Makalu

Nakasar Zuci

 • "Ki tafi gidanku na sake ki!"

  Runtse idanu na yi jin sautin muryar Adamu a kaina, yana furta kalaman da suka kusan sanya ni haihuwar cikin da ke jikina. Da sauri na dago jajayen idanuwana da suka gajiya da kuka na sauke a saitin sa.

  Wani irin tashin hankali da ciwon rai suka dirar mani, ji nake kamar na daura hannu a kai na kurma ihu ko zan samu raguwar tashin hankalin da nake ciki, amma ina, ba na tunanin hakan zai yi wani tasiri ko na yi, domin kuwa ba shi da amfani.

  Runtse idanuwa na yi ina jin yadda kalaman Adamu ke sake ihu a kaina, ban san me zan ce ba, ban san ya zan fahimci kalubalen da nake ciki a yanzu ba. Na jima da sanin akwai rana irin wannan da za ta fado rayuwata, na san ba ni da mafita a cikinta, domin kuwa komai ya faru tunanina yana ba ni ni ce sila, in da ban yarda na auri Adamu ba, ba yadda za a yi a irin wannan lokacin na dare wanda kowanne bawa yana kwance yana huta wa ransa, amma ni kuma ina nan ina amsar takardar sakina daga hannun mijina.Me ya fi wannan torzarci a rayuwata, a matsayina na 'ya mace?

  Ji na yi ana tunkuɗa ni gami da kokarin tada ni daga inda nake zaune.

  Da sauri na kwato kaina daga duniyar tunanin da na afka, Adamu ne a kaina idanuwansa sun kaɗa sunyi jajir kamar wanda aka ɗiga wa dakakken barkono sai faman hirji yake yi kamar zai ci babu.

  "Tashi ki tafi gidanku Badi'a, na yafe zama da ke a matsayin matar aure gare ni".

  Ya sake fadi. Yana tura ni waje gami da banko kofar dakin da karfi.

  Durkushewa na yi kasa, wanda hakan ya yi sanadiyyar bugar cikin da ke jikina, wani irin zafi da zugi ne suka ziyarce ni, da sauri na runtse idanuna ina jin yadda duniyar ke sauya mani, ji nake yi kamar tashin alkiyamata ce ta zo.

  Sosai nake jin sanyi a jiki saboda lokacin na sanyi ne gashi ko mayafi babu a jikina da zai taimaka min wajen kare kaina. Ban damu ba don na san tashin hankalin da nake ciki ya shallake komai a yanzu. Wai ni ce aka watso waje kamar wata kayan wanki.

  Wai ni ce aka tsana aka kore ni cikin dare, kodayake ba zan yi mamaki  ba, in na yi duba da sanadin da ya kawo haka.

  "Na tsane ki Badi'a na tsani auranki! Ki je na yafe miki zama da ni, na yafe wallahi ki tafi gidan ku".

  Sautin Muryar Adamu kenan da nake jiyowa daga cikin daki cikin wani irin yanayi mai kama da kuka. Hakan ya kara rikitar min da guntuwar natsuwa ta da na yi zaton ta yi saura a gare ni. Wai ni ce yau Adamu ya tsana. Wai ni ce yau ya kora. Kaicon wannan rana! Na sani rayuwata ta gama lalacewa, ba ta da wani amfani.

  Miƙewa na yi cikin matsanancin yanayi ga zafin da nake ji a duk lokacin da na ji cikin na juyawa, wanda na tabbata ya bugu ne a sa'ilin da na durkushe.

  Shima kenan da bai zo duniya ba, ya fara sanin tashin hankalin da ke cikinta, ina ga kuma ya zo, ai lamarin ba zai kallu ba. Zuciyata na ji ta tsinke, ina tunanin makomar abin da ke cikina, wanda na tabbata in har na haife shi kashin mutum sai ya fishi kyan gani ga idanun mutane.

  'Ina kika dosa?'.

  Na ji wani sashi na zuciyata ya sanar da ni hakan. Sosai na ji duniyar ta sake hautsine mani, ba abin da nake tunawa sai maganar mahaifina a ranar da aka daura mani aure na zama matar Adamu.

