Makalu

Blogs » Kagaggun Labarai » TSIYA DA WASALI: SHAFI NA BIYU

TSIYA DA WASALI: SHAFI NA BIYU


 • *1995*

  Ta waiga hagu da damarta, ta kasa kunne na 'yan daƙiƙu ba ta ji motsin kome ba sai na ruwan da ke wucewa ta rariya, ta hanga ga ƙofar gidan da ke garƙame da Kwaɗo ta waje, ta maka mata harara ta murguɗa baki, sai kuma ta daka tsalle ta kama 'yar katangar da ke gabanta, kamar kyanwa haka ta haye saman katangar, kana ta dire a ƙasa inda ta wanzu a cikin kangon ginin da ke jikin gidansu ta baya. Ta sunkuya ta tsittsince 'yan kayanta da ta fara jefowa wajen, kana ta lafe daga lungun kangon ta buɗe jakarta ta ɗauko kazal da wata jar hoda. Ta zazzaga a hannunta ta fara ƙawata fuskarta da ita.
  Ta daɗe tana kwalliyar kafin ta gama ta miƙe ta zaro wata shuɗiyar doguwar riga daga cikin jakar, ta ɗora akan kayan shan iskar da ke jikinta. Ta saka ɗan ƙaramin tarhar rigar, ta rataya zungureriyar jakarta. Har ta doshi hanyar fita daga kangon sai kuma ta dakata tamkar wacce aka tsayar, ta waigo tana duban can ƙarshen kangon inda wata curin ƙasa ke tare. A hankali ta saki wani yalwataccen murmushi. Ta ƙarasa ga kasar ta tone kaɗan ta zaro wani turare a kwalinsa. Ta rungume shi a ƙirjinta idanuwanta a lumshe, sai kuma ta buɗe ta fesa shi kaɗan a jikinta tamkar wacce bata so ya ƙare. Ta maida shi ma'ajiyarsa ta juyo ta fice daga gurin ta nausa hanyar da za ta maidata cikin gari. A ranta take godewa Allah da Kawunta da baya son jama'a su raɓe shi ya ƙaura daga cikin gari ya zo ƙarshen Kano yake zaune, inda babu 'yan saka ido babu munafukai, babu handamammu, babu jarababbu, maƙotansu tsilli-tsilli ne, idan ba taro ake ba baka sanin da mutune a unguwar.
  ***

  "Tun da tazarar kilomita goma tsakaninmu nake jiyo ƙamshin wanzuwarki gurin nan."

  Ya furta sa'ilin da ya miƙe ya isa gareta ya kama tattausan hannunta. Sai kuma ya saki hannun da sauri yana buɗe tafin, gashi nan wani gun ya farfashe wani gun ya yi jajur. Ya tamke fuska yana duban kwayar idanuwanta masu girma da sheƙi.

  "Yanzun ma ta katangar kika fito ko? Ki daina dan Allah, zan fahimta idan har na jiki shiru na sha faɗa miki hakan." Ya furta a tausashe.

  Ta yi wal! Da ido tana duban siririn karan hancinsa. Ta sani dama sai ya yi ƙorafi, dan haka ta ɗau salon canja zancen.

  "Kai kam ta yaya za ka ji ƙamshi na a tazarar kilomita goma? Ka kuwa san nisan."

