Makalu

Featured Create an Ad

Ya Faru Akan Kai Na: Babi na Biyu

 • HAIRANAH ko tafiya take tana tuna HEESHAM, ita tunda take bata tab'a ganin mutum irinsa ba, ya ita da lemarta ya wani ce tasace, murmushi tayi kawai, irin yana da futuna matuƙa.

  Saidai mezai faru????.. Tana karyo kwanar layinsu taci karo da wani mutum.... Nan goshinsu ya haɗu yabada wani sauti guf, dajin zafi sosai mutumin yaja baya yana me dafe goshin nasa da cewa "sorry, Sannan ya durƙusa yabi cefanan nata dan kwashe mata kasancewar tunda sukaci karo suka sub'uce ahannunta suka zube.

  Itama hannunta dafe da goshin nata ta durƙusa tana tayasa kwashewa.

  Nan suka kalli junansu ai atare zuciyarsu tabuga kamar yanda kukasan ana buga ganga.

  Nan HAIRANAH taja wani numfashi tare da saurin tashi ganin ya gama kwashe mata cefanan...

  Ahankali cikin nutsuwa ya tashi shima da kallanta ya miƙa mata cefanan yana me qarema kayan jikinta kallo tare murmushi yace, "kiyi hakuri ƙanwata, bansan kin tawo ba daban shigo da sauri ba..

  Jiki a sanyaye HAIRANAH ta karb'i cefanan nata zuciyarta bata dena bugawa ba, batace mishi komai ba taratsa ta gefensa ta wuccesa tana me juyowa tana kallansa, ahaka ahaka har ta isa gidansu.. Namma kafin ta shiga sanda ta juyo ta kallesa dakyau, yana nan tsaye inda ta barsa yana kallanta, sanda tagama ƙaremai kallo tsaf kana ta juya ta shige gidan nasu..

  Da mamakinta shiko ya ɗauke idansa daga ƙofar gidan nasu, tare daci gaba da kallan Layin nasu daga sama har ƙasa, kana dai gani kasan wani abu yake nema, candai ya tsaida idan nasa akan wani gida, ganin da yayi kamar ana ƙoƙarin fitowa daga gidan ne yasashi saurin buɗe wata black motarsa me masifar kyau ya shige cikinta...

  Yana kallo wasu maza biyu ne suka fitto daga cikin gidan daga ciki kuma yaga an kulle gidan, har mazan suka tafi idansa nakan gidan, haka a ƙalla ya b'ata sama da awa uku yana cikin motar tasa hankalinsa nakan wannan gida amma baiga wani ya qara fitowa ba, dan dole badan yaso ba haka ya kunna motar tasa yabar Layin...

  HAIRANAH ko tana shiga gidan nasu taga Yayarta NUWAIRA tana karatun littafin hausa, bayan ta ajiye cefanan zama tayi a kusa da NUWAIRA ɗin kasancewar zuwa Lokacin anɗauke ruwan saman..

  Haka ta zabga uban tagumi tana mamakin zuciyarta, gabanta na tsananta faɗuwa yayin da hankakinta yayi mummunan tashi, sakamakwan gane karatun zuciyar tata da tayi...

  Nan take hawaye ya zubo mata cikin tashin hankali tadafe ƙirjinta jin wani yanayi daya farayi mata.

  Ta fahimci rikicinta da HEESHAM da sukayi a kasuwa *WASA NE*

  Cin karo da tayi da wannan mutumi rashin sani ne,

  Kallansa da tsayawa da tayi jin kalamansa na bata haƙarin da yayi *GANGANCI NE*
  Dan gashi yana san zame mata masifa a rayuwa..

  Zuciyarta ba abin da ayanzu take hasko mata sai fuskarsa da murmushinsa, haka kawai taji tana sanshi tana ƙaunarsa tana san qara ganin fuskarsa tana san ta qara jin muryarsa..

  Hawaye ya qara zubo mata...

  Daidai lokacin NUWAIRA tadafa kafaɗarta batare data kalleta ba bare tasan Awane yanayi take, cikin sanyayyiyar muryarta tace da ita, "Hmmm, labarin nan yana ban takaici, gaskiya marubuciyar nan banza ce, waifa yarinyar wuccewa kawai tazoyi, sai ta haɗu da saurayin shikenan tafara sanshi da ƙaunarsa, yanzu gashi tazo gida wai tarasa sukuninta tana san zama kamar wata zararriya, kiji ƙarya fah..

