Makalu

Blogs » Kagaggun Labarai » TSIYA DA WASALI: SHAFI NA FARKO

TSIYA DA WASALI: SHAFI NA FARKO • ƘAUYEN TANƊAU 1997


  Cikin talatainin daren mai gauraye da hadari baƙi ƙirin take ta ratsa gonaki da kwazazzabai zuciyarta a bushe babu alamar tsoro ko kaɗan, sai ma idan ta ci karo da marmara ta sa ƙafa ta dake ta da ƙarfi kamar ita ke ƙara mata nisan tafiyar. Ba ta dakata ba har sai da ta isa bakin wasu bishiyoyi biyu da suka zama kamar ƙofa ga maƙabartar.
  Ta tsaya ƙyam! Tana ƙarewa cikin maƙabartar kallo, ta ɗaga kanta sama taga yadda baƙin hadarin ya lulluɓe hasken farin watan da ya haska doron duniyar, ta sauke idonta a hankali tana maida dubanta hagu da damarta, babu alamar wata halitta irinta a ilahirin gurin. Ta ƙarasa gefen bishiyar ta sunkuya cikin wasu tarin ciyayi da karare ta kama lalube a cikin baƙin duhun har sai da ta ji ta cafko ƙarfen Fitilar kwai, ta jawota ta aje gabanta, ta karkace gefen zaninta ta zaro Ashana ta ƙyasta cikin fitilar. A take haske ya gauraye ilahirin gurin. Ta miƙe ta ƙara dosar gefen ɗayar bishiyar ta kama lalube, ba daɗewa ta zaro magirbi da wani ƙaramin shebur. Ta riƙe su a hannunta ta doshi cikin maƙabartar bayan ta tsallake wani gulbi da damina ta kawo shi, wani Kwaɗo mai raban shan bugu ya yi tsalle ya maƙale mata ƙafa, ta haske shi da fitilarta tasa hannu ta wafce shi ya shilla can wani yankin, ta ji kukansa da na sauran 'yan uwansa da ke cikin gulbin da ta tsallake, ta yi kamar ta juya, wasu shuɗaɗɗun zantuka suka wuce kamar iska cikin kunnuwanta.
  _"Har ki je ki dawo kar ki juya, idan kika juya kar ki yi kuka da ni, ki yi da kanki, na gama taimakonki Zawwa! Na gaji!!_"
  Ta ɗaga ƙafa da hanzari tana dosar sashin da ta tabbatar nan ake binne sabbin matattu. A cikin hancinta take zuƙo ƙamshin nasarar dukkan burinta. Wasu sasakun zantukan suka ƙara wucewa cikin zurmin kunnenta.
  _"Idan har kina so ki haifi ɗiya Mace, sai kin yanko hantsar Mace mai tsohon ciki da gashin kanta, da shi za a yi miki siddabarun da za ki haifeta. Idan har kina son Bawa ya warke, sai an yi masa wanka da ruwan farko da aka wanke wannan jaririyar, a take zai warke, sai dai ki sani wanda ya rasa ƙafa ya rasa kenan har abada tunda an riga da anyi kuskuren yankewa, zai dai warke da ga nannaɗewar da ya yi, zai kuma buɗe baki har ki ji ya ce miki _Ina ƙaunarki Zawwa!_. 'Yar da kika haifa ita ce za ta rama miki dukkan abinda kika rage, ita ce za ta juya miki Hameedu Siddiqu da dukkan Ahalinsa a tafin hannunta yadda kika kasa har kuwa zuwa kushewarsa. Dan haka ki je a daren yau ki haƙe kabarin da yake na farko daga ɓangaren hannun damarki, ki tone shi za ki tarda mace mai ciki a cike. Idan kika wuce yau, kin wuce burin rayuwarki kenan har abada ba ki ƙara samun wannan damar. Shekara biyun da muka yi muna jiran wannan ranar ta tashi a tutar banza da wofi, kar ki tsaya, ki tafi, ko da mahaifinki ne zai mutu a yau, kar ki tsaya, ki tafi!"_
  Kuwwar zancen ya cika kunnenta ta tsaya ƙyam gaban sabon kabarin tana sauke ajiyar zuciya tamkar ƙadangaren da ya haɗiyi kunama.