  "In har kika yi sake wani abu ya fallasa akan lamarin nan, kar ki sake ki tunkaro mani gida, ki nemi wani wajan da za ki kafa rayuwarki".

  Abin da  mahaifina kenan ya sanar da ni wanda na tabbata har kasan zuciyarsa  haka ne, ba abin da ba zai aikata ba in na yi duba da yadda ya dauki son rai ya fifita shi ga komai, sannan ya dauki kunyar duniya ya fifita akan kunyar lahirarsa.

  Runtse idanu na yi zuciyata na sake narkewa da tashin hankali matsananci, ban san ina zan dosa ba, ban san wacce alkibla zan fuskanta ba. Na san ba ni da damar daukar kafafuwana na doshi gidan mu don na san kallon arziki ba zan samu ba.

  Juyawa na yi na dubi dakina na aure. A da kafin Adamu ya gille igiyoyin auren namu wan da bai haura wata daya da kwanaki ba, amma a yau na zama bazawara wacce aka sake ta tsakar dare.

  A hankali na shiga taka kafafuwa na na doshi kofar da za ta fidda ni daga gidan Adamu a matsayin sakakkiya, zan fita ne ba tare da na san inda na dosa ba, na sani na gama rayuwa a filin duniya tunda aure na ya mutu, abin da nake tutiya da shi wanda ya fi komai a rayuwata wanda shi ne zai rufamin asiri, tun da ya balle ai rayuwar tawa ce gabadaya ta balle.

  Tafiya nake yi cikin duhun daren bayan na fice daga cikin gidan Adamu. Garin ya yi tsit ba ka jin motsi sai kukan g'yare da karnuka, gabana ya shiga yankewa yana faduwa wai ni ce yau nake bin dare na ballo daga gidan mijina ina tafiya, tafiyar da ban san ina za ta kai ni ba, ba ni da gurin zuwa, na sani ba ni da damar tunkarar gidan mahaifina don na tabbata ba zan samu karbuwa ba ko ta dakika daya daga gare shi, mahaifiyata ce mai jin tausayina, ita kadai ce wacce za ta ji k'aina ita ce mai share mani kuka na, ita ce kawai take kalubalantar yanayin da nake ciki. Ina tsoron zuwa gare ta, don na san in har na je zan iya jawo mata matsala ita ma a gidan auren ta, igiyoyinta za su iya ballewa kamar yadda nawa suka balle. Ba zan so haka ba, ba zan so a ce ta dalilina mahaifiyata ta rasa gidan aurenta ba.

  'can ya kamata ki nufa, domin kuwa ba ki da wani wajan zuwa illa gidan mahaifanki'.

  Wani sashi na zuciyata na ji ya bijiro mani da wannan tunanin. Shiru na yi kamar mai son canko wani abu, na ji wani kwarin guiwa ya zo mani akan na tafi gidan iyayena, can ne ya fi dacewa da ni. Hakan kuwa aka yi.

  Ina isa kofar gidanmu da yake ba nisa da gidan tsohon mijina Adamu, gidan a kargame, na same shi kamar yadda na yi zato. Zuciyata ba ta karye ba, sai kara min kwarin guiwa take. A hankali na shiga kwakwasawa, gabana na daɗa tsinkewa.

  "Waye a nan?".

  Na ji sautin muryar mahaifiyata. Hakan ba karamin mamaki ya ba ni ba, jin ita ta amsa a maimakon na ji ta mahaifina wanda nake jira ya bude yana gani na yayi mani korar kare.

  "Ni ce!"

  Na amsa ta cikin rawar murya. Shiru ne ya gitta tsakani. Na sani, cewa Mahaifiyata ta gane ni, na sani fargaba da mamaki suka cika ta shi ya sa ba ta sake tanka mani  ba. Na san tunanin mafarki za ta kawo wa lamarin nawa ba wai a zahirance ba.

  "Badi'a!"

