Makalu

Featured Create an Ad

Rayuwar Zamani: Babi na Biyu

 • Dedicated to Autan Hikima.

  Raihan na komawa office ya aiki masinga akan yaje yace ma head din ko wani department yana son ganinsa aconference hall, babu 6ata lokaci duk yabi ya fadamusu kafin ya koma ya sanar da zuwansu.

  Yana zaune a office kafin ya fara komai yaga hoton kannen nasa dake cikin karamin frame fuskar Muhievert ya shafa yace "I love you sister but you won't understand why am always harsh toward you. Change for good please (inasonki kanwata amma ba zaki gane mai yasa nake takuraki ba, dan Allah ki chanja hali)" ya fad'a yana murmushi sallaman Baba masinja ne ya katse mishi tunani bayan ya amsa masa sai yace ya duba mishi office din Abbu koya iso bai dade ba ya dawo yace ya iso, tashi ya yi ya wuce conference hall bai kai minti goma ba yaji sun shigo tashi yayi ya kira Abbu kafin ya dawo ya zauna ajerin kujerun da ke jikin babban table din babu dadewa Abbu ya fito atare suka tashi sai da ya zauna sannan suka gaisheshi suma suka zauna babu 6ata lokaci kowa ya gabatar da duk ayyukan da akayi acikin Department dinsa da yake duk sun saba da barin record hakan ya saukaka musu k'ar6a Abbu yayi ya fara gani, inda za'ayi signing yayi inda yaga da bukatan karin bayani sai ya sake tambaya kafin Raihan yayi stamping sannan ya k'ara musu albashi daga kan k'ananan maaikatan zuwa manya kafinnan ya sallame su sosai sukayi murna tare da mishi fatan alkairi.

  Ammi ce a kitchen tana dafa abinci dan duk kudin su bata wasa da damarta wajen yima mai gida girki in dai ba abunda yaran suke sonci ba duk wani girkin Abbu ita takeyi bata sakaci da hurumin mijinta tana aikinta tana ta salatin Manzo (s.a.w). Chan dai tayi shiru tana tunanin yarta kafin tayi ajiyar zuciya sai da ta gama komai ta kwashe na Abbu akularsa wanda yake daban dana yaran gida harma dana bak'i kafin ta kira kande cikin dadin murya ba cikin nuna isa ba tace idan sun gama gyaran cikin gidan su jera abincin a dining na Abbu su kai sama na yaran abari ak'asa sai su saka turaren wuta aduk kusurwan gidan domin ya fitarda kamshin daya shigo daga kitchen sai Ac shima su kunna dan kamshin ya bada abu mai dadi kafin ta wanke hannunta ta nufi sama. 

  Dakin Abbu ta shiga ta k'ara gyarawa tare da sanya turaren wuta sai d'akinta shima ta gyara ta saka turaren wuta ta kunna Ac kafin ta shiga band'aki ta wanke tas ta fesa airfreshner daganan ta shiga wanka tare dayin alwala fitowa ta shiga shafe shafen su humra don lokacin sallah bai karisa ba, kaya ta saka riga da zani mai manyan pattern wanda akayi design din jikin kayan da pattern din bayan tayi simple makeup ta duba agogo taga har lokacin salla yayi da sauri tasa hijab dinta tayi kabbara bayan ta idar ta dad'e tana yiwa iyayenta da yaranta da mijinta addu'a kafin ta tashi daga kan darduman. Tana idarwa taji horn din mota ajiye hijab din tayi ta fita danyi musu sannu da dawowa.

  ♾♾♾

  Yana karasawa ya bar gurin da gudu saboda ya san halin Goggo sarai yanzun nan sai ta daka mai dundu kama baki tayi tana cewa "yau ni dannan zau ce dama ni na mutu, lallai ubanka zai zo yatarar dani wato har ya haifi dan da zai iya fadamin haka da sauri ta kwalawa Ibro kira ta mika mishi waya ungo danno min layin balarabe yi abu da jiki maza-maza karka 6atamin lokaci" ringing daya biyu ya dauka yana cewa "hello Goggo" tace "elon ubanka, eh nace elon ubanka ko kanada magana ne sai kuma ta fashe da kuka, wato d'an nan katuromin hatsabibin yaronnan saboda yazo ya cimin mutunci koh? ya zageni tatas daga ni har zuria ta balarabe kayi kokari da kai da wannan munafukar matar taka".

