Rubutu

Blogs » Kagaggun Labarai » Damuwata: Kashi Na Biyu

Damuwata: Kashi Na Biyu

 • "Malam ya isheka! Wallahi Allah kana daf da kaini bango wanda zan ajiye komi a gefe na kwatarmana 'yancinmu dan haka ka bari kawai cikin girma da arziki ko in shayar da kai ruwan mamaki, Uwata tawa ce ni kad'ai, eh na amince hakan sai ka barmin d'iya ta shak'i iskan 'yanci kamar ko wani yaro tunda ka nesanta kanka da ita."

  Dafa bago na yi idanu waje domin jin yarda Mama ke magana ya jefani cikin rud'ani.

  "Kingama d'iban albarka naki?"

  Na jiyo Baba ya furta a hankali wanda na shiga cikin mamakin jin  muryan nasa cikin sanyi tamkar banasa ba, domin zan iya cewa tunda na taso ban tab'a jin maganarsa a hankali irin wannan ba.

  "Da saurana"

  Mama ta ambata muryanta na rawa alamun ta soma kuka. Dafe goshina na yi cike da damuwa domin wata rana bana jin dad'in yarda Mama ke amsawa Baba zantuka kai tsaye ba ladabi irin na Mata zuwa ga Mijinta.

  "Ina saurarenki isash-shiya."

  Wannan karan cikin masifa Baba ya ambata lamarin da ya kuma sanyamin jiki kenan na sake lafewa sosai dan in jiyo zantukan da kyau, zuciyana sai harbawa ta ke yi tamkar zata fito daga ma'ajiyarta.

  "Malam kaji tsoron Allah wallahi saninka bai amfana maka komi ba tunda kake kan cutar da mutanen da basu san ta ina aka hau ba balle su san inda za'a sauka, kafi kowa sanin li'irabi akan k'addararren al'amari amma saboda son zuciya irin naka ka bi ka ta ke ka juya masa baya to wallahi ka sani laifi kake aikatawa mai girma wanda Allah sai ya tambayeka kiwon mu da ya baka a matsayinka na shigabanmu kuma Malami wanda ke koyar da mutane bin haryar sanin Allah da Manzonsa."

  Lumshe ido na yi cikin jin k'arin mutuwar jiki, kalamn Mama suna amsa kuwwa a cikin kunnuwana.

  'Uwata ta wace ni kad'ai' shi ne kalman da ke maimaita kansa a cikin brain d'ina. Gyara tsayuwa na yi cike da burin sanin fassaran kalman. Shiru ban sa ke jin motsin komi ba dan ko tari ban jiyo Baba ya yi ba haka Mama ta daina shesshekan kukan, jikina ya sake macewa, kwakwalwata ta d'auki zafi ainun, kukan da najiyo Mama ta fashe da shi mai sauti kamkar wacce aka duka yasa na zabura kamar zan shiga cikin d'akin sai kuma na tsaya cak ina jan numfashi sai nima na fashe da kukan cikin rashin fitar sauti, jikina sai rawa yakeyi. Jin alamun tafiya za'a fito sai na koma mazaunin da Mama ta tashi da sauri na soma juya kunun ayar tare da sauke kaina k'asa hawaye na d'iga saman zanin jikina.

  Inaji a jikina kallona Baba ke yi sadda ya fito, ban d'ago ba balle in gaishesa kamar yarda nasaba, kimanin mintoci biyu zuwa uku ya bar wurin batare da yaja min tsakinsa da ya saba ba. D'agowa na yi na rakashi da ido daf da zai shiga zauren ya waigo muka had'a ido ya juya da sauri ya fice na sake ware manyan idanuna da sukayimin nauyi, cike na ke da mamakin sauyawarsa lokaci d'aya daga mai sababi zuwa mai sanyi domin tunda na mallaki hankalina Baba bai tab'a shigowa ya fice batare da ya zagi Uwana da Ubana ba ko da kuwa barci na ke yi ya shigo gidan tabbas kafin yafita sai ya zo inda na ke ya zunbud'amin zagi sannan zai tafi, abin har ya zamemin jiki shi yasa yau da baiyi sabon nashi ba na shiga mamaki.