  A hankali ta ɗaga shebur ɗin ta fara yashe ƙasar kabarin zuciyarta cunkushe da mamakin ganin ba a gama rufe kabarin ba, akwai alamun ba a fi mintuna da gama binnewar ba. Ta ɗago tana sharce gumin da ta fara yi. Ta buɗe kunnuwanta tana sauraran gefe da gefenta, sai dai ba wani motsi. Ta yi baya da sauri sa'ilin da wani zazzafan tunani ya ɗarsu a ranta. Ta haska gefe da gefen kabarin, a karo na farko da wani abu mai kama da fargaba ya daki tsakiyar ƙirjinta ganin da ta yi babu sawayen waɗanda suka binne gawar! Ta ƙara haskawa sosai babu wata alamar da ke nuna an tako gurin. Ta aje fitilar a hankali a ƙasa lokacin da dukkan jikinta ya bata ba ita kaɗai ba ce a ilahirin maƙabartar. Ta riƙe ƙugunta tana shafa Wuƙar Iccen da ta suke a gurin. Ta ɗaga murya da ƙarfi ta ce, "Akwai mutum anan?" Shiru ya ratsa sai amsa kuwwar muryarta. Ta sake cewa "ko waye ya fito muyi sulhu!" Nan ma shiru sai ma kukan wasu firgitattun tsuntsaye da amsa kuwwar muryarta ya tashe su daga bishiyon da suke fake.
  Ta yi ajiyar zuciya ta ƙarasa ga kabarin ta ci gaba da yashewa da shebur har sai da ta fara hango farin likkafanin da aka rufe gawar da shi. A lokacin ne kuma mamaki na biyu ya shige ta ganin an haƙa kabarin ba yadda ake yi ba. Wannan rami kawai aka yi mai faɗi da tsayi aka tura gawar aka maida mata ƙasa aka rufe. Da hanzari ta jefar da shebur ɗin tasa hannu ta fara ture ƙasar da ita, a lokacin da hannunta ya kai jikin gawar ne abin ya faru, numfashi ta ji mai ƙarfi numfarfashi irin na baƙar wahala, ba ita gawar kaɗai ke numfashi ba hatta tsohon cikin jikinta motsawa yake yi, ta yi baya cikin kaɗuwa kiris ya rage ta juya wata dakakkiyar zuciyar ta tsayar da ita bayan ta harba mata jumlar _"idan kika wuce yau kin wuce burin rayuwarki kenan, har abada ba ki ƙara samun wannan damar har abada!_" Ta ƙara duƙawa da hanzari cikin ramin tana ci gaba da ture ƙasar numfarfashin na ƙara kusantar dodon kunnenta.
  Ta daɗe a wannan halin kafin ta gama gabaɗaya ta saka hannayenta biyu ta yaye likkafanin da ƙarfi ta jefar shi gefe. A lokacin ne ta yi tozali da ita, doguwar mace da bata gaza shekaru goma sha takwas ba, duk da jini ya cika fuskarta da gefen wuyanta da ke bulbular jini hakan bai hana ta ganin kyawun surarta mai matuƙar razanarwa ba cikin hasken fitilar kwan da ta dallareta da ita.
  Hannunta ta saka ta jawota da ƙyar daga cikin kabarin ta shimfiɗe ta gefe, ta tsaya a kanta tana ƙare mata kallo zuciyarta na daɗa tsinkewa.
  Alamar da ta gani na bakinta da ke motsi ya sakata duƙawa da sauri ta saka kunnenta a saitin bakin.