  Gaskiya marubutan nan suna raina mana hankali, nifa bazan tab'a yarda mace tana fad'awa soyayya me zafi haka ba, Sannan a lissafi irin nawa rashin hankali ne mace me mutunci da daraja taje tacema namiji tana sanshi.. Tana kawowa nan azancenta, taja tsaki daci gaba da cewa, ba wata Soyayyar dazan bari tayi tasiri cikin zuciyata har na barta ta haifarmin da wani tunani bare tasani shiga cikin wani hali halin dazai kaina ga fad'awa tashin hankali..

  Kigafa wannan, daga kawai ganin mutum akan hanya sai tawani faɗa cikin Soyayyarsa, saboda tsabagen shashanci da toshewar basira da kuma ɗorama kai damuwa......

  Hawayene ya qara zuboba HAIRANAH, cikin wani hali tace, "Aunty Ba kawai bane, ba shashanci bane, ba kuma toshewar basira bane, ba ɗorama kai damuwa, wallahi ƙaddarace, wallahi *YA FARU AKAN KAINA* yanzu yanzun nan..

  Yanzu naganshi, Yanzu na sanshi, yanzu yayi min magana, kuma yanzu na fara sanshi, kuma san nashin qara shigata yake, bin jinina yake, ina jin shigarsa kamar yanda kika san yanda mutum yake shan ruwa, kamar yanda kike fad'a yanzu, Nima yana san hanali sukuni, wallahi nidai ina sanshi.....????????????

  Ahankali NUWAIRA ta sauke hannunta daga kafaɗarta, tare da zuba mata ido cikin mamakinta tace, "HAIRANAH? ???? me kike cewa ne, kina magana nefa akan kin fad'a Soyayyar wani mutumin dabaki sanshi ba yanzu..

  Cikin nuna mata tabbaci HAIRANAH ta goge hawayenta da bayan hannunta tace, "kwarai Aunty, ina sanshi kuma saina Auresa, zanje nayi sallah yanzu naroki Allah kan lamarin, idan nasamu nutsuwar zuciyata, sai naje na gaya masa tunkan mama tadawo taganni cikin wannan halin, kuma dan Allah wannan yazama magana tace nidake, bana san mama tasani dan Allah, HAIRANAH na faɗin hakan tatashi da barin tsakar gidan tayi cikin falansu zuwa shashinsu dan aiwatar da abin datace....

  NUWAIRA tabita da kallo cikin matuƙar razana, dan hankalinta baqamin tashi yayi ba, dan haka itama tashi tayi tabi bayanta dan ta magance matsalar yanzu yanzu tunkan abin yayi nisa...

  Aiko NUWAIRAN na zuwa bedroom nasun taga HAIRANAN har tashiga toilet, zama tayi gefan gado tana jiran fitowarta cikin mamakinta.

  Aiko HAIRANAH na fitowa NUWAIRA tatashi tasha gabanta tana cewa, "Amma baki da hankali, ban tab'a sanin ke wawiya bace sai yau, ya za'ayi daga ganin mutum kiji kina sanshi har kina maganar zakije ki gaya masa kina sanshi, anya kina cikin hankalinki kuwa, anya kinsan abin da kike cewa kuwa..
  Cikin jin haushinta HAIRANAH tace, "Toh aunty ni nayi kaina dazaki sha gabana kina tuhumata, Allah ne fa yayini yayiki yayi wanda ya had'ani dashi yanzu, lefine danna tsinci kaina cikin wannan halin bayan kinsan banice da zuciyata ba.

  Allah ne fa da komai namu, Aunty ina iliminki yake, ina tunaninki yake, wallahi kamar saukar ruwan sama haka naki sanshi da ƙaunarsa ya mamaye zuciyata, idan bazakiji tausayi na ba kuma zaki gaya min magana me dad'i ba, dan Allah Aunty na rokeki Karki qara tarata da wannan zancen dan zanji tsanarki da gaske cikin zuciyata. Takai k'arshen zancen da had'e hannuwanta biyu alamar rok'o????????

  NUWAIRA tacije bakinta dan taji zafin kalamanta tace, "Haka kikace.

  HAIRANAH ta sauke hannayenta da ratsawa ta gefanta tana cewa, "Aunty ai nace, Saidai kuma gaba..

  NUWAIRA najin hakan taficce daga bedroom d'in taje tasakama kofar falan nasu key, tayi bedroom d'in Mamansu takwanta tana cewa "zanga ta'inda zaki fitta kije wajen nasa ki gaya masa kina sanshi wawiya kawai..

  Sallar azahar HAIRANAH ta gabatar, kana tahau rokwan Allah kan idan san wannan bawa nashi alkairi ne a gareta yasa tasamesa cikin sauqi, ya shiga cikin lamarin ya daidaita al'amuran.