  Da tunanin sauyin nasa na tashi na shiga d'akin Mama bata a falo kai tsaye na shiga uwar d'aka na hangota kwance saman gado ta juyawa k'ofar shigowa baya tana kuka cikin k'aramin sauti a sanyaye na hau gadon na kwanta a jikinta na fashe da kuka mai k'arfi, a rud'e ta juyo ta rungume ni tana shanye kukanta amma yak'i shanyuwa ba yarda ta iya dole ta biyemin muka cigaba da kuka tamkar wad'anda aka yiwa dukan tsiya. Zuwa wani lokaci Mama ta tsaida kukan ta soma shafamin baya alamun rarrashi amma ban san tanayi ba sabida a lokacin ma naji wani sabon kuka na zuwamin, na ko b'are baki na yi ta yi cikin sark'ewar tari.

  "Ya isa haka nan Uwata, bakiga nima da kike tayawa na hak'ura ba, bakomi haka Allah ya nufemu da zama a k'asan jagora mara fahimta kinga kenan hak'uri ya zame mana dole."

  "Mama ba rashin fahimta ba ne tsabar rashin adalci ne a matsayinsa na Malami amma sam bai aiki da saninsa, wallahi wani zubin in ya aikata abu tamkar ba mai koyar da d'aliba ilimi ba."

  "Uwata kalamanki akan hanya suke Malam baiyi mana adalci ko kad'an, bai aiki da sanin da Allah ya hore masa haka bai duba sadaukarwan da muke kanyi masa domin hakkinmu da ya rataya a wuyarsa bai saukewa, ban tab'a damuwa ba saboda ina da rufin asirina wanda har wasu na ke taimakawa amma a hakan ban tsiraba saima biyoni da tijara da ke kanyi akan abinda yasan rayuwa ce ba wanda yafi k'arfin fuskantan irinta."

  "Mama muyi ta hak'uri wata rana sai labari."

  "Shi ne abinda na ke nusar da ke amma ki sani da gajiya fa."

  "To ya zamuyi da shi?"

  "Uhm a kwai Allah ai kuma kinsan dan yasan ke ce lagona shi yasa ya ke b'ata miki domin raina ya b'aci, tun kina k'ara yake min wannan d'abi'ar amma zuwa sadda kika girma sai ya sanja salo da yawan ambatarki da sunar asara alhalin ke d'in arziki ce mai tarin yawa domin wani daga cikin dukiyar da na ke tak'ama da shi har shima ya ke cin moriyarta ke ce silar albarkansu."

  "Ni kuma Mama?"

  "Eh ke ce Uwata domin bayan na sayi idan nan mun tare sai b'arayi suka shigo suka sacemin abinda ya ragemin na kudi wanda na b'oye zanyi jari, anyi abin da kwana biyu kika shigo da kaza budurwa makwafciyata marigayiya Iya Mai Kunu ta baki dan kiyi kiwo to itace tayi ta zuba mana 'ya'ya na saidasu ma siya miki tunkiya da matashin rago wanda Hajiya Inna ta cika kud'in domin ita ta siyo a k'auye da haka suka cigaba da hayayyafa ta hanyar saida raguna ina k'aro tumakai, kajin suma ina saidawa tare da tara kudad'en cikin amincin Allah a shekaru uku zuwa hud'u nasiya firjin wanda yanzu muke kan samun abin rufin asiri da shi."

  "Ikon Allah Mama a she ina da k'ashin arziki haka amma Baba ke kirata da suna mara albarka?"

