Featured Create an Ad

Makalu

Blogs » Kagaggun Labarai » Duhun Damina: Babi na Bakwai

Duhun Damina: Babi na Bakwai

 • Ku latsa nan don karanta babi na shida.

  Saturday 4:00pm

  Cikin atamfa riga da skirt ta shirya, ta ɗaura ɗan kwalinta irin ta Zarah Buhari wanda ya ke matuk'ar yi mata kyau. Ja gira ta ja mai kyau, gwana ce wurin kwalliya ba dama.

  Ta shafa lipstick nude, kasancewar bata cika son kwalliya mai yawa ba. Idanunta ta sa kwalli, ta ja eyeliner wanda ya basu daman fito da zahirin yanayinsu.

  A gaban madubi ta tsaya, tana kallon kanta ko akwai abunda yayi nakasu a jikinta. Sahibinta, Annurin zuciyarta na tafe zuwa gareta, dole ta bashi tsantsar kyau da kwalliyar da yake buk'ata.

  Samun kanta ta yi da sakar wa kanta murmushi, tana yaba kyaun surarta, da kuma kwalliyar da ta cancad'a. Koren atamfanta ya karb'eta, anya ma akwai kalar kayan da Juwairiyya zata sa ya kasa amsan fatarta? Babu a tunaninta, sai dai in bata sa shi yanda yakamata ba.

  Turarukan gaban madubin ta fara zara ɗaya bayan ɗaya tana feshe jikinta, bayan ta gama da su ta ɗauko humrah ta ɗiba cikin hannunta tana gogawa a kusurwan jikinta. Hatta bayan kunnenta sai da ta shafa, tana mai shafe sauran da ya rage a hannunta da kuma fuskarta.

  Bata san ya aka yi ta fad'a farin cikin nan ba, ba yau ne farkon ziyararsa wurinta ba, amma ji take kaman yau zata fara ɗaura idanunta a kansa. Ko dan muryarsa na jiya da kalaman ƙaunarsa gareta ya sa ta ji hakan?

  Numfashi ta sauk'e, tana ci gaba da kallon kanta a madubin nan, tana tuno farkon had'uwarsu, tana tuno ɗauke kai da basarwarta a lokacin da ya tunkareta a cikin makaranta.

  Ita ta san ya tafi da imaninta, amma macen da ke cikin jikinta, ba zai barta ta bada kai ba. Hakan ya sa ta ƙi sauraransa ya biyota har gida cikin motarsa.

  A yanzu haka, da suka yi shekara tare da juna, bazata iya fad'an yanda aka yi suka surke suka zama abu guda ba. Tana jinsa can cikin ɓargonta, tana jin duniyarta ya ta'allaka da nasa.

  "I love you (ina sonka) Abdulwahab ɗina!"

  Ta furta a fili, ta rungume hannayenta tana lumshe idanunta tare da jin soyayyarsa na fizgarta, ina ma, ina ma tana da iko?

  Abunda ta tuno ya sa ta bud'e idanunta, ta turo bakinta tana kallonta jikin madubin. Har ranta tana son ya furta kalaman nan, tana son kasancewa tare da shi, tana son su zama abu ɗaya, tana son duniya su shaida da halaltacciyar zamansu. Amma ya zata yi?

  Ƙarar wayarta yasa ta sauk'e ajiyar zuciya, tana mai kawar da tunaninta ta ɗauko ta kara a kunnenta.

  Gyalenta kawai ta ɗauko, ta sanar da Mamanta isowarshi kafin ta fice dan shigo dashi ciki kamar yanda ta saba.

  *****

  Motarsa ya bud'e ya fito bayan ya kashe wayar. Zuciyarsa na zumud'in ganin sahibarsa, yana son ganin kwalliyar da tace zata yi masa saboda ta yi masa kyau.

  Jikin motarsa ya jingina bayansa, ta yanda zai sark'e idanunsa cikin nata da zarar ta fito zuwa garesa. 

