Rubutu

Blogs » Kagaggun Labarai » Damuwata: Kashi Na Uku

Damuwata: Kashi Na Uku

 • "A wacce duniya na ke ni Nana Khadijatu? Wacce kalan rayuwa ce  haka? Wani irin bak'i dare na fad'o cikinsa mai mugun duhu? K'alu innalillahi wa Inna ilaihin raji'un!, Allahumma igfirli war hamni. Lahaula waka quwwata illa billahil aliyul azim. Shin Baba wani kalan mutum ne? Shin haka keyiwa sauran d'iyoyinsa ko ni kad'ai ya ke b'e ke yiwa hakan? Hakik'a Baba bakayimin adalci ba, ba ka kyautata min, ka tozartani tozarci mafi muni, wallahi  na tsane...

  "Allaha natuba ka yafemin fushin zuciya ne amma bazan tab'a tsanar wanda ya yi silar kawoni duniya ba."

  Na ambata tare da tura kaina tsakanin cinyoyina ina girgizawa, kuka na kuma fashewa da shi cike da jin matsanancin tausayin kaina tare da Mama, kimanin mintoci goma shabiyar saanna na tsagaita da kukan domin ya kasa yimin maganain zafin da na ke ji a ruhina sai ma k'aramin rad'ad'i sa ke yi.

  Cikin layi na mik'e zuwa toilet na d'auo alwalla na zauna saman darduma domin bazan iya tsayuwar gabatar da sallar nafila ba. Istiggifari na soma ja batare da nasan yawan adadinsa ba domin saida nayi iya yina sannan na koma kan yiwa Annabi S.A.W salati shima nayi bakin yarda ya samu sai na cike da hailalah, na d'ora da ambatar sunar Allah AL-DAFI'U. Na sami awa biyu a zaune cikin amincin Allah na somajin natsuwar jiki da ruhi na samuwa gareni, Alhamdulillah na kama ambata a fili ina jan hanci ruwan hawaye kuwa wannan ba'a maganarsu domin jin natsuwa ya soma rab'ata sai wani rauni na daban ya nashe ruhinta tare da k'arin zubar ruwan jurwaye, tausayin kaina na ke ji tamkar irin wacce ta rasa kowa a duniya.

  Gyara zama na yi na soma tashibi na musanman ga Allah S.W.A dan samun cikar mizani da ayyukan alkhairi ranar sakamako wato _Subbahanallahi wa bi hamdihi wa Subbahanallahil azim._ Ban san adadin carbi nawa na ja ba amma na san dai natsuwa ya gama nashe ruhina da dukkan gab'b'aina.

  Samun kaina nayi da sakin murmushi, idanu na lumshewa cike da jin matsanancin barci. Barcin ne ya soma fizgata na tsuke baki na cigaba da ambaton addu'ar tafiyar da k'uncin zuciya a'a asirce duk dan na k'ara samun natsuwa, ba jimawa kuwa barci ya d'aukeni batare da na sani ba.

  A firgice na farka jin muryan Mama na kirar sunana. Rik'eni tayi ganin yarda nake zaro idanu cike da tsoro.

  "Uwata koma barcinki banzo dan na tasheki ba, nazo duba yarda kika kwana ne, kuma alhamdulillah tunda alamu ya nuna kin sami barci mai dad'i."

  Shafo fuskata na yi na ce "Mama rana ta fito banyi sallar subahi ba."

  "Garin ya hakan ya faruwa uwata?"

  "Mama bari inyi sallah dai."

  "To maza tafi kiyi dan yanzu kusan k'arfe takwas na safe muke ciki."

  Da sauri na mik'e na fad'a bayi. Bayan na idar da sallah Mama ta sake shigowa d'auke da jug tare da cup ta ajiye a kusa dani ta kuma fita ta dawo rik'e da madaidaicin kula, murmushi na yi na rik'o hannunta na ce "Mamana Allah ya biyaki da dubun alkhairori, ina sonki Mamana sama da son da na ke yiwa kaina."

  "To Uwata nagode, yanzu maza ki karya kizo ki wuce wurin walimar Fanta dan ta shigo har sau biyu duk kina barci."