  Na ji ta ambata tana kokarin buɗe kofar. Ban amsa ta ba, illa wasu hawaye masu ɗumi da na ji sun wanke mani fuska, tausayinta nake ji, tausayi mai tsanani. Na san mahaifiyata ta fi kowa shiga tashin hankali da halin da nake ciki, ita kaɗai ce a duniyar nan wacce ta kula ni, ta karɓe ni da ƙaddarar da na samu kaina, in ka zare mahaifina da ƙaninsa Kawu Dantani, wanda shi ya zama kanwa uwar gami wajen sanya mahaifina ya tsane ni, har ya ji ba ya ƙaunar gani na a filin duniyar nan, a dalilin sa na ɓoye sirrin da ke ɓoye.

  "Ya sake ki ko?".

  Abin da mahaifiyata ta tare ni da shi ke nan. Bayan ta buɗe ƙofar ta janyo ni zuwa soron gidan. Wani kuka ne na ji ya zo mani ban san lokacin da na sanya hannu na rufe bakina ba, ina girgiza kai. Haske tocilan da ke hannun mahaifiyata shi ne ya ba ni damar ganin yanayin da take ciki, na tsayin wata da kwanaki da na yi ba tare da ita ba. Ta rame, ga suffar shiga damuwa nan duk ta bayyana a gare ta.

  "Dama na san za a yi haka. Duk lamarin da ba a ɗora shi a turba ta gaskiya ba, ƙarshensa ƙarkon kifi zai yi".

  Ta sake faɗi tana girgiza kai, ga wasu ƙwalla da suka tarun mata a idanu, duk da ƙoƙarin ɓoyewar da take yi hakan bai hana ni gani ba.

  "Na shiga uku!"

  "Badi'a ba ke ce kika shiga uku ba, ni ce na shiga uku, domin dama ke nake jira tuntuni, kuma dama na san kina tafe, shi ya sa tun da kika bar gidan nan ban runtsa ba dare da rana ina zaman jiran ki, don na san wannan auren naki  ba inda zai je, zai ɓalle!".

  Zare jikina na yi da sauri jin takun tafiya daga tsakar gidanmu, na tabbata mahaifina ne. Da sauri na dubi mahaifiyata, cikin yanayi na firgici idanuna a warwaje, bakina sai karkarwa yake yi. A hankali na shiga ja da baya, ina ƙoƙarin ficewa amma riƙon da na ji mahaifiyata ta yi mani ya katse mani hanzarina.

  Da idanu na shiga yi mata alamu da ta sake ni, ina tsoron zuwan mahaifin nawa, domin na tabbata ba ni ce zan fi shiga matsala ba, rayuwar auren mahaifiyata nake tsoron faɗawar sa matsala.

  "Ba in da za ki je Badi'a, nan ne ya fi dacewa da ke, domin kuwa ba ki da inda ya fi nan gidan."

  Wasu hawaye suka sake kawo mani hari, da sauri na shiga faɗin.

  "A'a Umma, ki rabu da ni na tafi, ba na son abin da zai kawo saɓani tsakaninki da mahaifina. Ina ƙaunar kwanciyar hankalinki, ba na buƙatar rayuwar aurenki ta yi ƙarƙon kifi. Don Allah ki bar ni na tafi".

  "Badi'a na bar ki ki tafi fa kika ce? ina za ki tafi in na barki? Shin kina da wani waje wanda ya fi gidan mahaifinki ne? Ko ina za ki shiga a faɗin duniyar nan babu kamar nan ɗin da kike ƙoƙarin guje mawa. Duk matsala duk runtsi da wani ƙalubale da za ki samu a rayuwarki ba inda ya fi gidan mahaifinki, don haka tun wuri ki canza wannan bahagon tunanin naki. Badi'a ba yadda za a yi na bar ki ki tafi. Ke fa 'ya mace ce.

  Shin ba kya tunanin halin rayuwar zamanin nan da muke ciki? Kina tunanin in kika wuce kika tafi akwai wata daraja da kima da za ki tadda a can din da kike tunanin tafiya...?".

  "Karima!".

  Na ji sautin muryar mahaifina kamar dirar aradu. Ban san lokacin da na fizge hannuna ina ƙoƙarin kwasawa da gudu ba. Cikin hanzari mahaifiyata ta taro ni.

