya bashi kenan.

  Har ya kai k'ofa ya dakatar dashi dacewa "Bala ashirya min ķanķara, ka sanar da Ukasha ya kula da motsin su ina zuwa."

  "Yes sir! Ya fad'a yana mai sarawa ogan nashi ya fita.

  Murmushi yayi ya gyara zaman belt d'in shi yace "Galadima, galadima."

  Glasses d'in shi ya sanya, ya saka hular shi ya gyara zaman star d'in shi yafito.

  Tafiyar sa kad'ai zaka kalla kasan cewa mazam ma suna suka tara.

  Kan tebur yasa mesu sunyi cirko-cirko suna jiransa.

  "Hey. Kaine J.J d'in?
  J.J ya bashi amsa da "Yeah. You don't need an explanation."

  "Kai ni ba dogon zance yakawo ni ba kasake min yarana kawai."

  "Ko akwai dokar da tace asake masu laifi batareda an hukunta su ba?

  "J.J indai kana son aikinka to ka sake min yarana kafun zaman kujerar ka ya gagareka."

  "Kaine kake gab da rasa kujerar da kake akai, domin kuwa Allah ne kadai zai hanani makaka akotu matuk'ar na gama hađa bayanai akanka."

  Wata irin dariya yayi yace "yaro baisan wuta ba sai ya taka".

  **********

  ASEEYAH BASHEER ALEEYU

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Yadda ake hada KFC chicken

  Posted Thu at 10:11 AM

  Assalamu Alaikum, barka da sake saduwa a cikin shirin girke-girken Bakandamiya tare da ni mai gabatar muku da shirin. A yau in sha Allah zan nuna mana yadda ake hada KFC chicken. Abubuwan hadawa Kaza Flour Man gyada Bread crumbs ko cornflakes Kwai Maggi ...

 • Yadda ake hada egg masala

  Posted Thu at 9:57 AM

  Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa a cikin shirin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau na zo mana da yadda za a hada egg masala a saukake. Abubuwan hadawa Dankalin turawa Albasa Carrots Maggi Mangyada Kwai Yadda ake hadawa Farko za ki wanke dankal...

 • Jini Baya Maganin Kishirwa: Babi na Uku

  Posted Jan 12

  Ku latsa nan don karanta babi na biyu. Sakinah ta share hawayen da ke zuba kan kuncinta kafin ta ce. "Insha Allahu Umma zan yi aiki da dukkan abin da ki ka umarce ni da shi da yardar Allah, ba zan taɓa baki kunya ba". "Yauwa Sakinah Allah ya yi miki albarka". "Amin"...

 • Yadda ake baked awara

  Posted Jan 11

  Barka da sake saduwa a cikin shirin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau na zo maku da sabon girki wato yadda za ku hada baked awara. Abubuwan hadawa Awara Kwai Carrots Seasoning Cooked minced meat Muffin tray Albasa Yadda ake hadawa Farko za ki yanka a...

 • Bayanan masana game da ingantattun hanyoyin ƙayyade iyali

  Posted Jan 8

  Mene ne ƙayyade iyali? Ƙayyade iyali ko tazarar iyali ko kuma family planning a Turance wani mataki ne da ma'aurata kan dauka don hana mace daukan ciki domin rage yawan haihuwa akai-akai, ko ƙayyade yawan ‘ya’ya da za ta haifa ko dai ma don wasu dalilai na ...

 • Ma'aurata: Babi na Biyu

  Posted Jan 8

  Idan baku karanta babi na daya ba to ku latsa nan don karantawa. Ana kiran sallah asuba ta farka daga bacci addu'an tashi daga bacci tayi kafin tayi miƙa tana salati ga Annabi S.A.W kai dubanta tayi a gefen da Fahad yake kwance tayi, har yanzu yana nan yana bacci kamar...

View All