Rubutu

Blogs » Kagaggun Labarai » Damuwata Kashi Na Hudu

Damuwata Kashi Na Hudu

 • "Babu tukuici a tsakaninmu Uncle, dan kawai na yi aikin da ya zamamemin abin alfahari, Ni tamkar d'iya ce ko ince k'anwa a gareka."

  "Nasan da wannan just ina son jin ra'ayinki akan abinda na k'udurta yi miki ne sabida yarda kika farantamin ta hanyar fitar da ni kunya da abinda na nemi alfarma matana da ta yimin amma tak'i sai ta sanyaki gashi kinyi abinda nasan bazata iya shi ba, kinga kin cancanci a faranta miki ta hanyar rukuici."

  "Uncle ka gama faranta min tunda ka ya bi aikina."

  Na amsa cikin fitar da siririyar dariya domin ainun naji dad'in yabon da ya yi min.

  "Wato bazaki fad'aba kenan ko?"

  "Please Uncle ka amince komi na yi a gidan nan nayisa ne domin Allah, badan abiyani ba, ka tuna fa kace nid'in tamkar Fanta ka d'auke ni, kaga kenan yarda bazaka biya Fanta ba nima ba zaka biyani ba."

  "Allah ya yi miki albarka."

  Ya furta hakan a hankali.

  "Amin."

  Na amsa da sauri ina sakin murmushi domin ina son jin an ambatamin kalmar albarka a rayuwata shi yasa kusan kalaman Mama gareni albarka ce mafi yawa.

  Murmushi na ji yayi mai sauti ya rab'a gefena zai wuce, daf da kunnina naji ya ce "Ki dafamana ruwan Lipton mai kayan k'amshi tare da yangen na'a-na'a, yarda dai zai fito da k'amshinsa mai gamsarwa."

  Ban amsa ba saida na ji ya kai k'ofar fice kitchen d'in sannan na ce "To Uncle."

  Juyowa ya yi na yi saurin juya masa baya.

  "Muna da yawa Nana Khadijatu dan haka a cika fulas kamar biyu."

  "Insha Allah Uncle."

  "Very good."

  Ya ambata tare da barin wurin na raka hanyar da yabi da ido cike da mamakin sakewarsa dani yinin yau lamarin da ya zomin a bak'on lamari dan sam ban d'auka haka ya ke da sauk'in hali ba tare da iya mu'amala mai kyau da wanda basu ishesa kallo ba tamkar ni.

  Bayan wucewarsa da mintoci na yi tsam ina nazarin lamarin sai kawai wani nishad'i ya ziyarce ni na cigaba da aikina cikin kuzari inayi ina ambatar sunayen Allah a zucci sabida yin hakan ya zamemin d'abi'a na musanman.

  Tunanin soya naman kaza ya zomin domin su k'ara da shi, ta ke kuwa na soma aikin cikin hanzari. Na kammata kenan ina tsaftace wurin Aunty Nafisa ta shigo cikin jifana da kallon da na tsana wato na wulak'anci.

  "Abban Hafiz ya shigo nan ne?"

  "Eh."

  Wani ashar na ji ta antayo wanda ya sakani tsayawa tsak da abin da na keyi jikina na rawa saboda da yarda na tsorata.

  "Uban me ya sanar miki?"

  "Babu komi Aunty kawai ya umurceni da in dafa masu ruwan Lipton ne sai naga dacewar in soya musu kaji domin karrama bak'in."

  Saukan mari na ji a saman fuskata kafin indawo hayyacinsa ta sakarwa cabinet duka a take man gyad'an danayi amfani da shi ya watso na d'aka tsalle gefe amma duk da haka sai da ya zubomin a yatsun k'afa cikin gigita na kwalla ihu Aunty Nafisa ta kuma d'aukeni da tagwayen mari tare da d'ora kafarta ta ta ke yatsun da man gyad'an ya tab'amin na kuma fasa ihun da yafi na farko k'ara ta k'ara danne yatsun aikam ban san lokacin dana kai mata duka ba na sameta a kusa da ido ta fasa ihu tare da janye jikinta na zube saman guiwayona ina kuka cikin ciccira saboda yarda na ke jin zafin na ratsamin brain yafi gaban kwatance.

  Ban san me ya faru ba sai jiyo muryan Uncle na yi cikin k'araji na cewa "Nafisat! kul kika soka mata wuk'ar nan,shin kin hauka ce!?"

  Ina jin kalman wuk'a na mik'e a guje zan bar kitchen d'in Uncle ya nemi rik'eni na hankad'ashi gafe na fice sai dai kafin in fice falon ya kamani ya rik'e gam a jikinsa.