  "Uwata kenan wannan halin Malam ne tijara dik wanda ya tsana ko da kuwa kullum zai kwanta ya bi ta kansa ya wuce ba zai daina aibatashi ba, ni kaina bai barni ba duk da ranar da na yi masa wanda ya ke fankama shi mai dukiya ne yafi k'arfi wulak'anci."

  "Mama wai me yasa ya tsaneni to?"

  Shiru Mama bata amsamin ba sai na Kuma jefo mata tambayar da ke cimin rai.

  "To Mama ko dai nid'in ba d'iyarsa ba ce kamar yarda Maman su Khamila ta ke ambatamin kalman karere?"

  "Yau she ta kiraki da wannan sunar?"

  "Tunda nayi hankali ta ke ambatamin sunar shi yasa bana son zuwa gidan ke kuma sai ki matsamin akan sai naje munyi zumunci da 'yan uwana."

  Shiru Mama ta yi na zuba mata ido cikin fad'uwar gaba.

  "Mama gaskiya ta ke fad'a ko?"

  "Uwata ke d'in ba karere ba ce domin ita da d'iyoyinta arzikinki suke kan ci dan da kud'inki mijinta ya sami bud'i har ta zama haka ta sami bakin kiranki da sunar banza amma zanyiwa tufkan hanci daga yau bata sake ambatamin ki sunar."

  "Mama wai kina nufin Baba Usman ke ce kika ranta masa kud'in da keyin sana'a shi ne dalilin da dik sati ke kawo miki riba?"

  "Eh, jari na bashi dik in aka sami riban sati sai ya raba uku ya bani kaso d'aya ya rik'e kaso biyu."

  "Ikon Allah Mama kina da hali mai kyau shi yasa muke ganin haske a lamuranmu."

  "Dik ke ce sila Uwata."

  "Uhm Mamana ta kaina."

  Na ambata cikin murmushi domin labarin ya farantamin rai ainun.

  "Uwata in har ina numfashi bazakiyi kukan damuwa ba sai bisa rubutaccen al'amari."

  "Allah ya amince hakan Mamana."

  "Amin."

  "Yawwa Mama wai me a baya jama'a sun nunamin kulawa da k'auna kamar yarda na ke gani anayiwa yara?"

  "Sosai kuwa an nuna miki k'auna Uwata, dan a yarintarki ke d'in mai masoya ne domin Allah ya hore miki farin jini na ban mamaki, ga samun kyauta a wurare da dama."

  "To Mama me yasa yanzu sai naga kamar suna k'yamata?"

  Na cillo Mata tambayar cikin tsareta da idanu. Kauda kai naga ta yi zuwa can najiyo muryanta cikin rawa.

  "Uwata kinfi gaban a k'yamaceki duk da ta...

  "Duk da me ne Mama?"

  "Tashi muje mu kammala aikinmu tambayoyin sun isa haka Uwata."

  "To Mama amma dan Allah kidaina yiwa Baba kuka sabida yanajin dad'in ganin hawayenki abin da na lura da shi kenan."

  "Na bari Uwata, taso muje muna aiki kina bani labarin yarda d'alibanki ke amsan karatu."

  Mike'ewa na yi ina maijin natsuwar ruhi ganin Mama tana walwala.

  "Ina sonki Mamana."

  "Uwata ni baki ba zai iya d'aukan furucin son da na ke yi miki ba saboda akan ki na fuskanci rayuwa kala-kala shi yasa na ke jin dirin duk abin da ke damunki a ruhina."

  "Mamana hoo ni kam a bakinki na tab'a jin ana jin damuwar wani zuciya cikin wata zuciyar."

  "Uwata kenan."

  "Mama kina da abinda kike son sanarmin amma kina kauce masa, dan Allah meye shi? Kuma aina danginki suke nima nasoma zuwa garesu ina yin hutu kamar yarda Aminiyata Fanta ke tafiya Maiduguri hutu."

  "Kome kike son sani game da ni zan sanar miki amma ba yanzu ba."

