Rubutu

Blogs » Kagaggun Labarai » Matar Farko: Babi na daya

Matar Farko: Babi na daya

 • Bismilahir-Rahmanir-Rahim

  Kalmar danda?asa tana nufin uwargida matar farko kenan gun miji.

  Littafi na uwayen gida ne amma al?alamina bazai iya rubuta komai ba sai na gaisheku ?ogalawa, aminai na kenan abin alfahari na: my Ruksad,?awata Lasmin,Faiza matar yaya nd Affa, ?awayen amana abokan rufin asiri ina ?aunarku matu?a fatana ubangiji yabarni a taredaku ya zaunar daku lafiya da oganninku ya albarkaci zuri'a. Ameen.

  Dacewa da cancantarku itace tasa na saudakar da littafin nan baki ?aya gareku, ?awaye, aminai, ?an uwa kuma masoya na asali bana yaudara, HIBBATULLAH MOM KHAUSSAR & MARYAM SCHOLAR, ha?i?a babu wata kalma da zanyi anfani da ita dan bayyana matsayinku gareni domin Allah ne ka?ai masani ?aunar da kuka min ko nace kuke kan yi, ina muku fatan dukkan alkhairi na duniya da lahira. Much love!

  *******

  Garin lullu?e yake luf, iska na ka?awa me sanyin da?i saboda sanyin la'asar da ya sauko da kuma ruwan sama da aka gama kasancewar lokacin damuna ne. Tafe take tana tsalle da igiya ga hannunta ta cilla igiyar tana tsallakawa. Matsakaiciyar yarinya ce me kimanin shekaru goma a duniya, hankalin ta kwance take da ka ganta kasan tana jin da?in tsallen. Can ta kai ga wani icce inda yara matasa kamarta, da wadanda suka fita da wadanda basu kai ta ba zazzaune sunata gidan ?asa, kowa ya natsu yanata gidanshi dan ba me so gidan wani yafi nashi. Murmushi yarinyar nan ta yi wanda yama fuskarta kyawu sosai duk da ita ba wata kyakkyawa ba ce, da alama abin ya bata sha'awa. Cikin hanzari ta cillar da igiyar da ke hannunta sannan ta fa?i zaune cikin ?asar tafara tara ?asa itama tana ginin, "Habbi! yaushe kikazo ba ko magana?" cewar Hure ?aya daga cikin yaran nan. data juyo taga Habbi zaune cikinsu tafara gini itama, murmushi Habbi ta sake yi, kuma sai ta koma ta game fuska gim kamar wacce ta tuna wani abu "Tohm yada ha?e fuska kuma?" harararta Habbi tayi "wai Hure ina ruwanki dani ne, an taho yin ?aki ba'a biyo min ba gashi nakawo kaina hanyar bata ?acemin ba" dariya Hure ta ?yal?yale da ita dan yanzu tagano bakin zaren kenan dan an barota ne take fuska, hakan kuwa ?ara ?ule Habbi yayi, ganin hakan yasa Hure cewa "yi hakuri gorata bazan sake baroki ba" bata cemata komai ba saidai ta?an saki fuskarta daga gimtsetan da tayi, haka sukaci gaba da wasannin su cikin ?asa har saida sukaga magrib na gabatowa suka watse kowa yayi hanyar gidansu, Habbi da Hure kam tare suka taho domin unguwarsu ?aya shiyasa ko ina tare suke zuwa, ana kawowa ?ofar gidansu Hure ta shige abinta bayan sunyi sallama, kwana kawai Habbi tashiga itama takai gida domin katangar gidansu ma ?aya ce, har tasa ?afa cikin gidan kuma sai taja ta tsaya tana duban jikinta yadda tayi bu?un bu?un da ?asa kamar an tonota daga rami, dam gabanta ya yanke yafa?i dan tasan sai tasha fa?a domin mahaifiyarta ta hanata wasar ?asa, la?ewa tayi nan bakin garka tana zura kai taga ko Amma tana tsakar gida, aikuwa zura kanta kenan taga Amma dur?ushe gindin murhu tana hura wuta, da sauri ta janyo kanta tayi tsaye tana tunanin yadda za'ai tashiga, ta da?e nan tana le?e amma Amma bata bar tsakar gidan ba.

