Featured Create an Ad

Makalu

Blogs » Kagaggun Labarai » Afnan: Babi na Daya

Afnan: Babi na Daya

 • A garin Gandi gari ne karami na fillani da akwai wani mutum da ake kira malam ado bafillatanine ALLAH ya axurtashi da dukiya ta shanu ado yana da mata daya hafsat da yaya uku Abdallah shine na farin kuma shine kadai namiji sai hajara da qaramar su afnan yar shekara goma wacce duk tafisu kyau kasancewar ita tabiyo inna wato mamansu hafsat Ado mutum ne miskili sosai wanda ke ketatar iyalansa da dukiyarsa saboda bai son matarsa hadin iyayene auren xumunci aka masu shiyasa duk cikin ya'yan yafi tsanar afnan saboda kamarta da inna ya fison abdallah.

  Kamar kullum hajara da afnan sukanje rafi debo ruwa da tulunsu inna tace hajara ki kula da afnan sosai kinsanta da rigima da neman tsokana karki barta taje ko ina tace tor inna, suka dauki tuluna suka fice tfy suke su biyu da kagansu xakaga kamarsu fuskarsu dauke da murmushi suna tafe suna hira kamar wasu qawaye hr suka xo xasu wuce wani gida ta dubi hajara tace lah hajja na tuna jiya  maryam ta dawo daga qauyensu kixo muje mu gaidata tace aa ai Inna tace kar muje ko ina kema ba zaki biya ba ki bari idan mun dawo rafi sai muzo. Ta ce gaskiya ni sai naje tace wlhy ki ka je in gayawa Abba.

  Jina hajara ta kira abba yasa afnan ta sha jinin jikinta tasan baya kaunar ta sai ya mata dukan tsiya ta mirgina bakinta tace tor kije abinki baxanje dake ba kafin hajara tayi mgn tuni ta juya ta cnza hanya,tana qoqarin shiga wani lungu bata ankaraba tayi karo da mutum tulun dake hannunta ya fadi ya fashe, a tsorace ta fito da harshenta tana kadawa tana fadin la la la la Allah baxan yardaba sai ka biyani tuni idanunta sun fara fito da kwallah ta maida idanunta kan tulun tana kallon yanda ya watse ido ya tsuramata cike da mamakin kyawunta da wayonta ta katse masa tunani tana fadin
  ni wlhy baxan yardaba sai anbiyani.

  ***********

  Murmushi yayi hade da sauke kwayar idonsa akanta xuwa tulun dake qasa yace tor ya xanyi baxaki yafemin tulunba, ta turo bakinta cabdi ai wlhy baxan yardaba sai kabiyani tuluna yace kinga ni ba dan nan garin bane bansan komai anan ba kixo ga motata can muje garinmu insiyamiki, ta maida idonta jikin motar tana kallo kafin ta dubeshi tace lah kaine da waccan motar,ya gyada kansa alamar eh tace tor ni baxan bika ba anan xaka biyani tuluna kona maka duka ,ta cire mayafin kanta ta daure qugunta dashi alamar fada zata yi dashi.

  Ya tsurawa kanta ido yana kallon yanda kan yasha qanana kitso ya kwanto mata a gadon bayanta tace malam kai nake jira fa, murmushi yayi akaro na biyu yana kallonta yace gaki yanayinki mai sanyi kinada fuskar salihai ashe ban cankaba ba haka kike ba naga har dambe xakiyi dani tace ni kabiyani tuluna abbana xai min duka sosai yace tor ya sunanki kafin na biyaki tulun tayi far da ido tana kallonsa kafin tace AFNAN yace sunanki mai dadi ke kuma mai kyau,tayi murmushi tace kaifa menene sunanka yace Adnan tace naka sunan ba dadi babushi a garinmu ban taba jiba kokai ba musulmi bane ,ya dan dubeta  kafin yace bnyi kama da musulmi bane,ta tabe bakinta tayi shiru abinta.

  Yace muje kikaini gidanku acan xn biyaki tulunki tfy suke cike da nishadi tana bashi lbr yana dry wani sa'in yayi murmushi hr suka iso gidan ta shiga gidan tasami innarta tana gyaran shinkafa takirata inna kizo ana nemanki kafin inna tayi mgn tuni ta juya ta fice jiki a sabule inna tafito da mayafinta tana tunanin idan ba rigima afnan ta dauko mata ba tunda inna tafito yake kallonta dattijuwar kirki mai mutunci baiyi mamakin kyaun afnan ba dan yaga ibda ta daukoshi cike da girmamawa ya gaidata yamata bayanin yaxo nan garinne duba gonakin mahaifinsa da ya siya anan garin da kuma haduwarsada afnan kana ya ciro kudi bandir na hamsin ya bata akan tasiyawa afnan wani tulun.