  Kukan data k'ara sawa ya d'aga hankalin Malam Balarabe arikice yace "haba Goggo dan Allah kiyi haku..."  bata bari ya karasa ba tace "nace hakurin ubanka wallahi zan tsine maka tunda baka da mutunci" ta fada tana wurga wayan.

  Goggo! Goggo!! Goggo!!! Da sauri ta fito tana cin goro tana kokarin gyara zaninta "nace lafiya daiko kake min kira haka ubana dan ko ubana ne kawai zai kirani irin haka banza gantalalle mara mutunci"

  Hararanta yayi kafin yace "ba lafiya ba Goggo taya za'ayi ke kici abinci ki rage sannan wai inci? ai wannan ci bayane kawai cin abincin da kika rage haka kawai nasan ba wai wani wanke hannu kikayi ba kilama kinaci na bakin naki na komawa ciki but you're expecting me to eat this haba ai wannan abincin dabbobi ne kawai zasu iya ci ni kuma kinga mutunne ba dan kuikuyo ba" salati Goggo tayi ta rike baki tana kallonsa har zata d'auko muciya ta bi bayansa sai kuma ta fasa tace "lalle dannan wuyanka yayi kyauri ya isa yanka, wato nikake fadawa haka saboda ka mugun rainani wlh ba laifinka bane laifin uban kane daya aikoka kaci zarafina kuma na gode amma dan uwarka mai zakaci inba wannan din ba sai dai idan zaka dafa danwake inkuma ba haka ba sai dai fa ka kwana da yunwa".

  Hararanta yayi yace "cin abincin gidanki ko virus ni kinga tafiyata zanje naci indomie da kwai awajen mai shayi koba komai yafi wannan dattin tuwon da kika rage".

  Haushine ya kama Goggo kawai ta saka kuka tana cewa "oni yau naga yaro jarababbe aiko iyayenka zan sama duk sai naci mutuncin su".

  ♾♾♾

  Awani babban mall suka tsaya koda taga haka ba tace komai ba dan tasan suna da bukatan sayan kaya saboda haka itama ba tace kala ba ta fita suka shiga kantin vibration din wayanta ne yasa ta tsaya ganin mai kiran yasa tayi murmushi.

  "Hello darling brother my one and onl...." bai bari ta k'arasa ba  azuciye ya amsa da cewa "waye darling din naki kina matsayin kanwata gida daya muke kwana muke tashi but you cant check on me kullun banganinki da safe, da dare kuma kinyi barci shin me kike nufi me kike tunani kina koyawa yan uwanki eh?"

  Marairaicewa tayi kafin tace "Yaya plx am sowie yaukan zan jira kadawo cox i really missed you dear kayi hakuri zan kiyaye ba zan sake haka ba kaji"  ok kawai yace har zai kashe wayan sai kuma ya sake cewa "kar ki kuskura ki kai 6 awaje baki dawo gida ba" kafin ma ta amsa ya kashe ta6e baki ta ajiye wayan ta shiga ta iske harsun gama jakarta ta fitar ta cire makudan kudi ta mika musu sannan tace "gashi idan ya rage sai ku raba chanjin.

  Zaune yake a farfajiyar gidansa yana shan iska Hajiya ta shigo rike da tray babba "barka da hutawa baban Raihana" murmushi yayi kafin yace "yawwa barka dai uwar 'ya'yana wani beta kika had'omin tun dazu kamshi ke tashi? Alhaji kenan baka rabo da zolaya.

  "Ammi me kika dafa mana" Zahra data dawo daga makaranta kenan ta hangosu a gurin shan iska shine ta nufi gurin dan ta gaishesu hannu ta mika zata bude flask din cikin zolaya Hajiya ta buge hannunta tana cewa "ban sani ba yar nema kije dinning naku yana chan "haba Ammi ni gaskya da Abbu zanci koh Abbuna? ya amsa mata da eh yana murmushi.

  Ammi tace "haba dan Allah wallahi kai kake shagwaba su da yawa saboda meye ba zataje gurin yan uwanta ba?.

  "Yawwa ai naji dadin haka gwanda data zauna kinga Ammi shikenan sai in had'a da nata da nawa duk saina cinye" Raihan ya fad'a dan neman tsokala.

  Ammi tace "gaskiya kam gwanda kayi hakan" aiko tanajin haka ta ta6e baki tayi kitchen aguje shima yabi bayanta yana dariya rufe kofan yayi tayi ta ihun ya budeta amma yaki Ammi kam bata kulasu ba ta mijinta takeyi shi kuma Abbu bai kula ba sai da yazo shiga shine ya bude daya ganta yayi dariya kad'an yana bata hakuri dan yasan Zahra akwai daru.