  "Sai yaushe Mama?"

  "Ranar da zaki bar gabana zuwa gidan mijinki."

  "Taf! Mama ba rana kenan tunda Baba ya ce ba zan...

  "Zancen Malam ba fad'ar Allah ba ne, ki d'aukeshi tamkar holok'o wanda akeyiwa lak'abi da hadarin Kaka  wanda bazai tab'a zubda ruwan sama ba duk kuwa bak'in da ya yi sannan Malam cewa ya yi bazaki samu mijin da na ke yi miki fatar samu ba, ba wai bazaki tab'a yin aure ba."

  "Mama ni da shi ya ambatamin hakan wai sai dai in k'are a gyaran d'akin dabbobi ba dai zama inuwar aure ba."

  "Shi Malam d'in?"

  "Eh Mama."

  "Yaushe ya furta miki wannan alkaba'in kalma?"

  "An kwana biyu, dan kawai Anas ya zageni na buge masa baki akan idonsa shi ne yazo ya ke ambatamin wai ba zanyi aure ba balle na haihu sai dai in k'are a kwashe kashin dabbobi."

  "Ta Allah ba tashi ba, wuce muje na gaji da jin zancen Malam raina kuma b'aci ya keyi."

  Fitowa na yi na hura gawayi na d'ora mai a wuta saida na soma suyar meetpie sannan Mama ta fito na kalleta ta sakarmin murmushi na taso na mik'o mata robar meetpie d'in dana kwashe na ce "Mama ci kiji yayi dad'i kuwa?"

  D'auka ta yi ta gutsira cikin gyad'a kai
  "Kai Uwata yafi sama da abinda ake buk'ata, gobe zakiyi mana sai mu ajiye muna sha da tea."

  "Mama dik santin ne haka har kika manta gobe ina wurin hayaniya kuma jibi zanje wurin babban hayaniya mai lasisi."

  "Oh na tuna gobe kuna wurin yayen Fanta, Lahadi da laraba kuma kina wurin samun lada na kyau."

  "Uhm Mama wallahi ba dan kin nuna kina son ina zuwa koyarwan nan ba wallahi da hak'ura na yi saboda hayaniyar yaran kad'ai ciwon kai ke sakamin sannan gashi ba wanda ke hurd'a dani makar mujiya na ke zama, abin haushi Malaman makarantar suyi ta bina da kallo tamkar mai d'auke da nak'asa, Allah nagaji Mama ki amince na zauna gida tare da ke kawai yafimin samun natsuwar ruhi."

  "Uwata ki daina hasko wani mugun abu a tare da ke kawai komi zakiyi ki yisa dan Allah insha Allah nasara na tare da ke."

  "To Mamana."

  "Da kyau Hafizan Uwata."

  Murmushi na yi na maida hankali kan aikina ina mai jan istiggifari a asirce domin tuba ga laifukan da na aikata natare da na sani ba. Mama kuma ta zauna ta cigaba da d'ura kunun aya a robobi, tana gamawa k'awata Fanta ta shigo da k'awayenta su biyar had'i da ita, ban sansu ba amma na hango duk suna kama da juna, sai k'amshin turare suke bugawa na lumshe ido domin naji dad'in shak'ar k'amshin kasancewata ma'abociyar son k'amshi. Suka zube suka gaida Mama cikin girmamawa kamar yarda sukaga Fanta ta yi.

  Kunun ayar mai sanyi Mama ta basu tare da d'iban musu meetpie ganin tana shirin rabe musu Fanta ta d'auke robar tana cewa "Mama wallahi ya ishesu haka kuma sunci wanda zan basu gobe ehe."

  Dariya na soma k'awayen na tayani tare da dawowa kusa da ni suka kewayeni kamar zasu fad'omin cike da nuna k'auna a idanuwansu, kallonsu na yi sai naji wani dad'i na ratsani domin wannan shi karo na farko da k'awaye suka nunan kulawa batare da watsamin kallon banza ba ko jamin tsaki da zarar munyi ido biyu da su.

