Makalu

Ta faru ta kare: Babi na daya

 • Tunda suke maganar gawar kurun ta tasa a gaba ta dask'are a wurin bata ko motsin kirki, yanda kasan wata statue haka ta tsaya k'ik'am, kowa da abinda yake fad'a amma banda ita kowa yana masa adu'a banda Ameena, zaune kurun take kaman wata icce, kuka take amma bana hawaye ba, kukan zuci takeyi gashi k'iri k'iri ta kasa gaskata mutuwar nan, ga gawa agabanta tunka a nad'e gawar ta ganta amma tana gani tamkar ba gawar bace ba, muhammad d'inta ze tashi dogon sumace yayi yaya zasuce ya mutu? Su k'ara masa lokaci mana ze farfad'o...ta ayyana a ranta!!! Mazane suka shigo suka durk'usa suka d'auki gawar ta muhammad dake cikin farin k'yalle, kana an ninninkeshi acikin tabarma a zura a makara!! Mik'ewa tai ta rike makarar

  "Me kenan zakuyi? Ina zakuje da muhammad, ku barni ko a haka zanta kallon abuna, kurun ku bud'emun fuskar sa, dan Allah karku tafi dashi, ku k'ara masa lokaci dogon suma ce yai" Tausayinta kowa keji, sun kula bata cikin hayyacinta mahaifi muhammad da mahaifin ta sune sukazo suna k'ok'arin b'anb'are Ameena daga jikin makarar data kama ta rirrik'e hannu bibbbiyu da k'yar da sid'in goshi ta sake shima seda k'wace da k'arfin tuwo! Se sambatu takeyi

  "Karkumun haka, Akwai maganar da Muhammad ze gayamun daren jiya, ban saurareshi bane ku barshi ya gayamun, koda iya itace, ku taimakamun muhammad ya sanar dani abinda yakeso ya sanarmun, idan baku barshi ya fad'amun ba nima mutuwan zanyi, idan munje cen seya gayamun" babu wanda ya saurareta de d'aki aka wuce da ita aka kwantar da ita masu rarrashi sunayi masu ban baki sunayi amma se sambatu take ga alama Ameena batasan ma metakeyi ba ta zauce mutuwar muhammad ta mata dukan a kawo wuk'a kenan!!!! Ganin abun bame k'arewa baneba ya sanya su daddym Muhammad suka kira likita yazo ya sharara mata allurar bacci.

  ***************

  Mustapha kabeer sharad'a da kuma Muhammad D'ayyib kagara Aminan junane, tun tasowarsu secondry school d'aya suka halarta kuma ajinsu d'aya, had'in kansu yakaisu ga zamtowa aminan juna har sukaje jami'a suka karancin building enginearing a tare, lokaci d'aya suka kammala bautan k'asane kurun ya rabasu kowa yaje nasa garin, bayan sun kammala a tare suka soma harkokinsu tunkan su samu aiki, Alhaj mustapha shine ya soma samun aiki a wanj kampani me zaman kansa na gine gine, yayinda Muhammad ya samu aikin sa daga baya a k'ark'ashin gwamnati, seya kasance mustapha yafi muhammad k'arfi haryake taimakonsa daidai gwargwadon iyawarsa, dama cen shi mustapha d'an wanine sunada arziqinsu, yayinda shi kuma muhammad iyayensa ba masu kudi mahaifinsa ma'aikacine kurun a k'ark'ashin gwamnati me rufin asiri......

  Haka har sukayi aure suka hayayyafa, yayinda Muhammad ya zamto yaro a k'ark'ashi mustapha kasan cewar shi mustaphan yakai ga company nasa na kansa, dukda haka seyawa muhammad manager na company d'in inda shima lokaci d'aga ya bunk'asa kasancewar ana matuk'ar jida sharad'a builder's kasancewar su k'wararru masu iya zane da gini na zamani....basu tsaya anan ba seda suka kaiga kawo kayan gini daga waje wanda akasari acen kurun ake samunsuu kayan qawata gida da sauransu, da wannan suka yada a zango a Abuja harkansu ta tsarin gine gine ya bunk'asa akeji da Sharad'a builder's sosai da sosai....

  ************
  Muhammad sunusi shine babba awurin Alhaj muhammad, yayinda yakeda k'annensa susu 4....Yusuf shine me binsa se kuma Bunyameen daganan se yara mata Salma da zuhra, matarsa d'aya wannan ya sanya suke uwa d'aya ubansu d'aya...

  Alhaj Almustapha kuwa ya jima da aure be haihu ba, dan kuwa har muhammad sunusi yakai shekaru 12 aduniya be haihu ba, seda yakai kusan 13 sannan aka haifi Ameena yarinyace da akeji da ita wanda seda ta share shekaru goma sha hud'u tukunna mahaifiyarsu ta haifi wani Namijin dayaci sunan kakan sa Kabeer anace dashi Kb junior.

  ************

  Mom Nu'aiym

  ************

  Sadaukarwa ga Ameena jibril muh'd (slimxy)

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Yadda ake hada KFC chicken

  Posted Thu at 10:11 AM

  Assalamu Alaikum, barka da sake saduwa a cikin shirin girke-girken Bakandamiya tare da ni mai gabatar muku da shirin. A yau in sha Allah zan nuna mana yadda ake hada KFC chicken. Abubuwan hadawa Kaza Flour Man gyada Bread crumbs ko cornflakes Kwai Maggi ...

 • Yadda ake hada egg masala

  Posted Thu at 9:57 AM

  Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa a cikin shirin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau na zo mana da yadda za a hada egg masala a saukake. Abubuwan hadawa Dankalin turawa Albasa Carrots Maggi Mangyada Kwai Yadda ake hadawa Farko za ki wanke dankal...

 • Jini Baya Maganin Kishirwa: Babi na Uku

  Posted Jan 12

  Ku latsa nan don karanta babi na biyu. Sakinah ta share hawayen da ke zuba kan kuncinta kafin ta ce. "Insha Allahu Umma zan yi aiki da dukkan abin da ki ka umarce ni da shi da yardar Allah, ba zan taɓa baki kunya ba". "Yauwa Sakinah Allah ya yi miki albarka". "Amin"...

 • Yadda ake baked awara

  Posted Jan 11

  Barka da sake saduwa a cikin shirin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau na zo maku da sabon girki wato yadda za ku hada baked awara. Abubuwan hadawa Awara Kwai Carrots Seasoning Cooked minced meat Muffin tray Albasa Yadda ake hadawa Farko za ki yanka a...

 • Bayanan masana game da ingantattun hanyoyin ƙayyade iyali

  Posted Jan 8

  Mene ne ƙayyade iyali? Ƙayyade iyali ko tazarar iyali ko kuma family planning a Turance wani mataki ne da ma'aurata kan dauka don hana mace daukan ciki domin rage yawan haihuwa akai-akai, ko ƙayyade yawan ‘ya’ya da za ta haifa ko dai ma don wasu dalilai na ...

 • Ma'aurata: Babi na Biyu

  Posted Jan 8

  Idan baku karanta babi na daya ba to ku latsa nan don karantawa. Ana kiran sallah asuba ta farka daga bacci addu'an tashi daga bacci tayi kafin tayi miƙa tana salati ga Annabi S.A.W kai dubanta tayi a gefen da Fahad yake kwance tayi, har yanzu yana nan yana bacci kamar...

View All