Makalu

Blogs » Kagaggun Labarai » TSIYA DA WASALI: SHAFI NA UKU

TSIYA DA WASALI: SHAFI NA UKU

 • *KANO 2018.*

  Idan har wannan duhun shi ne duhun kabarin da ya ji ana bada labarinsa a can wata duniya da ya gaza tuna ko da sunanta, to tabbas zai dawwama yana kiran a maido shi cikin duniyarsa shi kuma zai tafi ga wani tudu ko da na saman dutse ne ya yi ɗaki a bisansa ya shiga ya fara bautawa mahalliccinsa har i zuwa ranar kushewarsa!

  Ga dai bakinsa na motsi yana kira da dukkan ƙarfinsa a maida shi cikin rayuwarsa zai gyara gabaɗaya lefukansa sai dai fa a cikin kunnuwansa baya jin sautin muryarsa haka baya jin danshin hawayensa da yake jin saukarsu a dukkan wata gaɓa ta jikinsa. Bai san adadin daƙiƙun da ya kwashe a wannan yanayin ba ya dai ga sa'adda wani haske daga can wata kusurwa cikin kusurwowin da bai san yawansu ba ya bayyana tamkar ratsowar hasken rana a jikin hujjajjen labule. A cikin hasken ya hangi ƙafa, ƙafar ma irin ta mutum, sai dai an datseta daga jikin cinyarta da gangar jikinta. A jikin ƙafar akwai wani rufaffen takalmin danƙo irin wanda ya taɓa sani a wani wurin da tunaninsa ya gaza hasko masa. Tsoro da firgicinsa bai yawaita ba sai da ya hangi ƙafar na tahowa gare shi da wani irin taku mai ƙarfin da ke fita da sautin kukan mutum. Bai san ya juya cikin matsananin duhun yana zabga gudun bala'i ba sai da ya waiwaya ya hangi cinyar ta biyo shi ita da wannan hasken jini na bulbula daga gaɓar da aka rabata da gangar jikinta. Bai fahimci jinin shi ne hawayenta ba sai sa'adda ya ji wata murya da ta taho daga inda take na kiransa da ya maidata jikin cinyarta da gangar jikinta.  Cikin wani irin matsanancin firgici ya ƙara ƙaimin gudunsa a yayin da a kowane takunsa da zai ɗauke ƙafar ce ke sauke tata akai. A sa'adda ta cimma shi ne ta daka tsalle ta dake shi a baya ya faɗi tim! Ta gabansa haƙoransa na haɗuwa da ƙasan wurin suka yi nasu guri. Yana gani ƙafar ta tako ta jikinsa ta tsaya a tsakiyar ƙirjinsa tana tsiyayar jini, zugi da azabar raɗaɗin da yake ji a bakinsa ya hana shi taɓuka kome.
  "Kai MAIDA ni jikin cinyata jikin gangar jikina kafin ka mutu!"
  Ya ƙara jin sautin muryar ya fito daga saitin da ƙafar take. Runtse idanuwansa ya yi da ƙarfi ganin ƙafar ta sake daka wani tsalle za ta faɗo a jikinsa. Firgigit ya yi ya buɗe idanuwansa yana tashi zaune a matuƙar tsorace kan tafkeken gadon nasa  mamakin abinda ya saka shi komawa barci bayan sallar asuba na baibaye shi. Jikinsa na rawa ya kai hannunsa ya shafo bakinsa ya ji babu kome sai dai fa zai iya rantsewa da Allah kan ya ji ƙasa-ƙasa a tafin hannunsa, da sauri ya kunna fitilar gefen gadonsa yana ƙarewa jikinsa kallo, sai kuma ya miƙe ya shige cikin toilet ya tsaya gaban madubi yana kallon fuskarsa.
  A sannu ya dawo gefen gadon ya zauna yana riƙe kansa da hannu biyu jin kamar zai dare dan azabar damuwa. Ya daɗe yana ganin abubuwan tsoro da jin labarinsu sai dai fa bai taɓa cin karo da irin wannan ba ko a cikin tsatsunoyoyin mutanen farko. Abu ne muraran da ya gama sanin toshensa ake sake nuna masa har a cikin mafarkinsa. Shin me zai kira haka rahma ko baiwa? Ke nan ba ƙaramar baiwa ba ce ga mutumin da zai na ganin waɗanda ya zalunta a cikin mafarki? Ba kuma ƙaramar rahma ba ce ga mutumin da zai farka daga mafarkinsa ya dinga jin nadamar abinda ya aikata har ya janyo masa yin mummunan mafarkin na cukurkuɗa ruhinsa da gangar jikinsa. A cikin kansa yake jin girman haƙƙin mutumin da ya zalunta na masa gingiringim! A kuma kullum safiya a sa'adda hantsi ya dubi ludayi wani ƙunci da azabar ɓacin rai ke sabunta kansu cikin zuciyarsa har ya gagara kurɓar ruwa domin sanyaya ruhinsa, har kuma ya gagara yin mu'amala mai kyau da jama'arsa, har a dalilin haka baya iya fitowa daga gidansa sai bayan 12:00 na rana. Duk mene dalili? Saboda a irin wannan lokacin ne mutumin da ya zalunta ya rasa wani abu mai muhimmanci a halittarsa duk ta silarsa, silar son zuciyarsa, silar ƙaunarsa ga halittar da ta kawo shi cikin duniya. Halittar da duk abinda ya aikata dominta bai amfane shi da kome ba. Bai kuma ji kwanciyar hankalin da ya bazama cikin duniya domin dawwamar da shi a cikin rayuwarsu ta su uku kacal! Sama da shekaru ashirin(20) kenan.

