Makalu

Featured Create an Ad

Ya Faru Akan Kai Na: Babi na Daya

 • Kasancewar yana yin yana yin damuna, hakan yasa kasuwar cika maqel da mutane, kallo d'aya zakama kowa awajen kasan Allah Allah yake yayi yasai duk abin dazai siya yabar kasuwar, musamman idan kayi duba da yanda hadari ya hararo wanda shima kallo d'aya zaka mai kasan k'iris yake jira ya sauko da ruwa..

  HAIRANAH tana d'aya daga cikin mutanan dake siye siye acikin kasuwar, sai siyan abubuwa take sauri-sauri gudu-gudu tana Allah Allah tagama siyan komai akan lokaci kan saukowan ruwan, dan tasan idan tagama siyan komai koda ruwan yasauko bata da matsala Dan tana d'auke da y'ar lemanta

  Lokacin data gama siye siye hakan yayi daidai da shigowar HEESHAM cikin kasuwa.....
  Kyakkyawan saurayi ne wanda ya had'u tako ta'ina, ya had'u irin sosai d'innan, fari ne tas irin wannan farin me tafe da cikakkiyar lafiya, me kyau ne na qarshe irin tsaftataccen kyau d'in nan me tsayawa arai, shekarunsa bazasu wacce Ashirin da huɗu ba, yana da jiki irin wannan jikin da ake kira da samun irinka sai an tona, ma'ana shidai baza'a kirasa dame jiki ba, sannan baza'a saka shi a sawun y'amushashshu ba sirara, yana dai tsaka tsaka, tsayinsa yayi daidai dana samari irin SAMARIN NANAH, kallo d'aya me hankali zaimai yasan yana da wayo sosai me tafe da karfin basira tare da wadatar ilimi zallah, dama tunaninka zai baka koda ace rainan nan qasar ne ba shakka yana samun kulawa sosai arayuwarsa, musamman idan kayi duba da tarin hutun dake tare da fatarsa..

  Waige waige yake yi yana duba direbansu, daga kawai bara ya sai abu saiya shanyasu a mota kamar wasu kayan wanki...

  Shaaaaa ruwan sama ya b'arke kamar da bakin kwarya, nan take mutane kowa ya fara shigewa shagunan mutanen kasuwan dan gudun kada ruwan yadakesu..
  Arayuwar HAIRANAH tana San taga ana ruwa tana tafiya acikinsa da lema akanta, Dan haka nan take ta bud'e lemarta cikin murmushi dan haka kawai taji wani dad'i aranta, tasan hakan baya rasa nasaba da yanda tagama siyayyarta.

  Saidai me iska ce me qarfi ta figi lemar tata tayi gaba can da nisa zuwa wajen HEESHAM dake kici kicin gudu dan kar ruwan ya jiqasa shaqaf, ai nan take yaga lema gabansa, ya fara waigen daga inda tafito, shi dai anasa iya waigen baiga me ita ba, Dan haka ya d'auka da murna, baibar wajen ba dan yasan akwai me lemar anan kusa dashi..
  Aiko kamar ya sani Dan karyowar kwanan HAIRANAH kenan ta hangi lemarta a hannunsa ya tare ruwan abinsa tare da kallan shagunan mutane yana Allah Allah yaga direban nasu ya jasa sutafi, dan yasan Shehu bashi da sauri akan komai na rayuwa.....

  HAIRANAH takai hannunta daniyar kwace lemarta saidai hannun nata na tab'a na HEESHAM tayi saurin janyewa, sakamakwan wani shock da yayi ram da hannayen nasu, nan take HEESHAM ya zuba mata ido, ZUCiYARSA na bugawa kamar yanda tata take bugawa, tunda suke basu tab'a jin irin wannan shock haka ajikinsu dan sun tab'a wani ba... Wannan wata alamace tada'akwai wata alaƙa me girma a tsakaninsu..

  HEESHAM ya galla mata harara yace, "malama ya zakizo da hannunki me kama da wayar lantarki ki tab'ani.
  HAIRANAH itama ta gallamai harara tace, "ban gane ba, kana nufin haka kawai zanzo na kama hannunka dan rashin tarbiya, kawai nazo kwatar lemata ce arashin sani hannuna ya gogi naka, maza kabani lemata in qara gaba dan ina da abin yi.....

