Featured Create an Ad

Makalu

Blogs » Kagaggun Labarai » Akwai Illah: Babi na Daya

Akwai Illah: Babi na Daya

 • Wannan rubutu ba rubutu ne da kuka saba cin karo da shi ba, rubutu ne da ya dauko zallar gaskiya. Na so publishing dinsa a lokacin da na bada tsokacinsa, amma hakan bai yiwu ba saboda dalilan da na bar wa kaina sani.

  Ga Akwai Illah ba a dunkule ba, ga akwai Illahn da mutane da yawa suke neman hanyar samunsa, ya same ku cikin sauki.

  Gyara, kushe komai ma ina maraba dashi in ya zo ta hanya mai kyau. Nagode.

  *****

  Maiduguri, Borno State, 8:50am

  "Duk da rayuwa tana ci gaba da juya ni yanda ta so, ban fasa jin sassauci cikin lamurana ba tunda na riski labarin salwantar Kaltum".

  Murmushi take sakarwa kanta tana k'arewa surar jikinta kallo a doguwar mirror [standing mirror] d'in da ke mak'ale jikin bangon fankacecen d'akinta.

  Juyi tayi mai ban sha'awa tana k'ara fad'ad'a murmushinta.

  "Wayyo ni Fanne dad'ina, ko ba komai zan fara sabuwar rayuwa, ga dukkan alamu Na'eem ya k'yasa cikin kwanakin nan. Me ya fi min hakan dad'i? Duniya juyi-juyi".

  Murmushinta bai b'ace ba, tsantsar farincikinta da annurinta na bayyana saman fuskarta.

  Ji take kaf duniya a yau, babu mahaluk'in da ya kai ta farinciki.

  D'ago kanta tayi tana daidaita dubanta a kan k'aton hotonta da wata matashiyar budurwa, wanda a kallo d'aya zaka bawa kowaccensu shekaru ashirin da 'yan kai.

  Murmushinta bai gushe daga fuskarta ba ta shafa hoton tana mai kad'e jikin, duk da ba k'ura ko kad'an a jiki.

  "Allah sarki Kaltum aminiya, ina rasa dalilin da yasa wani lokaci nake jin ina tausaya miki a cikin zuciyata, bayan kwata-kwata bai dace inyi hakan ba, farinciki da annashuwa yakamata in dauwama a ciki, rashinki a gareni alkhairi ne.

  Me nake k'aruwa da shi a wurinki a lokacin da muke tare? Meh kike saka min da shi a duk lokacin da alhairaina suka yawaita gareki? Sam babu komai, sai bak'in ciki da tashin hankali".

  A lokaci d'aya annashuwar fuskarta ya kau, ta shimfid'a b'acin rai da tantsar tsanar da take yi mata bisa fuskarta. Abubuwan da ya faru a baya ya shiga dawo mata cikin kwanyarta.

  "Na tsaneki, na tsani duk wanda zai baki farinciki, na tsani murmushinki, na tsani..."

  Bata samu damar k'arashe zancenta ba, sakamakon k'arar wayarta da ya katseta.

  Nauyayyar numfashi ta sauk'e tana mai kai dubanta kan gado inda wayar ke ruri.

  Hannunta da ke kan hoton ta janye sai dai cikin rashin sa'a, hoton ya gauce yana barazanar fad'owa. A hanzarce ta cafke sannan ta janyo wayar tana duba mai k'iran nata.

  "Na'eem!"

  Ta karanta a fili tana mai wadata fuskarta da murmushi, bata d'auki wayar ba sai da ta kalli hoton hannunta, ta kad'a gashin idanunta murmushi bai bar leb'b'anta da ke wadace da jan baki mai d'aukan hankali ba.

  "Bai kamata in rasa ki kuma in rasa hotonki ba Kaltum".

  Danna wayar tayi ta mak'ala a kunnenta tana mai lumshe idanunta.

  "Hello" Ta furta cikin sanyayyar muryarta.

  *****

  Lagos, Najeriya

  High court of Lagos state (Lagos Island)

  Ranar Litinin, tara ga watan Junairu na shekarar dubu biyu da goma sha bakwai. Farfajiyar kotun da ke Lagos Island (High court) cike yake da mutane masu d'abi'a, addini da yare daban-daban.

