Makalu

Ban Zaci Haka ba: Babi na Daya

 • Bismillahir rahmanir rahim.

  GARIN KADUNA

  Tun kan ta gama shiga falon ta soma kwala mata kira "Aunty! Aunty!! Aunty!!!. Cikin sauri wata farar mace, mai matsakaicin jiki ta fito, daga hanyar kicin hannunta rike da ludayi, da alama miya take motsawa, "Na'am lafiya kuwa kike yi min irin wannan kira?" Duk a lokacin guda wacce ta kira da Aunty ta jero mata wadannan tambayoyi. Bata amsa ba don ganin tana daf da cimmata, ai da sauri ta ƙarasa wajen matar tare da fadawa jikinta tana fadin "Aunty Zuhra ce fa, wai dole sai ta kwace wayar hannuna." Ta dire maganar tana komawa bayan Auntyn.

  "Allah kuwa Aunty karya take yi, daga ganin ina yin game shi ne ta kwace ta gudo fa." Zuhra ta fada, lokacin da ta iso gaban Aunty, kamar zata yi kuka. "Aunty ni ce fa na fara ɗaukar wayar, don na aje sai ta dauke, shi ne ni kuma yanzu na kwace fa." A shagwabe take magana.

  Dariya ma suka ba Aunty gaba daya, don ta kasa cewa komai, sai bin su take da ido, fuska dauke da murmushi, tana son diramar yaran idan suna yi wani farin ciki take ji na musamman, tana tuna wani lokaci can baya.

  "Oya ya isa, ke dai Zuhra baki girma yanzu Nasreen din ce kike biyowa da irin wannan gudun?" Aunty ta yi tambayar tana tsare Zuhra da ido.

  "Aunty ba ki ganin ita ta fara tsokanata? Kuma sai ni za a yi wa faɗa." Ta yi maganar tana maida kwallar da suka taru a kwarmin idonta.

  "Kin san dai har yanzu Nasreen yarinya ce, lallabata ta kamata ki yi, ba ki biyota da gudu haka ba." Aunty ke maganar.

  Buɗe baki Zuhra ta yi da niyyar magana, sai ko idon su ya haɗu da na Nasreen dake yi mata gwalo. Kwafa kawai ta yi tare da barin wajen tana mai jin haushin, yadda kullum Aunty take goyon bayan Nasreen akan abubuwan da take yi.

  "Haba Nasreen, haba yarinyata, me yasa kike yi wa Zuhra haka?" Aunty tana maganar ne tana birkito da ita gabanta. "Ba zan kara ba Aunty." Cike da ladabi ta yi maganar.

  "Yawwa yar Aunty, yi sauri ki je ki bata hakuri kin ji ko?" Fuska dauke da murmushi Aunty ta dire maganar.

  "To." Nasreen ta amsa tare da fara tafiya.

  Girgiza kai Aunty ta yi sannan ta koma kicin din, suna ci gaba da aiki ita da masu aikinta.

  Nasreen na shiga dakinsu wato wanda suke kwana, ta yi saurin nufa wajen Zuhra tana faɗin "Sorry Sister." Kallonta kawai Zuhra ta yi ba tare da ta iya furta komai ba, ƙara ƙasa ta yi da murya tana ci gaba da bata hakuri, har kamar zata yi kuka, sai can Zuhra ta saki murmushi tare da kai wa Nasreen dukan wasa ta ce "Allah ke ko? Don kin ga Aunty tana goyon bayan ki ko?" "A'a." Nasreen ta fada tana girgiza kai, fuska dauke da murmushi.

  "Kin ga tashi mu shirya lokacin islamiyya ya yi fa, kin san dai kullum ana lura da time na zuwan mu ga yi BOSS na hanya, kuma da ya iso gidan nan ya ji labarin bamu tafiya da wuri mun shiga uku." Turo baki Nasreen ta yi tana kunkuni, akan yadda BOSS ya takura su. Tana shiryawa tana kunkuni ta gama, lokacin ita ma Zuhra ta shirya. Fita falo suka yi ko wacce dauke da jakarta na makaranta.
  Kai tsaye kicin suka shiga inda Aunty ke aikace-aikacen ta, "Aunty mun gama shiryawa." Nasreen ta fada lokacin da suka shiga cikin kicin din.

  "A'a'a yau kune kuka yi shirin makaranta da wuri? Ko dai don kun san BOSS din ku yana hanya ne, shi yasa?" "Lah! Aunty wai dama da gaske zai dawo ne?" Nasreen ta yi saurin tambaya.