  "Ki bar ta tafi tun kafin na iso wajen nan karima, in kuma ba haka ba wallahi tallahi har ke a yau ɗin nan cikin wannan daren sai kin bar gidan nan".

  Kalaman da mahaifina ya shiga furtawa ke nan, yana dosowa gare mu, kamar wani mayunwacin zakin da ya hango nama.

  Gabana ya sake tsinkewa, wani kuka ya ƙwace mani sai ƙoƙarin fizge hannuna nake yi amma ina, na kasa.

  "Malam ba yadda za a yi ka ce na sake ta ta fice, so kake yi rayuwar da ka bada kamasho akai ta sake ficewa ta kafa mai lasisi ko me? ina ƙaunar 'yata, ina buƙatar rayuwarta ta inganta, ba yadda za ayi ka yankar mata tikitin fara rayuwa wacce ƙarshenta ta yi ƙarkon kifi. Ban shirya fuskantar wannan baƙar ranar ba, wancan ma da aka yi ta ishe ni".

  Wani kallo na ga mahaifin nawa na watso mana, idanuwansa kamar za su faɗo ƙasa, sai faman hirji yake yi. Ina tsoronsa da kuma abin da zai ɓata masa rai a duniyar nan, domin bai iya ɓacin rai ba, sam-sam ba shi da juriya, don kuwa na ga hakan, wanda sanadin shi ne rayuwar tawa ta koma a baibai.

  Ma'aikacin reka ne mahaifina a matsayin maigadi sama da shekaru masu dama yake aiki, rana ɗaya ya zo mana da batun an kore shi daga  aiki. Ranar mun shiga tashin hankali ni da mahaifiyata, domin kuwa wannan aikin da shi muka dogara. Cinmu, shanmu, sutturarmu, kudin makarantana, duk wannan aikin ne amma rana daya baƙin labari ya tadda mu, dole muka shiga jaje. Sai dai abin da ba mu sani ba, ashe sanadin korar aikin shi ne kama  mahaifina aka yi dumu-dumu wajen satar kayan gidan reka, ana fidda su ba tare da kowa ya sani ba. Shi ne mai bin dare yana buɗewa, wasu daga cikin ma'aikatan marassa tsoron Allah suna satar kayan shi kuma ana ba shi ɗan hasafi wanda bai taka kara ya karya ba. A rayuwar mahaifina mutum ne mai son abin duniya, bai san babu ba, domin duk ranar da ya kasance ba shi da kudi to a wannan ranar cikin fushi zai wuni da neman rigima da mahaifiyata, sai dai ba ta biye masa ko kaɗan yakan gama faɗace-faɗacensa ya ƙyale ta.

  Cikin wannan yanayin na rashin aikin yi ƙalubalen rayuwa ya fara dirar mani, domin kuwa makarantar da nake yi mahaifina  zare ni daga cikinta ya yi, ya tabbatar mani ba shi da damar ci gaba da biya mani kudin makaranta. Hakan ya ƙara dagula mani lissafi. Ba yadda na iya, haka na tattara littattafaina da kayan makaranta na cusa a ma'ajiyar da sai baba ta gani, domin na tabbata in ba  wani ikon Allah ba, duk da buri da fata da naci akan karatuna ni da makaranta har abada!

  Ai kuwa hakan ce ta kasance, mahaifiyata ba yadda ba ta yi da shi a kan nuna masa illar rashin karatuna ba, amma ya yi burus da ita, sai ma cewa da ya yi in tana da kudi ta ci gaba da biya mani, ai ni ma 'yarta ce, ba shi kaɗai ba ne nake da  haƙƙi a kansa, ai tare suka taru suka haife ni.

  Wannan magana ta yi wa mahaifiyata ciwo sosai da sosai, ba ta ce da shi ƙala ba.

  Daga wannan rana mahaifiyata ta ɗauri aniyar neman sana'ar yi, kuɗinta na adashe da take yi wanda bai taka kara ya karye ba, shi ta nemi alfarmar a ba ta kwasa ta kurkusa.

  Da wannan damar ta yi amfani ta fara dafa mani shinkafa garau-garau ina kaiwa bakin titi.