  Shin wai ta yaya zai iya tsayuwa a gaban mutumin da ke amsa sunan Bawa Ɗan Malle domin neman gafararsa?Ba Bawa kaɗai ba, baya jin kafatanin zuri'ar Bawa za su dube shi da rahma. Sai dai fa ba zai gaji ba, yanzu ya fara nemansa da dukkan zuri'arsu, da taimakon ubangijinsa zai nemoshi ko da kuwa yana binne ne a ƙasan ƙasa dan ya nemi gafararsa, dan haka ya jawo wayar da ke gefensa ya latso number mutumin daya bawa  haƙƙin kula da masu shige da fice a can tsohon ƙauyensu domin kawai ya ji zuwan Bawa cikin garin duk da kuwa an tabbatar masa shekaru ashirin kenan ba a ƙara jin ɗoriyarsa ba tunda ya kwashi iyalinsa suka tafi. A cikin zuciyarsa yake jin wannan kiran da zai yi shi ne na ƙarshen da zai sada shi ga muradinsa!
  *** *** ***

  "In buɗe maka zuciyata?"
  Kyakkyawar santaleliyar budurwar ta furta daga bakin ƙofa.

  Da kallo ya bita har ta maida ƙofar office ɗin ta rufe ta taho ta ja kujerar kusa da shi ta zauna tana kafe shi da mayatattun idanuwanta.

  "Ina neman tsari..."
  Ya furta yana ci-gaba da duba tarin takardun gabansa, ganin ta yi shiru ya saka shi ɗagowa yana daɗa tamke fuska.

  "...Ki tashi ki tafi, kin fi kowa sanin abinda shigowarki nan ke haifarwa..."

  "Na shirya hakan, dan hakan ma na shigo, ina so inta maimaita shekarar idan har kana tare da ni anan."

  "Ba ki da hankali,  ki fita daga nan na ce ba maganar banza ba, bansan nuna ɓacin raina gareki na gaji da miki tsawa da hantara, na gaji da ganin mummunar fuskarki ta fitsara a gabana, ke ko kunya baki ji kaf makarantar nan sun san kina bibiyata, to ba wannan wasan na zo yi nan ba..."

  "Kullum sai ka faɗa mini haka, amma ana cewa watarana sai labari. Ni tambayarka na zo yi."

  "Game da me fa?"
  Ya furta yana tattare hankalinsa kanta fuskarsa a cunkushe.

  "Ɗazu na ganka kana satar kallona me ke nan? Sannan ka ƙi faɗa mini dalilinka na faɗar da ni a jarrabawa, shin dan na ƙara maimaita shekarar ne ka ci gaba da ganina ko?"

  Dafe kansa ya yi cike da nadamar zamansa a office din har ta same shi, shi kam koyarwar nan ƙoƙari take ta zame masa Annoba,  yarinyar ta gama shiga rayuwarsa ta gama tsaya masa a duk inda bai zata ba a tun ranar da ya fara lecturing a makarantar. Ya rasa waye ubanta a garin na Kano da aka kasa ɗaukar matakin abinda take masa ko da ya faɗawa manyansa na jami'ar, shi ba gwanin wulaqanci ba amma da ƙarfin tuwo sai da ta koya masa yake yarfa mata shi a cikin mutane sai dai fa babu alamar yana damunta. Lokaci ya yi da ya kamata shi ya ɗauki mataki da kansa, dan haka ya ɗago yana dubanta a ƙuntace.

  "Ina ne gidanku?  Ya kamata na ga Babanki."

  Ta washe masa jerarrun fararen haƙoranta.
  "Ƙara ta za ka kai gunsa ko? To gashi..."

  Ta furta tana zira hannu cikin jakarta ta fiddo da wani kati mai kyau da aka ƙawata shi da ruwan zaiba ta aje masa gabansa.

  "...Amma dan Allah ka faɗi kome banda zuwa office ɗinka da nake yi..."

  Ta furta a marairaice, sai kuma ta ɗan duƙo gabansa tamkar mai tsoron wani ya ji abinda za ta faɗa, ƙamshin fitinan nan turarenta ya surare zuwa cikin hancinsa har sai da ya lumshe ido ya buɗe cikin nata da suke wani irin maiƙo dan kyau.

  "...Idan Mami ta ji wannan labarin wallahi sai ta kusa karyani. Kai kanka kasan ba wahalar karyewa zan yi ba dan kuwa ka sha yi mini ba'ar ƙafafuwana kamar na Barewa..."
  "Oh! Ni kuwa wai ina ka taɓa ganin Barewar da kake mini ba a da ita...?"
  Ta furta tana mai cije laɓɓanta na kasa a hankali, sai kuma ta ƙara wara idanuwanta tana daɗa duƙowa gabansa tamkar mai son haɗa hanci da shi.
  "...To dan haka ka rufa mini asiri yadda na saba rufa maka..."

  "Ni kike rufawa asiri dan baki da kunya?"
  Ya furta da zallar mamaki yana saka hannu ya harba katin ya yi nasa guri.