  "Please Uncle ka sakeni intafi wurin Mamana kada ka kashe mata ni, wallahi ba zan sake shigo mata gida ba, kace tayi hak'uri saboda Fanta na ke zuwa dama kuma daga yau ban sake zuwa."

  Ganin yarda na ke magana kamar bana hayyacina sai ya soma jijjigani yana ambaton sunana da k'arfi, still ban daina son kufcewa ba tare da jadda masa bazan sake shigowa gidan ba, gyara runguman da ya yi min ya yi tare da cewa "Please calm down Deejah, no one can harm you again, I'm with you."

  Cak na dakata ina gwama numfashi, jin yarda hannunsa ke yawo a gadon bayana

  Kimanin mintoci biyu zuwa uku sannan ya sakeni na zube saman kneel d'ina ina cigaba da kuka mai sauti domin zugin da yatsun keyimin bana wasa ba ne.

  "Kalla kigani Nafisat, shin wannan shi ne sakamakon da ya dace kiyiwa wacce ta faranta miki ta hanyar fitar da mijinki kunyar idanun abokansa? Haba Nafisat, daga taimako sai ki nemi halakata? To wallahi kinji na rantse wannan shi ne karo na farko kuma na k'arshe da zaki sake aikata wannan rashin hankalin a gidana, yanzu da banzo ba soka mata wuk'ar zaki yi ko me?."

  "Da ka bari kaga me zanyi mata da wannan tambayar 'yan sandan naka?"

  "Nafisat kina son in fusata na sauke fushina akanki ko?"

  "Sakina zakayi Abban Hafiz ko me?"

  "Ko me zanyi idanunki zai ganemiki."

  "Wai me nufinka a kan wannan shegiyar yarinyar?"

  "Abinda zuciyarki ta karanta miki kuna ita ba shegiya ba ce kinsan waye mai sunar."

  "Na rantse da tsarkin mulkin Ubangiji baka isa ka tijarani gaban wannan mai suffan aljannun ba dan zan iya yin ajalinta wallahi dan haka tun wuri ka dawo hayyacinka ko in...

  "Mahaukaciyar banza da wofi wacce girmanta ya zama na iska, dalla rufemin baki mai bak'in hali kawai wacce ko jininta bata kyale ba, Allah ya kawo miki sauk'in wannan jarabar "

  "Ni d'in Abban Hafiz?"

  "Yes ke!, Ko da abinda zakiyi ne?"

  "Na rantse sai naci Uban Aljannan yarinyar nan."

  "Kidai ci naki!"

  "Muhseen! Ni kake zagi a gaban wacce ta isa ba?"

  "Ba zagi ba, ina daf da nad'a miki duka billahil azim Nafidat!"

  Ina jin yarda Uncle yayi furucin cikin mugun fushi na ji wani k'arfi ya zomin na tashi na fad'a d'akin Fanta na kulle tare da zare key na fad'a saman gado na tura kaina cikin filo na fashe da kuka mai fitar da hucin yaji a ruhi. Na d'auki lokaci ina yin kukan kafin ciwon da marata keyi ya dakatar da ni na koma juye-juye ina ambaton sunar Allah. Jin ya lafamin sai na tashi da k'yar ya bud'e bedside drawer na d'auko tablet na b'alli really extra tare da maganin ciwon mata nasha na koma na kwanta ina mai addu'ar samun sauk'i a cikin raina. Zuwa can na kuma tashi zaune na tsirawa yatsun k'afana ido sunyi bororai,biyu cikinsu sun fashe sakamakon murjesun da Aunty Nafisa ta yi.

  "Oh ni Deejah wai me nayiwa wannan baiwar haka da zafi ne?"

  'Bakiyi mata komi ba tsabar mugunta ce irin nata wanda har jininta bata bari ba.'

  "Na yarda mugunta ne kuma insha Allah bazata sake ganina a gidanta ba balle ta nemi kasheni. I'm sorry Fanta nasan hakan bazaiyi miki dad'i ba amma dole ne na yi nesa da 'yar uwanki tun batayi ajalina ba."

  Komawa nayi na kwanta inajin tsigan jikina na tashi alamun zazzab'i zai kamani, tun ina karanta wasik'an jaki har barcin wahala ya d'auke ni batare da na shirya ba.

  Jin ana tab'amin k'afa yasa na farka nayi arba da Beebah rik'e da almakashi tana bud'e bororan, su Fanta sun kewayeta, ganin na tashi sai duk suka soma jeromin sannun amsawa narik'ayi a hankali cikin dushewar murya.

  "Uwata sannu kinji?"

