Makalu

Blogs » Kagaggun Labarai » TSIYA DA WASALI: SHAFI NA HUDU

TSIYA DA WASALI: SHAFI NA HUDU

 • ***
  A karo na uku ya ƙara duba agogon hannunsa yana jan tsaki cikin zuciyarsa. Tattara takardun gabansa ya yi gefe, ya miƙe ya doshi bishiyar da yasan tana zama ita da abokan karatunta. Tun daga nesa ya san bata cikinsu dan haka yaja ya tsaya kansa na daɗa zafi. _To wai ta zo makarantar ɓoye masa take yi ne ko me?_. Ya ƙara ɗaga idonsa saitin bishiyar yana hango 'Yar baƙar ƙawarta Hanifa kamar ya tambayeta ina take amma tuna girmansa da ajinsa yasa ya fasa. Bai san tana da muhimmanci har haka a rayuwarsa ba sai yanzu, bai ma san yaudarar kansa yake da bata gabansa ba sai a yanzu da ya shafe awanni huɗu cur! Cikin makarantar bai ji ko da sautin dariyar ta ba balle ta kwankwasa masa ƙofa ta fara zuba masa wannan nacin nata mai tsaya masa arai ya hanashi sukuni cikin barcinsa. A jiya da ya ce mata ta kyale shi ko na wata guda ne har ransa da gaske yake baya buƙatarta. Sai dai fa a yanzu da ya fara fahimtar ta ɗau ƙudurin cika muradinsa ya fara tsorota. Sai ya ji kai shi fa nufinsa ta ƙyale shi da zuwar masa ofis, ba wai ta hana idanuwansa ganin taba. Har yanzu yana mamakin yadda ta ƙyaleshin, bai ma zaci za ta iya ba ganin yadda take yawan ce masa _soyayyarsa ta zame mata jarabar da bata iya barinta sai an haɗa mata da ruwan rubutun ayar haihaita haihaita limatu'aduna,_ to ko rubutun ta fara sha? Ya girgiza kansa da sauri yana bawa kansa dariya ganin zai koma irinta. Shi fa ba wai sonta yake yi ba ko wani abu, shi dai kawai baya so yaga rana ta zo ta wuce ba tare da ya yi tozali da ita ba, _ashe haka mata ke da abin mamaki?_. 'Yar ficiciyar yarinyar daya raina gashi nan ta barshi a tsakiyar rana tana ƙoƙarin ganin bayansa gurin nemanta. Yaja numfashi ya fesar yana kumbura bakinsa. Sai kuma ya zura hannunsa a aljihu ya fiddo da katin da ta bashi jiya. Ya tsura ma cikakken sunan da aka maƙala a adireshin ido yana rasa tuna inda ya san sunan. Juyawa ya yi kawai ya koma ofis ya zari mukullin motarsa ya fice. Baya jin zai iya bada lecture a wannan lokacin da ya fahimci kewarta na gabda saka shi kurma ihu a tsakiyar lakcarori 'yan uwansa.

  *** *** ***
  Ita kaɗaice tsaye gaban tangamemen mudubin tana ta zuba kwarkwasa. Ta jawo wannan riga ta gwada ta yasar gefe ta jawo wannan gyale ta yatsine fuska ta cukurkuɗa shi ta jefa bisa gado, haka tayi-tayi har sai da ta kusa ƙarar da kayan sif dinta kafin ta zakulo wata dakakkiyar rigar shadda irin me maiƙon nan. Ta sakata ta naɗa ɗauri ya zauna mata cif, ta ƙara kallon kanta a madubin ta tabbatar babu gurin kushewa kana ta jawo jakarta ta zira takalmanta ta fice tana ta baza uban ƙamshi.