  "R-ru-ruuwa". Ta ɗago tana mai waigawa hagu da damarta, babu alamar ko kwantaccen ruwa balle ta ɗibar mata shi tasha. Ta kaɗa mata kai alamar babu, a zuciyarta tana jin tana ƙara ɓata lokaci ne, wannan matar dole mutuwa za ta yi, ta yanke abinda za ta yanka kawai ta kama gabanta. Da wannan shawarar ta karkace za ta zaro wuƙar ƙugunta, a karo na biyu matar ta ƙara buɗe baki tana kallonta cikin hasken fitilar kwan da ke tsakiyarsu. Ƙara kasa kunnenta ta yi bakinta tana saurararta.
  "Ki-kk--yn-fidda cik-cikin jikinaa."
  Auwal marra da ta yi wata mummunar razana ta yi baya tana ƙare mata kallo cikin taraddadin ko mutan ɓoye ke mata wasa da hankali.
  "Mutum ce ke?"
  Sai da ta yi tambayar ta gane bata buƙatar amsarta ga wacce ta yiwan.
  Gabanta ta ƙara komawa ganin tana ta ƙoƙarin ɗaga hannunta saitin cikinta. Ta tsurawa cikin ido tana ganin yadda yake motsawa ta cikin doguwar farar rigar alharinin jikinta da ta gama rinewa da jini.
  Wani haske ya wulga cikin idanuwanta sa'ilin da ta tuna maganarta ta ƙarshe da shi.
  _"Amma ta ya ya zan gane kabarin mace mai ciki a cikin jerin kaburburan?_"
  _"Kin manta yau shekara biyu kenan da na ce miki ki dawo zan baki rana? Ki tafi kawai, ki je ga kabarin da na wassafa miki._" _Ta miƙe har ta kai ƙofa ta ji wasu zantukan nasa masu wuyar fahimta._ _Kin ga, kome kika tarar cikin kabarin ki yi amfani da shi naki ne, halalinki ne Zawwa!_"
  Kamar ta farka daga mafarki haka ta zabura ta ɗora hannunta kan cikin tana shafawa. Idan har za ta fassara yarensa wannan abin da ke cikin matar shi ne dukkan maganin damuwarta. A karo na farko da ta kira sunan Allah cikin zuciyarta tana ƙarasawa da sauri ta tallafo kan matar, "waye uban cikin da kike so a cire, zan cire tunda yana da rai bai kamata ku mutu tare ba dama, amma waye Babansa, me ya kawo ki wannan yanayin, ina ne garinku? Ta gaza magana sai mammotso baki da take yi, da ƙyar harafin Haaa ya fito jini ya biyo bayansa tamkar suna kwaata." "Haadirru ko Halliru? A ƙaryar nan suke? Tufafinki bai yi kama da na nan ba, ina ne garinku?" Ta ƙarasa mata da hanzari. Kaɗa mata ido ta yi tana mai ƙara buɗe baki, "Huuu." Sai kuma ta yi yaraf numfashinta na ɗaukewa tana zuƙo shi da ƙyar. Idonta ta kalla ta gane magana take mata dan tana ta son motsa hannunta. Hannun ta riƙo tana kallon Zoben Zinarin da ke jiki, gabanta ya yi wata mummunar faɗuwa ganin an saka abu kamar almakashi an tsaga hannun nata tun daga gaɓar farko ta hannu, a karo na biyu da ta yi mamakin yadda aka yi take numfashi har kawo i yanzu, ta kalli matar, "wannan kike so a cire?" Ta kaɗa mata ido. Da hanzari ta saka hannunta ta zare zoben, zarewar ya yi daidai da wata tsawa da aka tafka mai haɗe da walƙiya ta cika ilahirin maƙabartar. Matar ta yi wata irin miƙa mai gauraye da atishawa jini na daɗa bulbulowa ta cikin hancinta, kafin kuma jikinta ya saki, rayuwarta ta koma ga mai shi!
  A firgice ta yi kanta ta jijjiga sai dai ina ta riga ta tafi, ta sauke idanuwanta kan cikinta da yake wani irin motsin neman agajin gaggawa, a lokacin ne kuma ta ji sautin muryarsa.
  "Ya Laɗeefu, Ya Hakeemu, Zawwa! Mai za ki yi da gawa?"