  "Hello kana inane kazo yanzu? a dayan bangaren Sulaiman yace "yanzu na ajiye su daddy agida "ok na baka nanda mintina talatin karka kuskura ka wuce hakan kasameni a gidan Anty Raihana" tsaki yaji kasa kasa kafin yace "ok toh angama saina zo" tsaki tayi tace "karma kazo nidai na baka minti talatin.

  Anty Raihana data tsura mata ido tace "kedai baki rabo da masifa toh Allah kyauta miki" dariya tayi tace "amen Anti ni kinsan bana son bata time" Anty Raihana tace "wai kwata kwata minti nawa kika min daza kice nanda minti talatin" dariya tayi sannan tace "ahaba Anty wallahi na kai awa biyu kuma kinsan yau inason inga yan gida musanman yaya Raihan saboda 3wk kenan ban ganshi ba har gwara Zahra muna ganin juna a school su Yazid kam na manta when last muka had'u shiyasa zan koma da wuri Anty tace "lalle ma yarinyannan wai wato kinfi karfin kije gaida Raihan ne kafim ki fita school ko kuma what d reason behind this you ur stupidity? ta6e baki tayi tace "kai dan Allah Anty ni banda tym ne shiyasa.

  D̥ͦI̥ͦD̥ͦE̥ͦE̥ͦY̥ͦL̥ͦO̥ͦV̥ͦ T̥ͦḀͦK̥ͦU̥ͦC̥ͦE̥ͦ

  Lιĸe, coммenт and share

  Sannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa aj e вa.✍

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Ma'aurata: Babi na Bakwai

  Posted 6 hours ago

  Ku latsa nan don karanta babi na shida. Bayan wata d'aya Soyayyar Maryama ta hana Habib sakat, duk yanda yaso ya ya k'ince ta ya kasa hakan yasa ya yanke shawarar tunkarar ta zuwan sa uku gidan da k'yar ya samu ya shawo kanta ta amince da soyayyarsa Iya tafi kowa ...

 • Akwai Illah: Babi na Hudu

  Posted Thu at 10:06 AM

  Ku latsa nan don karanta babi na uku. 10 Junairu 2017 10:00am Maiduguri Borno State Wayarsa ya zaro daga aljihunsa tun da ta fito daga gida. Ta madubin motarsa ya ke kallonta duk da hankalinsa na kan abunda yake dannawa a wayarsa. Kafin ta iso ya sak'ala wayar a alji...

 • Waye Zaɓin Munibat? Babi na Hudu

  Posted Mar 22

  Ku latsa nan don karanta babi na uku. Bismllahir Rahmanir Rahim Ban sake sanin inda kai na yake ba sai farkawa nayi, naga Anty da sauran mak'otan mu sai sannu ake min, ni dai ido kawai nake rabawa ina k'ok'arin tuno abunda ya faru, da sauri na koma cikin d'aki ina dub...

 • Matsalolin da waya ke kawowa cikin zamantakewar ma’aurata da hanyoyin warware su

  Posted Mar 22

  A wannan zamanin da muke ciki na yawaitar wayoyin hannu kirar smartphone ya kawo sauyi babba a cikin zamantakewar iyali. Duk da cewa tana da matukar amfani musamman duba da irin zamanin da mu ke ciki, sai dai a bangare guda kuma illolin da wayar ke haifarwa a zamantakew...

 • Darasin Physics: Bayanin banbanci da ke tsakanin mass and weight, dimension, position, distance da displacement

  Posted Mar 22

  Darasinmu na yau zai kawo mana bayani ne game da wasu muhimman abubuwa a physics wanda sanin su na daga cikin ginshikin fahimtar karatun physics. Wadannan abubuwa kuwa sune mass and weight, da dimension da position, da distance da kuma displacement. Ku biyo ni ga bayana...

 • Duhun Damina: Babi na Daya

  Posted Mar 11

  بسم الله الرحمن الرحيم اسلام عليكم و رحمة الله تعالى وبركاته Sharhi Wannan littafi nawa ƙiƙirarre ne, kashi ashirin cikin ɗari, ko ma in ce bai kai ba shine gaskiya, kuma akansa na ƙirƙiri labarina. Mas'alar da na ɗauko a yau mas'ala ce mai girma, hakan yasa na ƙirƙ...

View All