  Na tsinkayi muryan Mama daga nesa.

  "Mama kinga yar... Sai kuma na fashe da kuka batare da na fad'i abinda nayi nufin fad'a ba.

  "Please Khadijatu kiyi shiru yanzu Beebah zata gyara wurin ki sami sauk'in zafin."

  Motsawa Uncle kai nayi ina mai rintse ido jin yarda ciwon ke yimin zafi. Tabbas badan ganin Uncle a wurin ba da ihu zanyi ta zabgawa domin nasan ina da raki, abu kad'an ke sakani kuka haka ciwo komin k'ank'antarsa ina iya yi masa kuka. Kunyar idanun Uncle ya taimaka nayi jarumta amma duk da haka saida nayi k'anin kuka wato kwalla. Bayan Beebah ta gama gyaramin k'afar Uncle ya fita ba jimawa ya dawo tare Aunty Nafisa ta isa gaban Mama ta gaisheta cikin girmamawa wanda na bawa zuciyata cewa Uncle ne ya sakata yinsa dole.

  Inda na ke ta iso ta yi k'asa da murya tamkar mai rarrashina ta ce "Banyi nadamar k'onaki ba saima nishad'i da na wadata shi, tamakr irin haka zan cigaba da baki assignment har ki gane bakin rijiya ba wurin wasar makaho ba ne."

  "Nagode Aunty, Allah yayi miki abinda kikayi min."

  Na ambata yarda kowa zai jiyoni sab'anin nata.

  "Amin."

  Su Fanta suka amsa domin d'aukansu addu'a Aunty Nafisa keyimin yayin da a gefenta ta ware ido tana kallona na sakar mata murshi tare da yunk'urawa na mik'e Mama tayi hanzarin rik'oni.

  "Mamana zan iya takawa fa."

  "Nasani Uwata, mujeĀ  ahakan kawai kinsan bazan barki ki tafi da kanki ba."

  D'ora kaina nayi saman kafad'unta cike da shagwab'a har da wani tale baki irin na yara. Aikam su Fanta suka saka dariya ina kallo shima Uncle saida ya murmusa ya yin da Aunty Nafisa ta zabgomin harara cikin dibara. Har gida su Beebah suka rakomu tare da Uncle wanda wannan shi ne shigowarsa karo na farko.

  Har na yi wanka na ci abinci kad'an bisa turasawar Mama tare da shirin barci duk su Fanta na nan basu da niyyar tafiya gida. Duk da inajin barci sabida maganin da nasha har da na sa barci amma sai na zauna ina sauraren hirarsu wanda baki d'aya yake gudana akan bak'in halin Aunty Nafisa.

  Zuwa can Fiddausi ta kalli agogo ta ce "Kuzo mu tafi dare ya yi kuma gashi gobe zamuyi asubanci."

  "Gobe zaku koma?"

  Na cillo mata tambayar.

  "Eh amma Kano zamu tsaya muyiwa k'anwar Momy kwana biyu sai mu wuce sabida ankoma makaranta musanman sister Beebah da ta ke aikin taimakon al'umma."

  "Masha Allah sister Beebah ina godiya da kulawarki sosai."

  "Bakomi Deejah sai dai muna son sanin abinda ya faru kika k'one."

  "Tsau-tsayi ne kawai, na gama soya kaji na ajiye maid'in, sam namanta da shi kusa dani sai kawai na shuresa shi ne ya zubemin a yatsu."

  "Ikon Allah, wallahi sadda Uncle ya sanar da cewa tsau-tsayi ne jinsa kawai na yi dan d'aukana aunty masifa ce ta k'onaki ya b'oye gaskiyan dan nasan zata aikata hakan dubi da yarda ta tsaneki babu gaira babu dalili."

  "Kai Fanta banda k'azafi dai."

  "Bintu wallahi dan baki san muguntan Aunty Nafisa ba ce shi yasa na ce tare da ku zan koma, na shak'i 'yanci."

  "To karatun naki fa?"

  "Wallahi dan shi ne amma ina kammalawa zan dawo gida nagaji da masifa wanda duk girmana wata rana dukana takeyi."

  "Duka fa!?"

  Bintu ta ambata idanu waje.

  "Sosai kuwa dan kawai yanzu Uncle ya saka mata doka ne mai tsauri shi yasa ta daina amma ko 'ya'yan bata barinsu Shan iska da bala'inta."

  "Ikon Allah amma in haka ne Aunty Nafisa ta fiye fad'a tare da saurin hannu."

  "Kema kya dai dawo rakiyarta domin ni ce zan bada shaidan haka saboda har yanzu bayana da shedan dukanta."