  "To so nawa wai? Ko ɗazun da na ganka kana satar kallona ai ban faɗawa wani ba, haka rannan da na ganka kana kallon tafiyata ban faɗawa wani ba. To ko rannan da ka turo mini goodnight ta number da ban sani ba ai ko Hanifa ban faɗawa ba duk kuma ina haka ne dan kar na zubar maka da ajin da kake ta riritawa."
  Ta ƙarasa tana langaɓe kai.
  _Aji?_ ya furta a ƙasan ransa yana jin dariya-dariya na kama shi, sai dai da sauri ya gintse tuna wacece a gabansa.
  "Haƙabiyya sunanki ko...?"
  "Kullum sai ka manta sunana, wayyo duniya, Ya Allah na roƙe ƙa da girman zatinka ka zare soyayyar wannan bawa naka daga zuciyata ka sanya finta a cikin zuciyarsa."
  Ta faɗa tana saka hannu bibbiyu ta riƙe kumatukanta.
  Ya buɗe bakinsa sosai yana dubanta, ya daɗe yana saƙa yarinyar ba lafiya take ba bai taɓa jaddada zatonsa ba sai yau. Ga mamakinsa sai ya ji hannunsa a ƙirjinsa yana shafa saitin zuciyarsa.
  "Allah ya tsare ni da wannan mugun fatan naki, ki tashi ki tafi daga nan kina haddasa mini ciwon kai da wannan turaren naki mai warin tafarnuwa! Sannan rashin muhimmancinki gare ni yasa ba na iya ko riƙe sunanki, ya kamata ki gane ni ba Malamin da zan tsaya soyayya da dalibata yarinya ƙarama marar kunya kamarki ba ne. Wai shin a ina kike koyan wannan fitsarar? A ina kamarki tasan ta dubi tsabar idon namiji duk girmansa ta furta tana sonsa...?"
  "Sir a dubu biyu da sha takwas (2018)  muke ba a dubu ɗaya da ɗari tara da casa'in da takwas (1998) ba, sannan boarding school na yi fa inda ake gudanar da rayuwa fiye da kala ɗari, to ko kafin na gama aji uku na ƙaramar sakandiren malamai biyar suka ce suna so na nasa ƙafa na ture saboda Allah ya riga da ya ƙaddara ni taka ce. Sa'annan ni ba yarinya ba ce ba za ka gane ba ne, to ko in miƙe ka ga tsayina? Shekaru ashirin fa saboda Allah haba Sir ya kake kallo nane a idonka?"
  Ya ƙanƙance ido yana kallonta kansa na daɗa tamkewa da mamakin da take bashi a duk buɗe bakin da za ta yi.
  Tabbas ba yarinya ba ce a gurin kowane ingarman namiji irinsa, sai dai fa ta yi yarinya ace kamarta ta iya bibiyar namiji da wani shirmen soyayya.
  "Ka damu na tafi ko...?"
  Ta furta a sanyaye tana miƙewa tsaye.
  "... Zan tafi amma idan ka faɗa mini wannan kalmar."
  "Wacce fa?"
  "Wacce nake faɗa maka kullum."
  "Bansanta ba."
  Ya furta yana buɗe wani ƙaton text book da ke gabansa.
  "Sir Please... Ko sau ɗaya ne..."
  "Ba sunana Sir ba, ki kirani Huzaif ɗina kawai, Sir ai ba a kawo masa wargin ana sonsa."
  "Dan ALLAH, ka ji...?"
  "Ya Rabbi!"
  Ya furta yana bubbuga biron hannunsa a goshinsa. Sai kuma ya tsura mata ido ganin yadda ta wani narke kamar mai shirin kuka.
  "Idan na faɗa za ki kyaleni ko na wata guda ne?"
  Murmushi ta yi da ya tsinka zuciyarsa, ya kai hannunsa kamar zai taɓa nata da ke aje gefensa sai kuma ya share.
  "Idan har ka faɗa ne daga zuciyarka zan kyaleka iya yadda kake so.
  "To Haƙabiyya kina burgeni. Shi kenan?"
  "Shi kenan kam, na tafi to. Amma kar fa ka manta ina ƙaunarka sosan gaske, ba kuma za ka taɓa samun iri na ba. Haka ba zan taɓa manta ka ce ina burge ka ba"
  Daga haka ta juya akan takunta mai cike da kwarkwasa. Ya bi bayanta da kallo har ta buɗe ƙofar ta fita, sai dai fa kafin ya sauke wani kwakkwaran numfashin ƙofar ta sake buɗewa sai gata ta leƙo tana haske shi da murmushin da ke tsaya masa arai ya hana shi sukuni har cikin barcinsa.
  "Sir faɗa mini gaskiya, da na juya bin bayana ka yi da kallo ko..?"
  Da ƙarfi ya daki teburin gabansa yana miƙewa tsaye.
  Ba shiri ta rufe ƙofar tana dariya. Ya koma daɓass ya zauna yana riƙe kansa, sai yanzu kalamanta suka dawo cikin kunnuwansa, murmushin gefen baki ya ƙuɓce masa, wai _ba zai taɓa samun kamarta ba._ Ko waya faɗa mata akwai mace a gabansa? Shi baya buƙatar a so shi baya kuma buƙatar ya so wani. Shi fa kwata-kwata bai ma kawo zama da mace a lamarinsa idan har ba wani mutum guda da ke cikin rayuwarsa ya ga ya zama irin abinda yake so ba, ya ga ya samu macen da za ta kula da shi har ƙarshen zamansu. A sannan ne yake jin zai iya duba me zai yiwa kansa idan lokacin bai ƙure masa ba.
  *
       Kai tsaye gurin ƙawarta Hanifa ta yi da ke tsaye bakin gate tana ta jiranta. Da gudu ta ƙarasa ta ruƙunƙumeta tana tsungulinta.
  "Keee! Kinsan Allah plan ɗinki ya mugun yi, ke kinga yadda ya rikice ya gigice yana rawar mazari tamkar Michel a club?"
  Hanifa ta tureta tana harararta cikin wasa.
  "To sau nawa dama na faɗa miki kika ƙi ji? Ai fa ki daina bari yana treating ɗinki kamar wata yar 14, ki nuna masa kin isa macen da ke buƙatar irinsa cikin rayuwarki ba shi ba ma ke ko da sa'an Babansa za ki iya gog..."
  Ta yi sauri ta rufe mata baki tana janta gefe.
  "Ban fa san ɗanyar balagarki, ni ki faɗa mini mene tsarin goben?Allah har yanzu ji nake kamar na koma, ke har fa miƙo hannu ya yi kamar zai taɓa ni ya fasa, ya rabbi! I'll never forget this moment...!"
  Ta dakata tana lumshe idanuwana.
  "...Ko ya zan ji hannunsa? Ina feeling kamar ya kai taushin na Gebriel na cikin novel din(The boss takes his wife)."
  "Ko kamar bayan kada ne haka zai taɓa ki da shi."
  "Eh na ji ina sonsa a hakan ma. Ni ki faɗa mini tsarin goben na ƙagu ɗan mitsitisin bakinsa ya furta yana so na."
  "Lokaci ne fa zai zo, ko a yanzu akwai wacce ta isa ta yi daɗewar da kike yi a gunsa idan?"
  "Kai kai Hanifa kina gigita Ni fa, ke kaɗai ke ba ni tabbacin wataran Huzaif nawa ne."
  Yauwa to bari kiji tsarin, ta lalubi kunnanta ta raɗa mata. Ta daɗe shiru, sai kuma can ta mata murmushi adaidai lokacin da direbanta ya ƙara so.
  "Shi kenan to mu haɗe goben." Daga haka ta shige motar suka yi gida.
    Tun a falon ƙasa take kwala mata kira, ganin ba ta ganta ba ya saka ta hawa sama zuwa cikin ɗakinta nan ma bata nan. Ɓangaren Abbansu ta yi sai dai fa tunda ta doshi hanyar da za ta kaita bedroom ɗinsa take Jin hayaniya. Dan haka ta ƙarasa saɗaf-saɗaf ta tsaya a bakin ƙofa tana saurararsu.
  "Ni ba hanaki neman Hamidu na yi ba, mummunan ƙudurinki kansa nake so ki cire. Zawwa! Ba fa da wannan alƙawarin muka baro ƙauye ba, kar ki zama cikin mutanen da Allah ke la'anta saboda rashin cika alƙawarinsu. Shin wai ba cewa kika yi har abada ba ki sake ambato mini sunansa ba? To menene ya yi zafi da tun farkon shigarmu shekarar nan har yau da muke ƙarshenta  kika tsiri tada mini hankali kan lamarinsa?"
