Makalu

Featured Create an Ad

Rayuwar Zamani: Babi na Daya

 • Sulaiman bai yi mamakin ganinta ahakan ba domin hakan dabiar tace. taku take cikin isa da gadara irinta 'ya'yan masu kud'i y'a'yan masu hannu da shuni, Muhievert kenan yarinya fara doguwa kyakyawa, gata da k'ira mai kyau tsaruwarta ya zarce duk inda mutun ke tunani. Akance mutun ba komai yake iya samu ba arayuwa itakam Allah ya mata baiwar kyau kyaun jiki da k'ira mai kyau ba za'asa haskenta acikin abunda ya k'ara k'awata siffarta ba domin asalin kyau take dashi irin na mutanen Yobe, ga ilimi na addini dana zamani sai dai kuma abunda taji aranta shi takeson aikata wa sam-sam bata duba kyaunsa da rashinsa duk abunda take so shi take aikatawa.

  Sanye take cikin riga mai guntun hannu launin fari da kuma gajeren wando baki ta kama gashinta da bakin ribon ta mai dashi ta gaba sannan tayi irin kwalliyar daya dace da shigarta, rike take da d'an k'aramin jaka wanda ta saka jotter da biro aciki sai farin takalmi mai tsini sam-sam ba zaka kalleta ka sata acikin jerin masu imani ba sai dai ahlul kitab domin batayi kama da wacce za'a cewa musulma ba.

  Tafiya takeyi kamar wata hawainiya sai karairaya takeyi tana cin chewgum kamar wata karuwa tana isowa yayi saurin bud'e mata gidan baya kafin ya gaisheta ta amsa ciki-ciki rufe mata k'ofan yayi da sauri sannan ya shiga ya ja tare da d'aukan hanyar Federal University Bauchi State muryar ta yaji tana cewa "ka tsaya a jifatu saboda akwai abunda zan saya ka kuma k'ara gudu kada nayi latti" ya amsa da "toh hajiya.

  Suna isa bata tsaya ya gama parking ba kawai ta bud'e k'ofa ta fita, shi damuwarsa bai wuce da ace taji ciwo ba yanzu sai ta jawa mutun wani bala'in kamin ya gama tunanin har ta fito, abun mamaki ya ganta da sweet a hannu da sauri ya fita yana cewa "Hajiya akwai kaya a cikine?" ta amsa da "aa daman ga abunda naje saya" tana magana ta nuna mishi sweet din hannunta kafin ta shige mota, atakaice yaja d'an karamin tsaki shima ya shiga ya tada motan suka nufi hanyar makaranta aranshi yana cewa daman abunda

  yarinyan tazoyi kenan!

  Yana zuwa yatarar dasu a falo, sallama yayi kafin ya nemi guri ya zauna ya shiga gaishesu, cikin kulawa suka amsa da fara'a kafin kannenshi suka gaida shi shima ya amsa tare da tambayar su yaya karatu? Sannan ya k'ara da tambayar ina Muhievert? Ammi ce ta amsa da cewa "ai kaima kasan bata kaiwa karfe takwas a gida indai ba tare da kwakwaran daliliba".

  Murmushi ya kirkiro kafin yace "hakane amma yau satin mu uku rabon damu ga juna kuma wai gidan mu d'aya tana matsayin kanwata atleast ba zata iya jira in dawo mu gaisa kafin ta rufe k'ofan d'akin nata ba gaskiya Ammi ni banajin dadin abunnan ki saka baki ta dena shegen gantalinnan tunda shi dai Abbu bame zama bane ni keda alhakin kula dasu amma ni banganta bama balle insan ta ina zan fara gyarawa. 

  Abbu dake kwance akan sofa yana lallatsa naura me kwakwala yace "ni dai nagaji da magana kullun akan yarinyannan ban san dai ko sai ta