  "Deejah kawo in tayaki soyawa."

  Cikin 'yanmatan wata ta ce da ni, kafin inyi magana Fanta ta zabga ashar cikin cewa.

  "Kan uban can! Bintu kurance zaki bawa suyar abina wallahi baki isa ba bani wurin in zauna tunda ladar ya isheki kuma kowa ta koma gefe ko in watso mata ruwan mai ta koma gida sa tanbo."

  Me zasuyi in ba dariya ba, Mama kam barin wurin ta yi dan lamarin Fanta yafi k'arfinta.

  "Fanta ke dai kin fiye rowa da alama zan koma k'awance da Deejah na barwa su Fiddausi ke."

  "Kai nima da Deejah zanyi tunda gidansu ana raba kunun aya mai dad'i."

  "Fiddausi uwar kwad'ai to ba mai kwacen k'awa, domin Fanta a kayi Deejah ita kad'ai dan kusani ehe."

  Dariya muka saka. A haka na kammala suyar muka shiga d'akina na shiga wanka bayan na shirya na d'auko mana abinci tare da kayan sanyi muka baje muna ci ana hira. A nan Fanta ke sanarmin daga inda k'awayenta sukazo wato daga asalin garinsu Maiduguri wanda na gano 'yan uwan juna ne dan tushensu d'aya suka fito.

  Sai kallonsu na ke yi wayayyu da su ko wacce da babban wayarta tana latsawa sai a nan na hango ta Fanta sabuwa dal na zare ido ta kwashe da dariya tana cewa "Uncle ya bani gift d'azun da safe naso shigowa na nuna miki amma Aunty masifa ta hanani fita, zan baki tsohuwar tawa ki shigo gari tunda kin zama 'yar k'auye Mama ta ce zata siya miki kince a'a haddar Qur'ani kike son had'awa, kin had'a Haddar kince ta barshi ba kyaso, Allah yanzu komin k'auyancinki sai kin bari na koya miki har kan arziki ki bar yawo da rakata kashi, gidan layi, haba K'awata ga aji ga komi kina yin abu tamkar wacce batayi jami'a ba."

  Murmushi kawai na yi ina yabawa iya surutun Fanta, ko yamu bata had'iyewa. Su kam dariya suka sanya suna taya Fanta cashemin, littafi addu'o'i na d'auko na soma dubawa dole suka rabu dani dan nak'i tofa kalma.

  "Wai Aunty Nafisan ce Aunty masifa Fanta?"

  Bintu ta ambata cikin tsare gira wanda hakan da ta yi na hango kamarsu da Aunty Nafisa sosai sama da Fanta.

  'Wata k'ila uwa d'aya suke.'

  Na ambata cikin raina.

  "Eh ita fa, ko kema kin san sunar ya dace da ita wallahi ba dan ina jin tausayin halin da Deejah zata shiga ba na kewata da tare da ku zan tafi na huta da sababinta kamar tsohuwar makauniya."

  Duka Fiddausi ta taska mata a cinya cikin cewa "Shegiyar gora Allah k'ara bana ban zuwa ba kika ce ni ce banson amoreni zaki zo, to madallah da kiga ganewa idanunki, halinta na 'yammatanci na nan ba abin da ya sanja."

  "Aikam dai Aunty Nafisa ta shiga uku da fad'a kowa yazo wurinta sai ya gudu shi yasa Momy ke yawan ambatar hak'urin Fanta data iya zama da ita na tsawon shekaru biyar bata kawo k'orafin fininarta ba."

  "Au har da ke Sakina kina biyewa sharrin su Fanta?"

  "Kinga Bintu zamu kwashi jakar uba da ke idan baki daina kirana ina yiwa Nafisa sharri ba."