  Shi kuwa mahaifina ban san abin da ya shiga kansa ba, domin kuwa miƙe ƙafa ya yi ya koma matar gida, ita kuwa mahaifiyata ta zama mijin, komai ya koma gare ta; ci da sha duk ita take yi a 'yar wannan sana'ar.

  Ba a je ko ina ba muka cinye jarin, shi kuwa mahaifina ko a jikinsa illa masifa da fadace-fadace da ya zaman masa abin yi. A kullu yaumin ba cas ba as.

  "Amma Malam kana ganin wannan zaman da kake yi shi ne mafita a gare mu? iyali fa gare ka. Ya kamata ka zama jajirtacce a gidanka, rashin aikin reka din nan ba shi ya zama karshen rayuwarka ba. Kyau dai ka yi wani kokarin domin neman abin yi".

  Mahaifiyata ce ta tari mahaifina da wannan maganar, ganin rayuwar sai kara shurawa take amma ba wani abin da ya canza. Maimakon ya amshi wannan shawara da ta zo masa da ita ta kirki, amma saboda kin Allah ya baɗe idanuwansa da toka ya dube ta.

  "Ba dole fa! in za ki iya zama da ni a haka ki zauna. In kuma ba za ki iya ba kina iya tafiya, gaba na da nisa baya ce ta tafi".

  "Haba Malam...!"

  Da sauri ya daga mata hannu cikin ɗacin rai da nuna fushi a kan maganar da ta yi masa.

  "Ke Karima! Ni fa ba wani aiki da zan sake nema, tun da an kore ni a wannan shi ke nan. Dama shi kadai ne abin da na dogara da shi, shi kadai ne na iya. Kin ga ke nan a yanzu haka ba ni da wani tasiri. Girma ya zo mani, ba ni da wani waje da zan je na durkusa na nema aikin yi".

  Ba Ummata kadai ba, hatta ni sai da na firgita da jin kalamansa. Na shiga duban shi. A girme dai ban ga wasu shekaru da mahaifina ke da su ba wanda za su hana shi aiki, ko da kuwa dako ne ba. Yana da lafiyarsa, yana da karfinsa. Ba abin da ya yi rauni daga gareshi, amma yake fadin ba zai iya wani aiki ba.

  Mahaifiyata ba ta sake bi ta kansa ba tun ranar da ya fadi mata wannan kalaman, haka ta shuri takalmanta ta doshi wajen yan uwanta ba tare da ya san abin da ta je yi ba. Sun taimaka mata da abin da ba a rasa ba, ta dawo ta sake kafa wata sana'ar, muka ci gaba da yin garau-garau ina kaiwa bakin titi kamar yadda na yi a can baya. Sai dai wannan komawa tawa da na yi a karo na biyu ta bambanta da ta farko, domin kuwa na tadda dan'uwan mahaifina kawu Dantani wanda suke 'ya'yan kishiyoyi.

  Mutum ne shi mai shegen son abin duniya, ga neman matan tsiya, shi ya sa ya kafa kes a nan bakin titi yana sayar da kayan hatsi. Sai dai ya kafa ne da biyu. Na gano hakan ne bayan mun dau lokaci da shi ina zuwa wajen da garau-garau duk macen da ta zo wucewa sai ya kalle ta, ko siyayya kika zo to sai ya tare ki da maganganu, wanda suka kamata da wanda ba su kamata ba. Ba ya kunyar ya saki baki ya fadi maganganu marassa dadi a gabana, a matsayina na 'yarsa.

  Ban taba zaton wani abu mai kama da haka zai faru tsakanina da shi ba. Ya fara ja na da wasa kamar dai gaske.

  Na yi mamakin haka da farko don ban taba zaton akwai rana daidai da daya ba zai zo mani da sakakkiyar fuska ba. A rayuwar da na yi da sanin sa bai taba duba na da idanun kirki ba, iyaka ta da shi gaisuwa in ya ga dama ya amsa, in bai ga dama ba sai dai ya hantare ni.

