Makalu

GARIN NEMAN GIRA

 • GARIN NEMAN GIRA...!*

  *ZULAIHAT HARUNA RANO*

  Ya faru a gaske.

  Cikin nutsuwa ta miƙe tana naɗe sallayar da ta yi sallah a kai, bakinta yana motsin da ke nuni da addu'a take yi. A hankali ta kai dubanta kan ƙaton agogon bangon falon, wanda ya nuna mata karfe goman safiya saura daƙiƙu biyar. Sallah ce ta walaha ta yi wadda ta saba yinta karfe tara zuwa sha daya na safe, ta ajiye sallayar ta fita tsakar gida wajen mahaifiyarta ta yi mata magana murya a sanyaye.
  "Sannu da aiki Mama."
  "Yawwa har kin idar?"
  "Eh! Na idar, kawo na tayaki ki huta." Tana maganar tana tattare ragowar kayan wanke-wanken da maifiyar ke kwashewa.
  Kamar daga sama ta tsinkayi muryar mahaifinta yana kwada mata kira, cikin hanzari ta zube kayan tana amsawa da, "Na'am Baba."

  Wani sakaran kallo ya yi mata. jikinta ya yi matuƙar sanyi, ko ba a tambaya ba ta san kallon da yake mata kallo ne na zallar tuhuma.
  "Ke Zulaiha!"
  "Na'am Baba." Ta amsa.
  "Ya muka yi da ke shekaranjiya?"
  "Ka yi hakuri Baba wallahi har yanzu shiru ne."
  "Shiru ko?" Ya tari numfashinta.
  "To bari ki ji, wallahi kin ji na rantse ko? Nan da kwanaki bakwai idan har ba ki fito da miji ba sai ranki ya ɓaci, ke kullum cikin niƙafi da safa kin ki bude fuska ɓalle har wani ya ganki ya ce yana so, to wannan karon ba zan taɓa ɗaga miki ƙafa ba. Tunda nake ban taɓa ganin mai baƙinjini kamarki ba." Yana gama maganar ya juya fuuu ya bar gidan.

  Kuka Zulaiha ta fashe da shi, tana jin zafin furucin da mahaifinta ya yi mata. Musamman kalmar mai baƙinjini.
  Cike da takaici mahaifiyarta dake fitowa daga madafi, ta bi mai-gidan nata da kallo tare da girgiza kai cikin tausayin halin da yarta ke ciki. Tana nan tsaye tana kallon Zulaiha, ta rasa da wacce kalmar zata lallasheta sai kawai ta ce, "Tashi ki je ki sha rubutun gidan Malam Audu, kin san ba'a son ana tsallake?"
  Mahaifiyarta ta fada murya a sanyaye. Jin haka Zulaiha cikin kuka mai ciwo ta amsa.
  "Ni wallahi Mama na gaji da shan rubutun nan har yanzu babu wani cigaba kullum jiya-i-yau kawai zan daina shan rubutun nan." Da alamun ƙarfafa gwiwa mahaifiyar ta ce.
  "Ki dai daure ki sha ba a san inda za a dace ba, ɗazu mun yi magana da Hadiza gobe zaku je wajen wani malami ko Allah zai sa a dace."
  Cike da mamaki Zulaiha ke kallonta, tana mamakin ya za a yi ta zama mai bibiyar Malamai haka? 'Kenan Umma itama bata yarda da kaddara ba kamar Baba?' Wasu zafafan hawaye suka gangaro daga idonta.
  Ba tare da ta ce komai ba ta nufi ɗaki, zuciyarta na mata wani irin ɗaci, bata ɗauki maganin ba ta yi zamanta.

  Malam Usman na fita ransa a matukar ɓace da zaman yarsa a gida babu mijin aure, magana ake masa amma sam hankalinsa ba ya kan masu maganar, "Haba Idi kai ka wani dage sai magana kake masa ya yi banza da kai shin dole ne sai ka yi masa maganar?" Daya daga cikin mutane hudun da ke zaune a kofar wani shago ne yake maganar.
  "Ba haka ba ne Musa, kaima kasan dai musulmi ɗan-uwan musulmi ne, kuma na tabbatar da Malam Usman ya ji zai amsa." Malam Audu dake zaune gefe ya faɗa.