  Gajiya da tayi daga tsayi yasa ta tsugunna abinta taci gaba da wasar ?asa, cen ta zura kai daga tsugunnan da take tana le?en tsakar gida, "wayyyoo kaina yafashe" da ?arfin gaske tafa?a bayan tayi ?ara ganinta tayi zaune dirshen tsakar gida sakamakon gullu kutsen da tayi, saida ta ware ido ta kalli Amma sannan ta tuna wani abu taji ya izota lkcin da ta le?o kai daga tsugunnun da tayi, da sauri ta mi?e a tsorace dan tunaninta ko aljani ne ya izota dan dama kullum Amma na hanata zama bakin ?ofa tace aljannu keda kwai, ?ulli taji an sakar mata ta bayanta wanda saida cikinta ya ?ulle da gudu tayi cikin Amma "Wayyoo Amma aljani" "ba aljani ba dai she?an ?ar kunyar uwa kin gama le?en?" Amma ta fa?a tana watsa mata harara "Tun ?azu fah naganta tadawo daga wasar ?asa ?utun-?utun da ita kamar ?iyar birwai ashe da tazo bata shigo gidan ba zaunawa tayi bakin garka ta ?aura wata sabuwar wasar" sai a lokacin Habbi taga yayanta murya cen cikin ma?oshi tace "Yaya dama kaine ka turoni ba aljani ba?" kara ya ?auka bakin murhu da gudu tayi inda Amma tana ihu, Amma tace mishi "yi ha?uri kyaleta nasan yadda zan hukunta ta" ajiye karan yayi yatafi ya ?auki buta yayi bakin garka dan yin alwalar magrib, Habbi kuwa da?i taji dan tasan hukuncin Amma baya wuce tasata dakan fura, itakam da a ta?a lafiyar jikinta gara ta wuni tana daka. Ganin Amma ta shiga sallah yasa itama ta cire kayanta tanufi bayi tayo wanka sannan tazo tayi alwala tashige ?aki.

  Zaune suke suna cin abinci itada Amma, tuwon dawa ne da tsanwar miya (malohiya) Habbi ta maida hankalinta sosai kan cin abincin dan sam ita bata wasa da cikinta, dubanta Amma tayi tace

  "Habbi shin ban hanaki zuwa wasar ?asa bane?"

  "Kiyi hkri Amma daga yau bazan sake zuwa ba"

  "Uhmm kullum haka kike fa?a ai, amma haryanzu baki daina ba, Allah dai ya shirya min ke yasa ki dunga jin magana ta, idan kina wasar ?asa yaushe samari zasu ganki suce suna so ko bakyaso inyi siriki ne?"

  Rufe ido Habbi tayi tana dariya "ohh Amma ni ?ar ?arama dani zanyi samari, sai na girma nayi nono za'a soni, Amma in nafara samari suna bani ku?i ke zan dunga ba mu cika buhun ku?i muje birni"

  Cike da jin da?i ta ?arashe maganar, sosai Amma tayi dariya, "kenan buhu zaki cikamin da ku?i ?ata?"

  "Eh Amma tunda Affa ya?i sani boko in zama malamar makaranta in dunga baki ku?i, kinga in nafara samari ai sai in cika miki buhu da ku?i ko"

  Murmushi Amma tayi, a ranta tana jin haushin rashin saka Habbi boko da mahaifinta ya?i kawai saboda ra'ayin kansa wai ?iya macce wayewarta batada wani anfani kawai tasamu ilimin addini shine daidai amata aure ba wani boko ba,

  "me kike tunani Amma?"