  Idanko sanshi ba alkairi bane a gareta ya cire mata sanshi kadda ya barta dashi ko miskala zarratan..

  Tana shafa addu'arta tafad'a tunaninsa.

  Baqi ne shi irin kyakkyawan baqin nan wanda ake kira da black beauty, yana da hanci zir me kyan fasali, fuskarsa doguwa ce ga d'an sajensa mekyau, yana da ido Masu kyau na d'aukar hankali, jikinsa ko irin jikin nan ne irin na k'arfafan mazaje, ma'ana lafiyayyu Masu ji da kansu, shidai yana da jiki amma bacanja ba, dan jikin nasa bame muni bane, kallo d'aya zaka mai kasan yana da ilimin boko...

  HAIRANAH na kawowa nan a tunanin nata ta lumshe idanta, wallahi ita dai tana sanshi, kuma koyana so ko baya so saiya Aure ta!!!.????

  Tana gama gayama zuciyar tata haka tatashi taje zata bud'e kofar falan nasu tajita a rufe, tasan NUWAIRA ce ta kulle dan karta fitta, hmm, yau bata jin futuna dan haka sai kawai ta koma bedroom d'insu ta haye gado, har a Lokacin hawaye bai dena zuba mata ba, cikin lokaci k'ank'ani ko bacci yayi awan gaba da ita...

  NUWAIRA tadawo bedroom d'in nasu ta qarema HAIRANAN kallo taja tsaki, tace "wallahi indai ina tare dake bake ba zuwa wajen wani katan garde kice kina sanshi shashasha kawai..

  Tana faɗin hakan ta juya dan bud'e ƙofar falan nasu dan jin kamar mamansu tadawo,

  *Auntyn luv tace um um NUWAIRA ƙaddara tana kan kowa fah, kuma batu na luv ba'a cikamai baki inji XEE qawa ga SAILUBAH a samarin bana????*

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Ma'aurata: Babi na Bakwai

  Posted 5 hours ago

  Ku latsa nan don karanta babi na shida. Bayan wata d'aya Soyayyar Maryama ta hana Habib sakat, duk yanda yaso ya ya k'ince ta ya kasa hakan yasa ya yanke shawarar tunkarar ta zuwan sa uku gidan da k'yar ya samu ya shawo kanta ta amince da soyayyarsa Iya tafi kowa ...

 • Akwai Illah: Babi na Hudu

  Posted Thu at 10:06 AM

  Ku latsa nan don karanta babi na uku. 10 Junairu 2017 10:00am Maiduguri Borno State Wayarsa ya zaro daga aljihunsa tun da ta fito daga gida. Ta madubin motarsa ya ke kallonta duk da hankalinsa na kan abunda yake dannawa a wayarsa. Kafin ta iso ya sak'ala wayar a alji...

 • Waye Zaɓin Munibat? Babi na Hudu

  Posted Mar 22

  Ku latsa nan don karanta babi na uku. Bismllahir Rahmanir Rahim Ban sake sanin inda kai na yake ba sai farkawa nayi, naga Anty da sauran mak'otan mu sai sannu ake min, ni dai ido kawai nake rabawa ina k'ok'arin tuno abunda ya faru, da sauri na koma cikin d'aki ina dub...

 • Matsalolin da waya ke kawowa cikin zamantakewar ma’aurata da hanyoyin warware su

  Posted Mar 22

  A wannan zamanin da muke ciki na yawaitar wayoyin hannu kirar smartphone ya kawo sauyi babba a cikin zamantakewar iyali. Duk da cewa tana da matukar amfani musamman duba da irin zamanin da mu ke ciki, sai dai a bangare guda kuma illolin da wayar ke haifarwa a zamantakew...

 • Darasin Physics: Bayanin banbanci da ke tsakanin mass and weight, dimension, position, distance da displacement

  Posted Mar 22

  Darasinmu na yau zai kawo mana bayani ne game da wasu muhimman abubuwa a physics wanda sanin su na daga cikin ginshikin fahimtar karatun physics. Wadannan abubuwa kuwa sune mass and weight, da dimension da position, da distance da kuma displacement. Ku biyo ni ga bayana...

 • Duhun Damina: Babi na Daya

  Posted Mar 11

  بسم الله الرحمن الرحيم اسلام عليكم و رحمة الله تعالى وبركاته Sharhi Wannan littafi nawa ƙiƙirarre ne, kashi ashirin cikin ɗari, ko ma in ce bai kai ba shine gaskiya, kuma akansa na ƙirƙiri labarina. Mas'alar da na ɗauko a yau mas'ala ce mai girma, hakan yasa na ƙirƙ...

View All