  "Sannu Audu kai kana tunanin ya ji abin da kake faɗa kenan? Tab ai yanzu sam Malam Usman baya cikin nutsuwarsa mutumin da ke da ƙatuwar budurwa a gida babu mijin aure ta ina zai samu kwanciyar hankali?"
  "Tabbas kuwa ai dama duk wanda ya sai rariya yasan zata zub da ruwa, ka duba lokacin da ake tashen zuwa wajenta da aure amma suka yi biris gashi yanzu suna nema ido buɗe amma ya gagara." Cewar ɗayan mai amsa suna Malam Isah.

  "Ai ni nan Allah Ya ƙara kawai zan yi masa don ba wani ya hana shi auranta da wuri ba, sai a fara shiga malamai da bokaye ko za a samu masansani"
  "Hahahah...!" Gaba daya suka kwashe da dariya banda Malam Umaru da ya ce, "Allah Ya ganar da ku amma sam abin da kuke yi ba shi da kyau, ku zauna kuna gulmar dan-uwanku musulmi." Yana gama faɗin haka ya suri takalminsa ya bar wajen. Tsaki su ka ja su ka ci gaba da gulmarsu don ba hira suke ba gulma ce zalla.

  ***

  Kamar kullum, Zulaiha na zaune tana karatun Alkur'ani mai girma ta ji sallamar mahaifinta. Ta dakata da karatun, ta amsa cikin girmamawa.
  "A'a sannu Zulaiha ana ta karatun ne?"
  "Eh." Ta amsa fuska cike da mamakin yadda Abbanta ya shigo fuska sake. Bayan gyara zama yana kallonta ya ce.
  "Kina jina ko?" Ta ƙara nutsuwa bayan gyaɗa kai.
  "Ki saurareni da kyau magana zamu yi mai mahimmanci, magana ce akan aurenki da na bayar. Kin san dai yadda na ɗaga miki ƙafa har zuwa wannan lokaci ko?" Gyaɗa kai ta yi kamar ƙadangaruwa, don ta kasa furta komai, tana jin shi ya cigaba.
  "Yau Allah ya amshi addu'ar mu, domin kuwa ya kawo miki mijin aure har gida..."
  "Mijin aure?" Mahaifiyar Zulaiha ta fada daidai lokacin da take fitowa daga ban daki
  "Eh! Mijin aure." Ya bata amsa kai tsaye.
  "Kai Masha Allah! Gaskiya na yi murna da jin wannan daddaɗan labari. Daga ina kuma yake?"
  "Ɗan nan garin ne, ba kowa bane sai Garba..."
  "Wanne Garban kenan?"
  "Garba Calli!" Ya dire maganar a hasale. Ganin haka sai ta sanyaya murya cikin lallashi ta ce.
  "Haba Malam Calli fa? Mutumin da duniya ta shaida dan iska ne, kuma shekaranjiya ya dawo garin nan, amma ka ce shi za ka aura mata?"

  "Shi na yi niyya, kuma shi zan bata." Ya furta hakan cikin masifa, bai jira cewar ta ba ya bar gidan. Kuka Zulaiha ta fashe da shi na baƙin ciki wunin ranar zubur.
  Wasa-wasa ƙaramar magana ta zama babba, domin kuwa Malam Usman ya dage da shirye-shiryen biki, sosai hankalinta ya yi ƙololuwar tashi, don har cikin zuciyarta tana tunanin yadda rayuwarta za ta kasance a gidan Calli, mutum da ya gama zagaye duniya ya bar garinsa na haihuwa, har na tsawon shekaru goma, sai rana tsaka ya dawo, shi ne zai zama mijin aurenta, abin haushi duk wannan abin da ake ko sau ɗaya kafar Calli bata taɓa takowa da sunan zuwa wajen ta ba, ta dai kallon ikon Allah.

  Ranar wata Laraba, ana saura kwana uku daura aure, Zulaiha ta samu mahaifinta a dakinsa cikin girmamawa ta gaishe shi, sama-sama ya amsa mata don kuɗi yake kirgawa. Shiru na mintina biyar suka biyo bayan zaman da Zulaiha ta yi, sai zuwa can ta ce.
  "Baba dama zuwa na yi na fada maka, don Allah ka sanya Garba ya zo mu je asibiti domin a yi mana gwaji, don gudun kamuwa da wata cutar." Ai ko kamar jira yake ta gama sai ko ya hauta da faɗa, inda ya tabbatar mata da babu wani zuwa gwaji da za su je, ko so take ya faɗa masa haka, shi kuma ya ce ya fasa auren, haka jiki a sabule ta bar ɗakin.