  "Ubanka zan yi!" Ta furta a matuƙar fusace tana juyowa saitin da yake. Yana tsaye hannunsa aka, rataye yake da wata jakar fata alamar daga tafiya yake, a shekaru ba zai gaza ashirin da biyu ba.
  "Haadiru me ya sa ka biyo ni? Yaushe ma ka dawo? Me ya saka ne ka rainani duk sa'adda zan yi abinda ke gabana sai ka shiga tsakiya?"
  "Dawowata ke nan fa na ganki kina ta sauri kin yanki daji shi ne na biyo ki, ɓace mini ma kika yi sai yanzu na gano ki a nan. Yanzu Zawwa ba za ki daina biyewa Tsohon can ba, na tabbata shi kaɗaine zai haɗa ki da gawa a wannan talatainin daren kan abinda ya fi kowa sanin Allah ke..."
  "Rufan baki shashasha marar kishin ubansa!" Sai kuma ta yi shiru tuna dama dole tana buƙatarsa, dan da babu shi da sai dai ta bi ta hanyar da asirinta zai tonu watarana, dan haka ta yafito shi, "zo ka ga." Ya matso a hankali yana leƙa gawar matar.
  "Ta mutu, amma abinda ke cikinta na motsi, ta buƙaci kuma da a cire mata shi dan ya rayu, ina kimiyyar da kake koyo? Ba an koya muku fiɗa ba? To maza zo ka farka ta ka zaro abinda ke cikinta!"
  Baya ya yi yana kaɗa kai da sauri da sauri. "A'a ban iyawa, wannan zalunci ne, a'a Zawwa ki tashi mu tafi, idan fatalwa ce za mu rayu da jininta a zuriyarmu, idan Aljana ce za ta buwaye mu. Ba a ma gama koya mana ba, ba kuma a bamu shaidar mun iya ba".
  "Haadirr! An dai koya ko?"
  "Eh".
  "To so kake na zagi Tsohonka a karo na biyu?"
  "A'a...".
  "To maza ka zo ka tsagata ka ciro abinda ke ciki, kar ka damu ta riga da ta zama gawa, haka wani ran ka anqaza, na kuma san cikin jakarka ba ka rasa abin aikin, idan ma babu ga wuƙata ta icce. Zo ka yanka ta".
  "Anya zan iya..."
  "Za ka iya! Kasa a ranka za ka iya kome!!"
  "To ai kar na je na yanki abinda ke cikinta, to dai hasko mini sosai".
  Ya furta a sanyaye yana sauke jakar ƙasa.
  "Yauwa akwai zabira cikin jakata da ita ake yi, kai ni kam fa ina tsor.."
  "Ba na son kalmar nan ka sani ko! Ba na so!! Ita ce silar kwantar da rayuwarka da tawa. Zo ka yi aikinka!!!"
  Ta furta masa a tsawace, idanuwanta sun yi jajur tamkar da hayaƙi aka lulluɓeta.
  "Ki haskan sosai to..."
  Suka duƙa gabaɗaya jikin gawar. A sannu ya saka zabirar ya tsagata daga saman mara, ya cewa Zawwa ta danno masa cikin daga ƙirjinta ta turo shi ya yo ƙasan. Ta saka ƙarfinta ta danno cikin ya taho shi kuma ya ƙarasa jawo shi ya saka zabirar ya raba cibiyar da mabiyarsa, a sannan aka fasa wata irin tsawa mai haɗe da rugugin aradu, wata baƙar guguwa da ta taho daga yamma ta lulluɓe su, ya haɗe da sautin kukan jaririyar da ta kwalla da dukkan ƙarfinta, ruwan saman ya kece tamkar da bakin kwarya yana sauka da ƙarfinsa a ilahirin maƙabartar.