  kasheni zataji dadi ba gashi dai Allah ya bamu ku dukanku masu hankali da natsuwa ilimin addini babu mai nuna muku sai dai ku nunawa wasu sai dai duk da haka Allah ne ya jarabce mu da halin Muhievert kuma abunda ya dace shine addua dan duk wani kokari munayi ni da Amminku da yayar taku amma abun nata sai gaba yakeyi" salim yace "haba Abbu dan Allah ka daina fadan haka mu dai mu cigaba dayi mata addua harta shiryu ta gane gaskiya, Zarah na school koh?" Ammi ta amsa da "eh yanzu ta fita itama wai tana da lecture din karfe tara ganin cewa zatayi latti yasa bata jira kun gaisa ba wad'annan kuma yau suna midterm break shiyasa basuje ba" Laure ce ta shigo tare da sallama ritsinawa tayi ta gaidasu sannan tace "Hajiya na kammala aikin akwai wani abunda zanyi ne" Ammi ta ce"okay toh bari inzo in duba nagode miki sannu da aiki zaki iya tafiya Sahura zatayi sauran" godiya Laure tayi sannan ta koma kitchen "ina kuma zataje Ammi?" Raihan ya tambaya "yau za'ayi bikin wata kawarta na islamiya kasan Laure da son zuwa biki shine ta nemi izinin zuwa" ajiyar zuciya kawai yayi yana tunanin Muhievert bai sake magana ba ya nufi dinning suma suka mara masa baya yau daga su sai yan samarin yaranta.

  Suna isa makarantar sai ga tawagarta sun iso da sauri har suna rige rigen bud'e mata k'ofa bayan ta fito ta tsaya musu kallon tara saura kwata amma bai dame suba tunda dai suna samun rabonsu a jikinta tsaki taja sannan tace "haba Slimzy wai meye haka kukeyi sai kace wasu 'yayan kaji please behave mana" duk da maganan ya dan bata musu rai basu wani damu ba saboda sun riga sun saba da irin haka dan ba sabon abu bane a gurinta juyawa tayi ta kalli Sulaiman sannan tace "zaka iya tafiya idan nayi zan nemeka, ba tare da taji amsar saba tayi wucewar ta ko waiwayar sa bata sake ba.

  "Muhievert kinsan cewa idan na shiga aji banason kowa ya kuma shiga ko? dan haka ki fita kafin ran kowa ya 6aci" kallonsa tayi atsanake kafin tace "tsaya tukunna wai ma meye matsalarka da latti na ko an saka gadi nane? In dai ba gadina aka saka ba saika rike damuwarka ka bar shiga nawa yanzu in shiga ne ko na fita dan banson matsala? takaici ne ya kamashi kawai ya tattara kayanda ya bar ajin.

  Sulaiman bai tsaya jiranta ba kamar yanda tace zata neme shi idan ta gama mota yaja yayi wucewarsa dama yasan in ya tsaya jira shine dai zai sha zama gida gashi ko karyawa baiyi ba, yana zuwa ya samu har Laure ta ajiye musu da sauri ya wanko hannu ya d'auki nashi ya faraci dan gaskiya yunwa yakeji shi bai san ko tsutsan ciki ke gareshi ba dan yanzu ya fiye saurin jin yunwa.

  Suna kammala breakfast yace dasu Abbu "Ni zan wuce office gashi har tara ya wuce kada na makara" Abbu yace "ok sai nazo dan inason in koma Yobe gobe akan wani aiki dana fara ga chan brief case dina ka wuce dashi, Allah kiyaye hanya" ya amsa da amen sannan ya fita.

  Yana fita yaci karo da Sulaiman ya tsaya suka gaisa sannan yace "ka kaita makarantan koh, ka cigaba da hakuri da ita dan Allah kamar yanda ka saba dan nasan cewa kana hakuri Allah ne zai shirya Muhievert" ajiyar zuciya yayi tare da d'an murmusawa kafin yace "bakomai wlh ranka ya dad'e ai yanzu an zama d'aya ni ina mata kallon kanwata ne, zaka wuce kenan ko inzo in kaika ne?" shima murmushi yayi sannan yace "ka barshi kawai sai na dawo kar abubuwa su maka yawa tunda zaka kai Abbu kuma ga 'yar rigimata yanzu sai ta bullo da wani abun ka kula da gidan dan Allah" toh kawai yace mishi yana mamakin inda ita 'yar rainin wayon ta samu halinta.

  Ammi ce ta shiga kitchen dan ta kira su Sahura su zo su kwashe kayan da sukaci abincin tana shiga ta samu suna faman aiki zama tayi a kujeran dake jikin centre table din cikin kitchen din sannan tace "ina fata dai kunci abinci saboda na sanku yanzu zakuce sai kun gama ko mai da ko mai kafin kuyi karyawa".