  Ranar juma'a aka ɗaura auren Zulaiha da Garba, a kuma yammacin ranar da ƙarfe shida, aka sadata da dakinta cikin rakiyar addu'ar mahaifiyarta, masu kawo ta ba su wani jima ba suka mata sallama, sai ita ɗaya a gidan tsananin tsoro ya kamata, haka bacci ya ɗauke ta saukar gigitaccen mari ya farkar da ita, da mamaki take kallon Calli wanda ya zube a kan gado ko a jikinsa, tun daga wannan rana rayuwar Zulaiha ta shiga cikin matsala, domin dai Garba cikakken dan duniya ne, sam baya sarara mata ga duka ga matsin da yake mata, a haka dai har ta yi wata biyar a gidan, duk ta fige ta rame ta sauya kamani.

  Shi kam gogan sai ya yi kwana uku har hudu baya gari, a hankali ciwo ya fara kama Zulaiha tun tana iya daure wa har dai ta nufi asibiti, don ciwon ya ci karfin ta, tana ko zuwa taga likita baya tambayoyi ya bata takardar don a gwada ta, cikin lokaci ƙalilan aka gama mata gwaje-gwajen har da na HIV take aka gano tana dauke da wannan cutar, sosai ta rikice da jin wannan sakamakon.

  Ko da ta bar asibiti bata zame ko ina ba sai gidansu. Sosai mahaifinta ya firgita da jin bayanin Zulaiha, aiko take ya kira Calli, babu kunya Calli ya fada masa, eh yasan yana dauke da wannan ciwo, dama don ya goga mata ciwon ne ya yadda ya aureta, iya ruɗu Malam Usman ya shiga, ya yi matuƙar nadama da abin da ya aikata ga shi yanzu abin da ya faru.

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Nakasar Zuci

  Posted Dec 7

  "Ki tafi gidanku na sake ki!" Runtse idanu na yi jin sautin muryar Adamu a kaina, yana furta kalaman da suka kusan sanya ni haihuwar cikin da ke jikina. Da sauri na dago jajayen idanuwana da suka gajiya da kuka na sauke a saitin sa. Wani irin tashin hankali da ciwon r...

 • Duk mace na bukatar sanin wadannan abubuwa guda 6 kafin ta yi aure

  Posted Nov 29

  Aure abu ne mai matukar muhimmanci a rayuwar mutum don ya zamo cikar mutuntaka ta dan adam. Allah madaukakin sarki ya halicci mata daga jikin mazaje domin su matan su zama natsuwa a gare su, ya kuma sanya soyayya da shakuwa a tsakanin wadannan jinsin guda biyu.  A...

 • Ko kun san adadin yawan nutrients da jikinku ke bukata?

  Posted Nov 24

  Samun abinci mai kyau da kara lafiya, wato good nutrition, ya dace ya zamo daya daga cikin burin kowani dan adam da ke raye.  Ya kasance mun san adadin yawan abinci mai kyau da jikkunanmu ke bukata, sannan mun san addadin yadda ya kamata mu rinka motsa jikinmu, kum...

 • Yadda ake hada buttered chicken

  Posted Nov 22

  Assalamu alaikum barka da sake saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau insha Allahu zamu gabatar da shirin yadda za ki hada buttered chicken. Abubuwan hadawa Kaza Ginger and garlic paste (citta da tafarnuwa)  Albasa Yoghurt Butter Fresh cream ...

 • Yadda ake hada papaya drink

  Posted Nov 22

  Assalamu alaikum barka da sake saduwa a cikin shirin Bakandamiya a yau insha Allahu zamu gabatar da shirin yadda za ki hada natural papaya drink Abubuwan hadawa Papaya (gwanda) Sugar Ruwa Zuma (optional) Yadda ake hadawa Farko za ki yanka gwanda ki cire ma...

 • Alamomi 8 da za ki gane cewa namiji da gaske yake

  Posted Nov 22

  So wani irin yanayi ne da kan sa mutum ya tsinci kansa a cikin wani hali na daban. Sai dai mi? Abu ne shi mai dadi a kuma gefe guda abu ne mai matukar ban tsoro. Duk da kasancewar sa hakan bai zama abin ƙyama ga mutane ba. Da yawa kan rungume shi da hannun biyu. A gefe...

View All