  "Na sani fa, saboda hakan na mallaka miki turaren da na san zai yi wahala a samu mai irinsa domin kawai in dinga bambance ki cikin tarin mata, ke ko wani ya haɗa alaƙar jini da ke ko yake rayuwa a inda kike yi da na yi tozali da shi zan gane yana da alaƙa da ke, ina jin ko da a hali na makanta ne ba na kasa shaidaki Hamd..." Ta sanya hannu da sauri ta rufe bakinsa tana girgiza masa kai idanuwanta rau-rau.
  "Allah ya raba ka da mutuwar tsaye, ina roƙon mahaliccinmu da idan da hakan a cikin ƙaddararka ya maido mini ita kaina, bana fatar wani mummunan abu ya same ka daga nan har ranar da babu ɓurɓushinmu. Ina Sonka sosai Huzaif, fiye da abinda idaniya ba ta iya ƙididdiga!"
  "Ya ilahi! Hamdiyya!! Ki aure ni dan Allah, gobe, kin ji?"
  Ya furta da wani irin yanayi da ya saka jikinta rawa ta dunƙule hannayenta cikin cinyoyinta tana ƙasa da idanuwanta.
  "Ki dube ni dan Allah, za ki aure ni? In zo gun Kawu goben?"
  Ta girgiza kai da sauri tana kallonsa da murmushi.
  "Akwai lokaci, amma me ya sa tunda muke tare yau tsayin shekara guda kenan baka taɓa cewa in aure ka ba sai yau?"
  "Ban sani ba fa, kawai yanzun na ji kin zama gabaɗaya rayuwata, ina jin kamar tazarar taku guda kawai za ki bada a tsakanimu da niyyar barina zuciyata ta tsarwatse na zama gawa. Da gaske da bugun zuciyarki rayuwata ke tafiya yadda ya dace. A dukkan numfashin da zan ja na fesar da tunaninki nake yinsa na kuma tabbata ke ce silar zamana hakan a yanzu. Ina sonki sosan gaske, ban ma san ta yaya zan fayyace shi ba ki gane ƙololuwar matsayinki a gare ni, ke, ko wuƙa za a siyo a tsaga zuciyar mu ƙididdiga soyayyarki da ke kewaye da ita?"
  Ta saka dariya sosai tana duban wasu baƙin turawa da ke can gefensu suna ta ciye-ciye.
  "Ni dai ina son irin Lemon can.. "
  "An gama, da kuma me?"
  "Da kuma zamowarka nawa ni kaɗai tal!"
  "Kin samu, har abada ba na haɗa ki da wata, har abada, na rantse da Allah!"
  Ta kyalkyale da dariya sosai tana dukan teburin da ke tsakiyarsu.
  "Yanzu to menene na rantsuwar saboda Allah? Na yarda fa, na sani babu wata da za ka duba da sigar da ka dube ni. Na yarda da kai irin yardar da nake jin ko ba na raye ba za ka nemi wata da sunan soyayya ba".
  "Ai fa ki barni na rantse, kina gani jikina har rawa yake, ban taɓa jin son wata halitta ba irin yadda nake jin naki, kin kanainaye dukkan ruhina, ba na kaffara idan na rantse miki da mahallicina wannan iskar da nake zuƙa ina fesarwa da alfarmarki nake yi, da babu ke da tuni na daɗe da zama tarihi, ke ce tsanin cikar dukkan buri na, burin da saboda shi nake ƙara kusantarki a kowacce thaniya. Kar ki guje ni domin Allah Hamdiyya, kar ki juyan baya a kome da zai faru watarana, ki zamo mai yafiya gare ni. Dan Allah".
  "Huzaif! Ya isa dan Allah, kana sawa ina jin ba daɗi, ina saƙa wasu cunkusassun lamura marassa ma'ana, waya ce maka zan iya barinka? Wane ya ce maka za ka iya ɓatan ran da har zan ƙullace ka? Babu wannan abin, idan ma akwai ba zai yi tasirin da zai taɓa alaƙarmu ba ko da kuwa menene shi, ko da kuwa girmansa ya kai tafkin Nilu ba zan taɓa juya maka baya. Wallahi ka ji rantsuwa ba dan Kawu ba gobe zance ka fito. Amma baya so, haka ina son dukkan abinda yake so fiye da zatonka, banda haka..."
  "Na gode Allah da ba fiye da ni kike son ba."
  Ya tari numfashinta yana kashe ta da ƙayataccen murmushi.
  Hararsa ta yi tana miƙewa.
  "Shi ke nan ma to ka ja na fasa maganar, kuma tafiya zan yi, Kawu ya kusa dawowa.
  "To 'yar Kawu, na ji, bari na rakaki har kwanar unguwar".
  "In dai ba ƙofar gida za ka rakani ba ai da sauki, ina maraba".
  Suka fara takawa a hankali.
  "Ko za ki yi mini rakiya gida?"
  "A'a, ka bari sai wani lokacin, yanzun sauri nake dan na ci tuwo miyar zogale da zafinsa, yauwa na tuna, yaushe za ka kai ni gurin Umman naka?"
  "Garinmu da nisa sosai, kullum kina mantawa da hakan".
  "Amma tunda ka zo tsayin shekara guda ban ji ka ce mini ka tafi ganin gida ko ganin Umma ba".
  "Waya faɗa miki? Idan na ce miki a kowane dare ina zuwa can ba lalle ki yarda ba".
  "Ehn.. Za ka fara cukurkuɗa magana irin ta masu lalura ko? Bari dai na kawo ƙarshen kome, watarana da daren za ka ganni tsulum a gidanka, sai na rakaka ziyarar ganin gidan da kake zuwa."
  Ya yi dariya sosai mai haɗe da tari.
  "Ina fatar hakan, wannan ma buri nane."
  "Ka kula kana da burirrika da yawa...?"
  "Amma kuma ke kike lulluɓe da dukkan burikan ai, ke dai Allah Ya nuna mini ranar da za ki zo da daddaren."
  "Amin Huzaifatu".
  Ta furta tana mai harɗe hannunwansu tamkar turawan da aka gayyata rawa tsakiyar taro.
  ***

  "Idan zan rufe gidan nan sau goma sai ta fita sau goma, wannan sakacinki ne da iya ɗaurewa ƙarya gindi. Na ce shi wankan dole ne? Idan za ki kauce daga gabanta me ya sa ba za ki rufe ta a ɗaki ba?"