  Anya akwai wasu kalaman da zai iya aiyana soyayyar Juwairiyya a zuciyarsa? Baya tunanin hakan, amma ba zai yi ƙarya ba, tun da yake, tunda Allah ya bashi daman furta kalman so ga ɗiya mace, bai tab'a jin irin soyayyar da yake yi wa Juwairiyya ba.

  Ta ko wani fanni ta had'u ne, she is a wife material (matar da ya dace a aura). Ga ilimi, boko da arabi, ga nutsuwa, ga iya kwalliya, ga kyau. Shi dai ya yi dace in ya sameta, yayi dace idan iyayensa suka bashi dama kafin wani ya yi masa ƙafa.

  Kunyarta, yafi komai yi masa dad'i. Yanzu zata fara sauk'e kai tana rufe fuska da hannayenta. Wanda duk cikin 'yan matansa bai tab'a samun hakan ba. Shi ba ɗan iska bane, bai tab'a zina da 'yar kowa ba, amma zai bada shaidar kwarai akan Juwairiyya, abunda sauran 'yan mata zasu iya basa bazata tab'a iya damk'a masa ba.

  Fitowarta ya sa ya dawo da tunaninsa wuri guda, yana ɗaura idanunsa akan ƙafafunta da ta sanya dogin takalma, da ya ƙara bawa tafiyarta armashi. 

  Murmushi da zallar farin ciki ya samu kansa a ciki a lokacin da idanunsa ya sauk'a kan fuskarta da ke cike da annuri.

  Bai iya amsa sallamarta ba har ta iso daf da shi, ta janyo mayafinta tana rufe fuskarta.

  "Ya yi yawa kallon nan, ka san bana son kallon da idanunka suke min".

  "Ya zanyi toh Juwairiyya? Sonki duk ya tagayyara ni".

  Dariya ta sakar masa, tana mai jin dad'in kalamansa.

  "In akwai kalmar a hausa kenan ko? Mu shiga ciki".

  Bata barshi ya ce komai ba ta shige gaba yana biye da ita a baya. Idanunsa na yawatawa cikin shigarta, yana kallon bayanta da take sarrafa shi a hankali.

  Runtse idanunsa yayi tare da yi wa kansa fad'a, sai dai kafin ya bud'e idanunsa tuni ya ji ta cikin jikinsa, turarukanta na masu kai ziyara hancinsa.

  Bai san lokacin da ya rik'eta ba, yana mai kai bakinsa kan wuyanta tare da sauk'e numfashi. 

  Hannunta ta yi anfani dashi wurin turesa, tana ja da baya ganin karon da suka yi na neman haddasa abunda bata yi zato ba.

  Gam ya rik'eta, yana kasa sarrafa kansa. Bakinta ya ke laluba amma ta ƙi basa had'in kai. Sai dai shi da ya yi niyya, tuni yasan hanyar da ya bi, yasa ta langwabe a jikinsa, tana sallama masa kanta.

  Bata saba ba, bata tab'a tsintar kanta cikin rik'on namiji ba. Bata tab'a samun kanta cikin irin wannan yanayi ba. Hakan yasa hawaye masu d'umi suka fara zaryo mata, amma jikinta bai iya motsin kirki ba.

  A kuncinsa ya ji hawayenta, bai dawo hayyacinsa ba sai da ya tuno inda ya ke da kuma wacce ke tare dashi. Hakan yasa ya cire bakinsa a hankali yana runtse ido, tare da jin kunyar aika-aikar da ya yi. Tsoro sosai ya shiga zuciyarsa, yana mai jin takaicin aikinsa.

  Shin me ya hau kansa? Ya aka yi hakan ya faru garesa?

  Zama ta yi a gefe tana ci gaba da zubar da hawaye bayan ya saketa, ita kanta bata san me dalilin kukan nata ba, bata san me yasa ta ji tsoron abunda ya aikata mata ba. Ta dai kasa sarrafa kanta, ta kasa ajje hankalinta wuri guda bare ta san abun yi.