  Abu kamar wasa muka saba da shi, har ta kai ta kawo yana kara mani kudi a ciniki, ko in wani irin yan tasha din nan ya ci ya hana ni kudi sai ya biya ni. A cikin haka muka hadu da Adamu, ya nuna yana so na, domin mutum ne mai mutunci da sanin ya kamata, ba ruwansa. Duk da lokacin shekaruna ba su haura sha shidda ba haka muka kulla soyayya da Adamu sai dai a lokacin kawu Dantani sam bai kaunar haka, domin kullum cikin kawo mani ƙauli da ba'adi yake, wajen kushe Adamu. Duk hakan bai sa na ji na canza daga matsayin da na bai wa Adamu a zuciyata ba.

  "Badi'a zo na aike ki wajen Suwaiba".

  Kamar daga sama na ji sautin Muryar Kawun nawa daga cikin dan kes din nasa. Da hanzari na mike ban kawo  komai ba na isa gare shi. Leda ya miko mani dauke da kayan cefane.

  "Kai wa Suwaiba, ki ce mata ina nan zuwa".

  Gyaɗa masa kai na yi. Haka kawai na ji gabana na faɗuwa, musamman irin kallon da na ga yana yi mani wanda ban taɓa ganin hakan ba.

  Shi dai ba kallon fushi ba ne balle na ce fushi yake yi da ni. Kallo ne wanda na kasa fassara irin shi.

  Da wannan tunani na kwashi ƙafafuwana na tafi, zuciyata cike da saƙe-saƙe, har na isa. Sai dai abin mamaki ban tadda kowa a gidan ba, dakin Suwaiba a kulle. Hakan da na gani ya tabbatar mani ba ta nan shiru na yi ina wani tunani. Shin in zauna na jira ta ne ko kuwa na maida masa kayan? Wata zuciya ta ce da ni 'zauna ki jira ta, kila ba nisa ta yi ba.' Haka na samu waje na zauna jikina sukuku ba alamun ƙarfi kamar wata maras lafiya.

  Sosai na faɗa tunanin rayuwa. Ban yi zato ba kawai na ji alamun motsi a kaina, na buɗe idanuna na ga kawu Ɗantani kaina sai faman bi na yake yi da kallo kamar zai haɗiye ni, yana faman lasar laɓɓansa.

  "Suwaiba ba ta nan don haka yau ke ce za ki maye gurbinta. Na daɗe ina jin wani iri a game da ke, yau kuma nake so ki amince da ni Badi'a, ba tare da kowa ya sani ba muyi mu gama ba wanda ya sani".

  Wata irin faɗuwar gaba na ji ta ziryarce ni. Ban san lokacin da na miƙe jikina ya shiga karkarwa ba, a hankali na shiga ja da baya.

  Wani tashin hankali na ji ya kara ziyarta ta. Ban san lokacin da na fashe da kuka ba lokacin da na gama fuskantar inda ya dosa da batun sa, ina ja da baya a hankali, ban yi aune ba kawai na ji ya cafke ni gami da rufe mani baki. Nan na shiga kiciniyar ƙwatar kaina amma ina, kafin na yi wani yunƙuri na ji ya tura mani wani abu cikin hanci. Kafin lokaci kaɗan na fice daga hayyacina.

  Daga wannan lokacin ban sake sanin in da kaina yake ba, sai dai na farka na gan ni yashe tsakar gida, mahaifiyata ta ɗora hannu aka, sai faman kuka take, idanuwanta sun ƙaɗa sun yi jajur. Gabaɗaya ta gama ficewa daga hayyacinta. Daga wannan lokacin kwanyata da zuciyata suka fara tariyo mani abin da ya faru.

  Ban san lokacin da na fashe da kuka ba. Na zabura ina kokarin tashi amma ina, na kasa. Wani irin zafi da zugi nake ji a tsakanin cinyoyina.

  Ji nake yi kamar ana caccaka min kibiya a tsakanina. Ban san lokacin da na sulale zuwa kasa ba.

  "Badi'a waye ya aikata miki wannan mugun abun? Waye ya shirya ganin rayuwarki ta yi ƙarkon kifi? Badi'a faɗa min waye sanadin aikin nan? Ki faɗa mani!".