  "Haba Maigida, a mari take ne da zan dinga kulle ta ko a gidan mahaukata? Ina dalilin da za ka matsa har haka, na faɗa maka bana sanin za ta fita, yanzun ma zaune muke tana gyaran zogale na ce bari na kewaya kafin na fito ta fice, idan tsaron dole ne ka ƙara tsayin katangarka mana. Amma Allah ba zan zauna ina maka gadin ƙatuwar budurwa kamar Hamdiyya ba."

  Motsin da suka ji a ƙofa ya saka su waigawa gabaɗaya suka yi arba da ita tsaye tana ta zare idanuwa kamar Barewa a bakin Zaki.

  "Daga ina kike, ba saboda ke na rufe ƙofa yau ba?" Kawu ya furta.

  "Can baya naje, ka yi haƙuri dan Allah."

  "Wanene shi yaron?"

  Ji ta yi hantarta ta cure guri guda jin tambayar daga sama. _Yaushe Kawu yasan abinda nake yi?_. Da sauri ta gayyato juriya ta aza saman fuskarta.

  "Tambayarki nake ko, a ina kuka haɗu."

  "A asibiti, tun sa'adda aka kwantar da Baba."

  Ya bi ta da kallo daga sama har ƙasa yana mamakin yadda ta bashi amsa ba gargada.

  "Shekararku guda ke nan? Ba ki taɓa faɗa mini ba balle ma na yi matsayin da zai nemi izinin nemanki a gurina, kike fita da shi ko'ina a cikin Kano, har sai da mutunen waje suka ankarar da ni, wai ni Sahabi ɗiyata ke yawo da wani  ƙato a gari."

  "Ka yi haƙuri..."

  "Zan haƙura, amma faɗa mini, wacce wasiyya mahaifinki ya bar mini?"

  Shiru ta yi tana raba idanuwa.
  "Tambayarki nake yi ko!?"
  "Umm...Cewa ya yi ka kula dani, kar ka bar Ni na kula kowa a waje."

  "Saboda me ya ce haka?"

  "Saboda kaine jininsa guda ɗaya da ya rage, kuma yana so ka haɗa ni aure da Yaya Haruna."

  "Shi Yayan wanene shi a gurina?"

  "Ɗan ka ne."

  "Ke kuma fa?"

  "'Yar ka ce, 'yar amana."

  "Da mahaifinki ya roƙi hakan gurina me na ce masa?"

  "Ka yi masa alƙawarin za ka yi duk abinda ya furta koda kuwa shi ne abu na ƙarshe da za ka gabatar a rayuwarka ba Ni da miji sai Yaya."

  "To yanzun da kike kula wani me kike son mai da ni?"

  Ta yi shiru, dauriyar tata ta gama kaiwa ƙarshe.

  "Tambayarki nake Hamdiyya!!"

  "Kawu wallahi...*Ina...ina son sa ne."*
  Ta furta hawaye na rige-rigen isa gurbin wuyanta.

  Baki kawai ya buɗe daga shi har matar tasa, ya tsura mata ido yana jinjina girman zamanin da yake ciki.

  "A'a, share hawayenki, kinsan me za a yi? Na fasa jira Harunan ya dawo daga Kwaleji, nan da wata guda zan ɗaura muku aure, dan haka ki ɗauko son da kike yiwa wancan ɗin ki maido shi kan Haruna, ki kuma haƙura da shi ki ba ni haɗin kai mu cika burin marigayi."

  Zuciyarta ta buga tamkar za ta tarwatsa allon ƙirjinta ta fito, ji ta yi ruhinta na ƙoƙarin arcewa daga gangar jikinta, sai dai hakan bai hanata riƙe kanta ta fasa ihun da amsa kuwwar sa ya ratsa sabon ginin nasu ba.

  "Wallahi Kawu ba na son Yaya shi ma baya so na, Ni Huzaif nake so idan ban same shi ba mutuwa zan yi."

  "Babanki ma sa'adda ya auri Babarki baya sonta ba ta son shi, wanzuwarki anan yanzu shi zai tabbatar miki da cewar bayan auren sun so juna har suka samar da ke. Babu abinda ya kashe su Hamdiyya."

  Kawu ya furta yana sunkutar buta ya fice daga gidan.

  Rarrafawa ta yi ta faɗa ɗaki cikin gunjin kuka, auren wani ba Huzaif ba nan da wata guda abu ne da bata taɓa zaton faruwarsa ba. Da girman Allah ta yi rantsuwa idan ba shi ba sai dai ta mutu ba aure, rabin kukanta tana yi ne dan tausayin Kawu da kanta sanin rabuwarsu ta zo, ta sani tunda ya furta babu kuma wani abu da zai tada zancensa, haka idan har ita jinin Kawu ce da gaske to kuwa tunda ta furta Huzaif take so ita ma babu wani abu da zai tada hakan. Ta tuna adanannun kuɗaɗenta da Huzaif ke yawan bata tana ɓoye su cikin kango, ba ta zaci amfaninsu zai zo mata da wuri haka ba, tabbas sun ishe ta ta yi duk abinda za ta yi, ta tafi duk inda take so ita da masoyinta suyi aure, idan yaso bayan ta haihu sai ta zo gun Kawu ta bashi haƙuri. Da wannan tunanin ta ji hankalinta ya ɗan kwanta, sai dai fa ba za ta iya jira har zuwa ranar haɗuwarsu nan da sati guda ba. Dole ne ta neme shi a gobe, amma ta yaya? Sau ɗaya ya taɓa nuna mata layin gidan da yake. Da wannan tunanin wani zazzafan zazzaɓi ya silalo ya lulluɓeta.
  ***