  Inna tace aa wlhy kabar kudin baxamu karba ba tulun me tulun bnxa daxaka bada maqudan kudi haka akansa yace bakomai nabawa afnan ne taqara wurin xuwa makaranta tace duk da haka baxamu karba ba kaje abinka tulu na yafe kafin su ankara afnan ta karbe kudin tana fadin inna aini bn yafe ba ai ninace ya biyani tuluna cike da kunya innan ta sunkuyarda kanta qasa yace tor shikenan tunda na biya ynxu na huta ko tace eh yaushe xaka dawo ne batare daya amsa mataba yayiwa innan sallama ya juya ya fice.

  ***********

  Haka rayuwa ta ciga ba da tfy a agarin gandi da dadi ba dadi yayinda inna ke cikin qunci sosai lokacin da hajara ta fada cikin wani hali a ranar wata talata hajara ta dawo daga makarantar boko tare da afnan ta hadu da wani saurayinta daya nace mata ya hana mata sukuni yanuna qaunarsa gareta taqi amincewa sanin kowaye lado.

  Lado bashida kirki gashi kowa yasanshi da sata ba tsabta koda yaushe cikin datti yake haqoransa jawur koda yaushe ya bude baki xaiyi mgn kamar ka xuba da gudu saboda doyi hakan yasa hajara ta qauracewa buqatarsa tanuna ita karatu xatayi tanaso tayi ilimi taxamo wata aba a rayuwarta hakan yayi matuqar harxuqashi yace aurene kije kiyi da wani kigani bokonma bake bashi hr abada ya juya ya fice afnan ta dubesa kai tsaya!!!!! cak ya tsaya batare da ya juyoba tamiqawa hajara jakarta kana ta isa inda yake tsaye ta xaga ta gabansa tana masa wani duba qasa qasa.

  Mekake nufi mekake taqama dashi waye kai, a harxuqe yake kallon qaramar yarinyar yace ni lado ne kowa yasanni a garinnan bana ragawa wnda ya tabani saboda babana nada garken shanun dana lunka naku mtsewwwwww taja dogon tsaki hade da xubar da yawu a gefensa tace ashe kai banxane kaiba kowa bane tunda baka kashewa kuma baka rayawa kuma duk wnda kaga ya mutu Allah ya  kasheshi kaine sanadi dan haka bakada abinda xakayiwa hajjata banxa dakai.

  Kafin ya ankara tuni ta fisgi hannu hajara sun fice cike da bacin rai yayi kwafa ya fice tare da alqawarin ganin yaga bayan hajara kpda xatabar suniyarne gabaki daya.

  Latsa nan don karanta babi na biyu....

No Stickers to Show

X

Da Dumi-Dumin Su

 • Ku latsa nan don karanta labarin Saurin Fushi Na Kawo Da Na Sani. A wani ƙauye akwai wani mutum  ana kiran sa Abu Sabiru, ya kasance mai tsananin haƙuri da kawar da kai akan wasu al’amura. Dalilin da ya sa ma ake kiransa Abu Sabiru kenan. Yana zaune tare da matarsa kyakkyawar gaske ...
 • Ku latsa nan don karanta darasin rana ta uku. DARASI NA 1 Matakan rubutun gajeren labari A jiya mun yi bayani akan matakan da ake bi wajen tsara labari, yau kuma za mu bayani a takaice kan matakan da ake bi wajen rubuta ingantaccen labari. Waɗannan matakai ba tabbatattu ba ne, ma'ana ba wajibi ne...
 • Ku latsa nan don karanta babi na shida. Habeeb na kwance a kan doguwar kujera ya ji an murɗa handle ɗin ɗakinshi tare da turo ƙofar a hankali. A hankali ya buɗe idanunsa da suka yi nauyi sakamakon ciwon kan da yake fama da shi. "Fateemah" ya faɗa a ransa, lokacin da ya kai duba ga Jummai da ke ts...
 • Mon at 1:39 PM
  Posted by Bakandamiya
  Uwargida ba za ki yi dana sanin koyan yadda ake yoghurt in fruits ba. Domin kuwa kayan dadi ne sosai da sosai kuma cikin mituna kalilan za ki hada. Ba a ba yaro mai kiwiya!!! Wannan recipe yana daya daga cikin recipes da muka koyar a zauren Free Ramadhan Classes with Umyuman a nan Bakandamiya. Abu...
 • Hadin special salad nawa na musamman ne! Ga sauki ga dadi, uwargida sai kin gwada za ki bani labari! Wannan ma yana daya daga cikin recipes da muka koyar a Ramadan a shirin girke-girkenmu wadda aka gabatar a zauren Free Ramadhan Classes with Umyuman. Shin ko kin tuna gashin tsokar kaza da muka koya...
 • Red velvet cake, cake ne da mutane da dama suke so kuma kuma suke son ci. Saboda haka, akwai hanyoyi daban-daban na yin red velvet cake, ga yadda na ke nawa cake din na kawo muku. Wannan yana daya daga cikin recipes da muka koyar lokacin Ramadan anan Bakandimya. Domin ganin duk jerin recipes din da...
View All