  Wasu na shige da fice cikin ofisoshin Kotun, wasu kuwa na kai komo da takaddu a hannunsu suna isar da su inda ya dace.

  Motocin d'aukan masu laifi zuwa gidan yari guda biyu na ajiye gefe guda. Jami'an 'yan sanda na zube birjik ko ta ina, wasu na rik'e da masu laifi wasu kuwa na tsaye gefen motocinsu.

  K'arfe Tara cif agogon da ke sak'ale saman kotu yayi k'ara, yayi dai-dai da shigowar motar Barrister Fatima farfajiyar kotun.

  Wuri ta samu ta ajiye motar, ta fito rik'e da rigarta da sauran muhimman takaddun da zai anfaneta a zamansu.

  Sanye take da doguwar riga na kanti fari, ta yane kanta da bak'in mayafi. Babu komai fuskarta sai foda da ta shafa da man baki.

  Farfajiyar kotun ta tsaya kallo, duk da zuciyarta na cike da fargaba, ko kad'an fuskarta bai nuna hakan ba.

  Cikin izza da k'asaita take ajiye takunta, tana mai sawa a ranta babu wanda zai iya ja da ita a kan gaskiyarta.

  Yawu mai tauri ta had'iye jin taku daf ita, bata juya ba, haka zalika bata nuna firgicinta a fili ba, a dake ta ci gaba da takunta idanunta na kan k'ofar da take son shigewa.

  "Uhm! Uhm!!" Barrister Anthony ne ya yi gyarar murya, yana mai sassarfa dan ya cimma mata.

  "Barrister Fatima!"

  Amon muryarsa ya dakatar da ita, ta waigo tana mai wanke zuciyarta dan ta samu damar amsa duk wani kalma da zai fito daga bakinsa.

  "Yes Barrister Anthony, how may I help you? (Na'am Barrister Anthony, da me zan iya taimakonka?)".

  Suit d'in jikinsa ya gyara, murmushi shimfid'e saman fuskarsa. Kallonta ya ke yi daga sama har k'asa, yana kallon k'ank'anuwar halittarta a wurinsa.

  A kullum yana mamakin jarumtarta da hak'ikancewa a kan abunda ta san ba za ta iya gamawa ba, ba za ta tab'a samun nasara ba, me na ji da kai bayan ya san duk kafiyarta da naci irin nata ba za ta iya kayar dashi ba? Shin ta manta suna gida ne Najeriya?

  Murmushin takaici ya yi, fuskarsa na cunkushewa, yana k'ara b'ata sauran kyawun da take gani a zahiri.

  Jin shirun nasa yayi yawa, ba za ta iya jure kallon da suke sakarwa juna ba, shi yana mata na raini, ita kuwa na wurga masa na "Ka yi kad'an, dan nice da gaskiya".

  "Ina da abun yi Barrister Anthony".

  "Har yanzu kina kan bakanki kenan? Na d'auka mun wuce wannan gab'ar Barrister".

  Matsowa yayi daf ita, ganin ta dakata tana dubansa.

  K'amshin turarensa da ya had'u da warin jikinsa ya zaryo hancinta, tuni 'yan hanjinta suka hautsina, ta kawar da kai gefe ta ja baya tana had'e fuska.

  "Ba za ki iya ja da ni ba duk kwanyarki, Hamza ya cancanci mutuwa, d'an ta'adda ne rik'akk'e".

  Ware idanunsa yayi yana mai nuna mata fahimtarsa shine gaskiya, ko ta k'i ko ta so.

  Kalamansa, ya shiga tsakiyar zuciyarta ya k'ara tsananta bugunsa, ya ?ara mata tsoro da fargaban wannan shari'a mai zafin gaske.

  Dakewa ta yi, ta dubesa da kyau, ko da wasa bata yadda ta nuna tsoronta saman fuskarta ba, ta yi iya ?ok'arinta wurin lullub'ewa da murmushi mai k'ayatarwa.

  "Good luck Barrister Anthony!" Muryarta a dake ya fito, bai nuna tsoro ko rauni ba.

  Ta juya cikin takunta, ta shige cikin ofishin tana barin bak'in ciki, b'acin rai da mamakinta a zuciyar Anthony.