  "Au wai duk wannan abin da ake baki sani ba? To gobe uwar haka yana gidan nan" Da zallar farin ciki Aunty ta gama maganar. "Ta sani sarai Aunty iskancinta ne ya motsa, ni ki zo mu wuce time yana tafiya, kar ki ja mana dukan latti" Zuhra ta fada tana hararar Nasreen. "Tab ai ko muna dawowa gidan Alhaji babba zan wuce, ba zan zauna ya zo ya takura min ba, a koma yi mana mulkin mallaka."

  Cikin zuciyarta take wannan maganar, amma a fili sai ta cewa ta yi "Allah ya kawo shi lafiya." Ta karasa maganar tare da fara tafiya, dukkan su da kallo suka bita, girgiza kai Aunty ta yi cikin tausayin Nasreen din, don ganin yadda lokaci daya yanayinta ya sauya.

  Karfe biyar da minti arba'in suka dawo daga makaranta, Nasreen bata shiga dakinsu ba sai da ta biya ta yi wa Aunty sannu da gida, ko da ta shiga dakinsu cire kayan makarantar ta yi, kai tsaye wanka ta shiga, shaf-shaf tana fitowa ta sona shirya cikin wani wando mai kalar pink iya gwiwa, rigar jikinta fara tas da kadan ta rufe mata cibiya, kanta sanye da hular sanyi mai kalar wandon ta, sosai ta yi kyau duk fuskarta babu wani kwalliya da ta yi, bata fita falo ba, don sam zuciyarta babu dadi, har ga Allah bata kaunar BOSS ya dawo gidan nan, tana ji a ranta daga ranar da ya dawo zata kuma rasa farin cikinta a karo na biyu.

  Sosai ta yi zurfi cikin tunanin ta, har bata san time da aka kira sallah ba, Allah ya sa ma ba yin sallar take yi ba, tana daga cikin bedroom din ta fara jiyo hayaniyar yaran gidan, ma'ana dai sun dawo daga gidan Alhaji Babba, mtsww ta saki siririn tsaki, tana lumshe ido cikin son ta kawar da tunanin da ya addabeta.

  Zuhra da ke tsaye tun ɗazun tana kallon Nasreen ta matsa bakin gadon tare da zama, ta yi kamar minti uku sannan ta fara magana.

  "Lafiya kuwa sister?" Ta tambaya tana juyo da ita.

  Murmushi Nasreen ta saki, tana faɗin "Me kika gani Yar'uwa?" "Abubuwa da yawa na gani, Nasreen ɗazun ba haka kike ba, amma tun da kika ji BOSS zai dawo sai kika daga hankalinki, me yasa haka ko kina son ki bata ran Aunty ne?" A sanyaye Zuhra ta yi mata tambayar.

  Girgiza kai Nasreen ta yi, tana kara boye damuwar dake ranta, ta ce "Sam ba haka ba ne sister, tunanin Ummi nake yi."

  Ta dire maganar tana mai yin murmushin karfin hali.

  "Ki yi mata addu'a, shi ne kawai abin da za ki yi wanda zai faranta mata, sannan ki yi kokarin boye damuwar ki akan BOSS, kin san dai Aunty ba zata ji daɗi ba, saboda BOSS jininta ne, kuma duk cikin mu babu wanda take yi masa son da take yi wa BOSS, ke ce ta biyu da Aunty ke nunawa so a fili.

  "In sha Allah zan yi yadda kika ce, na gode da shawarar ki" Nasreen ta amsa tana jawo jakar makarantar ta.

  Murmushin jin dadi Zuhra ta saki tare da nufa toilet don yin alwala. Tana idar da sallah ta fita falo inda ta bar Nasreen cikin bedroom din.

  Can a falo kuwa Dady wato Alhaji Ma'aruf, zaune tsakiyar iyalinsa, da kallo ya gama bin su daya bayan daya, sai dai idonsa bai hasko masa wacce yake son gani ba, muskutawa ya kara yi tare da cewa "Zuhra ina yar'uwarki take ne? Na ga ban ganta ba tunda na dawo." "Tana cikin daki Dady, babu mamakin bata san ka dawo ba, home work take yi." Zuhra ta bashi amsa cikin ladabi.

  "Jawad maza je ka kira Aunty Nasreen ka ce in jini." Da sauri yaron ya nufi bedroom din,

  Zaune ya sameta kamar yadda Zuhra ta barta, matsawa ya yi jikin gadon tare da riko hannunta, ya ce "Aunty Dady yana kira wai ya dawo." Murmushi ta yi tana shafa kan Jawad ta ce "Ka cewa Dady gani nan zuwa, ina yi masa sannu da dawowa." A duniya tana son Dady, don Dady yana son farin cikin ta.