     "Ni fa har abada ɗin da na ce na nufin har Hamidu ya nemo mu domin yafiya. Ban za ci yana da zuciyar da zai kwashi shekaru ashirin ba tare da ya neme ka kan haƙƙin ka ba ban za ta ba wallahi. Haka a yanzu ne yarinyar ta yi girman da za ta iya kama mini zuciyar namiji kome shekarunsa, dan haka Bawa sai dai ka yi haƙuri ba zan iya yafewa Hamidu ba har abada, alƙawari na ɗauka sai na nemo shi na dasa masa ciwon da ni kaɗai ke da maganinsa. Sai na dasa masa dafin ƙaunar yarinyar nan na barshi ya same ta a ƙarƙashin inuwarsa na tsahon kwana uku kacal!A bayan ya mallaka mana dukkan abinda ya mallaka ta dalilinmu a sannan kuma zan saka kakkaifar adda na datse alaƙar da na haɗa ɗin na maida shi ɗan kwikwoyin da zai na bibiyata kullum safiya yana tanɗar tafin ƙafata har ƙarshen rayuwarsa..."
  "Kin yarda ki maida diyarki bazawara saboda son zuciyarki Zawwa ki kashe rayuwar yarinya ƙarama?"
  Ya furta da zallar mamaki, a karo na farko da ya ji tsoron ƙiyayya irin tata na damunsa.
  Sakar masa wani murmushi ta yi da iyakarsa fatar baki a bayan ta saka siraran yatsunta ta ɗauke kwallar idonta. A sannu ta miƙe daga inda take ta isa gabansa tana sanya hannu ta  janye rigarsa da ta rufe dungulmin ƙafarsa, ta tsura mata ido na 'yan mintuna tana kallo kafin kuma ta ɗora hannunta a kanta, ta runtse ido ta buɗe su cikin na Tsoho Bawa da ke dubanta a tsumaye.
  "Ba zan tozarta rayuwarta ba duk da ya tozarta tawa ya maidani matar nakasasshe. Idan ana neman haihuwa domin barin baya, barin wanda zai maka addu'a, barin wanda za a kira a ce jininka ne, kasani a yau zan faɗa maka wani abu da baka sani ba, ni na  shafe shekaru biyu cif ina neman haihuwa irin ta ɗiya mace domin kawai ta ɗaukar mini fansa kan abinda Amininka ya mana. Bawa ko ina da niyyar yafewa Hamidu wallahi da Allah na yi rantsuwa ba zan yafe masa tunda har aka shafe shekaru ashirin bai waiwayemu. Dan haka kabar mana mugun tun..."
  "Kenan ba ki tsoron reshe ya juye da Mujiya?..."
  Ya tari numfashinta yana haki.
  "...Ba ki kuma tsoron ƙaddarar da za ta haɗa abinda ke ko ni ba za mu iya hanawa ba balle rabawa. Ba ki tsoron jarabtar da za ta saka ita ɗiyar taki ta dubi tsabar idon ki ta ce miki bata rabuwa da Hamidu ba kuma ta mallaka miki dukiyar Hamidu? Zawwa na tabbata a ranar fashewa za ki yi namanki ya yi ɗaiɗai a dandaryar ƙasa saboda baƙar ƙiyayyar da ke lulluɓe a ruhinki, ni kam ba ni da ƙafar da zan tashi na tattara namanki domin kai ki makwancinki ina dai da bakin da zan buɗe domin yi miki dariya. Kar ki fara wannan wasan, kar ki fara abinda baki san ƙarshen sa ba idan har na isa mi..."
  "Ka isa! Amma ka sani idan har ta rayu a ɗumina tsahon shekaru ashirin, ta tsotsi hallittar nan biyu da ke tsakanin ƙirjina ba za ta taɓa ture abinda nake so ba, ba kuma za ta zambace ni ba irin yadda Aminka ya yi. To balle ma na buɗe bakina na faɗa mata shi ne sanadin rasa ƙafarka guda ɗaya. Shin wata ɗiya ce ta halak da za ta ji wannan ta kasa ɗaukar fansa?"
  Murmushi ya sakar mata mai ciwo yana daɗa auna shekarunta cikin hankalinsa.
  "Shi kenan Zawwa je ki nemi Hamidu ki aura masa Haƙabiyya bisa ƙudurinki. Ni Bawa ba zan sake tunasar da ke ko ƙoƙarin hanawa ba. Zan dai dawwama yi miki addu'ar samun nasara. Allah Ya baki sa'a."
     Haƙabiyya da ke laɓe bakin ƙofar ta dafe ƙirjinta tana ambaton sunan Huzaif cikin zuciyarta. Sai kuma ta zare ido tana girgiza kai, inaa! Dole nema ta turo shi gidansu ya nemi aurenta kafin Mami ta gano mutumin da take nema ta aura mata. Ta ƙara jingina kanta sosai jikin ƙofar ko za ta jiyo suna wani ƙusƙus ɗin, ba ta san ta taso za ta fito ba sai da ta buɗe ƙofar ta kuwa ta fi luuu za ta faɗa ta tare ta a jikinta tana kallonta cike da zargi. Da sauri ta ƙaƙalo murmushi tana yatsina fuska sai kuma ta riƙe saitin goshinta.
  "Mami Allah goshina ciwo yake, wayyo zai rabe."
  Ta furta a marairaice tana yarfe hannu.
  "Ciwon kan ne sai kin biyo ni har nan? Ina magungunan ɗakinki?"
  "Babu fa, ni dama faɗa miki zan yi gobe kar a tura mini driver zan dawo da kaina. Kakarsu Hanifa ce ta faɗo daga gujerarta ta gurɗe ƙafa, to za mu je dubo ta."
  Ta ƙara kallonta tana nazarinta kamar me son ganin wani abu.
  "To ba za ki je ba..."
  "Mami... Dan Allah mana...Washh.. kaina!"
  "Ya ki Autata, ƙyaleta zo ki zauna nan ina da maganin ciwon kai a drawer."
  Tsoho Bawa ya furta yana yafitota.
  Da sauri ta tafi gunsa ta zauna tana tankwashe ƙafa.
  Zawwa ta bisu da ido sai kuma ta taɓe baki ta fice daga ɗakin.
  "A ina ne shi gidan Kakar tasu yake.?"
   "Nassarawa."
  "To shi kenan Allah ya kaimu sai kuje, amma kar ki yi maghriba."
  _yesss_.  Ta furta cikin ranta tana jin daga gobe burinta zai ida cika.     
  [19/12/2019, 11:22 am] Lady BINGEL\ud83d\udc0d: @LamtanaB
  *** *** ***
  Acan cikin wani ɗaki da aka gina a ƙarƙashin ƙasa a tsakiyar wani baƙin daji dake yamma da wata kushewa. Wata ƙwarya ce da ke cike da wani baƙin jini ta fara girgiza tana darewa, jinin cikinta ya fara toroƙo yana zaɓalɓala tamkar yana bisa garwashi, kafin kuma ta tarwatse gabaɗaya jinin ya fallatsa a ilahirin farin mayanin da aka kewaye ɗakin da shi, a sannan ne Ragon ya bayyana yana kuka, sai kuma ya yi tsit! Yana tsurawa mutumin da ke zaune acan kursuwar ɗakin kan wata baƙar kujera ido, a hankali kuma ya durƙushe a gurin yana kafa ƙahonsa a ƙasa tamkar wanda ya yi tozali da manyan dawa.
  Mutumin da yake dattijo baƙi, mummuna na haƙiƙa ya miƙe tsaye hannunsa dafe da wata baƙar sanda da aka sassaƙa mariƙinta da siffar kan mujiya. Ya taka a hankali zuwa gaban ragon ya ja ya tsaya idanuwansa a rufe. Ya buɗe baki ya fara furta wasu irin kalmomi yana kiran wani suna, ba daɗewa wanda yake kiran ya bayyana a gabansa ta cikin wani duhu, a sannan ne ya yi shiru ya buɗe idanuwansa yana kallonsa.
  "Abinda muke aikinsa sama da shekaru ne ka turo mana Rago a madadinsa?"
  "Ayi haƙuri kuskure ne..."
  "Ba ma aiki da kuskure...!"
  Ya furta da tsawa har sai da mutumin ya ja baya.
  "...Da wannan kuskuren naka za ka rasa abinda ka fi so a duka rayuwarka, kar ka manta numfashinta tamkar kwan jimina yake a hannuna, a kowane lokacin da na tunzura zan iya sakinsa ya tarwatse a gaban idanuwanka. Na baka mako guda da ka kawo mini wannan yarinyar tunda har ta riga da ta taɓa wannan ƙyallen, idan ka kuskure hakan ka fi kowa sanin irin jinyar da zan iya saukar mata da sunanka!"
  "Zan kawo ta ko gobe ka ce, amma a ɗan daɗa ba ni lokaci na ƙarshe, a kuma duba wannan alfarmar da na nema, a duba darajar addinina tunda an umarci na nemi wani 'yancin... Zan kawo ta cikin biyayya da dukkan abinda kake so."
  Dattijon ya juya ba tare da ya ce masa uffan ba ya koma kujerarsa ya zauna ya rufe idanuwansa. Sai can ya ɗaga masa hannu alamun ya tafi ya gama magana da shi.
  *** ***