  Idan lissafinta na tafiya daidai wannan shi ne mutum na goma da ta tambaya ko yasan Huzaif yana bata tabbacin bai sani ba.
  "Malam, bai fi shekara fa da zuwa nan ba, za ka ganshi dogo fari mai yawan suma? Yauwa a sabon Bankin nan Silver da aka buɗe yake aiki."
  Ta furta cike da sarewa.
  "'Yan mata na faɗa miki ban san shi ba, ni nan unguwarmu ce anan aka haifeni, ke idan da baƙo cikin unguwar nan ni zan fara sani saboda tsabar sa idona, Ni fa baƙo guda na sani anan unguwar shi kuma ya fi shekara guda nan, haka ba Huzaifu sunansa ba. ki dai yi tunani ko dai ba haka sunansa yake ba? Kina ta Banki-Banki wai shin menene ma shi bankin ko wata sabuwar gonar shinkafa ce?"
  Rashin sanin me za ta ce masa ya saka ta wucewa gaba kawai. Sai kuma ta dakata tana sauke numfarfashin gajiya. Ta ɗaga kanta sama idanuwanta suka dallare da zazzafar ranar da ta haska doron duniyar, ta sanya siraran yatsunta ta ɗauke gumin da ya taho ta silin hancinta yana ƙoƙarin shige mata baki. A lokacin ne kuma ƙofar wani gida da ke can nesa da ita ta buɗe ya fito cikin shirinsa tsaf na jamfa da wando.
  "Huzaif!" Ta furta da wata marainiyar murya, kafin kuma ta ɗaga ƙafa da sauri ta isa gare shi. Bai ji zuwanta ba sai ji ya yi ta shige tsakiyar ƙirjinsa. Hakan wani abu ne da bai taɓa shiga tsakaninsu ba a tsayin lokutan da suka yi tare. Da hanzari ya jata cikin gidan yana maida ƙofar ya rufe gudun idanuwan mutane.
  "Na wahala sosai, tun safe nake walagigi cikin unguwar nan ina nemanka, me ya sa babu wanda ya sanka?" Tana jin yadda bugun zuciyarsa ya canja, sai dai hakan bai hanata sake ruƙunƙume shi ba tana sakin gunjin kuka.
  "Ya isa...Shiiiiiiiiii, ki yi shiru haka bansan kuka fa, me ya faru da har zai saka ki wahalar da kan ki kina nemana, me ya sa ba za ki iya jira zuwa satin da za mu da haɗu ba."
  Ya furta a hankali cikin kunnuwanta yana shafa bayanta.
  "Kawu ne wai aure zai mini da Yaya Haruna nan da wata guda."
  Tamkar an saka baki an bushe wutar aci bal-bal haka tunaninsa ya bushe a cikin kwalkwalwarsa. Sakinsa ta yi a hankali jin shirun ya yi yawa ta lalubi idanuwansa da suka kaɗa jajur da ɓacin rai.
  "Kar fa ka damu, na gama yanke mana shawara mai kyau, ka gudu da ni can garinku ayi mana aure, bayan na haihu sai mu zo gun Kawu mu bashi haƙuri, kaga a sannan ba zai raba mu ba."
  Ya bita da kallo yana gyaɗa kai tamkar marayan ƙadangare.
  "Ki ka ce kar na damu?Koya mini yadda ake hana damuwa tasiri a zuciya dan Allah. Hamdiyya, ke zan rasa fa gabaɗaya ki tafi ga wani na amma kike cewa karna damu saboda kina da wata gurguwar shawara..?"
  "Ba gurguwa ba ce da ƙafafunta wallahi, ni ce na baka damar ka ɗauke ni ka kai ni koma ina ne ayi mana aure, ba zan taɓa rayuwa da wani idan ba kai ba. Ya kamata ka haddace hakan..."
  Yadda ya danƙo kafaɗunta da hannuwansa yana buɗe mata manyan idanuwansa ya razanata.
  "Aurenki nake son yi a gaban iyayenki da waliyyanki ba auren da zan zo ina nadama ba. Son ki nake da dukkan zuciyata ba dan na rabaki da kowa naki ba saboda son zuciyata. Ki ajewa ranki ni Huzaif ba zan taɓa aurenki ba da yardar Kawunki ba."
  "Ina jin zafi sosai."
  Ta furta tana cije bakin riƙon da ya mata.
  Sakinta ya yi gabaɗaya ya juya mata baya yana ɗauke kwallar da ta fara tarar masa.
  "Mu yi haƙuri da juna, ki manta da Ni, ki kuma fice daga nan."
  Cikin wani irin tashin hankali ta shawo gabansa jikinta na karkarwa.
  "Hu...Huzaif ni na haƙura da kai kake cewa?"Sai kuma ta ƙarasa gabansa tana dunƙule hannuwanta ta fara dukansa a tsakiyar ƙirjinsa.
  "Baka isa ba, saboda Ni aka halicce ka, saboda mu dawwama tare, ka sha furta mini haka, wallahi baka isa ba."
  Sai kuma ta durƙushe a ƙasan ƙafafuwansa tana bubbuga kanta.
  Da sauri ya ɗago da ita yana share mata hawayen cikin ƙarfi hali. A hankali ta saka kanta a kafaɗarsa tana sauke ajiyar zuciya.
  "Me kike so na yi? Ina kike so na kai dumbin soyayyarki, ina kike so in sanya rayuwata a sa'adda wani zai nesantani da ke? Ya ilahi! Dama zan iya dawo da ranar da na fara ganinki..."
  "Na tsani kalmar dama, ka sani ko?
  "...Da na ɗauke waɗannan kalmomin uku da suka haɗa ni da ke na furtawa wani su, wanin da ba zai taɓa barina ba."
  "Ba zan taɓa barinka ba, ka daina wannan zaton, ka yarda kawai da shawara..."
  Ta yi shiru jin saukar wani abu me ɗumi a dokin wuyanta.
  A gigice ta ɗago da ɗumbin mamaki da tsoro tana duban idanuwansa da suka yi caɓa-caɓa da hawaye. Wasu shuɗaɗɗun zantukansa suka wuce cikin kunnuwanta.
  _Hamdiyya ban taɓa kuka ba ko da ina yaro. Na sha ganin Innata na kuka saboda yunwa amma ni ba na yi. A gabana yunwa ta kashe Abbana da Baffana da Yayuna biyu kowa yana kuka amma ni ina gefe ina kallonsu._