  Zawwa ta yi wani kukan kura cikin zafin nama ta warce jaririyar daga sandararen hannunsa ta rungumeta a ƙirjinta, ya kai kallonsa ga jakarsa, ya yi gunta da sauri ya zaro wani mayani mai kauri ya rufa musu, a tare suka doshi wata babbar bishiyar ceɗiya da ke kusa dasu suka zube ƙasanta suna sakin numfarfashi. Idanuwansu ya shilla kan gawar da cikinta ke buɗe ruwa nata sauka kanta, Haadiru ya runtse idonsa da ƙarfi yana gudun nuna tsoronsa a fili dan ya so ya rufe cikin gawar a maidata kabarinta. Zawwa kam ɗauke kanta ta yi ta sake rungume jaririyarta gudun kar ruwa ya taɓa ta ya tafi da wankan farko da za a yi mata dan bawa Bawa ruwan ya yi maganin lalurarsa.

  Ba daɗewa ruwan ya ɗauke, sai na sassanyar bishiyar da ke kaɗawa tamkar ana wani yayyafin. A tare suka sauke ajiyar zuciya suna duban juna kafin kuma su janye kallon zuwa ga gawar, ya buɗe baki zai yi magana ta tari numfashinsa. "Kai, mai da gawar cikin kabarinta ka rufe yadda ba wanda zai gane anyi haƙa a gun."
  "Eh hakan za ayi, amma fa cin mutuncin rai ne a sakata a haka ba tare da an ɗinke inda muka tsaga ba."
  "Babu wannan lokacin Haadirr, ta mutu shi ke nan, bata buƙatar wani ado a tare da ita..."
  "Amma Zawwa ya za a yi..."
  Wani kallo da ta wurga masa ya saka shi datse zancen, ya miƙe kawai ya isa ga gawar, gefen doguwar rigarta ya kalla, babu inda zai iya yaga a jiki. Dan haka kawai ya zare rigar jikinsa ya sunkuya ya naɗe cikin gawar da ita ya ɗaure tsam, kana ya jata a hankali ya jefa cikin kabarin. Ya ɗaga shebur ɗin ya fara maida mata jiƙaƙƙiyar ƙasar. A lokacin ne aka haska wata walƙiya mai tsananin haske, ta haska masa can gabansa cikin wata duhuwa ya ga alamar mutum a tsaye yana dubansa. Sakin Shebur ɗin ya yi ya juya a guje zuwa inda Zawwa ke tsaye rungume da jaririyarta.
  "Na..naa rantse da Allah ba mu kaɗai ba ne anan, kin ga?"
  Ya furta bakinsa na rawa yana nuna mata saitin duhuwar.
  Ta ɗaga fitilar kwanta tana haske gurin, sai dai wayam babu kowa, babu ma alamar akwai wani mahaluƙin da zai iya wanzuwa gurin. Duhuwar tsakankanin wasu kabubbura masu tudu take.
  A tare suka kalli juna, a karo na farko da ta saka hannunta ta sharce wani sassanyan gumi da ya tsiyayo mata tun daga lokon hancinta. Ba Haadiru kaɗai ba ne ya san da wani a tare da su, hatta ƙofar tsiron duk wani gashi da ke jikinta abinda yake ta ankarar da ita kenan tun farkon bayyanarta cikin maƙabartar!

  "Haadiru mu ɓace a gurin nan..."
  Ta furta a hankali tana takawa kusa da shi sosai.
  "...Idan ma da wani bibiye damu za mu gane anan gaba."
  Ya tsura mata ido cikin tsoro mabayyani, kafin kuma ya sunkuya ya ɗauki jakarsa da sauran kayan aikin su fara tafiya ba ko waiwaiye, haka ba wanda ya ƙara cewa da ɗan uwansa kome har suka fita daga cikin maƙabartar. Suna gabda isa gidan Haadiru ya ja ya tsaya yana duban Zawwa da ke ƙoƙarin shigewa ta ƙofar baya da aka rufeta da wani kakkauran buhu na Algagara.
  "Zawwa me za a cewa Baba wai, kar kalamanmu su saɓa.
  Juyowa ta yi ta dawo saitinsa ta tsaya, a sannan ne kunnuwanta suka daɗa zuƙo mata wani abin. Ta yi wani murmushi cikin duhun bishiyar da suke ƙasanta ta matsa jikin Haadiru sosai daidai saitin kunnensa ta masa raɗa.