  Tun sa'adda ragon ya ci laya, hankalin tsiraran mutanen unguwar ya ƙi kwanciya har sai da aka tattaro malaman unguwar suka dinga karatun Qur'ani kusurwa-kusurwa. Sai dai fa har ƙarfe bakwai na dare Hamdiyya ba ta dawo hayyacinta ba, sai dai Hadiyya da ta fara nutsuwa tana ta basu labarin abinda ya faru da daɗewar da Hamdiyya ta yi da Huzaif ba tare da tasan wane ne shi ba.
  Sai wuraren ƙarfe tara na dare ta buɗe idanuwanta suka sauka kan matar Kawu da ke gyangyaɗi, ai sai ta miƙe firgigit ta rungumeta tana sakin kuka.
  "Yanzu da ni ce na yi amfani da yankin da shi kenan ni zan ɓace ko. Wayyo Huzaif! Na tabbata yaudararsa suka..."
  "Ki ka ƙara kira mini wannan sunan sai na tattakaki a wurin nan wawiyar yarinya kawai."
  Kawu da ke gefe a tsaye ya faɗa a fusace yana zare takalmin ƙafarsa ya yi gunta. Da sauri matar ta sha gabansa tana girgiza masa kai.
  "Kinsan Allah Hanne banda dare ya yi da a yanzun za ta bar garin nan, ta tafi can Kaduna gurin Iya ta zauna kafin lokacin aurensu da Haruna."
  "A dai yi haƙuri zuwa safiyar, har da yarinta fa Maigida."
  "Ba wani yarinta sai wannan shegiyar bokon da na bar ta ta yi, ai duk  Haruna ya jawo na sanyata, sai yanzu nake nadamar dama tun tana 12 na kulleta a ɗakin mijinta, za ki bar kallona ko sai na fauɗeki shashasha wacce aka yi rabon kunya da mutunci babu ita."
  Da sauri ta sauke idanuwanta ƙasa tana daɗa ɓoyewa  a bayan Haule.
  Shiru suka yi gabaɗaya har ya gama ɓaɓatunsa ya fice.
  Sai dai fa da sassafe ya ce ta haɗa kayanta su tafi. Haka ta haɗa tana ta kuka, ita ba abinda ya fi ɗaga mata irin ta samu damar ganin Huzaif kafin su tafi. Ta sani har a ƙasan zuciyarta da ace Huzaif yasan Manager yaudararsa ya yi ba zai taɓa ma karɓar ƙyallen ba. Ita tsoronta ɗaya ma kar su gaji su zuƙe jininsa ba tare da ya sani ba. Tuna hakan ya sakata ƙara rushewa da kuka tana ɗora hannu aka. Kawu ya ja tsaki mai ƙarfi yasa hannu ya zuba mata wani ranƙwashi a tsakiyar kai. Da sauri ta haɗiye kukanta sai ajiyar zuciya har suka isa Kadunan.