  Jummai tace "Yau kam mun karya Hajiya sai dai hajiya karamace batayi kariba kuma har anyi duk abunda ta buk'ata" tsaki Ammi taja kafin tace "ku bar zancan yarinyarnan ita ta sani idan ma taga dama tayi ta zama da yunwa ni dai kuje ku gyara min dinning mun kammala" Kande tace "Hajiya kiyi hakuri ki rage fushi da ita dan Allah kawai kiyi ta mata addua insha Allahu watarana sai labari" murmushin takaici Ammi tayi kafin tace "Allah ya shirya mana zuri'a domin yanzu Rayuwar Zamani ya dukusar da tarbiyyan da muke kok'arin bawa yaran mu saboda Son Zuciya irin nasu".

  Suna fitowa daga lecture ta fito sai kace ana tura ta, da sauri ta nufi office din Prof Maisamari babu neman izini tayi shigewa abunta sai dai abunda ta gani shi yayi mugun daga mata hankali kuma ya razanata Malamin da ake mishi kallon mutumin kirki ana girmama shi ashe mugu ne azzalumi gashi yau ta kama shi dumu dumu yana aikata zina tare da wata matar aure wacce take ajinsu kuma wannan abu tasan ba zai wuce dan ta samu saka mako mai kyau ba dadi ta d'aya basu san ma ta shiga ba kuma kila ya manta rufe k'ofan ne hakan yasa ta rufe tayi saurin fita ta samu guri ta zauna a k'ofar nashi sai da ta kusan awa tana zaune sannan matar ta fito tana waige-waige duk kallon nata bata kula da Muhievert ba ta wuce tana murnar cewa ta haye babu sake zaman wannan jarabawan, ita kuma tana ganin matar ta tafi itama tayi tafiyarta dama danta rufa musu asiri shiyasa ta zauna (ina zaki damu duniya tabbas duniya abun tsoro ne yana rud'an d'an adam wannan shine abu mai girma dake faruwa cikin jami'a babu tsoron Allah matar aure zataje ta yaye mutuncin aurenta dan kawai abun duniya haka yan mata zasu lalata rayuwarsu dan samun abun duniya su bawa malamai kansu dan kawai suci jarabawa daganan kuma shikenan sun samu sana'a suna yaudaran kansu iyayensu ko mazajensu saboda Son Zuciya ya Allah ka rufa mana asiri duniya da lahira kasa mufi k'arfin zuqatanmu malamai kuji tsoron Allah domin ance kama tudinu tudan duk abunda kayi za'a maka". 

  Yana shiga kowa yatashi aka fara gaishe shi d'aga musu hannu kawai yayi sannan ya shiga lifter dan zuwa office dinshi a second floor ya fita yana shiga ya ajiye jakanshi sannan ya fita zuwa first floor inda office din Abbu yake bayan ya ajiye brief case din ya wuce third foor danyin supervision din ayyukan da akeyi a ranar.

  Abbu na fitowa awanka ya kira sulaiman yace mishi idan yana gida ne ya jirashi yanzu zasuje office, bayan ya ajiye wayan ya shiga yayi wa Hajiya Rashida sallama sannan ya fice ya shige mota suka kama hanya kamfaninsa dake cikin garin Bauchi.

  ♾♾♾

  Dan jakan uba wato tun safe kanata zuba barci sai kace kaza zaka fito ne ko sai na fito da kai mara mutunci ko ance maka gidan ubanka nan din?" tsaki yayi yana cewa "haba dan Allah Goggo ya zaki zo kina damun mutane da safe sai kace wata...."

  Da sauri ta amsa da cewa "sai kace wata me dan ubanka karasa mana fisararre ni bansan cewa haka uwarku Aisha ta koya muku ba tarbiyyan data baku kenan amma uban naka zai zo ya sameni ai mara kunyan banza.

  Yatsine fuska yayi "toh in banda ke bama kinsan in ba dan ance nazo na duba ki na danyi kwana biyu ba kema kinsan ba abunda zai kawoni tunda bakya tsinanamin komai sai masifa da zagin iyayena na yau daban na gobe daban ni kam dama ke kika mutu ba kakanmu ba saboda shi kam baya takuramana kamar yanda kika tsanemu".

  Shuran daya matane ya dawo da ita daga duniyar

  tunanin data shiga yace "ke kuwa Aisha meyasa kika shiga tunani haka? ba tare data kalleshi ba tace "wlh tunani na yaron nan kasan sam bayajin magana, sannan bashiri suke da Goggo ba ni kam hankali na bai kwanta da zuwanshi ba shiyasa tun farko naso ka aika Salma ko Sarah ko Kabir tunda Sulaiman bayanan sbd Hanif bayajin magana yanzu zai jawo mana wata fitinar".