  "Huzaif ka ga kuka fa kake, menene ya yi girma haka da har ya fi mutuwar Abbanka?"
  "Ki barni na yi suna da daɗi sosai, ina jin wani irin sanyi yanzu haka, matsalarmu da tawa na neman kaɗar da hankalina daga jiki na."
  Zare ido ta yi gabaɗaya tana dubansa da mamaki.
  "Wace matsala ce gareka? Yanzu dama akwai abinda ke damunka baka taɓa faɗa mini ba? Wannan ne son da kake ikirarin kana mini? Har akwai wani abu naka da zan gagara sani?"
  "Ki yi shiru dan Allah, kin sani ba na son abinda zai tada miki hankali, abin ne yana da matuƙar girma, ban jin a 'yan shekarunki za ki iya ɗauka..."
  "Wai mene ne, ka faɗa mini dan Allah, ko da ba zan iya kome ba zan maka addu'a ai, menene ke damunka da zai iya zautar da kai har ka zubar masa da hawaye?"
  "Hamdiyya ki bar..."
  "Ta sanya hannu ta rufe bakinsa da sauri tana kaɗa masa kai."
  "Shi kenan idan ba ni da matsayin da za ka iya faɗa mini damuwarka wallahi na juya na tafi ba za ka ƙara gani na ba."
  Ta juya da sauri tana sharce kwalla ya riƙo ta Yana juyo da ita gabaɗaya.
  "Ki yi hakuri ba na so ki kalle ni wani mutumin banza ne."
  "Ba zan taɓa kallonka haka ba ko me za ka aikata ka sani ai, wai menene? Ko giya kake sha kake son ka bari ka kasa?"
  Wani ɗan guntun murmushi ya ƙubce masa. "Ta fi ƙarfin shan giya, kin gane ne..."
  Sai kuma ya yi shiru yana kallon rinannun idanuwanta, da za ta yi kuskuren matsawa jikinsa sosai za ta iya jiyo bugun zuciyarsa da ya sauya cike da tashin hankali, ya runtse ido da ƙarfi ya buɗe yana ƙara tauna maganar.
  Ta yi narai-narai tana dubansa ganin yadda fuskarsa har wani ja ta yi da rashin nutsuwa.
  "Kai fa nake sauraro..."
  "Zan faɗa, amma...Kin gane, ina sabon aikin da na ce miki shi ya kawo ni garin nan yau shekara guda ko...?"
  "Ta kaɗa kai da sauri tana matsowa kusa da shi."
  "...To ban daɗe da fara aikin ba na saba da manager din Bankin gabaɗaya, yana matuƙar yaba kwazona, ya ɗauke ni kamar yaronsa na jini. To, yau wata guda ke nan ƙaddarar ta faru gare ni. Wasu maƙudan kuɗaɗe ya ba ni cikin jaka in kaiwa wani babban Attajiri gidansa, ya kuma ba ni ne dan kar kowa ya farga zan iya riƙe wannan kuɗaɗen, sannan shi Attajirin shi ya nemi da na yi shiri kamar Almajiri a yayin da zan kai masa saƙon saboda baya son a san yana da ajiya ma a bankin, sai dai dabararsu ba ta yi ba, dan kuwa ina gabda isa ga gidan wasu mutane da bansan su wanene ba suka rufe ni da duka da saran wuƙa, ƙarshe suka kwace jakar suka tafi da ita, kin ga..?" Ya furta yana buɗe kafaɗarsa sai ga wani babban yankan wuƙa ya sha ɗinki.
  Ta yi baya da sauri tana toshe bakinta, duk da ciwon ya warke bata taɓa ganin mummunar yanka irinsa ba.
  "T.. t...to cewa suka yi ka biya musu?"
  Ta furta gabaɗaya jikinta rawa yake.
  "Kusan hakan, amma ta hanyar ɗora mini wani aiki mai mugun wahala da haɗari..."
  Ya yi shiru yana sanya hannunsa a Aljihu ya zaro wani farin kyalle mai zanen kan Mujiya.
  "Kin ga wannan shi ne damuwata Hamdiyya, shi ne tashin hankalina da rashin nutsuwata. Manager ne ya je gun wani Malaminsa kan batun kuɗin, to shi ne ya bashi wannan farin ƙyallen da cewar idan har aka zuba jinin mace na haila a jikin wannan ƙyallen a take wannan kuɗin za su dawo duk inda suke, to shi ne Manager ya ba ni alhakin samo jinin tunda Ni ne silar ɓatarsu. Ya kuma gargaɗeni da idan har ban samo ba nan da cikarsa wata uku a baƙin aikina kenan, zai kuma yi mini zagon ƙasa yadda ba zan ƙara samun aiki a yankin nan ba. Hamdiyya, aikin nan shi ne dukkan rayuwata, da shi nake ciyar da mahaifiyata nake siyan magungunanta nake kula da Maraya."
  Ya furta yana ɗauke kwallar idonsa.
  Ita kam gabaɗaya tunaninta ya ɗauke, tana ganin wani abu mai kama da tsafi ƙiri-ƙiri a gabanta, da ƙyar ta haɗiye wani bushasshen yawu ta ce da shi. "Amma shi ne baka taɓa faɗa mini wannan matsalar ba, ai da tuni na sama maka mafita, Allah banfi sati biyu da yin wanka ba..."
  Ganin yadda yake zare ido yana yin baya ya sa ta yi shiru.
  "...Kana mamaki ne? Wai ni har sai yaushe za ka yarda ina maka son da zan iya mallaka maka dukkan rayuwata?" Ta ƙara takunta gabansa, kafin ya farga ta fisge ƙyallen hannunsa.
  "Bari mu gama da wannan matsalar kafin na aurenmu. Na tafi, ba zan dawo ba sai da abinda kake so a jikin wannan ƙyallen."
  Daga haka ta juya, ya bi bayanta da kallo har ta ja masa ƙofar gidan a fuskarsa.
  Wata juya ya ji ta kwashe shi ya yi taga-taga ya dafe bango yana sauke nannauyan nishi. A can ƙasan zuciyarsa wani abu ke cure masa yana zungurarsa da wani mummunan kuskure da zai jawo cikin rayuwarsa!
  *** ***