  Taxi ta tare zuwa Lamiɗo CR da ke Nassarawa L.G.A, ba daɗewa suka isa har cikin unguwar, ta sauka ɗan nesa kaɗan da gidan ta tsaya cike da taraddadi tana hangen gate ɗin, haka kawai take jin wata kunya-kunya ko kuwa sanyin jikine na mamayarta. Ta ƙara kallon jikinta tana jijjiga kai, sam bata kula kwalliyar ta yi yawa ba sai yanzu. Ta zuba wata uwar shadda sai ka ce me zuwa gaida uwar miji irin zuwan farkon nan. Abin ma sai ya bata dariya ta murmusa kawai tana ɗaga kafaɗarta guda ɗaya alamun oho dai. Ta ɗaga ƙafa a hankali ta taka har zuwa bakin gate ɗin gidan. Ta buɗe siraran ƙofofin hancinta tana shaƙar ƙamshinsa na kullum da ta saba ji a jikinsa, ko gizo ƙamshin yake mata ita dai tabbas ta ji ƙamshi. Ta ɗaga hannu za ta buga ƙofar sai kuma ta janye jin wani tunani ya tsunguleta, _Anya idan ta shigar masa gida yanzu a matsayinta na ɗiya mace cikakkiyar budurwa me zai ɗauketa?._ Ta girgiza kanta da sauri tana jaddadawa zuciyar da ke tsungulinta abinda za ta yi fa normal ne, tana sonsa babu kuma wani damuwa dan ta je masa har gida sun yi hira ta ƙara nusar da shi irin ƙaunarsa da take yi._To idan kuma ya goronta miki kina binsa gida fa?_, wata zuciyar ta tunasarta, ta yi baya a sanyaye daga jikin ƙofar idanuwanta har sun yi narai-narai, ta ɗaga ƙafa za ta bar gurin sai dai jin ƙofar na motsi ya sakata dakatawa ba tare da ta juyo ba. Tana jin sa'adda aka maida ƙofar aka rufe sai kuma ta ji shiru alamun an tsaya ana kallonta. A sannu ta waigo idanuwansu suka game cikin na juna. Sun fi ƙarfin minti guda a wannan halin kafin ita ta yi azamar janye nata idon jin jikinta na rawa ta ko'ina. Tunda ta yi wayo, ko kuwa tunda aka haifeta bata taɓa ganin babban mutum dattijo irin wannan dake tsaye gabanta mai kyawunsa ba. A sannu ta ƙara cira ido za ta dube shi sai kuma ta yi saurin dafe ƙirjinta bakinta na ambaton Allah, haka kawai ta ji wani tsoro ya shigeta a yayin da gabanta ya yanke ya faɗi. Da gudu-gudu ta fara yin baya domin barin ilahirin gurin.
  Sororo ya bi bayanta da kallo a sa'ilin da ya sanya bayan hannunsa ya sharce sassanyan gumin da ya fara tsattsafo masa duk da a tsakiyar hunturu suke. Idanuwanta yake haskowa cikin nasa, idanuwan da suka riga suka harba masa kibiya mai tsananin dafi inda ba zai iya cisgeta ba. Ya kai hannunsa saitin zuciyarsa yana jin wani zafi na taso masa, zafi da raɗaɗi irin wanda ya daɗe da yin bankwana da su acan wani lokaci. Ya sauke numfashi yana dudduba jikinsa mamakin abinda ya bata tsoro a halittarsa na daɗa baibaiye shi. Ya ɗago kai ya ƙara hangota tana ta zuba sauri ba ko waiwaye. Sai ya ji kamar ta tafi da kashi huɗu bisa shida na zuciyarsa, kamar ta tafi da dukkan ruhinsa da kafatanin wayoyin da ke cikin ƙwaƙwalwarsa, kamar ita kaɗaice linzamin 'yar guntuwar rayuwar da ta rage masa.
  Murmushi ya kwace masa murmushi irin wanda ya daɗe da manta yadda ake yinsa. Ya sanya tafukan hannunsa biyu ya rufe fuskarsa yana dariya, sai kuma ya janye yana shafa gemunsa da furfura ta fara ratsawa, a karo na farko ba'ad mururul sanaa da ya ji jikinsa ya girgiza, girgiza irin ta cikakken ɗa namiji mai buƙatar abokiyar rayuwa. _Ko wannan yaya sunanta? Ko gurin yaron nan ta zo? Bari dai naji._ Ya juya cikin gidan da sauri yana bugo ƙofar da ƙarfi.
  **
  A sa'ilin da ya shawo kwanar unguwarsa ne ya hange ta tana tafiya ko'ina na jikinta na girgiza tsabar sauri. Muttsika idonsa ya ƙara yi dan ya tabbatar itan ce ba gizau take masa ba, wani sanyi ya ziyarci zuciyarsa fuskarsa ta cika da fara'a, ya ƙara gudun motarsa ya ci wani irin burki a gabanta har sai da ta ƙara firgita kan wacce take ciki. Sai dai ganin motarsa ce yasa ta ja ta tsaya tana ƙoƙarin saita nutsuwarta.
  "Ke, me kike a unguwar nan?"
  Ya furta yana fitowa daga motar fuskarsa a cukune.