  "Ruga da gudu cikin ɗakina daga can ƙurya za ka ga wani shantu ka ɗauko mini."
  Daga yanayin sautinta ya gane ba ta buƙatar tambaya, dan haka ya zura da gudu dan cika umarninta, ita ma ta mara masa baya, sai dai ba ta kai da yaye buhun ba ta ji ana kici-kici da nishi, da sauri ta dawo saitin bishiyar tana ɗaga fitilarta sama ta haske fuskar Basamuden mutumin da ke biye da ita tun daga cikin maƙabarta. Tarkon da suke haɗawa dan kama ɓarayi ya kama shi. Wata igiya kakkaura ya taka da aka sakalota tun daga saman bishiyar aka binneta a wani rami. Kafarsa a ɗaure tana reto a sama a yayin da kansa ke ƙasa a haka Zawwa ta haske shi tana kashe shi da wani shu'umin murmushi.
  "Ki kwanceni dan Allah Ni ba da sharri nake nufinki ba, wannan jaririyar kawai za ki ba ni na binne, saboda kar a haifeta aka ba ni umarnin binne uwarta!"
  "Idan baka san sirrin guri ba ka daina bibiya, idan ba haka ba watarana za ka je inda zai kai ka ga kushewarka."
  Abinda ta furta masa kenan Haadiru ya iso ta bashi umarnin ya yi ta muƙawa mutumin shantun har sai jini ya fita a jikinsa, idan kuma ya sake ya yi ihu a take za ta yanke masa 'yan maraina. Ta furta masa tana nuna masa wuƙarta da ke suke a ƙugu. Jin haka yasa mutumin matse bakinsa yana jin ana bugunsa ko ta ina amma ba damar ihu. Sai da ta tabbata ya bugu shi kansa Haadiru ya gaji tukunna ta ce a dakata.
  Ta dubi mutumin da bakinsa ya kumbura suntum, "wanene kai, waye ya ce ka binneta?"
  "Ni ɗan aike ne, sai dai ko za ki kashe ni na gwammace na mutu akan na faɗa miki wanda ya aiko Ni."
  "Wane uban wannan yarinyar? A ina waccar budurwar take?"
  "Ki taimaka ki bar tambayata abinda ba zan taɓa amsawa ba. Ki kwance ni ki ba ni wannan jaririyar kafin Ogana ya samu labari, wallahi kinji na rantse ya san an haifi yarinyar nan dukkanmu kashe mu zai yi."
  Ya furta da ƙyar wani jini mai yauƙi na fita ta bakinsa.
  Haadiru ya yo bayanta a tsorace ya tsaya.
  "Zawwa ki basu yarinyar nan, kinga daga ganin zubin mutumin nan kinsan ba irin mutanenmu ba ne, kar muje mu jawowa yankinmu Annoba."
  Wata muguwar harara ta maka masa ta cikin duhun.
  Sai kuma ta karɓi shantun hannunsa ta laluba daga can ƙarshensa ta fara warware wani siririn murfi da aka yi mata a jikin shantun. Ba daɗewa ta zazzago da wasu kwayoyi guda biyu masu kama da sabulun salo 'yan ƙanana, sai dai ɗaya baƙa ce ɗaya fara daga cikin shantun. Ta ɗauki baƙar ta sunkuya saitin fuskar mutumin.
  "A karo na ƙarshe zan ƙara tambayarka."
  "Wanene oganka? Me ke tsakaninsa da waccar budurwar da ya saka ka binneta, a ina kuke, dan bansanka a wannan ƙauyen ba?"
  "Na ce ki kashe ni idan kina son..."
  Kafin ya ƙarasa ta jefa masa baƙar kwayar a bakinsa tasa hannu ta matse bakin nasa har sai da ya haɗiye. Kana ta miƙe daga kansa tana sakar masa murmushin mugunta. Ta zaro wuƙarta ta yanke igiyar da ta riƙe masa ƙafa sai gashi ya faɗo tim! Ta ƙara haske shi da murmushi bayan ta dallare fuskarta da fitilar kwan.
