Recent Entries

 • Tsiya Da Wasali: Shafi Na Goma

  March/1993 "Hameedu ka ga fa bishiyar da ya ce mu tumɓuketa har jijiyarta wai a ƙarƙashinta aka ce masa maganin yake." "Ni fa Bawa ba tumɓukewar ba ce damuwata, wai baka ji duka aikin fam Ashirin zai ba mu ba, waye zai masa aikin a haka idan ba mu da yake ganin ya raina ba? Haba shi talaka kul...
 • Tsiya Da Wasali : Shafi Na Tara

  Awanni uku cur! Suka shuɗe yana duƙe kansa a ƙasa ya tsurawa tarin garwashin wutan da aka samar da shi ta hanyar tsafi a cikin wani kasko ido. Tun yana hawaye da zufa na azabar raɗaɗin wutar har sai da kansa ya juye ya tafi luu zai afka cikin kaskon, a sannan ne mummunan Dattijon da ke zaune daga ...
  comments
 • Tsiya Da Wasali: Shafi Na Takwas

  "Kana ji waccar yarinyar da kuke tare ya kuke da ita ne?" Huzaif ya yi wani ɓoyayyen murmushi yana sanya hannu ya sosa ƙeyarsa cike da kunya. "Abba Ɗaliba ta ce..." "Au to to to." Abba ya furta yana ɗaga hannu ya zare hular kansa ya ajeta saman mota. "Ka daɗe kana fatar ganina cikin farin cikin...
 • Tsiya Da Wasali: Shafi Na Bakwai

  ***** Hankali tashe yake duban likitan yana duban jibgegen baƙin basamuden dake gefensa yana sharce gumi da gabjejen bayan hannunsa. Hannunsa ya dunƙule ya naushi bangon da ke gabansa a karo na biyar sai kuma ya cije baki yana yarfe hannun. Da sauri ƙaton mutumin ya matso kusa da shi zai riƙe shi...
 • Tsiya Da Wasali: Shafi Na Shida

  Ta fi ƙarfin minti goma tana sake karanta saƙon tamkar karatun Mauludi, sai take ganin kamar ba da hannunsa ya rubuta ba ko kuma ba ita zai turowa ba, sai dai fa daga Sururun Qalbyn naki da ya saka ta tabbata shi ne, haka saƙo nata ne ita kaɗai babu wata ma a zuciyarsa sai ita kaɗai ɗin! Wata dariya...
  comments
 • Tsiya Da Wasali: Shafi Na Biyar

  ****** Can cikin barcinta a tsakar kanta take jin muryar Iya nata bambanin faɗa tana kiran sunanta. Firgigit ta yi ta tashi zaune tana ambaton Allah. Sai dai tamkar wacce aka ɗorawa buhun siminti haka ta ji kanta ya mata nauyi, ta lumshe idanuwanta da suka kaɗa jajur ta buɗe su a cikin na Iya da ke...
 • Tsiya Da Wasali: Shafi Na Hudu

  *** A karo na uku ya ƙara duba agogon hannunsa yana jan tsaki cikin zuciyarsa. Tattara takardun gabansa ya yi gefe, ya miƙe ya doshi bishiyar da yasan tana zama ita da abokan karatunta. Tun daga nesa ya san bata cikinsu dan haka yaja ya tsaya kansa na daɗa zafi. _To wai ta zo makarantar ɓoye masa t...
 • Tsiya Da Wasali: Shafi Na Uku

  *KANO 2018.* Idan har wannan duhun shi ne duhun kabarin da ya ji ana bada labarinsa a can wata duniya da ya gaza tuna ko da sunanta, to tabbas zai dawwama yana kiran a maido shi cikin duniyarsa shi kuma zai tafi ga wani tudu ko da na saman dutse ne ya yi ɗaki a bisansa ya shiga ya fara bautawa ma...
 • Tsiya Da Wasali: Shafi Na Biyu

  *1995* Ta waiga hagu da damarta, ta kasa kunne na 'yan daƙiƙu ba ta ji motsin kome ba sai na ruwan da ke wucewa ta rariya, ta hanga ga ƙofar gidan da ke garƙame da Kwaɗo ta waje, ta maka mata harara ta murguɗa baki, sai kuma ta daka tsalle ta kama 'yar katangar da ke gabanta, kamar kyanwa haka ta...
  comments
 • Tsiya Da Wasali: Shafi Na Farko

  ƘAUYEN TANƊAU 1997 Cikin talatainin daren mai gauraye da hadari baƙi ƙirin take ta ratsa gonaki da kwazazzabai zuciyarta a bushe babu alamar tsoro ko kaɗan, sai ma idan ta ci karo da marmara ta sa ƙafa ta dake ta da ƙarfi kamar ita ke ƙara mata nisan tafiyar. Ba ta dakata ba har sai da ta isa...
 • Tsiya Da Wasali: Talla

  Shin wai ni yau bari na tambayeki. Shin wai Hameedu ƙafar Habu Maharbi ya cire ko kuwa ta Bawa? Shin wai Hameedu dukiyar Ladi ya cinye ko kuwa ta Bawa? Shin shi Bawan me yake zame miki ne banda miji? Shin akwai wani jini guda ko da na halittar kaza ne da kika dasa a tsakaninki da Bawan? Kai! Ko kuw...