  "Da gaske... HEESHAM ya katseta da fad'in hakan tare da wurga mata wani shegen kallo, kana yaci gaba da cewa, lemarki ko lemata, ta ina wannan lemar tazama taki, kinga malama qara gaba tunkan na yanke miki.

  Jin hakan yasa ran HAIRANAH b'aci, nan take tasa hannu ta riqe lemarta qam tana cewa, " wallahi saika bani lemata tunda ba taka bace, wallahi saika bani kayata, takai qarshen zancen kamar zatayi kuka, dama ita bata raina abin kuka, tana matuƙar san lemarta over, dan agidansu ba wanda yake tab'a mata abinta dan kowa ya tab'a sai sunyi rikici, dan takanas ta kano abokin yayanta SABIR dayaje kwatono ya siyo mata dan sanin qaunar da takema lema...

  HEESHAM yana ganin hakan ya kyalkyale da dariya, dan shi a rayuwarsa ba abin da yake so kamar yaga manya suna kuka???? koya saka mutum magana abin yana masa dad'i matuƙa azuciya, dan haka shima qara qanqame lemar yayi yace, "bazan baki lemar nan ba, dan ina tafiya naganta tazo gareni, kinga ko Allah ne ya turomin ita, dan haka saidai kiyi kukanki ki share hawayenki dan baki kam bazan baki ba...

  HAIRANAH tagane yaran idansa qir yake, tayi imani idan batayi da gaske ba tafiyan mata da lema zaiyi, dan haka ajiye cefananta tayi a gefe tana jan lemar HEESHAM naja, nan fad'a ya kaure, jama'ar wajen sai kallansu suke cikin mamaki, masu magana nayi masu kallo nayi, gashi ruwa ake sosai yanda ruwan yake sauka a qasa haka ruwan yake sauna akansu, amma dan bala'i Sam d'aya yaqi barba d'aya wannan lema.

  Shidai HEESHAM dama neman rikici da fad'a aikinsa ne, dan haka yayunsa suke fama dashi a gida????..

  HAIRANAH bata San halinsa bane, dan haka dataga da gaske bazai bata lemarta ba dan kowa yayi masa magana cewa yake lemarsa ce qarya take masa ba tata bace, dan haka sai kawai tafashe mai da kuka wiwi..

  HEESHAM mai zaiyi imba dariya ba, ya dinga kyakyatawa, mutan wajen suka dinga mamakinsa gashi yaqi sakin lemar, wani tsoho daga cikin wani shago yace, "haba kai ko yaro, maizai hana bazaka bar mata lemar ba, tunda ta kafe lemarta ce, kuma kaji wasu sunce tatace, maizai hana ka bar mata aiko takan ce ka bar mata tunda kaga ita mace ce..

  HEESHAM yaci gaba da dariyarsa yana d'agama tsowan hannu alamar yaji, Sannan yaci gaba da kallan bakinta da yanda take kukun, wallahi tunda yake tsokanar yayunsa bai tab'a jin nishad'i irin na yau ba, shiya d'auka ƴan uwansa ne kawai zasu mai kuka idan ya tsokane su, amma itama kalleta sai wani kuka take mai, kallanta yake dakyau yana auna shekarunta, ba shakka sa'arsace, dan bazata girme masa ba, Saidai su zama sa'annin juna....????

  HAIRANAH ko kuka take tsakaninta da Allah, can dayaji d'an tausayinta saiya tsaida dariyar da yakeyi tare da d'an sakar mata lemar amma ba dukka ba, idansu cikin na juna yace da ita, "Zan sakar miki lemar dan ganin damana, amma saikin gaya min sunanki..

  HAIRANAH ta gallamai harara cikin takaicinsa tace, "Bazan gaya ba, murmushin daya qara masa kyau yayi tare da d'an qanqame lemar cikin zaro ido yace, "Tunda bazaki fad'a ba, bara namiki me gabaki d'aya, ya kai qarshen zancen dasan funcike lemar DAGA hannunta...