  *****

  Garin Damaturu, 9:30am

  Tafe take tana sanye da riga da siket na atamfa, idanunta na rufuwa a hankali tana kokuwar bud'ewa.

  Layi take kamar wacce ta sha kayan maye, hannunta rik'e da cikinta tana yamutsa fuska.

  Kayan jikinta yayi bak'i, ya canja launi daga kalar kore zuwa wata kalar daban tsabar daud'a, farat d'aya in aka ce a k'idaya tsawon lokacin da ake sanye da wannan kayan zaka iya d'iba masa shekara da d'ori, sai dai la'akari da yanayin wacce ke sanye da kayan zai sa kayi tunanin akasin hakan.

  Gashin kanta bud'e yake, datti da k'asa turbune ya mamaye ya koma kalar hoda, kitson kanta ya cunkushe ba'a iya ganin tsagunsa bare a yi maganar fatar kanta.

  Siket na jikinta a yage, ana iya ganin farin siketin da ke ciki {under wear} wanda ya koma ruwan k'asa dan datti, ga jirwaye da shatin fitsari da ya mamaye.

  "Argghhh!" Ta furta lokaci d'aya tana d'aga k'afarta na dama.

  Bata iya sauk'ewa ta ci gaba da takunta ba, sai ma zaman dirshan da tayi a tsakiyar hanya tana d'ago k'afar.

  Hannunta ta sa a dai-dai inda jini ke b'ulb'ula sakamakon kwalbar da ya shige ciki.

  Ba tare da ta kula ko ta ji tsoro ba ta sa hannu ta cire kwalbar, tana mai jin rad'ad'insa har cikin kwanyarta.

  K'ara ta sake mai k'arfi cike da rauni, wanda ya fito daga ?asar zuciyarta, yana bayyana rauninta da azabar da take ciki.

  Hawaye masu ?umi ke sauk'o mata, sai dai hakan bai rage ko da kwayar zarra na daga cikin tashin hankali da azabar da take ji ba.

  "Allah sarki!"

  Cewar wani bawan Allah da ke zaune a k'ofar wani shago da ke gefenta.

  "Yarinyar nan tausayi take bani Yusufa".

  Tsaki Yusufa ya ja bayan ya kalli wannan mahaukaciyar, ya ci gaba da tattara kayan d'inkinsa.

  "Matsalata da kai kenan wallahi Jamilu, shegen tausayi, ka sani ko asiri tayi ya koma kanta? Zaka tausaya mata a matsayin me? Mutane nawa suke yi wa wani asiri ya koma kansu? Kana ganinta ka san babu abinda ta rasa a rayuwa, fara kyakkyawa, ina tabbatar maka ita ta yi asirin, k'aik'ayi ya koma kan mashek'iya, bar mu da labarin mahaukaciya mu yi abinda ya fisshemu".

  Muryarsa ya sauk'e can k'asa yana matsowa daf da Jamilu.

  "Kar ka sha mamaki 'yar lek'en asiri ce, ka rufawa kanka asiri".

  Jamilu bai tanka sa ba, ya cigaba da kallon yanayinta, har lokacin bata taso daga mazauninta ba.

  Fuskarta take kwab'awa tana rik'e cikinta.

  'Da alamu akwai abun da yake damunta' cewar zuciyarsa.

  Mintuna uku sannan ta samu damar mik'ewa.

  K'afar da ta soke ta fara takawa, zafin da ta ji tun daga k'afafunta har zuwa k'wak'walwarta ya sa ta dakata tana lumshe idanunta.

  "Subhanallah! Yusufa, ka ga abinda ya samu yarinyar nan? Jini ne ya zo mata, ka ga yanda ya b'ata mata jikinta. Tana ta rik'e ciki ashe ciwo cikin ya ke. Allah Sarki!".

  Bai tsaya ya ji daga bakin abokin nasa ba yayi wurinta, wuf Yusufa ya rik'esa.

  "Ai wallahi ba zan barka ka je ba, ka je ka mata me? Ina gaya maka ita tayi asiri ya dawo kanta zaka ce zaka wani taimaketa? Ita ta k'i taimakawa kanta shine kai zaka taimaka? Billahi baka isa ba, zamanin yanzu wa yake taimakon wani?".