  Shiru ta yi sanin har yanzu ba tada nutsuwar yin magana.
  Ya bita da kallo daga sama har ƙasa, ya kai kallonsa saitin gidansa da ke nesa da su, ai sai ya wara idanuwa Yana daɗa matsowa daf da ita.
  "Ke ba dai ni kika je nema gidana ba? Ke yanzu 'yar ficiciyar nan da ke har kin iya bin maza gidajensu?"
  "Sir, wai kai ma kana cikin jinsin maza ne...?"
  Ta furta da azama cike da jin haushin yadda muryarta ta fita a raunane.
  "Me kike nufi?"
  Ya furta yana tsareta da ido a bayan ya dubi jikinsa.
  "A'a wai naga kai ai malami nane ba ka daga cikin maza masu cutarwa..."
  Sai kuma ta riƙe haɓa alamun mamaki.
  "Sururul Qalby wai dama anan unguwar kake? Ya rabb! Na rantse na daɗe ina sha'awar zama cikinta. Ka ga gidan Kawuna can..." Ta furta tana nuna wani gida da yafi kowanne tsaruwa a jerin gidajen.
  "...To can na je duba jikinsa ya kwan biyu ba lafiya."
  Bai san sa'adda murmushi ya kwace masa har haƙoransa suka bayyana, ya daɗe bai ga rainin hankali irin wanda ake masa yanzu ba.
  Ta bi fuskarsa da kallo farin ciki na baibayeta, wai ita yau Sir Huzaif kewa dariya? Tirƙashi! Dole ta rubuta date ɗin ranar a Memo.
  "Ayya! Allah Ya bashi lafiya. Muje ki kaini nima na dubo jikinsa..."
  "A matsayinka nawa...?"
  Ta furta ba shiri tsabar ruɗewa.
  "A matsayina na malaminki mana wanda yake zaune unguwa ɗaya da kawunki."
  Ta yi masa murmuhi mai kamar yaƙe.
  "Sir sauri nake ance kar na kai maghriba."
  Ta ɗaga ƙafa za ta bar gurin sai kuma ta dakata tana waiwayawa ta hangi gidansa.
  "Ka ga wancan gidan mai gate baƙi da fari...?"
  Ya bi hannunta da kallo zuwa gidan da
  take nuna masa yaga gidansa ne.
  "Ehen ina jinki..."
  "Yanzu naga wani mutum babba mai kyau sosai ya fito daga gidan har muka gaisa, yana yanayi da kai sai dai na rasa ta ina. Allah yasa nan ne gidanka da kuma surukina na haɗu." Ta ƙarasa tana saka hannayenta biyu ta rufe fuskarta alamun kunya.
  Ya hangame baki mamaki na kashe shi, ya yi dariya, ya yi dariya har sai da ya dafe ƙofar motarsa.
  Ta bi shi da kallo tana jin ba daɗi, kamar ya ɗauke ta wata haka-haka, ita ba taga abin dariya a maganarta ba.
  "Haƙabiyya Bawa Malle..."
  Ya furta yana nunata da yatsa har sannan yana murmushi.
  "Shi ne cikakken sunana Sir..."
  "Kinsan da sunanki da na baban da na kakan duk ba daɗi ko?"
  "Na sani fa, da shi aka tsara za mu zo duniyar, ya za mu yi to?."
  "To kinga wancan gidan da kika ce na Kawunki ne? To nan ne gidan Babana. Idan kina son zubar da guntuwar kunyar shige gaba muje ku gaisa..."
  Ta yi tsuru tana sunkuyar da kai, ji ta yi kamar ta nutse. Ita fa sau ɗaya suka taɓa biyo shi ita da Hanifa dan su ga gidan nasa, bata za ci unguwa ɗaya yake da Babansa ba.
  "Shi kuma wancan kin ga mukullin gidan a hannuna. Babana baya da mukullin gidana, haka ni ina makaranta bare ki ga wani a gidana. Dan haka wuce ni ki tafi, gobe kuma kar ki yi fashin lecture, Idan kin zo ki leƙo ki tabbatar mini da zuwanki."
  Ta yi shiru tana harhaɗa lissafin tunaninta, ta ƙara waigawa ta hangi gidan da ake ce mata babu kowa. Ta tuna ƙamshin turarensa da ta ji a gidan yanzu kuma gashi tsaye gabanta daga motarsa ya fito ba daga gida ba. Ai sai ta zare ido ta matsa sosai tana shirin haɗa kafaɗa da shi ya ja baya.