  Malam yace " hakane kam Hanif bayaji sai dai kuma shine dai-dai da zaman gidan Goggo ki kwantar da hankalinki rashin jin maganar shi zai sa su zauna lafiya".

  ♾♾♾

  Sharif ne ya doso inda su Slimzy suke yai musu hy azarihin gaskiya shi dai friend din samra ne yana sonta da kuma yana son yaga ta shiryu amma abun yaci tura sabida yarda sauran ke hure mata kunne. 

  Dogone mai farfadan kirji da kaganshi kaga yanayi na hutu atare dashi yana da tsawo kuma yana da kaurin jiki gashi fari tas ya hadu dai-dai misali hasken su d'aya da Ilham kawar Muhievert dan sunfi Muhievert haske kyau kawai zata nuna musu da kuma kud'i shigar farar riga yayi mai bakin rubutu ajiki inda aka rubuta (crazy boyz) da bakin wando yana karisowa yayi sallama duk ba wanda ya amsa sai can yace "little kin gama lectures ne inyi dropping dinki? kallon sama da k'asa tayi mishi sannan ta d'auke kai dan batason wa'azin da yake mata chan kuma tace "eh na gama muje amma ba gida zani ba sannan idan kasan zakamin surutun daka saba ne gwara ka kyaleni inbi wani hanyan" murmushi yayi yace "kiyi hakuri ba zanyi ba ranki ya dade" sannan suka nufi motarsa kirar venz

  *******

  D̥ͦI̥ͦD̥ͦE̥ͦE̥ͦY̥ͦL̥ͦO̥ͦV̥ͦ T̥ͦḀͦK̥ͦU̥ͦC̥ͦE̥ͦ*

  Lιĸe, coммenт, ѕhare

  Sannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Ma'aurata: Babi na Bakwai

  Posted 6 hours ago

  Ku latsa nan don karanta babi na shida. Bayan wata d'aya Soyayyar Maryama ta hana Habib sakat, duk yanda yaso ya ya k'ince ta ya kasa hakan yasa ya yanke shawarar tunkarar ta zuwan sa uku gidan da k'yar ya samu ya shawo kanta ta amince da soyayyarsa Iya tafi kowa ...

 • Akwai Illah: Babi na Hudu

  Posted Thu at 10:06 AM

  Ku latsa nan don karanta babi na uku. 10 Junairu 2017 10:00am Maiduguri Borno State Wayarsa ya zaro daga aljihunsa tun da ta fito daga gida. Ta madubin motarsa ya ke kallonta duk da hankalinsa na kan abunda yake dannawa a wayarsa. Kafin ta iso ya sak'ala wayar a alji...

 • Waye Zaɓin Munibat? Babi na Hudu

  Posted Mar 22

  Ku latsa nan don karanta babi na uku. Bismllahir Rahmanir Rahim Ban sake sanin inda kai na yake ba sai farkawa nayi, naga Anty da sauran mak'otan mu sai sannu ake min, ni dai ido kawai nake rabawa ina k'ok'arin tuno abunda ya faru, da sauri na koma cikin d'aki ina dub...

 • Matsalolin da waya ke kawowa cikin zamantakewar ma’aurata da hanyoyin warware su

  Posted Mar 22

  A wannan zamanin da muke ciki na yawaitar wayoyin hannu kirar smartphone ya kawo sauyi babba a cikin zamantakewar iyali. Duk da cewa tana da matukar amfani musamman duba da irin zamanin da mu ke ciki, sai dai a bangare guda kuma illolin da wayar ke haifarwa a zamantakew...

 • Darasin Physics: Bayanin banbanci da ke tsakanin mass and weight, dimension, position, distance da displacement

  Posted Mar 22

  Darasinmu na yau zai kawo mana bayani ne game da wasu muhimman abubuwa a physics wanda sanin su na daga cikin ginshikin fahimtar karatun physics. Wadannan abubuwa kuwa sune mass and weight, da dimension da position, da distance da kuma displacement. Ku biyo ni ga bayana...

 • Duhun Damina: Babi na Daya

  Posted Mar 11

  بسم الله الرحمن الرحيم اسلام عليكم و رحمة الله تعالى وبركاته Sharhi Wannan littafi nawa ƙiƙirarre ne, kashi ashirin cikin ɗari, ko ma in ce bai kai ba shine gaskiya, kuma akansa na ƙirƙiri labarina. Mas'alar da na ɗauko a yau mas'ala ce mai girma, hakan yasa na ƙirƙ...

View All