  Wani ƙunci na ji ya ziyarce ni, ba wanda nake tunawa sai Kawu Ɗantani. Zuciyata na ji ta yi kumburi kamar za ta faso waje. Wai ƙanin mahaifina shi ne ya yi mani wannan aikin. Wannan wacce irin rayuwa ce? Wannan wacce irin baƙar rana ce a gareni?

  "Meye abin kuka a nan? Ai duk abin da ya faru ke ce sila. Tun da ke ce sanadin da aka ba ta min ƴa. Ke ce sanadin komai".

  Muryar mahaifina kenan na ji yana faɗin haka cikin halin ko in kula da nuna halin da nake ciki.

  "Malam ko dai ni ce na fi kowa rashin imani a filin duniyar nan, ba yadda za ayi na so ƴar cikina rayuwarta ta ɓaci.

  Kuma ka sani komai ya faru da ƴar nan kai ne sila".

  Wannan shi ne sanadin komai da ya faru a rayuwata Ƙanin mahaifina ya ɓata min rayuwa sannan ya zama silar da ya sanya mai sona ya guje mani, domin kuwa Adamu bai san da ciki ya aure ni ba sai da na kwanta rashin lafiya a gidansa ya kai ni asibiti aka tabbatar masa da cewa juna biyu gare ni har na tsawon wata uku, bayan an yi rufa-rufa an aura masa ni wanda mahaifina shi ne ya zama silar komai har ya yi ikirarin in har wani a cikinmu ni da mahaifiyata muka fasa abin da ke ɓoye sai dai mu san inda dare ya yi mana...

  "ku fice ku bar mani gida".

  Muryar mahaifina ta katse mani dogon tunanin da na afka.

  "Ba in da za mu wallahi. Domin kuwa nan gidan shi ne mazauninmu in ka kore ni ƴarka dole ka bar ta a gidan, kuma wannan abin da ya faru da Badi'a kai ne sanadin komai."

  Cikin muryar kuka da jin furucin da ke wanzuwa tsakanin iyayena ya ƙara tsinkar mani da zuciya. Da sauri na durƙushe na dubi mahaifiyata.

  "Umma don girman Allah ki sake ni na tafi. Komai zai faru da ni na yarda amma ba na bukatar a ce komai nawa ya shafe ki. Na yarda zan bar gidansa, zan tafi tunda ba ya son gani na, amma...".

  Dukan da na ji a bakina ne ya sanya ni saurin tsagaita abin da nake faɗi na sake rushewa da kuka.

  "Badi'a in har na cika mahaifiyarki ban so na sake jin kin yi yinkurin barin gidan mahaifinki, domin ba ki da inda ya fi shi. Ni na ji zan bar gidan domin dama can ɗauko ni aka yi aka kawo ni ba a nan aka halicce ni ba".

  Wani tunani ya faɗo mani. Lokaci guda na miƙe abin da nake ɓoyewa wanda shi ne silar komai shi zan faɗi ba zan manta ba, kafin aurena da Adamu sosai Kawuna ya yi ikrarin kashe ni, in har na furta wanda ya yi mani wannan aika-aikar. Lokacin kurarinsa ya yi tasiri a kaina, har hakan ya hana ni faɗa wa Umma wanda ya yi mani wannan aikin. Ba yadda ba ta yi da ni ba, na ce mata ban sani ba.

  Duban su na yi dukkan su har da mahaifina da yake ta faman hirji.

  "Kawu Ɗantani!"

  Shiru ya gitta tsakaninmu. Lokaci guda na ga Umma ta shiga duba na, cikin rashin fahimta kafin na ɗora da faɗin.

  "Shi ne sila Umma. shi ne ya yi mani wannan aikin ba wani ba ne...".

  Tun kafin na dire kalamaina, mahaifina ya yanke jiki ya faɗi, tamkar matacce. Ummata kuwa mutuwar tsaye ta yi na ɗan lokaci, kafin ta dawo hayyacinta. Ta shiga duba na tana zamewa zuwa kasa, ta yi zaman ƴan bori. Tashin hankali maras musaltuwa ya bayyana a fuskarta.

  Wannan faɗuwa da mahaifina ya yi  ita ce ta zama silar shanyewar ɓarin jiki gare shi, domin kuwa jininsa ne ya hau a lokaci guda. Umma kuwa hawayenta kasa tsayawa suka yi daga idanuwanta.