  Hangame baki mukayi jin ta kira Aunty Nafisa ba sakayawa.

  "Kunga dik abinda Fanta ta ambata gaskiya ne dan kowa a cikinmu yasan halin tijararta dan haka a binda yafi mu bita da addu'a kawai ba zaman cin mananta ba."

  "Maganarki gaskiya ne Beebah." Fiddausi ta ambata ahankali sai lokacin na tsoma baki kuma a karon farko dana na yi magana tun shigowarsu, domin sam na shafa'a ko gaisawa da juna ba muyi ba.

  "K'awata tunda kinsan halinta abinda yafi kici maganin zama da ita kawai, domin wasu haka Allah ke yo su masu fad'a batare da anyi musu laifin komi ba."

  'Kamar Baba kenan.'

  Na ambaci hakan a raina cikin lumshe ido wanda suke cike da jin barci.

  Ihu da naji sun saka yasa na bud'e ido da sauri, Fanta ta kyalkyale da dariya tana cewa "Bana sanar muku cewa muryanta mai dad'i ba ne, shi yasa take rowarsa dan sai ku d'auki sama da awa kuna zaune batayi magana ba sai murmushi kamar gonar auduga idan kunji tana surutu to da Mama ce ko ni idan nataki sa'a."

  "Kai Fanta banda sharri dai."

  Na ambata ina shafo wuyana.

  Wani ihun suka kuma sakawa na bisu da kallo ina hango yarintarsu sabida bisa alamu na girmesu duk da sun kaini girma da cika domin ko Fanta na bata shekaru kusan uku, su d'inma baza su wuce age mate dinta ba, Beebah ce kawai na hango zamu iya zuwa sa'anin juna dan ko kamewa tafi su haka itama na lura miskila ce dan bata cika magana ba.

  Tundaga lokacin suka cikani da tambayoyi dan kawai inyi magana ni kuma na biye musu dik da takuranin da sukayi. A ranar bak'in cikin da Baba ya sanyamin zuwan su Fanta ya sa na manta farin ciki ya maye gurbinsa. Sai da muka sallaci isha'i suka tafi bayan munci tuwon dare wanda ni da su muka yi aikin.

  Bayan sun wuce sabon hira muka b'ud'e da Mama mai cike da farin ciki sai misalin sha d'ayan dare na kwanta a d'akinta ina saman gado ita kuma tana zaune saman sallaya tana jan carbi.

  Kamar a mafarki na jiyo hayaniya ko da na bud'e ido Baba na hango ya wani shak'ure Mama a lungu, cikin magagin barci na sakko zan iso wurin tunanina dukanta yakeyi na bashi hak'uri amma muna had'a ido da shi ya saukemin mugun kallo da jajayen idonsa wanda hasken da bai wadaci d'akin ba ya haskomin fuskansa, na koma saman gado da sauri dafe da k'irji sabida a yawan shekaruna na fahimci sunnah Baba ke son ya yi da Mama cikin k'arfi.

  Wani sarawa kaina ya yi sakamakon jiyo kalaminsa gareni.

  "Koma ki kwanta ki saurari abinda kike burin ji da gani wanda shi ne ya ya janyoki d'akin kwana alhalin kinsan girkinta ne."

  "Wallahi Baba...

  "Kwanta abinki Uwata kunyarsa ba naki ba, maza ka haik'emin a gabanta Malam tunda burinka kenan taga tsiraicinmu."

  "Haka kika ambata ko Hurera? Zanko shayar dake mamaki yau Hurera."

  Ya amabata cikin wani nishi da ya gigitamin natsuwa, a kuma lokaci d'aya Mama ta rafka salati mai k'arfi.

  Ban san sadda na diro ba na fice zuwa d'akina na kulle k'ofa na jingina da shi na saki kuka jikina na mazari tamkar wacce aka watsawa ruwan k'an-k'ara.

Comments

2 comments