  "Tashi ka yi tafiyarka, ba ogan ka ba koma waye ka bashi wannan labarin idan har za ka iya. Yauwa, idan ka kasa bada labarin kar ma ka sha wahalar neman magani, ka ga makarin maganin a cikin shantun nan, ni kaɗaice kuma nake da irin maganin nan, oganka ko yana tafiya tsirara dan tsafi bai isa ya sama maka magani ba dole sai an neme ni, Ni din kuma ko labari na ba zai taɓa samu ba tunda ba za ka iya faɗa masa ba. Na barka lafiya."
  Daga haka ta juya ta yi shigewarta gida Haadiru ya rufa mata baya yana waiwayonsa!
  ***

  Kallonta yake yadda take shayar da jaririyar cikin farin ciki, ya dubi jikinsa da awanni goma sha biyu da suka gabata yake a kalmashe. Ai sai ya ja guntulalliyar ƙafarsa ya yi sujjada ga ubangiji mai girma a karo na uku. Ya ɗago ya ƙara kallon Zawwa da ke ta ƙoƙarin ganin jaririyarta na zuƙo ruwan nonon da ƙarfinta, sai abin ma ya bashi dariya.
  "Kai Zawwa! Allah shaidata ina matuƙar ƙaunarki."
  Ta ɗago ta masa farr! Da Ido.
  "Ka faɗa sau goma kenan daga buɗewar bakinka zuwa yanzu, ba wani nan ma ai marigayiya uwar Haadiru kake so."
  "To ke banda abinki shekara nawa yanzun ina son yin magana ba damar yi, ki barni na yi ta rera muku ita yau. Kayya! Ba na son tuna lamarin nan. Yauwa na faɗa miki ba a kishin matacce fa, yanzu ai ke ce a gabana ko?"
  Shiru ta yi tana duban kyakkyawar fuskar jaririyarta, a hankali ta fakaici idonsa ta ɗauke 'yar kwallar da ta maƙale gurbin idonta.
  "Ai an faɗa mini sa'adda Baba ya baka ni cewa ka yi baka so mai za ka yi da mace mai aikin maza, wai dan ina binsa Farauta."
  Murmushi ya yi ya shafi gemunsa da furfura ta fara ratsawa.
  "Wannan gulma ce irin ta mutanen gari fa, ni na ƙiya ne wai ganin shekaruna sun doshi arba'in ai na miki tsufa. To kuma sai kika nuna mini ban fi dan shekara 18 ba a idonki." Ya ƙarasa yana fashewa da dariya. Sai kuma ya sauke idonsa kan jaririya.
  "Wai ni wane suna za a sakawa ɗiyar nan? Na so kinji sunan mahaifiyar tata kinga da an maida mata shi."
  "Yo kai ma Bawa matar da ke gaɓar naƙuda a tsakiyar titi Ina za ta iya faɗar suna, wa ma zai iya tambayarta? Kai dai mu gode Allah kawai da har shi Haadirun ya iya taimaka mata ta haihu da kanta kafin ta rasu, yauwa ga wani zobe ma ta ba ni ka ganshi kamar zinari ne, ta ce a sakawa ɗiyar idan ta girma."
  "Oh Allah wannan rayuwa, ki ce har tasan abinda ta haifa kafin ta rasu..?"
  "Ai har ɗaukarta ta yi. Har yanzu ina tuno murmushin da ta bi ɗiyar da shi kafin ta kai ga kushewarta."
  Suka yi shiru gabaɗaya suna jinjina lamarin. Sai dai ita zuciyarta cunkushe take da tunanin ranar da Bawa zai gano a dalilin neman maganinsa ne ta samu jaririyar."
  "Ai shi ke nan ina ganin a saka mata Hameeda."
  Wata irin zabura ta yi ta miƙe jaririyarta ta fashe da kukan razana. Jikinta na rawa ta dawo ta zauna daɓass tana dubansa a dugunzume.