  Gyalen ta fara zamewa kafin tasa hannu ta cisge ɗankwalin kanta, ta zube ƙasan bishiyar tana sauke numfarfashi kamar wacce ta yi gudun famfalaƙi. Hannunta ta duba sai kuma ta yi jifa da ƙyallen a tsoroce tana binsa da idanuwa kamar wacce ke zaton yana dira a ƙasa zai ɓacewa ganinta. Dafe ƙirjinta ta yi tana matse cinyoyinta jin mararta na daɗa ɗaurewa a kowane lokaci za ta iya sakin fitsarin. Ta ƙara bin ƙyallen da kallo tana jin nadama na baibaiyeta, kome ya hanata nuna masa tsoronta? _So_, wata zuciyar ta nusar da ita. Amma kuma ta furta masa abinda ba za ta taɓa iyawa ba, ita fa har yanzu da ta yi jifa da ƙyallen ji take kamar an zuba ruwan dalma a tafin hannunta. Allah kaɗai shaidarta ba za ta taɓa iya aikata abinda ta furta za ta yin ba. Sai dai kuma a kowane thaniya idanuwanta na hasko mata hawayensa, na hasko mata girman tashin hankalin da yake ciki, anya ta cika masoyiyar gaskiya idan ta yi shakulatin ɓangaro da larurarsa? Shin ba ta yi butulci ba? To menene mafita, me za ta yi ta nuna masa girman soyayyarsa a rayuwarta? Ko ta bazama ta nemo masa kuɗaɗen? _Hamdiyya ko duka ƙauyenmu zan siyar ba za su dawo mini da abinda ke cikin jakar ba..._. Wasu zantukansa na kusan ƙarshe a jerin bayaninsa suka yi sururu zuwa cikin kunnuwanta. Ai sai ta cije baki tana jawo dankwalinta ta fara goge gumin daya jiƙa dokin wuyanta.
  Cikin rashin sanin abin yi ta miƙe ta fara tafiya a hankali tana daɗa dukunkune ƙyallen a hannunta, a sannan ne sunan wata ƙawarta guda ɗaya tal! Ya faɗo mata a zuciya, ta ja ta tsaya tuna tabbas Hadiyya na da kaifin tunanin da za ta iya bata shawarar abin yi, sai dai kuma sun yi faɗa watanni uku da suka gabata a ranar da za su bar makarantarsu ta kwana. Tun daga ranar kuwa ko a hanya suka haɗu harara ke gama su. Amma kuma ta san duk wannan abin jiranta take yi ta mata magana su shirya, dan haka ta juya ta bi hanyar da za ta sadata da gidansu Hadiyyar.
  *