         Ko da ya danƙata a hannun Iyan da ita kaɗai ta rage musu babba a zuri'ar, ƙanwar Uba take gare su. Ya daɗe yana roƙonta da ko shago kar ta sake ta tura ta, ta barta anan gida ta sakar mata dukkan aikace-aikacenta. Anan suka yi sallama ya juya ba tare da ƙara duban shiyyar da Hamdiyyar take ba. Ganin haka ya saka jikinta sanyi ta miƙe da gudu tasha gabansa tana sanya gwowowinta a ƙasa cikin hawayen da ta kasa hana zubarsu.
  "Kawu dan Allah kar ka tafi, Allah ji nake kana tafiya zan mutu, Kawu ka yafe mini domin Allah ka ji ƙaina ka rabani da nan."
  Zuciyarsa ta tsinke, jikinsa ya yi sanyi gabaɗaya, sai ya yi tsai! Yana duban kyakkyawar fuskarta a kaikaice.
  "Hamdiyya, me kika nema kika rasa a gurina da ba za ki iya yi mini abinda nake so ba?"
  "Babu Kawu, ka yi hakuri na daina, zan yi duk abinda kake so, amma ka maida ni gunka, ba na son hutun nan."
  "Dainawa ɗaya ce ita ce ki haƙura da wannan yaron ki bar tuna sa, wallahi kinga da girmana na rantse miki ba alheri ba ne gareki. Yanzu idan kika ce mini kin haƙura da shi ba zan barki anan ba tare za mu koma. Za ki iya haƙura?"
  Shiru ta yi sai wasu zafafan hawaye da ke sintiri a saman fuskarta.
  "Magana nake miki, za ki iya haƙura da shi?"
  "Kawu na tabbata shi ma yaudararsa aka yi, bai san..."
  Ganin fuskarsa ta canja ya sakata haɗiye kalamanta ta miƙe ta juya kawai zuwa cikin gidan.
  Ya daɗe tsaye yana ƙissima yanayin yarinyar, yana ji kamar zai yi wani kuskure, kamar ya bata dama ya yi magana da yaron ko zai gane wani abin. Sai dai kuma da ya tuna wasiyyar mahaifinta sai kawai yasa kai ya fita daga zauren yana mamakin abinda ya sanya jikinsa rawa tako'ina.
  Ya daɗe zaune daga can nesa yana hango gidan kafin ya tashi ya tafi a hankali tamkar mai jiran tsammanin wani zai iya kiransa, sai dai har yasha kwanar layin hakan ba ta faru ba, a hankali ya sauke ajiyar zuciya yana jin wani yanayi marar daɗi na ratsa shi, kafin kuma ya ɗaga ƙafa zuwa tashar da za ta sada shi da garinsu.
  Wani abu da bai sani ba shi ne, ya kawo ta inda ba zai ƙara tozali da ita ba har abada! Ta yiwu da ya yi haƙuri ya barta a gabansa da ƙaddararta ba ta yi musu yankan ƙauna ba!
  *** ***