  Idanu na zaro domin na manta da saukar Fanta. A hanzarce na kammala karyawa inda banci wani abin kirki ba duk kuwa da magiyar da Mama keyimin da na cinye. Wanka nayo na shirya dik a cikin gaggawa na fice da d'an gudu Mama ta rakani da addu'an alkhairi.

  Ina fitowa waje Baba na isowa, wuce shi nayi tamkar ban gansa ba duk kuwa da na gansa tare da abokinsa hakan bai sa na tsaya gaisar da su ba saboda hakanan naji tsanarsa danake kaucemawa ya dira a ruhina, mutuncinsa na son samun nak'asu a idanuwana.

  "Malam wancan ba Khadija ba ce ta gidanka?"

  "Ita ce."

  "Yaushe ta koma mara tarbiyya da har zata iya wucemu bata gaishemu ba."

  "Mallam Ilya wannan ba komi ba ne da alama hankalinta ne bai wurinmu."

  "Anya kuwa?"

  "Malam Ilya shigo kayi aikin dana rok'i arziki kawai yafi wannan zantukan d'iyoyin zamanin wanda in baka dasu a gidanka to danginka basa rasawa."

  "Oh to yanzu na gane gori kake son yimin akan...

  "Walalhi Malam Ilya ka yarda ba gori na ke yi maka ba kuma dan girman Allah ka bar zancen nan kada ta koma ta wani sigan da rayuka zasu ba'aci."

  Daga gaka Malam Ilya bai sake furta kalma ba ganin haka sai Baba ya ja hannunsa suka shige cikin gidan domin bawa Mama hak'urin abin kunyar da ya aikata daren jiya wanda son zuciya yayi masa jagora, shi ne dalilin gayyato abokinsa.

  ****
  Ina shiga gate d'in gidan su Fanta na hango Aunty Nafisa tare da Uncle sun jero cikin shigar alfarma, da alama wurin walimar zasu tafi. Na k'arasa na russuna cikin ladabi na gaisar da su. Uncle ne ya amsa tare da tambayata dalilin da yasa na makara zuwa wurin taron.

  Kasa amsa mishi na yi saboda da yarda jikina ya d'auki rawa sakamakon ganin yau ya tsaya yimin magana mai tsayi abinda baitab'a yimin ba tun sanin da na yi masa, maganarsa gareni bai wuce amsa gaisuwa shima atak'aice.

  "Oya taho muje dama can muka nufa."

  "No, bata kudin Napep kawai Abban Hafiz ta wuce"

  "Ba zan bata ba."

  "Me ye haka Abban Hafiz?"

  "Mele ne, kuma ki fita idanuna wallahi ko ranki yafi na d'azun baci, kin daiji na gaya miki, sokuwar banza kawai wacce ta girma amma tamkar ana k'ara mata rashin tunani, mitchew!!"

  Ai ko da Uncle zai duba na kusa kaiwa k'ofar k'aramin gate domin ina jin kalma Aunty Nafisa na bar wurin a hanzarce dan na san waye ita ba abin damuwarta ba ne ta rufeni da duka ta barni da ciwon jiki dan tasha dukan Fanta a gabana shi yasa na ke jin tsoronta ainun. Ina tsoron dik abinda zanyi atabamin lafiyar jiki shi yasa ita kanta Mama bata iya duka ba sam.

  Sai dai duk abin da Uncle ke fad'awa Aunty Nafisan sun shigo kunnuwana saboda ya bud'e murya, jin fad'arsa ya kuma rud'ani na k'ara sauri.

  "Khadijatu!"

  Na tsikayi muryansa na kwalamin kira ai a guje na fice wajen gate, cikin sa'a ina fitowa Napep na sauke fasinja na fad'a tare da sanar da shi inda zai kaini. Shima ganin yarda na ke bai tsaya b'ata lokaci ba ya fizga Napep d'in muka tafi. Sai sauke numfashi na ke yi tamkar wacce ta yi gamo da dodo sai lamari ya bani dariya na sunkuyar da kai na yi ta sauke murmushi. Taka burki da mai Napep ya yi ba shiri ya saka na d'ogo a  hanzarce cikin ambatar sunar Allah AL ALIMU.

  "Fito na ce ko in sab'a miki!."

  Fitowa na yi jikina na rawa zatona marina zaiyi sai ya nunamin motarsa na tafi cikin sanyin jiki na bud'e gidan baya na zauna tamkar munafuka.