  Tunda ta fara bata labarin har ta kai ƙarshe bakinta ke hangame, ganin har ta ƙare amma tana ƙame kamar wacce aka zarewa laka ya sakata saka hannu ta haɗe mata labban nata guri guda. A lokacin ne ta yi firgigit ta ja baya zuwa can ƙuryar katifarta tana leƙen cikin hannunwan Hamdiyya.
  "Wai menene haka kike yi mini kamar kin ga wata dodo."
  Da ƙyar ta buɗe bakinta ta ce da ita.
  "Ina nuna miki ne da ki tsaya can inda kike mu yi duk maganar da za mu yi ba tare da hannunki ya zo jikina ba, wai ma kika ce mini saboda kina son sa kika karɓi ƙyallen dan ki zuba masa jinin al'adarki majnuniya?"
  Ta kafeta kawai da idanuwanta tana gyaɗa mata kai.
  "To wawiya shashasha wacce aka yi rabon tunani babu ita, ba ki da labarin a cikin shekarar nan babu labarin da ake yi sai na shigowar 'yan mafiya? Har ta kai ko a hanya kika ga Mai Yalo kika tsaya siya sai dai ki ga kan ki a Injin 'Yan Yankan Kai a maidake kuɗin America. Yanzu da kina karɓar Ƙyallen kika zama kuɗi wa gari ya waya, da kin tafi kenan ba tare da mu muna da labarin abinda ya faru ba."
  Ta bi ta da kallo a tsorace sai kuma ta miƙe tana matse mararta..
  "Wallahi banda labarin nan, ke bari na yi fitsari..."Ta furta tana ficewa da sauri daga ɗakin.
  "To yanzu ya kike ganin za a yi, me zance masa, amma fa Hadiyya na yarda da Huzaif idan da abin cutarwa ba zai taɓa kusantata da shi ba, ke kanki shaida ce, naga kin yaba da halinsa tun lokacin da yake zuwar mana makaranta."
  "Idan kuma shi ma yaudararsa suka yi suka ba shi fa, bai san mene ba? Ke wai ma tambayata kike yi ya za a yi da shi, ai kinfi kowa sanin Ashana zan ɗauko mu ƙyasta masa ya ƙone ke ko tokar a ruwa za a zubata yadda ba mai ganin ɓurɓushinta."
  "Hadiyya ba zan iya ba, kin sani abin nan daga hannun Huzaif ya fito, idan na kona shi in ce masa me?"
  "Ki ce masa ya ɓace, kin neme shi kin rasa, ƙila matar Kawu ta share."
  "To shi kuma ya kike so ya yi da rayuwarsa? Ya sha ce mini saboda aikin nan ya baro garinsu mai nisa ya taho nan ya yi yaƙi da jahilci ya koyi Ingilishi dan kawai ya yi aiki, ya sha ce mini Idan ciwon mahaifiyarsa ya tashi sai ya zagaye kaf ƙauyensu ba mai taimaka masa da kwabon da zai sai mata magungunanta masu tsada. Ya kike so ya yi idan ya rasa aikin nan a dalilin wani abu ƙarami da ni zan iya sama masa?Ni kam zan tafi, dama zuciya ta ce ta kasa nutsuwa da lamarin shi ya sa na zo gurinki ko kina da wata dabarar."
  Ganin ta juya ya sakata saurin riƙota tana girgiza mata kai, gani take yi tana tafiya shi ke nan har abada ba ta ƙara tozali da ita. Ita kam da hakan ta faru gwara su dawwama suna faɗa da hararar juna, ko banza tasan dai tana rayuwa kusa da ita. Dan haka ta jawo ta suka dawo bakin katifar suka zauna.
  Shiru ta yi tana nazarin abin yi, sai can ta ɗago da sauri fuskarta a sake.
  "Kinsan me za a yi? Mu fara gwada ƙyallen, ba dai jini ake so ba? To ko jinin kaza mu zaba masa idan muka ga ba abinda ya faru, sai ki yi ƙunzugun da shi."
  "Kina ganin hakan ba zai lalata laƙanin dawowar jakar ba?"
  "Ke ba zai lalata ba, ƙila ma muna zuba jinin kazar ki ga jakar ta dawo, kika sani ma malamin ko kawai shi jini yake so kowanne iri ne."
  "Kai Allah har na ji daɗi, Dan Allah Hadiyya mu daina faɗa mana."
  Ta furta fuskarta a washe.
  Zungirinta ta yi tana harararta, "tashi ki bar mana gida, ban huce ba fa."
  A tare suka ƙyalkyale da dariya. Sai kuma ta miƙe har ta kai bakin ƙofa ta juyo tana dubanta.
  "Ke kamar fa jiya Lauratu ta can bayan layi ta haihu, bari ranar sunan idan aka yanka rago sai mu dangwali jininsa mu gani."
  "Shi ke nan kuwa ta zo gidan sauƙi, dama ina ta tunanin inda za mu yanka kaza ba tare da an sani ba, to mu haɗu ranar sunan kawai."
  Hadiyya ta furta tana miƙewa.
  *