  "I'm... I'm very sorry (Ki yi hak'uri)"

  Ya furta cikin sark'ewar murya, jikinsa na rawa. Ya rud'e iya rud'ewa ganin yanda take kuka ba tare da ta iya kallonsa ba.

  Bata tanka sa ba, ta goge hawayenta ta mik'e cikin takunta. Ko kallonsa bata yi ba ta koma cikin gidansu, tana mai barinsa inda yake tsaye, yana magiyar ta saurareshi ba laifinsa bane.

  *****

  8:00pm

  Sallah ya idar cikin ɗakinsa, yana jin jikinsa a mace har a wannan lokaci. Fargaba da tsoron hukuncin Juwairiyya yake yi, ta ƙi amsa wayarsa tun dawowarsa, ya tura mata sak'on ban hak'uri amma kamar bata gani ba.

  Daga lokacin zuwa yanzu, ya rasa abunda yake damunsa. Ya rasa wani matsala zai sa a gaba. Iyayensa ko kuma Juwairiyya da ta ke fushi dashi?

  "Ya Rabb!" 

  Ya furta yana mai huro iskar bakinsa, kwanyarsa na ci gaba da cajin neman mafita.

  Bai kai ga samun mafita ba wayarsa ya ɗau ƙara, cikin hanzari ya duba a tunaninsa Juwairiyyarsa ce, a bar ƙaunarsa. 

  "Ina wuni Daddy!"

  Ya furta bayan ya kara a kunnensa.

  "Ok, gani nan zuwa".

  Ya furta a tak'aice yana mai wurgi da wayan nasa kan gado.

  Kamar ba zai mik'e ba ya tashi, ya wuce ɓangaren mahaifinsa yana mai tunanin dalilin da yasa ya ƙirasa a wannan lokaci.

  *****

  Zafin da take ji a cikin idonta na dama yasa ta juya dan gyara kwanciyarta, jin zafin yana ratsata har cikin kwanyarta ya sa ta yi hanzarin juyawa tare da rik'e idon nata.

  Abu mai yauk'i ta ji yana bin hannunta, cikin jin zafin idanunta ta sauk'o da hannunta tana duba abun da yake fito mata.

  Ƙananan tsutsotsi ta gani farare masu rai suna yawo a tafin hannunta. Cikin k'yama da tsoro ta shiga yarfe hannunta tare da mik'ewa dan shiga ban ɗaki jin idonta na ci gaba da zafin da bata san ya zata kwatanta ba.

  Kafin ta isa ban ɗakin take numfashinta ya fara ɗaukewa, tana jin kamar ana fizgan numfashin tare da kwararo ruwan tsutsotsi daga idanunta.

  Cikin tsoro da azaba ta dafe idonta da hannayenta dukka biyu, amma hakan bai hana su ci gaba da zubowa ba.

  A daddafe ta shiga ban ɗakin, ta tsaya gaban madubin bayan gidan tana ƙok'arin bude idonta dan ganin abunda ke damun idanunta.

  Abun da ta gani ya sa dukkan gashin jikinta suka mik'e. K'yama, tsoro da fargaba yana nuk'urk'usar zuciyarta.

  Idonta na dama ne ya rub'e, yana ci gaba da fitar da ƙananan tsutsotsi ba ƙak'k'autawa. Ga zafin da yake mata har cikin kwanyarta.

  Motsin Mamanta ya sa ta k'wala mata ƙira dan ta kawo mata ɗauki akan abunda yake samunta. Sai dai ita kanta bata ji muryarta ba bare mahaifiyarta da ke kusa da bakin ƙofar toilet ɗin ta ji ta.

  Sautin muryarta ta ƙara, tana ci gaba da ihun neman agaji daga mahaifiyarta, amma ina, mahaifiyarta bata san tana yi ba.

  Kuka ta shiga yi, tana jin duniyarta ya zo ƙarshe, zafin idanunta na ci gaba da kai suka ga dukkan gabb'an jikinta. Numfashinta ya yanke, tana jin kamar ana zare ranta, ana fizge numfashin da yake bata daman ci gaba da rayuwar duniyarta"

  Firgigit ta farka daga mummunar mafarkin da ta yi, tana furta innalillahi wa Inna ilaihi raji'un.