  "Malama ki saki jikinki kada wannan munafuncin naki ya kuma janyo hankalinsa kanki abinda faruwar hakan zai iya janyo miki matsala da ni."

  D'agowa nayi ina kallon cikin idanun Aunty Nafisa tako zabgamin harara murmushin yak'e na sauke mata tare da maida fuskata gefe.

  "Wallahi sai naci ubanki bokan nan."

  Da sauri ya kalleta, ta kuma gabgamin harara, na b'ata rai tare da cewa

  "Babana ba boka ba ne."

  "Ubanki! Me ye shi, in ba Boka ba?"

  Sunkuyar da kai na yi sabida ban saba maidawa wanda ya girmeni da magana ba amma na k'udurta zanyi mata nasiha akan kada ka sake ambatawa mahaifina kalman Boka.

  Motsin tafiyar motar ya sanar dani Uncle ya shigo motar.

  "Khadija idan nakuma baki umurni kika tsallake to har gaban Malam zanje na baki kashi."

  "Kayi hak'uri Uncle."

  Bai tankamin ba sai nima na tsuke bakina ina cigaba da kallon gefen titi sannan inaji a jikina Aunty Nafisa kallon banza take watsamin tamkar yarda ta saba yiwa kowa.

  "Ke da Fanta abu d'aya na ke d'aukanku, wato k'annin matana dan haka kada ki sake aikata min abinda Fanta bazata iya yimin ba."

  "To Uncle, inshs Allah zan kiyaye."

  "Hakan yafi."

  "Abban Hafiz wai...

  "Nafisat idan kinsan kalman ki ba ta arziki bace to ki barta a ranki zaifi."

  Kallonsa na yi fuskan nan tasa a had'e tankar yarda na sanshi a baya. Ware min idanu ya yi ta mirror alamun me ye? Na sunkuyar da kaina k'asa a hanzarce cike da jin kunyar abinda na aikata wato kallo abin da na tsani ayimin.

  Daga haka ba wanda ga sake magana har muka iso harabar makarantar. Na kama k'ofa zan fita na tsinkayi muryansa cikin kaushi

  "Wait! Khadijatu."

  Komawa na yi na zauna ina wasa da zobben azurfan dake yatsana.

  Magana naji yanayi a waya bisa alamu da malamin makarantar ne, yana ajiye wayar nawa ta d'auki k'ara fito da ita nayi daga cikin pose d'ina mai kyau ainun wanda Mama ta yomin tarabar shi data shiga kasuwa.

  Mama ce ta ke tambayana yarda na isa na tabbatar mata da lafiyalau. Ina sauke wayar a kunnina idanunmu ya had'u dana Uncle samun kaina na yi da kallon cikin idanunsa tamkar yarda ya ke kallon nawa, musmushi ya yi tare da juyowa ya kalleni sosai na yi hanzarin sunkuyar da kai ina latsa gidan layina fad'in Fanta.

  "Nafisat dama k'anwar taki bata da waya baki sanarmin ba?"

  Yarda ya yi maganar ba wanda zaice shi ne ke fad'a d'azun.

  "Wa kenan?

  Ta ambata a dak'ile hankalinta na kan wayarta.

  "Nana Khadijatu."

  "Yau she na ke da k'anwa mai wannan sunar Abban Hafiz?"

  "Oh ya rabbi, a gaskiya baki da kirki Nafisat, yanzu k'awar Fanta ai k'anwarki ce inda kara."

  "Idan kuma babu karan fa?"

  Kafin ya bata amsa Abokinsa da ya kira ya iso dan haka sai ya bud'e k'ofar ya fice sun sami mintoci biyu zuwa uku sannan Uncle ya umurcemu da mu fito inda muna fitowa sukayi gaba muka rufa musu baya. Wannan damar Aunty Nafisat ta samu ta yi min gargad'i akan fita harkan mijinta. Ni sai lamarin ya zamomin wani kala domin tun tasowata bantab'a cin karo da wata nayimin gargad'i akan mijinta ba ko saurayinta. Haka nan kawai naji wani nishad'i na ratsamin ruhi a maimakon shiga k'unci domin Aunty Nafisat ta sokamin maganganu masu zafi wanda zasu k'ona min rai ta hanyar kiran Baba da Boka abin da ta hango na tsani jin kalman shi yasa a zantukan nata ta yi ta kiran Bokan Ubanki, amma sam basu k'onamin rai ba kamar yarda ta ke da buri.