  "Kin ga dan baƙar rowa a rariyar tsakar gidan za su yanka ragon."
  "Mu shiga kawai ai duk yan unguwa na ciki."
  Hamdiyya ta ba ta amsa.
  Suka kutsa kai zuwa tsakar gidan daidai lokacin da aka kayar da ragon aka zizara masa wuƙa.
  Zungurarta Hadiyya ta yi dan ta ƙarasa gurin, ta dube ta idonta na kwal-kwal da kwalla, "ke Allah tsoro fa nake ji..."
  "Ke dillah ba gwadawa za mu yi ba, Allah ya gama yankawa ya kwararawa  jinin ruwa ya bi rariya kin huta, ki ƙarasa kawai ki yi kamar za ki ɗauki buta ki jefa ƙyallen kan jinin mu gani."
  Ta saki hannunta ta fara takawa a hankali zuwa gurbin da mahaucin yake.
  Ita ma ta ɗan ja baya tana leƙenta ƙirjinta na matsanancin bugu. A lokacin ne ƙyallen da ta saki daga tsaye ya dira jikin jinin da ke malale a bakin rariyar, ta ja baya tana ganin lokacin da jinin ya yi wata irin kumfa yana tattare kansa guri guda ya dunƙule kamar curarriyar fura ya saita kansa zuwa saitin inda aka yanka wuyan ragon! Tamkar an saka gam an haɗe wuyan ragon haka ragon ya zabura ya yi fatali da mahaucin da ke duƙe kansa ya miƙe tsaye ya yi wata irin girgiza yana kallon saitin da Hamdiyya take, idanuwansu suka haɗu guri guda, kafin kuma shi da ƙyallen su ɓace ɓat! Tamkar ɗaukewar ruwan sama a tsakiyar sahara. Wuƙar hannun mahaucin ta silale daga hannunsa ta iso dandaryar ƙasar, daga bisani shi ma ya kife kanta a sume. Hamdiyya da Hadiyya suka runtuma ɗaki a guje suna sakin ihun kuka da kururuwa.
  "Rago ya ɓace!"
  "Rago ya miƙe ya haɗe kansa!!".
  Shi ne ɗaukacin abinda mutunen gidan sunan ke furtawa suna sheƙawa a guje da rige-rigen ficewa daga gidan.
  *** ***  Mu hadu a SHAFI Na uku.

  *FIKRAH WRITER'S ASSOCIATION*

  Had'akar fikrarrun marubuta guda uku sun sake zuwa muku da zafafan littattafai. *Rufaida Omar* da littafinta *RUMFAR KARA.* *Bingel Mita* da littafinta *HA'KABIYYA (Tsiya da wasali).* Sai *Fareedah Abdallah* da littafinta *BILHAQQI.*
  Kar dai ku manta fikrarrun matan basu fi saura ba amma rubutunsu daban yake da na saura, alk'alumansu na da matuk'ar kaifi gurin isar da sak'o, sun k'ware a wajen nuni cikin nishadi.

  Za a samu damar karanta littafan ne bayan an biya *N700* ta wannan acc no din 0452523875 Rufaida Umar Ibrahim. Gt bank.
  Idan kuma littafi daya ake so a cikin uku sai a tura *N300* kacal sannan a tura screenshot na shaidar biya ga daya daga cikin marubutan ta wadannan lambobin
  09077591726
  08038250500
  +249924524019
  Ga mai bukatar tura katin waya ma kofa a bude take, za ta iya turawa daya daga cikin marubutan.

Comments

1 comment