  A cikin wata biyun da ta kwashe gaban Iya ba ƙaramar gwagwarmaya aka sha ba. Sai dai a hankali ta fara manta wasu abubuwan da yawa, yayin da ta wani ɓangaren take gasgata zancen iya da kullum ke jaddada mata Huzaif yaudararta ya yi zai maida kanta kuɗi, shi ɗin ɗan mafiya ne matsafi, da ace ba shi ba ne da tuni ya neme ta ko da kuwa a birnin sin take ɓoye. Iya har alƙawari ta mata idan har Huzaifu ya bayyana kansa a gidanta kafin cikarta mako huɗu ita da kanta za ta sanya a ɗaura musu aure. Sai dai har watan ya ƙare babu shi babu alamarsa. Wannan abin ya ɗaga mata hankali ta yadda ba ta iya kwanciya saman filo ba tare da ta jiƙe shi da ruwan hawaye ba, tana tuna kalamansa, tana tuna sanyayyar muryarsa a yayin da yake jaddada mata irin soyayyar da yake mata, tana tuna kome na halittarsa. Kai tasha ta zo cin abinci ta ganshi tsaye a gabanta sai ta miƙa hannu za ta taɓa shi ta ji ta cafki iska.
  Ita fa babban burinta shi ne ta yi tozali da shi ta tambaye shi dalilinta na zaɓarta a matsayin abar wasansa, ta kuma tabbatar masa da har ya mutu ba zai taɓa samun wacce za ta ƙauna ce shi domin Allah irin ta ba, wani irin zafinsa ta fara ji da jin haushinsa, a karo na farko tun haɗuwarsu sama da shekara gudu da ta ji haushinsa cikin ranta.
  *
         A hankali take takawa zuwa 'yar kasuwar da Iya ta aiketa siyo bushasshen kifi, ranta a cunkushe yake sai harare-harare take ita kaɗai tana zoɓara baki sama. Cike take da jin haushin yadda har wata biyu Kawu bai zo ya ganta ba bare ta ji inda maganar aurenta da Yaya take. Ji take ita ma idan za ta shekara anan ba za ta taɓa nemansu ba suje can su ƙarata. Can kuma wata zuciyar ta zungureta da dama iyayenta suna nan...Tuna hakan yasa ta ja ta tsaya a gefen hanya a cikin idanuwanta take hasko yadda suke ƙaunarta, tana jin da ace suna nan da ba za su taɓa hana ta abinda take so ba, ba za su iya mantawa da ita har tsayin wata biyu ba. Hawaye suka fara ɗiga a gaban hijabinta, ta yi sauri ta ja gefen hijabin tana sharewa. A sannan ne ta ji an finciketa ta baya an jata da ƙarfi zuwa wani lungu da baya ɓullewa, ta buɗe baki za ta kwala ihu ta ji anyi wuf! An toshe mata bakin an haɗata da garu. Runtse idanuwanta ta yi da ƙarfi tana jin yadda zazzafan hucin mutumin ke sauka a fuskarta. Jin shiru ba a ce kome ba sai toshe mata baki da aka yi yasa ta buɗe idon ta sauke su a cikin nasa da suka canja kala sosai da wani irin yanayi da ta kasa wassafa shi.
  "Huzaif!" Ta furta can a ƙasan maƙoshi, a yayin da shi ma ya zame hannunsa yana dubanta a sanyaye.
  "Bazan iya jurewa ba, me yasa kike kuka, cikin satin nan kaf ina bibiye da ke kullum sai kin yi kuka, ni ne ko?"
  Kasa magana ta yi jin ya ma raina mata hankali. Da ƙyar ta danne zuciyarta tana jin ba za ta ƙara zubar da hawaye a gabansa ba.
  "Ki yi hakuri...Ban sani ba, ban san kina nan ba, ban san me ya faru ba. Allah shaida na wahala gun nemenki Hamdiyya.."
  Ya furta yana ɗora hannunsa a kafaɗunta.
  Cije bakinta ta yi tana jin wani zafin rai na mamayarta, da ƙarfi tasa hannuwanta ta ture nasa tana dubansa a zafafe, sai dai fa ta kasa ɗauke idonta kansa, haka ta gagara buɗe baki ta ce wani abu, gani take tana furta ko menene zai ga logonto, dan haka ta yi gefe za ta fice daga lungun ya yi saurin saka hannayensa ya dafe bangon ta zama a tsakiyarsa har suna jin zazzafan hucin junansa.
  "Ba za ki yarda ba ko...? Ba za ki sake yarda da ni ba ko...? Me zan miki ne...?"
  Ya yi shiru yana tura laɓɓansa na ƙasa cikinsa.
  A idonta sai taga ya mata wani irin kyau mai sanyin kallo, zuciyarta ta fara nutsuwa, sai kawai ta kauda kanta gefe tana jin ta faru ta ƙare...
  "...In rantse miki Hamdiyya...?"
  "Wallahi summa tallahi bansan kina garin nan ba sai a cikin satin nan. A tun ranar da muka rabu ban ƙara samun lafiya ba sai a..."
  Kayya! Zo muje dai..."
  Sai kawai ya jawo hannunta suka fito daga langun ta kuwa biyo shi kamar jela, ganin suna dosar titi ya sa ta fara ƙoƙarin tirjewa.
  "Ko da ace ni abinda kike za ta ne ba zan taɓa sai da jininki ba. Ko da ace Baba nane shugaban masu tsafi na duka duniya ba zan taɓa bari wani ya taɓa ki ba balle ni kaina. Ko da kuwa ace a dalilinki ni zan rasa tawa rayuwar ba zan iya ba Hamdiyya ba, ba zan taɓa iya cutar da ke har haka ba. Ki yarda da Ni!"
  A cikin sautinsa ta gama gasgata dukkan abinda ya faɗa ya fito ne tun daga lungun zuciyarsa. Jikinta ya yi sanyi gabaɗaya, a karo na farko da ta ji ta munafunce shi da har ta iya zaton zai iya yaudararta. Sadda kanta kawai ta yi ƙasa ta ci gaba da maida sahunta a duk inda ya ɗauke nasa.
      Basu wani daɗe suna tafiya ba suka zo inda ya sauka. Gidan ya ƙeru sosai har sai da ta ɗago da mamaki tana kallonsa, ya mata wani murmushi mai kama da yaƙe ya buɗe gidan suka shiga. Tsayawa ta yi tana ƙarewa tsararren falon kallo, shi kuma ya tafi ga fridge ya ɗauko ruwa ya zauna yana sha.
  "Bari ki ga na fita na kira yaro a gabanki zan aike shi ya samo miki ruwan sha, na san ba lalle ki sha na gidan nan ba."
  Yi ta yi kamar ba ta ji shi ba ta miƙe ta isa ga fridge ɗin ta buɗe ta ɗauko ruwan mai sanyi ta fara sha. A hankali ta lumshe idanuwanta  jin yadda sanyin ruwan ke tafiya da duk wata damuwarta. A daidai nan ta ji tsayuwarsa kusa da ita, sai kuma ya sunkuya a gabanta hannunsa ɗauke da Alƙur'ani mai girma.