  Dik shiru sukayi suna kallon Beebah domin sun tuno lokacin da abin ya faru.

  Numfashi na sauke a hankali idanuna kulle domin magan-ganun nasu ya isheni saboda bana son kojin sunar Aunty Nafisa balle labarin muguntarta. Jin sun cigaba da tattauna zancenta sai na haye katifana na juya musu baya cikin fatar samun barci ya d'aukeni. Ba jimawa Mama ta shigo ta sanar musu da sutafi gida dare yasomayi, sallama sukayi mata tare da yimin addu'ar samun lafiya suka fice.

  Jin fitarsu na tashi zaune na tsirawa yatsuna ido ina jin kwallah na cikomin.

  "Aunty Nafisa bakiyi ba wallahi, Uncle Muhseen bakayi dacen mata ba, Allah ya had'aka da ta gari."

  "Amin ya rabbi, wata k'ilama kece."

  Kallon k'ofa na yi idanu waje, Beebah ce tsaye ta sakarmin murmushi tare da k'arasa shigowa ta zauna gefena ta ce "Nadawo in kwana da patient d'ita ce."

  Kauda kai nayi ina hasko rashin tabbaci akan zance ta.

  "Hak'ik'a abinda na fad'a bashi ne dalilin dawowata ba, sanin dalilin da ya saka Aunty Nafisa ta k'ona ki ya dawo da ni dafatan zaki sanarmin da gaskiya ba dan na isa ba sai girman Allah."

  "Waya sanar miki da cewa ita ce ta k'ona ni?"

  "Babu kowa amma na rantse da girman Allah ko kaffara bazanyi ba ita ce sanadin k'onewar yatsun k'afafunki, in kuma ba ita bace kema ki rantse da girman Allah kamar yarda na yi."

  "Ita ce, shi kenan kin samu amsan?"

  Na ambata da sauri cikin kauda kai gefe.

  "No, ina son sanin dalilin faruwar hakan daga nan ni kuma zan sanar miki da abinda na hasko har ya janyo afkuwan lamarin."

  Tsirawa Beebah idanu na yi na wasu dak'ik'u, ita kam sai dokamin murmushi ta ke yi, zuwa can na sauke numfashi ta tashi ta isa bakin k'ofa ta kulle tare da tofa addu'a ta juyo muka zubawa juna idanu.

  "Sanar dani sanadin Deejah."

  Labari na bata daga sadda suka fice ni kuma na tafi d'ora girki har zuwa inda na farka na sami Beebah rik'e da k'afana.

  "A she abinda na hasko gaskiya ne to in haka ne ina addu'ar Allah ya tabbatar da shi ko Aunty Nafisa ta yi hankali sanadin rab'arta da zakiyi, dan walalhi Allah d'abi'unki sun burgeni, musanman rashin son hayaniyarki ga uwa uba aiki da ilimi, shi yasa na ce bazanbi su Safina Kano ba zan zauna tare da ke suje su dawo ta nan sai mu wuce gida."

  "Kai amma nagode da wanna k'auna."

  Na ambata cike da murna matsananci, wanda naga mamakin faruwar hakan a fuskan Beebah.

  "Sister Beebah dole inyi murna da ganin mace 'yar uwata a karo na biyu tun mallakan hankalina ta nunamin k'auna cikin kulawa managarci."

  "Ban gane ba Deejah."

  "Beebah, idan aka cire Mamana da zuri'ar Baba Umaru to Fanta ce ta farko da na had'u da ita ta k'aunace ni ba tare da yimin kallon banza ba tun mallakan hankalina a matsayin mace baliga haka ita ce ta bar abu mai mahinmanci na rayuwarta sabida ni, kamar yarda kika bar zuwa ziyara domin ki kasance tare da ni, kai wallahi nagode sosai, Allah ya faranta miki sama da wanda kika yimin."

  "Amin, amma kalamanki sun sakani a duhu zan so sanin labarinki."

  "Wannan a bayyane ya ke Sister."

  "To ina saurarenki."

  Zama na gyara tare da rungume filo sannan na soma cewa...

Comments

2 comments
 • Rahma kabir
  Rahma kabir Allah ya kara basira muna bibiye dake
  Nov 24 - Report
 • Salamatu Zakari
  Salamatu Zakari Wasa! Farin girki. I thought as much, Alhaji muhseen da fanta? Ikon mai duka. Ya Allah, lallaibkam Khadija kinga rayuwa. Ina nan ina hararo yuwuwar wani lamari\ud83d\ude0a. Any way muna biye. Mrs J Moon jinjina a gateki. In shaa Allah in darai da lfy...  more
  Nov 25 - Report