  Ganin hakan da HAIRANAH tayi, aiba shiri tayi saurin cewa "Sunana HAIRANAH????..

  Murmushin dai ya qarayi, tare da sakar mata lemar yana cewa, "Sunanki dadad'i HAIRANAH, yana fad'in hakan ya juya yabar wajen tabishi da kallan harara, kana ta d'auki cefananta da kallan mutanan wajen tajuya itama tabi tata hanyar...

  HEESHAM da murmushi akan fuskarsa ya bud'e motarsu ya shiga, Shehu direba ya kallesa yace dawowata kenan nake tambayar yallab'al INA kake yace min ka shiga ciki nemana.

  Kallan Yayansa AHMAD HEESHAM yayi Wanda yake karanta jarida kana ya maida kallan nasa kan Shehu direban Wanda ayanzu yaja motar ya Bashi amsa da, "ina cikin nemanka na had'u da wata Yarinya futunanniya...

  Da sauri yayansa AHMAD yace, "Dama akwai wanda zai kaika futuna HEESHAM...

  Cikin jin kunyar yayan nasa HEESHAM ya sunkuyar da kansa bai qara cewa komai ba, Shehu direba murmushi kawai yayi, dan shima yasan futunar HEESHAM daqer asamu Wanda yafishi.

  Latsa nan don karanta babi na biyu....

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Ma'aurata: Babi na Bakwai

  Posted 5 hours ago

  Ku latsa nan don karanta babi na shida. Bayan wata d'aya Soyayyar Maryama ta hana Habib sakat, duk yanda yaso ya ya k'ince ta ya kasa hakan yasa ya yanke shawarar tunkarar ta zuwan sa uku gidan da k'yar ya samu ya shawo kanta ta amince da soyayyarsa Iya tafi kowa ...

 • Akwai Illah: Babi na Hudu

  Posted Thu at 10:06 AM

  Ku latsa nan don karanta babi na uku. 10 Junairu 2017 10:00am Maiduguri Borno State Wayarsa ya zaro daga aljihunsa tun da ta fito daga gida. Ta madubin motarsa ya ke kallonta duk da hankalinsa na kan abunda yake dannawa a wayarsa. Kafin ta iso ya sak'ala wayar a alji...

 • Waye Zaɓin Munibat? Babi na Hudu

  Posted Mar 22

  Ku latsa nan don karanta babi na uku. Bismllahir Rahmanir Rahim Ban sake sanin inda kai na yake ba sai farkawa nayi, naga Anty da sauran mak'otan mu sai sannu ake min, ni dai ido kawai nake rabawa ina k'ok'arin tuno abunda ya faru, da sauri na koma cikin d'aki ina dub...

 • Matsalolin da waya ke kawowa cikin zamantakewar ma’aurata da hanyoyin warware su

  Posted Mar 22

  A wannan zamanin da muke ciki na yawaitar wayoyin hannu kirar smartphone ya kawo sauyi babba a cikin zamantakewar iyali. Duk da cewa tana da matukar amfani musamman duba da irin zamanin da mu ke ciki, sai dai a bangare guda kuma illolin da wayar ke haifarwa a zamantakew...

 • Darasin Physics: Bayanin banbanci da ke tsakanin mass and weight, dimension, position, distance da displacement

  Posted Mar 22

  Darasinmu na yau zai kawo mana bayani ne game da wasu muhimman abubuwa a physics wanda sanin su na daga cikin ginshikin fahimtar karatun physics. Wadannan abubuwa kuwa sune mass and weight, da dimension da position, da distance da kuma displacement. Ku biyo ni ga bayana...

 • Duhun Damina: Babi na Daya

  Posted Mar 11

  بسم الله الرحمن الرحيم اسلام عليكم و رحمة الله تعالى وبركاته Sharhi Wannan littafi nawa ƙiƙirarre ne, kashi ashirin cikin ɗari, ko ma in ce bai kai ba shine gaskiya, kuma akansa na ƙirƙiri labarina. Mas'alar da na ɗauko a yau mas'ala ce mai girma, hakan yasa na ƙirƙ...

View All