Makalu

Matar farko: Babi na biyu

 • Amma ji tayi kamar tafasa ihu dan takaici, take tausayin Habbi yakamata, tashin hankalinta yaya Habbi zatayi in taji zancen, yarinyar da ko ji tayi ance amma wani aure sai tace
  "Amma nidai in haka ake aure bazanyi ba dan bazan iya rabuwa dake da Affana ba"

  Jiki a sanyaye ta miƙe tashiga ɗaki, Habbi na zaune tanata wasa da ɗiyar lakarta, sai ado take mata tana cewa amarya tayi kyau, cen ta ɗago kai taga Amma ta raɓka uban tagumi tana kallonta "Amma! Amma!! Amma!!!" ta kira sunanta har sau uku shiru ba amsa, hakan yasa taje inda take ta dafata "Amma me kike tunani inata kiranki bakyaji, bakiga na shirya ɗiyata ba ko batayi kyau bane?"

  Murmushi Amma ta ƙwaƙwalo tana kallon ɗiyar lakar Habbi "tayi kyau sosai Habbi tashi kije kici gaba da wasarki" tashi tayi taje taci gaba da wasarta har kwana ya ɗauketa anan, dama kullum haka take daganan take bacci sai Amma ta ɗauketa.

  Cikin daren nan sam Amma bata runtsa ba tana ta tunane-tunane, ana kiran sallar farko ta tashi tahau kan sallaya, tana jin motsin Affa yadawo daga masallaci ta tada Habbi dan tayi sallah, Habbi na gama sallah ta gaida Amma sannan taje ta gaida Affa da yayanta, bata koma bacci ba zaune tayi tana wasa da ɗiyarta kafin gari ya waye tayi aikin da ta saba.

  "Wannan yarinya Allah ya yaye miki wannan larurar wasa, kiyi bacci kina wasa kuma tun asuba ki hau wasa, ina dalili abu kamar ibada wannan ai cuta ce" cikin faɗa Amma tayi maganar dan ciwon wasar Habbi yafara bata haushi.

  "Amma tayar da ita fah ne nayi tayi sallah, ke kin tasheni nayi sallah nima ai sai in tayar da ɗiyata ko?" tana dariya tayi maganar. Harararta Amma tayi "Idan na fasa ɗiyar sai inga da uban me zaki wasar" "yi hakuri Amma bazan sake ba".

  Fita Amma tayi daga ɗakin ta ƙyaleta, dan ita kullum haka take komai tace ayi hkri bazata sake ba "Gorata! Gorata!! fito mu tafi kar mutane suyi yawa bakin rijiya" cewar Hure ta kan katanga.
  "tana cen tana cutar, zaki fito ku tafi ko sai na tarar dake ɗakin nan"

  Habbi na ɗaki tajiyo muryar Amma, da sauri ta tattare kayan wasar tafito, bokiti ta ɗauka sannan ta tafita, tana fita a waje ta tarar da gorarta na jiranta, basu wani ɓata lokaci ba suka nufi bakin rijiya, kamar yadda suka so haka suka tarar bakin rijiyar babu mutane shiyasa kullum suke asubanci, cikin ƙanƙanin lokaci suka dawo gida, lokacin har Amma tayi shara, kwanoni Habbi ta tattara ta wanke kamar yadda ta saba, ita kuma Amma ta hura wuta ta ɗaura ɗumamen tuwo, bayan ta gama wanke-wanken wanka tayi tashirya dan zuwa islamiyah lokacin Amma na jiranta suci tuwo.takwas saura minti biyar tafita daga gida ta biyawa gorarta Hure suka tafi.

  Bayan tafiyarsu Hure makaranta, sosai Amma tayi rarrashin Affa kan ya janye zancen ɗaurawa Habbi aure, sai cemata yayi da zata ba kanta lafiya da tayi fatan alkhairi kawai amma aure babu fashi.
  Ranar Juma'a

  Bayan sallar jama'a, ɗaukacin jama'ar da suka sallaci juma'a a masallacin suka shaida ɗaurin aure tsakanin Abubakar Ali da Habiba Sani akan sadaki jikka hamsin, sosai Malam Ali da Affan Habbi ke farinciki, jama'ar dake gun kuwa sunsha mamaki sbda ganin Abbakar in ma baya gari da kuma ƙanƙantar shekarun Habbi, cikin ƙanƙanin lokaci zancen ya zagaye gari, ko ina zancen ake.

  Gabanta ne ya yanke ya faɗi wanda har yayi sanadiyar zubewar itacen dake kanta, hannunta ɗaya ta ɗaura kan ƙirji ɗaya ta dafe kanta, Habbi kenan! Hure dake gefenta saurin aje itacen kanta tayi tareda dafata "Gorata lafiya?"