  Jawad na fita ta mike, daret falon ta fita, duk da yadda ta yi kokarin dauko fara'a ta sanya akan fuskarta, sai dai duk da haka jikinta akwai alamar damuwa, musamman yadda take tafiya.
  Tun kafin ta karasa Dady ya ke sakin murmushi har ta isa wajensa, zama ta yi a ƙasa tana faɗin "Barka da dawowa dadyna."

  "Barkammu dai Yar Dady, Allah yasa lafiya na ga har na dawo baki zo falo ba?" Dady ya fada cikin fara'a.

  Yamutsa fuska ta yi ta ce "Dady yau kaina ke ciwo, tun da na dawo islamiyya." "Ayya sorry Yar Dady, fatar kin sha magani?" Cike da kulawa ya yi tambayar.

  "Zan sha ne, ina son sai na yi dinner." Nasreen ta fada tana jingina kai da jikin kujera.

  "Oya tashi ki je ki ci abinci, dama ke ka dai muke jira, idan kin gama sai ki sha magani ki kwanata."

  "To." Dady Nasreen ta amsa tana tashi, da kallo Aunty da Zuhra suka bita.

  Kai tsaye dining ta nufa, abinci ta zuba sannan ta fara tsagalar shi ba wai don tana jin ji ba, bata ci da yawa ba ta mike tsaye, "A'a ba dai kin koshi ba?" Aunty ta yi tambayar tana tsare Nasreen da ido.
  "Na koshi ne Aunty." Nasreen ta bata amsa.

  "Ok ki ɗauki panadol a wajen aje magunguna, sannan ki yi addu'a kafin ki kwanta." Cikin kulawa Aunty ke magana.

  Kiss Nasreen ta yi wa Aunty a goshi sannan ta wuce, kusan a tare Aunty da Dady suka girgiza kai, sannan suka ci gaba da cin nasu abincin.

  Tana shiga bedroom wanka ta fara yi, ta shirya cikin lallausan kayan barcin ta, addu'a ta yi kamar yadda Aunty ta yi mata tuni, sannan ta runtse ido tana fatar Allah yasa barci ya dauke ta.

  Have a nice sleep Nasreen.

  © Zulaiha Rano

  HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION (HWA)

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Jini Baya Maganin Kishirwa: Babi na Uku

  Posted Jan 12

  Ku latsa nan don karanta babi na biyu. Sakinah ta share hawayen da ke zuba kan kuncinta kafin ta ce. "Insha Allahu Umma zan yi aiki da dukkan abin da ki ka umarce ni da shi da yardar Allah, ba zan taɓa baki kunya ba". "Yauwa Sakinah Allah ya yi miki albarka". "Amin"...

 • Yadda ake baked awara

  Posted Jan 11

  Barka da sake saduwa a cikin shirin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau na zo maku da sabon girki wato yadda za ku hada baked awara. Abubuwan hadawa Awara Kwai Carrots Seasoning Cooked minced meat Muffin tray Albasa Yadda ake hadawa Farko za ki yanka a...

 • Bayanan masana game da ingantattun hanyoyin ƙayyade iyali

  Posted Jan 8

  Mene ne ƙayyade iyali? Ƙayyade iyali ko tazarar iyali ko kuma family planning a Turance wani mataki ne da ma'aurata kan dauka don hana mace daukan ciki domin rage yawan haihuwa akai-akai, ko ƙayyade yawan ‘ya’ya da za ta haifa ko dai ma don wasu dalilai na ...

 • Ma'aurata: Babi na Biyu

  Posted Jan 8

  Idan baku karanta babi na daya ba to ku latsa nan don karantawa. Ana kiran sallah asuba ta farka daga bacci addu'an tashi daga bacci tayi kafin tayi miƙa tana salati ga Annabi S.A.W kai dubanta tayi a gefen da Fahad yake kwance tayi, har yanzu yana nan yana bacci kamar...

 • Burina a shekarar 2020: Saurare na ya fi magana ta yawa

  Posted Jan 4

  Masana sun ce daga cikin abubuwan da suka sa dan Adam yin galaba a kan sauran halittu shi ne yadda yake iya hada kai. Don mutum shi kadai ba zai iya gwada karfi da zaki ko giwa ba. Amma idan ya hada karfi da sauran ‘yan uwansa babu kalubalen da ba za su iya t...

 • Yadda ma’urata ya kamata su bullowa matsalolin rashin lafiya idan sun taso a rayuwar aure

  Posted December 31, 2019

  Matsalar rashin lafiya matsala ce babba da ke taka muhimmiyar rawa wajen hargitsa zamantakewa da rayuwar iyali. Ba abu bane da mutum daya zai boye ma kansa ba tare da sanin aboki ko abokiyar zama ba. Saboda matsala ce babba da take bukatar shawara, tattaunawa a tsakanin...

View All