  "Wallahi summa tallahi ko sunan duniya ya ƙare ba za a saka mata Hameeda ba, kamar fa za a ce Hameedu ne, haba Bawa, kai jama'a! Innalillahi wai inna ilahhir raji'un, ban yafe masa ba wallahi, ba zan taɓa yafewa ba! Wato bayan kalmashe maka ƙafafu da ya yi har sace zuciyarka ya yi dan ka dinga begensa. Sai kuma ta rushe da wani irin kukan baƙin ciki da ke fitowa tun daga ƙasan zuciyarta. Jikinsa na rawa haka ya jawo ƙafarsa ya zo gareta, gabaɗaya sun rikita shi, ita kuka jaririyarta kuka.
  "Yi shiru ba yadda tunaninki ya baki ba ne haba Zawwa, na fa faɗa miki ni har mancewa nake da wani Hameedu..."
  "Ba ka mance da shi ba, da ka mance ɗazu ba za ka tura yaro gidansu ba daga miƙewarka. To bari ka ji abinda baka sani ba, ba za ka ƙara ganinsa ba a rayuwarka. Tunda ya yaudareka yasan ka gane ya bar garin nan da duka danginsa, ance yana ƙasar turawa ma."
  Ta furta tana jan bakin zaninta ta face hanci, sai kuma ta ci gaba da rera kukanta.
  "To ki yi shiru mana kai ni Bawa, wai Zawwa me zan miki a rayuwa ne ki mance Hameedu da abinda ya yi da duk wata tsiyarsa?"
  Tsit! Ta yi tana haɗiye kukanta. Ta zuba masa ido tana ƙare masa kallo daga sama har ƙasa, da ta iso kan dulgunminsa sai ta yatsine fuska tana shesshaƙa."
  "So nake ka sai da gonarka da awakinka biyu mu bar garin nan, mu tafi can inda ba wanda yasan ba ni ce na haifi yarinyar nan ba, inda za ta yi karatu ta zama irin abinda nake mata buri. Ba ma a birnin wannan ƙaryar ta mu za mu zauna ba, mu tafi wani birnin mai nisa sosai. Ni kuma na maka alƙawari daga ranar da muka bar nan ban ƙara tada zancen Hameedu!"
  "Shiru ya yi yana nazarin zancenta. Ta wani ɓangaren shi kansa ya gaji da zaman ƙauye ta yadda labarinsa ya tamfatsa ko'ina har zuwa ake yi ana kallonsa ga wanda Amininsa ya cuta har ya nakasar. Hakan ma wata mafita ce dan haka ya gyaɗa mata kai alamun ya amince. Ta yi wani juyi tana buɗa tamkar ba ita ke kuka yanzu ba, ta ƙare matse jaririyarta a jikinta tana jin sonta da ƙaunarta har a ƙarshen tsokar da ke tsakanin ƙirjinta.
  "Sunanta Haƙabiyya..."
  Ya bita da wani kallo sororo.
  "Haba Zawwa wane irin sunane wannan, ki saka mata na arziki mana..."
  "Allah sunanta kenan a gurina, shi ne fa sunan da nake ce maka na yiwa kakata Habi alkawarin zan saka mata shi duk ranar da na samu ɗiya mace.
  Shiru kawai ya yi tuna girman alaƙar da ke tsakaninta da Habi, har a bayan ranta gata nan sabuwa dal a gurin Zawwa. Sai ya girgiza kai yana mai jawo sandunansa ya miƙe tsaye.
  "Duk ranar da ta girma sai kunyi shari'a da ita kan sunan nan za ki ce na faɗa miki. Kuma ni da kaina zan tsaya mata ta kai ki har gaban ƙuliya manta sabo."
  Daga haka ya dogara ya fice daga ɗakin. Ita kuma ta bi bayansa da kallo da wani bushasshen murmushi a saman fuskarta, akwai alamun abinda ke duƙunƙune cikinta ya fi zare yawa!
  ****

  @Fulani Bingel

Comments

0 comments