  Idanunta ta fara tab'awa, tana duba lafiyarsu. Duk da ta ji su lafiya, bai sa zuciyarta nutsuwa ba, da gudu ta shige ban ɗaki tana duba idonta jikin madubi.

  Duk da ganin tabbacin lafiyar idanunta, bai hana tsoro ci gaba da ratsata ba. Zufa na ci gaba da keto mata, yana haddasa mata jin zafin da bata san ina zata ajje yanayin da take ji ba.

  Cikin tsoro ta koma kan gadonta, tana jin duniyarta ya kife. Hawaye ya shiga sauk'o mata, tana runtse idanunta dan ta daina ganin mummunar mafarkin da ta gama gani, sai dai kamar a wannan lokaci take yinsa. Tsoro ya shigeta matuk'a.

  "Na shiga uku ni Juwairiyya!"

  *****

  Dan mutum yana istimna'i bai zama ya rasa kunyarsa ba, bai zama ba zata ji tsoron kasancewa da namiji kamar yanda kowace budurwa take ji ba. Babancinsu kad'ai kenan da mai yin zina, ina nufin mai zina tana rasa kunya, kuma tana rasa tsoron kasancewa da namiji. 

  Ban sani ba ko kun gane nufina?

  Ku latsa nan don ci gaba da karanta babi na takwas.

  Alkalamin Maryamerh Abdul

No Stickers to Show

X

Da Dumi-Dumin Su

 • Thu at 7:22 PM
  Posted by Bakandamiya
  Ku latsa nan don karanta babi na bakwai. Bata iya komawa bacci ba tunda ta tashi daga wannan mafarkin. Ta yi kuka har sai da idanunta suka fara yi mata zafi, gangar jikinta da zuciyarta suna yi mata rad'ad'in da ita kad'ai ta san yanda take ji. Ƙirar sallahr asuba yasa ta mik'e cikin hanzari, tana...
 • Mece ce cutar mantuwa (amnesia)? Idan aka ce mutum na fama da cutar amnesia dai to ana nufin cutar da ke sa mutum ya manta abubuwa kamar abubuwan da su ke zahiri, da kuma bayanai game da wani abu ko kuma manta abinda ya faru da su da makamanta ire-iren wannan mantuwa. Mutane da su ke dauke da wanna...
 • Ku latsa nan don karanta labarin Saurin Fushi Na Kawo Da Na Sani. A wani ƙauye akwai wani mutum  ana kiran sa Abu Sabiru, ya kasance mai tsananin haƙuri da kawar da kai akan wasu al’amura. Dalilin da ya sa ma ake kiransa Abu Sabiru kenan. Yana zaune tare da matarsa kyakkyawar gaske ...
 • Ku latsa nan don karanta darasin rana ta uku. DARASI NA 1 Matakan rubutun gajeren labari A jiya mun yi bayani akan matakan da ake bi wajen tsara labari, yau kuma za mu bayani a takaice kan matakan da ake bi wajen rubuta ingantaccen labari. Waɗannan matakai ba tabbatattu ba ne, ma'ana ba wajibi ne...
 • Ku latsa nan don karanta babi na shida. Habeeb na kwance a kan doguwar kujera ya ji an murɗa handle ɗin ɗakinshi tare da turo ƙofar a hankali. A hankali ya buɗe idanunsa da suka yi nauyi sakamakon ciwon kan da yake fama da shi. "Fateemah" ya faɗa a ransa, lokacin da ya kai duba ga Jummai da ke ts...
 • Uwargida ba za ki yi dana sanin koyan yadda ake yoghurt in fruits ba. Domin kuwa kayan dadi ne sosai da sosai kuma cikin mituna kalilan za ki hada. Ba a ba yaro mai kiwiya!!! Wannan recipe yana daya daga cikin recipes da muka koyar a zauren Free Ramadhan Classes with Umyuman a nan Bakandamiya. Abu...
View All