  Daf da zamu isa wurin muta be na kalleta cikin murmushi mai sauti ta ware ido na kuma murmusawa tamkar zanyi magana sai kuma na tsuke baki hakan kuwa ya b'ata mata rai dan hannu ta d'aga zata zabgamin mari na yi saurin sunkuyawa ta sami iska wanda ya jata ta tafi zata fad'i na yi hanzarin tareta cikin ambatar sunar Allah RAHMAN. Da sauri Uncle ya juyo tare da abokinsa.

  "Lafiya?"

  "Normal Dear kawai d'an tuntub'e naji."

  Ta bawa Uncle amsa cikin tureni daga rik'on da nayi mata.

  "Allah ya kara kiyayewa."

  Abokin Uncle ya ambata.

  "Amin."

  Na amsa tare da gaisar da shi ya amsa cikin kauda kai gefe yana mai gaisar da Aunty Nafisat. Tamkar mai ciwon hak'ori haka ta amsa Uncle ya ja dogon tsaki ya yi gaba dan yaji haushin abinda tayiwa abokin nasa.

  Wuri na musanman Malamin ya kaimu wanda baida nisa da inda ya ajiye Uncle domin wurin maza daban mata daban. Hak'ik'a wurin ya tsaru matuk'a dan wurin manyan bak'i ne, lumshe ido na yi ina hasko sadda na zauna a cikin taro irin haka.

  "Alhamdulillah, ya Allah da ka bani ilimin addini da na zamani dai-dai misali, Ya rabbi ka bani ikon aiki da su ta hanya na gari."

  Na furta a hankali.

  Tsakin da Aunty Nafisat ta ja yasa na bud'e ido duk sai naji na takura sabida yarda Aunty Nafisat ke zabgomin harara da kuma idanun mutane da ya dawo kaina, murmushin yak'e na yi ta yi ina kallon idanunta ta kuma jan tsaki mai sauti sama da na farko sai na kauda fuska na yi kamar badani ta ke yi ba zuwa can na fakaici idanun Uncle na sulale zuwa wurin su Bintu wanda tun ganina suke ta d'agomin hannu.

  "Ayya Deejah kinyi kyau sosai."

  Suka ambata a tare.

  "Nagode, kuma kunyi kyau."

  "Deejah k'awarki tayi fushi da ke."

  "Safeena a tayani bata hak'uri, jiya na raya daren ne da yiwa Annabi salati shi yasa na tashi a makare."

  "Masha Allah, rayuwarki na kan burgeni matuk'a."

  "Uhm."

  Na ambata cikin sosa gefen idona.

  Haka suka yita min hira ina biye musu cikin jin dad'in kulawar da suke bani.

  'Karfe goma dai-dai aka soma kiran masu saukan suna yin karatu. Masha Allah shi ne abin ambata domin kowa a ka kira zaiyi karatu cike da kwarewa, Fanta harda kuka sadda akazo kanta lamarin da ya ja hankalin mutane sukayi ta sanya mata albarka tare da yi mata lik'in kud'i ciki har da ni da su Bintu, Uncle kam mu da muka rufeta ya yi ta zubawa 'yar dari biyar-biyar sabbi fil.

  'Karfe biyu da mintoci goma sha biyar aka tashi taron cike da farin ciki.

  Muna isa gida sallar azuhur mukayi. Ni da Beebah muka hau hidima da tulin 'kawayen Fanta zuwa la'asar dik sunka watse, muna zaune a d'akin Fanta sai hayaniya sukeyi na koma gefe na sami gefen gadon Fanta na zauna ina duba wayarta domin soma gane yarda ta ke saboda daga jiya zuwa yau na ji son rik'e babban waya. Maganar Aunty Nafisat na tsinkaya cikin hargajinta na fama.

  "Ke! dalla ta so ki dafamin abinci."

  Tsit d'akin ya d'auka na d'ago na bi su da kallo sai naga ni suke kallo sai na maida kai ga abinda na ke yi.

  "A haka Abban Hafiz ke ambatarki da k'anwata, inayi miki magana kin bawa banza ajiyata, uhm yayi miki kyau, labari zai isa kunninsa domin na san ke ba K'awata ba ce."