  "Dan girman Allah ka barni in taimaka mata, tana buk'atar taimako".

  Da iya k'arfinsa Yusufa ya shigar da shi shago, duk iya k'ok'arinsa na k'wacewa daga hannunsa kasawa ya yi.

  "Allah Jamilu bazan barka ka je ba, ka ma daina k'ok'arin k'wace kanka".

  Daidaituwa Jamilu ya yi ya gantsara masa cizo, ya fizge jikinsa ya fice daga shagon zuwa wurinta.

  Sai dai sama tayi ko k'asa ya kasa ganewa, ya duba gabar ya duba yamma babu ita babu alamarta, duk iya hangensa da waige-waigensa bai ganta ba.

  Tsaki ya ja yana mai jin takaici, cikin ransa ya ke jin bak'in cikin rashin ganinta.

  "Wannan wace irin rayuwa ce?" Ya furta a fili, idanunsa sun canja launi dan b'acin rai.

  *****

  Lagos, Najeriya, 11:00am

  "Court!" Cewar magatakarda tare da mik'ewa tsaye da sauran mahallara kotun dan shigowar Alk'ali.

  Bayan zaman Alk'ali kowa ya samu wuri ya zauna aka shiga rattabo k'arar da za'a fara.

  "Hamza, d'an kimanin shekaru ashirin-da-biyar ya kawo k'arar sojin Najeriya, bisa kama shi da su ka yi matsayin d'an ta'adda, bayan shi bai kasance d'aya daga cikinsu ba".

  Tashi ya yi daga mazauninsa bayan ya zo aya, ya isa wurin Alk'ali ya russuna ya mik'a masa takardar sannan ya koma mazauninsa.

  *****

  Ku latsa nan don ci gaba da karanta babi na biyu.

  Alkalamin Maryamerh Abdul

No Stickers to Show

X

Da Dumi-Dumin Su

 • Ku latsa nan don karanta labarin Saurin Fushi Na Kawo Da Na Sani. A wani ƙauye akwai wani mutum  ana kiran sa Abu Sabiru, ya kasance mai tsananin haƙuri da kawar da kai akan wasu al’amura. Dalilin da ya sa ma ake kiransa Abu Sabiru kenan. Yana zaune tare da matarsa kyakkyawar gaske ...
 • Ku latsa nan don karanta darasin rana ta uku. DARASI NA 1 Matakan rubutun gajeren labari A jiya mun yi bayani akan matakan da ake bi wajen tsara labari, yau kuma za mu bayani a takaice kan matakan da ake bi wajen rubuta ingantaccen labari. Waɗannan matakai ba tabbatattu ba ne, ma'ana ba wajibi ne...
 • Ku latsa nan don karanta babi na shida. Habeeb na kwance a kan doguwar kujera ya ji an murɗa handle ɗin ɗakinshi tare da turo ƙofar a hankali. A hankali ya buɗe idanunsa da suka yi nauyi sakamakon ciwon kan da yake fama da shi. "Fateemah" ya faɗa a ransa, lokacin da ya kai duba ga Jummai da ke ts...
 • Uwargida ba za ki yi dana sanin koyan yadda ake yoghurt in fruits ba. Domin kuwa kayan dadi ne sosai da sosai kuma cikin mituna kalilan za ki hada. Ba a ba yaro mai kiwiya!!! Wannan recipe yana daya daga cikin recipes da muka koyar a zauren Free Ramadhan Classes with Umyuman a nan Bakandamiya. Abu...
 • Hadin special salad nawa na musamman ne! Ga sauki ga dadi, uwargida sai kin gwada za ki bani labari! Wannan ma yana daya daga cikin recipes da muka koyar a Ramadan a shirin girke-girkenmu wadda aka gabatar a zauren Free Ramadhan Classes with Umyuman. Shin ko kin tuna gashin tsokar kaza da muka koya...
 • Red velvet cake, cake ne da mutane da dama suke so kuma kuma suke son ci. Saboda haka, akwai hanyoyi daban-daban na yin red velvet cake, ga yadda na ke nawa cake din na kawo muku. Wannan yana daya daga cikin recipes da muka koyar lokacin Ramadan anan Bakandimya. Domin ganin duk jerin recipes din da...
View All