  Habbi tace ganin tayi shiru kamar tana wani nazari, "bakomai Habbi"

  Sallamar Affa sukaji ya shigo ?auke da tire me kwanukan abinci da aka fidda musu waje, da sauri Habbi ta tashi ta kar?a tana mishi sannu da zuwa, Amma kuwa mi?ewa tayi ta shinfi?a mishi tabarma itama tana mishi sannu, duban Habbi yayi da takoma ta zauna tana cigaba da cin abinci
  "Habiba shiga ciki ki ?arasa cin abincin zanyi magana da Ammarki"

  "Tohm Affa na ma ?oshi"

  Ta fa?a tana mi?ewa tareda ?auke kwanan, saida ta wanke kwanan sannan tashiga ?aki tana wasa da ?iyar lakarta, dan Habbi akwaita da shegen son wasa shiyasa kullum bata girma.

  Tashi Amma tayi ta koma gefen Affa "Salamu wata shawara ce nake son nayi dake" "Tohm Malam ina jinka"
  "Dama munyi magana da abokina Malam Ali ne zamu ha?a zumunci mu ha?a yaron wajenshi Abbakar da yarinyar nan Habbi aure ya kika gani"

  Zaro ido Amma tayi "wacce Habbin kuma yarinyar da duka yaushe tayi shekara goma? Habaa yaushe Habbi takai a fara wani zancen yi mata aure?"

  "Salamu sanin kanki ne darajar ?iya macce ?akin mijinta, musamman yanzu da zamani ya lalace, kina gani yadda ake lalata yara ?anana garin nan, ba ?ara ma ayi ma yaro aure ba da yaje ya lalace a banza, kuma fah ba wai da an ?aura aure za'a kaita ba, zamu iya bari daga baya sai ayi shagalin biki"

  "Gaskiya Malam sam ban yarda da zancen nan ba, Habbi ?wara nawa ce da za'a mata aure, yarinyar da ko balaga bata yi ba me tasani a aure, bayan wasa me keda kwai a kan Habbi da zakace wani ka mata aure ko yau saida namata fa?a kan wasar ?asa fah haba Malam ka sake nazari dai"

  "Salamu matsayina na miji gareki, mahaifi ga Habiba kuma shuga a gidan nan inada ikon zartar da kowane irin hukunci, amma sbda in baki daraja nace dake shawara, auren wuri dai ba haram bane domin Annabi SAW da shekara tara ya auri Nana Aisha kenan kidaina kawo min hujjar Habbi tayi ?an?anta, ke kanki da aka kawomin ke gidan nan ai wasar ?asa kike har daga baya kikazo kikai wayo, me ya sameki? sai ita zakice wani tayi ?an?anta bayan ina gani duk da ?ananun shekarunta babu aikin da bata iya ba a gidan nan"

  Gaba?aya jikin Amma yayi sanyi dan tama rasa abin fa?a, amma tasan abinda Malam yake son yiwa Habbi ba adalci bane, ya tauyeta ya hanata karatun boko, sannan yanzu da ?ananun shekarunta yayi wani zancen aure, duk da tasan Malam Ali da matarsa Jidda mutanen kirki ne zasu kula da Habbi sam bai kamata ama Habbi haka ba, sannan ita kanta yadda ta sha?u da ?arta da shirmenta batajin zata iya rabuwa da'ita, cikin sanyin murya Amma tace

  "Na ha?aka da darajar Allah Malam kayi hakuri, nasan Abbakar yaron kirki ne, amma me zai hana amusu baiko in yaso nan da shekaru biyar sannan Habbi ta girma sai a ?aura auren, kaga lokacin tasan menene aure"

  "Salamu ranar juma'ar nan zamu ?aura auren Abbakar da Habiba, mun riga mun tsaida magana kuma ni bazan zama mutumen banza in tada zance ba..."

  *******

  Latsa nan don karanta babi na biyu....

Comments

1 comment