  Da sauri na d'ago har ta juya zata bud'e k'ofa na ce "Ayya Aunty ban san dani kikeyi ba, kiyi hak'uri muje na dafa."

  Batare da ta juyo ba ta amsa "Ban son gulma kawai in zakizo kizo ba sai kin cikamin kunni da karad'i ba."

  Baki bud'e na raka bayarta da ido cike da mamakin k'arfin halinta tare da nunan iko alhalin bai zama dole inyi mata aikin ba.

  Tsaki Beebah ta doka ta fice fuww, Bintu ta rufa mata baya Fanta ta janyo hannuna cikin cewa "Ba girkin da zakiyi mata dan ke ba 'yar aikinta bace."

  "Wallahi Deejah kada kiyi tunda bata san yarda zata nemi arzikin ayi mata abu ba."

  Fiddausi ta furta cikin fad'a.

  "Uhm nikam na tafi gidan Mama nasha kunun aya.

  " Safeena ta ambata tare da ficewa.

  "Jirani mu tafi dan nasan halin k'awata sai tayi girkin ni kuma ban shirya ta yata ba."

  Rik'o hannun Fanta na yi ta fizge ta fice da gudu Fiddausi ta rufa mata baya da gudu itana. Girgiza kai na yi na fito zuwa d'akin Aunty Nafisat hayaniyarta najiyo cikin muryan fad'a sai ban shiga ba na juyo zuwa kitchen na samu ta fitarmin da dik abinda zan buk'ata. Aiki na somayi cikin kwarewa domin amfani da kayan wutar baizamemin abin wuya ba dan nasaba taya Fanta girki da su sannan girki wani sashi ne na rayuwata domin idan ina yinsa har wani nishad'i na ke samun kaina ciki, lokuta da mada Mama kan kirani da Uwata sarauniyar girki, jin hakan na k'aramin k'aimi wurin ganin na dafa abinci mai rai da lafiya.

  A cikin awa biyu na kammala dafa jelop rice wacce ta ji kayan lambu da yankakkun Hanta tare da had'in zobo drink. Ina goge hannuna da towel najiyo k'amshi wani turare mai shegen k'amshi, juyowa na yi cikin lumshe ido sakamakon kasancewata mai son k'amshi,

  "Sannu da Aiki."

  Na bud'e idanu da sauri jin muryan Uncle wanda ke tsaye a bakin kofar kitchen hannayensa zube cikin aljihunsa.

  Kunya ce ta ziyarceni ganin ya ganni babu hijab, kai na sunkuye na ce

  "Yawwa, barka da yammaci."

  Banji ya amsa ba kuma ina ji ajikina kallona ya ke cigaba da yi sai na janyo hijab d'ina dake rataye saman k'ofa na sanya na d'ago muka had'a ido ya murmusa kad'an tare da shigowa ya nufi wormers dana zuba abincin ya bud'esu ya maida ya kulle ya d'auki cup k'arami ya zuba zobo drink dana  jefa k'an-k'ara cikinsa, ya d'auki sanyi.

  Gyashi na ji ya yi tare da hamdala duk a lokaci d'aya.

  "Dama ke Nafisat ta saka aikin dana sanyata?"

  Ban amsa ba sabida ban san amsar sa zan bashi ba sabida kada na ambata eh ya zamo na yi laifi a wurin aunty Nafisa.

  "Thank you Khadijatu, me kike so na baki amatsayin tukuici? Saboda kin farantamin rai ta hanyar fitar da ni jin kunyar abokan kasuwancina."

  Still ban ce komi ba dan wani yanayi na fad'a domin wannan shi ne karo na biyu tun zamowata budurwa da namiji ya tab'a yabamin har da neman zab'ina akan wani abu da zaiyimin na farantawa.

  "Uhm ina saurarenki."

  Muryansa ya katsemin tunanin dana fad'a.

  Kallonsa na yi kad'an sai naga ya cikamin ido kuma na kasa furta kalma.

  "Bakiji maganar da nasanar miki d'azun ba ko Khadijatu?"

  "Kayi hak'uri Uncle."

  "Oya na ji sarkin tuba, zama sanar da ni abin da kike so."

  Motsa yatsuna nayi cikin saita harshena na ce...

Comments

2 comments