  "Nima bansani ba gorata, gabana naji ya faɗi jikina wani iri kamar an ɗaure jijiyoyin jikina" Habbi tace murya ƙasa-ƙasa. "Eyyah sannu gorata, kiyi addu'a"

  Zaunar da'ita Hure tayi suka ɗan huta sannan suka tashi suka ɗauki itacen su suka nufi gida, Habbi da Hure sunsha mamaki ganin yadda aketa kallonsu ana ƙus-ƙus kamar wanda sukayi wani abu.
  Amma na zaune tana jan carbi Affa yashigo hannunsa ɗauke da wata baƙar leda fuskarsa fal da farinciki, Amma na ganin haka taji jikinta yaƙara yin sanyi,

  "Salamu ga wannan" "menene?" kallonta yayi kafin yace "ki buɗa ki gani mana" hannunta na rawa ta jawo ledar ta buɗa, alawa ce da goro, bata ɗago ta kalleshi ba kuma takasa cewa komai dan ko tantama batayi na ɗaurin auren ne, bata gama shan mamaki ba saida Affa ya miƙo mata kuɗi

  "ga wannan sadakin Habbi ne ki adana mata har lokacin da za'a bata abinta, sadakinta mallakinta ne dan Allah karki taɓa"

  Wani gululun baƙinciki ya tokare zuciyar Amma, ji take kamar tafasa ihu, kollon Affa kawai takeyi, saida yaƙara mata magana sannan tace "ka ajiye wajenka ai bani na ɗaura mata aure ba bare nayi mata ajiyar sadaki"

  "ai kin taɓa ki saka albarka ko? Habaa Salamu"

  "Kai ai ka saka albarkar ba dole ni sai na saka ba"

  Ta ƙarashe maganar tana miƙewa tareda shigewarta ɗaki, zaune tabarshi nan da kuɗi ga hannu da kuma ledarshi gabanshi, daidai lokacin Habbi tayo sallama ta shigo, tana ajiye itace tazo gun Affanta, sannu ya mata itama ta gaidashi, tana zaunawa idonta suka sauka kan alawa dake cikin ledar

  "Affana alawa ka siyo mani?" tana ɗaukar alawar tayi magana, murmushi ya mata "Eh Habiba duka naki ne" wani irin daɗi taji "Nagode Affa, amma ai ni ba tsohuwa bace bana cin goro saidai Kaka ta babban gida" tana dariya tayi maganar, shima dariyar yayi sannan yace

  "Habiba" "Na'am Affa"

  "Habiba matsayina na mahaifinki......"

  Latsa nan don karanta babi na uku....

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Yadda ake hada KFC chicken

  Posted Thu at 10:11 AM

  Assalamu Alaikum, barka da sake saduwa a cikin shirin girke-girken Bakandamiya tare da ni mai gabatar muku da shirin. A yau in sha Allah zan nuna mana yadda ake hada KFC chicken. Abubuwan hadawa Kaza Flour Man gyada Bread crumbs ko cornflakes Kwai Maggi ...

 • Yadda ake hada egg masala

  Posted Thu at 9:57 AM

  Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa a cikin shirin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau na zo mana da yadda za a hada egg masala a saukake. Abubuwan hadawa Dankalin turawa Albasa Carrots Maggi Mangyada Kwai Yadda ake hadawa Farko za ki wanke dankal...

 • Jini Baya Maganin Kishirwa: Babi na Uku

  Posted Jan 12

  Ku latsa nan don karanta babi na biyu. Sakinah ta share hawayen da ke zuba kan kuncinta kafin ta ce. "Insha Allahu Umma zan yi aiki da dukkan abin da ki ka umarce ni da shi da yardar Allah, ba zan taɓa baki kunya ba". "Yauwa Sakinah Allah ya yi miki albarka". "Amin"...

 • Yadda ake baked awara

  Posted Jan 11

  Barka da sake saduwa a cikin shirin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau na zo maku da sabon girki wato yadda za ku hada baked awara. Abubuwan hadawa Awara Kwai Carrots Seasoning Cooked minced meat Muffin tray Albasa Yadda ake hadawa Farko za ki yanka a...

 • Bayanan masana game da ingantattun hanyoyin ƙayyade iyali

  Posted Jan 8

  Mene ne ƙayyade iyali? Ƙayyade iyali ko tazarar iyali ko kuma family planning a Turance wani mataki ne da ma'aurata kan dauka don hana mace daukan ciki domin rage yawan haihuwa akai-akai, ko ƙayyade yawan ‘ya’ya da za ta haifa ko dai ma don wasu dalilai na ...

 • Ma'aurata: Babi na Biyu

  Posted Jan 8

  Idan baku karanta babi na daya ba to ku latsa nan don karantawa. Ana kiran sallah asuba ta farka daga bacci addu'an tashi daga bacci tayi kafin tayi miƙa tana salati ga Annabi S.A.W kai dubanta tayi a gefen da Fahad yake kwance tayi, har yanzu yana nan yana bacci kamar...

View All