  Haka muka kasance cikin bakin ciki da ɓacin rai abu goma da ashirin, rashin lafiyar mahaifina, cikin da nake ɗauke da shi, ga rashin walwala a duk fuskokinmu. Na rasa wa zan ɗorawa alhakin faruwa hakan, mahaifina da son abun duniya ya kaishi ga goyon bayan mutanen banza ya aikata ba daidai ba. Kokuwa irin naƙasar da zuciyarshi ta samu wajen tattare hannunshi ya zauna ɗaki wai ba zai iya nemo mana abinda zamu ci ba. Ko kuwa ni da na biyewa rashin wayau da ƙuruciyata na rika amsar kuɗin Ɗantani har ta kai ga wannan abun ya faru da ni.

  Kodai Ɗantani da ta shi naƙasasshiyar zuciyar  ta ja shi ga aikata mun fyaɗe ba tare da ya yi tunanin zumunci, da kuma halin da rayuwata za ta shiga a gaba ba.

  Dama duk wanda ya saba shinshine - shinshine, to tabbas zai shinshino abun da ya fi ƙarfin hancinshi. Kamar dai yadda Ɗantani ya aikata fyaɗe a kan wata ƙaramar yarinya, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarta. In da shi kuma aka yanke mashi hukuncin zaman gidan yari na har ƙarshen numfashinshi, tare da tara me tsanani.

  Karshe!!!

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Jini Baya Maganin Kishirwa: Babi na Uku

  Posted Jan 12

  Ku latsa nan don karanta babi na biyu. Sakinah ta share hawayen da ke zuba kan kuncinta kafin ta ce. "Insha Allahu Umma zan yi aiki da dukkan abin da ki ka umarce ni da shi da yardar Allah, ba zan taɓa baki kunya ba". "Yauwa Sakinah Allah ya yi miki albarka". "Amin"...

 • Yadda ake baked awara

  Posted Jan 11

  Barka da sake saduwa a cikin shirin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau na zo maku da sabon girki wato yadda za ku hada baked awara. Abubuwan hadawa Awara Kwai Carrots Seasoning Cooked minced meat Muffin tray Albasa Yadda ake hadawa Farko za ki yanka a...

 • Bayanan masana game da ingantattun hanyoyin ƙayyade iyali

  Posted Jan 8

  Mene ne ƙayyade iyali? Ƙayyade iyali ko tazarar iyali ko kuma family planning a Turance wani mataki ne da ma'aurata kan dauka don hana mace daukan ciki domin rage yawan haihuwa akai-akai, ko ƙayyade yawan ‘ya’ya da za ta haifa ko dai ma don wasu dalilai na ...

 • Ma'aurata: Babi na Biyu

  Posted Jan 8

  Idan baku karanta babi na daya ba to ku latsa nan don karantawa. Ana kiran sallah asuba ta farka daga bacci addu'an tashi daga bacci tayi kafin tayi miƙa tana salati ga Annabi S.A.W kai dubanta tayi a gefen da Fahad yake kwance tayi, har yanzu yana nan yana bacci kamar...

 • Burina a shekarar 2020: Saurare na ya fi magana ta yawa

  Posted Jan 4

  Masana sun ce daga cikin abubuwan da suka sa dan Adam yin galaba a kan sauran halittu shi ne yadda yake iya hada kai. Don mutum shi kadai ba zai iya gwada karfi da zaki ko giwa ba. Amma idan ya hada karfi da sauran ‘yan uwansa babu kalubalen da ba za su iya t...

 • Yadda ma’urata ya kamata su bullowa matsalolin rashin lafiya idan sun taso a rayuwar aure

  Posted December 31, 2019

  Matsalar rashin lafiya matsala ce babba da ke taka muhimmiyar rawa wajen hargitsa zamantakewa da rayuwar iyali. Ba abu bane da mutum daya zai boye ma kansa ba tare da sanin aboki ko abokiyar zama ba. Saboda matsala ce babba da take bukatar shawara, tattaunawa a tsakanin...

View All