  Da mamaki take dubansa ganin ya dafe ƙur'anin yana dubanta.
  "Na rasa me zan yi ki dawo da kallonki gareni irin na baya... Na rasa me zance ki gasgata dukkan abinda zan furta. A cikin idanuwanki nake hango rashin yardar ki gareni, dan haka zan miki rantsuwa da abinda ba a taɓa wasa da shi a kowacce irin saɗara... Ya Allah ina roƙonka da girman littafinka mai tsarki, idan har nasan abinda ya faru da wannan baiwa taka ya Allah ka..."
  "Wai menene haka! Kasan me kake yi kuwa...?"
  Ta furta da tsawa tana sanya hannu ta ƙarɓe ƙur'anin ta ajiye shi a gefe.
  "Saboda ni sai ka rantse da Alƙur'ani kasan girman hakan kuwa?"
  "To wai ya kike so na yi? Kinsan yadda nake ji a duk lokacin da na dubi cikin idanuwanki na ga tarin shakku da zargi? ..."
  Ya furta a marairaice yana yatsine fuska kamar mace.
  Jikinta ta ji ya mutu gabaɗaya da wannan salon nasa, ba shiri ta lalubi kujera ta zauna tana doka masa harara.
  Ganin haka ya sa shi ma ya miƙe ya zauna kusa da ita, ta matsa ya matso ta ƙara matsawa ya ƙara matsowa har sai da suka kai ƙarshen kujerar da take haɗe ga bango. Ta yi wuf! Za ta miƙe yasa hannuwansa biyu ya jawota ta faɗo gefensa.
  "Wai me ye haka ne? Kar ka ƙara taɓani Ni ba halalinka ba ce, wai ma baka san an ɗauran aure ba ne?"
  Ta furta a tsiwace.
  Bai ce kome ba sai tagumi da ya rafka hannu bibbiyu yana dubanta.
  Share shi ta yi ganin haka yasa ya sauke tagumin ya numfasa.
  "Ki yi hakuri... domin Allah ki yi yafe mini."
  Sauke ajiyar zuciya ta yi tana ƙare masa kallo, sai yanzu ta kula da ramar da ya yi sosai. Jikinta ya daɗa sanyi tana jin kamar duk ita ce silar damuwarsa.
  "Ka daina ba ni haƙuri dan Allah, na fahimta fa, nasan kome, koma ince na fika sanin ba za ka taɓa iya aikata haka gareni ba, rai nane ya ɓaci da naga har wata biyu baka neme Ni ba Huzaif, ta yaya zan nutsu? Ta yaya ba zan yarda da saka hannunka ba?"
  "Ban san haka ta faru gare ki ba sai a satin nan biyu da suka gabata da na dinga zarya unguwarku ko zan ganki sai na haɗu da wannan ƙawartaki ta makaranta, daga yanayin yadda na ga tana dubana a tsorace nasan wani abu ya faru. Da ƙyar na samu ta saurareni ta ba ni labarin abinda ya faru. Kinsan a tun ranar da muka rabu ban ƙara yin lafiya ba sai bayan wata guda. Ni kaina ba abinda ke daɗa zafafa jinyata sai rashin ganinki tsawon wannan lokacin ba ki biyo sahuna ba kinga lafiya alhali duk sati muke haɗuwa. Babban tashin hankalina kar ya zamana anyi miki auren ne. Ban zaci zan tashi daga jinyar ba duk da bansan mafararta ba. Haka nan na wayi gari na ji bayana ya riƙe, jikina ya saki na gagara ko juyawa balle na iya tashi. Kwanana biyu a kwance cikin kashi da fitsari kafin Allah ya jeho wani maƙocina. Shi ya tsaya kai da fata wurin ganin na warke duk da  da ƙyar aka iyi samun maganin lalurar, a cewar masu maganin wai jifa na aka yi."
  Ya yi shiru ganin har ta fara sharce kwalla.
  Suka yi zuruu na tsayin lokaci kafin ita ma ta bashi labarin duk abinda ya faru har haushinsa da ta ji.
  "Hamdiyya ki yafe mini duk ni ne silar kome da na buɗe miki lararuta. Yanzu da wani abu ya same ki shin ta yaya zan iya yafewa kaina...?"
  Ya numfasa idanuwansa sun kaɗa jajur.
  Wani murmushin ƙarfin hali ta masa tana girgiza kai.
  "Kar ka ƙara tuna hakan balle ka kalleni da shi. Idan har za mu yi zaman da za mu ɓoyewa junanmu damuwarmu babu gaskiya kenan. Na roƙe ka da ka ɗauki hakan a ƙaddarar soyayyarmu, mu kuma gode Allah da wani mummunan abu bai faru gare mu ba, gobe sai ka ga ya saka mana da abu mafi alherin wannan, kar dai ka ƙara taka inda manager take, dole kuma ka dage da addu'ar neman tsari ga ire-irensu. Sannan roƙona ɗaya gare ka, dan Allah Huzaif ka duba maraicina, ka dubi yadda Kawu ke ƙoƙarin raba ni da kai amma na ƙi hakan saboda ƙaunarka ta domin Allah da nake yi, ka dubi girman zatin Allah kar ka taɓa yaudarata, idan ma kana da niyyar hakan ka tafi tun yanzu, ka tafi wuri mai nisa can da ba zan ƙara ganinka ba, idan ka yaudare ni a bayan wannan yardar da na baka bansan ya zan yi da rayuwata ba, wani irin so nake maka da ba na fatar na aure ka ba tare da na rage fiye da rabinsa ba..."
  Ta yi shiru tana kafe shi da idanuwa, tana kula da sa'adda wani abu mai nauyi ya gilma a cikin idanuwansa, sai dai fa kafin ta farga ta jita a tsakiyar ƙirjinsa ya ƙanƙameta. Mutsu-mutsu ta fara za ta kwace ya ƙara matseta tamkar zai karya ƙasusuwanta.
  "Ki bar ni dan Allah, kin ji?"
  Ya furta da wata irin murya da bata san shi da ita ba, sai taji kamar ba Huzaif ɗin da ta sani ba, kamar an mata musayansa da wata halittar irinsa mai tarin daraja gunsa.
  Sassauta riƙon da ya mata ya yi yana shafa bayanta. A hankali ya buɗe tafin hannunsa wata 'yar ƙaramar ƙwaya ruwan ɗorawa ta bayyana. Tsura mata ido ya yi yana ƙoƙarin maida kwallar idonsa da ya rasa dalilin tahowarta a daidai lokacin da dukkan burinsa ke gabda cika. A ransa yake jin tabbas da waccar dabarar gwara wannan tafi kusa da tafarkin tsira, tafi kusa kuma da samun nutsuwa a zuciyarsa. Zare jikinsa ya yi da ga nata ya ɗago yana kallon cikin idanuwanta har sai da ta ji kunya, a sannu ya buɗe baki ya hure mata idon. A tare suka dubi juna da wani tattausan murmushi.
  *** ***

  MU HADU A SHAFI NA Hudu.
  @Fulani Bingel

Comments

0 comments