  "Sir, wallahi naga mutum dattijo a gidanka kuna yanayi har muka daɗe muna kallon juna..."
  "Da shi Baban nawa kuke kallon junan...?"
  "Huzaif wallahi fa na ce maka..."
  Ya ɗan dakata yana maida dukkan hankalinsa kanta jin ta ambaci sunansa kai tsaye, ya yi nazarinta na 'yan mintuna babu alamar wasa a tare da ita.
  "Idan baka yadda ba ka zo mu je ka gani tunda daga gidan ya fito nasan ciki ya koma. Ba mamaki yana da mukullin gidan kai baka sani ba."
  Ta katse masa lissafinsa.
  "Babu kowa gidana Haƙabiyya, in faɗa miki gaskiya Alhajina bai taɓa shiga gidana ba..."
  Sai kuma ya yi shiru yana kallon tufafinta daga sama har ƙasa, ya tsaida idonsa akan _isgar_ dogon gashinta da ta karyota zuwa kafaɗarta yaja wani siririn tsaki.
  "Ba dole shaiɗanu su dinga bibiyarku ba, ji wata banzar kwalliya da kika sha tamkar renon magajiya. Ga wani gashi kin fito da shi sai ka ce jelar Biri ke ko kunyar ƙazamun mutanen da za su ganki ma baki ji. To idan kin yi ne dan ki burge ni ma kin faɗo ko a farce ban ji kin tsaya mini ba. Sai ki je gida ayi ta miki turare kuke cewa ko me? Dan wannan abin da kike cewa kin  gani a gidana ba kome ba ne sai shaiɗanin Aljanin da kwalliyarki ta burge shi."
  "Na shiga uku! Kai wallahi a'a!!"
  Ta furta da ƙarfi a yayin da hawaye sif!sif!! Suka fara sauka kuncinta. Ta juya da gudu za ta tafi ya yi caraf ya riƙo hannunta, sai kuma ya saki hannun da hanzari yana yarfe nasa yana yatsine fuska tamkar wanda ya taɓa kashi.
  "Ke kinga tafi a hankali, tunda ina tare da ke ai ba zai biyo ki nan ba, shiga gaba na dan taka miki ki samu Taxi.
  Ya furta yana saka hannu ya sosa ƙeyarsa.
  "Ai sai ki yi ta addu'a kar muje ya zama taxi ya ɗauke ki zuwa bishiyar kuka."
  Wani irin tsalle ta yi gefe tana danƙo rigarsa jikinta na rawa ta ko'ina.
  "Innalillahi..., wallahi ban faɗa wa Mami gunka zan zo ba, ka taimaka ka kaini gida dan Allah ka taimaka mini."
  "Gurina kika zo kenan?"
  "Eh Allah."
  "Me za ki yi mini?"
  "Kawai mu yi hira."
  "To ai ga ribar hakan nan kin samu..."
  "Sir dan Allah ka taimaka mini in bar unguwar nan dan Allah."
  "To kar ki damu muje na saka ki ata wani abokina ku tafi ni ba zan iya tuƙa ƙi ba kina matsayin ɗalibata."
  Ta gyaɗa kai kawai tana daɗa ƙanƙame jikinta, har yanzu fuskar mutumin ke mata gizau a zuci.
  Tana nan tsaye ya kira wani abokinsa ba daɗewa sai gashi a taxi ɗinsa. Ta yi azamar buɗe gidan baya ta shiga ta zauna. Ya duƙo daidai fuskarta yana  mata magana raɗa-raɗa
  "Sai ki kiyaye daga yau kar ki ƙara zuwa gidan saurayi nemansa dan wai kina sonsa ko kuma kuna soyayya, bayan zubar da mutuncin kanki da za ki yi, za ki iya haɗuwa da baƙin Aljanu irin wanann da kika gani yau. Kinsan ance ko wane gida ko fili tare kuke siya da su, kana gini suma suna nasu ginin. To sai goben dai, ki gaidan Baba idan ya zo miki a mafarki.
  "Allah ya isa Hanifa!"
  Ta furta a hankali tana runtse idanuwanta.
  ***

  Koda ta je gida ta daɗe bata samu nutsuwa ba har sai da ta ware karatun Kur'ani a cikin ɗakinta ta kwanta tana saurara. A sannu ta fara jin nutsuwa har barci ya ɗauketa.
  Can cikin barcinta take jin wayarta na ƙara, ta miƙa hannu cikin magagi ta jawo wayar ta kai kunne.
  "Ya zo miki a mafarkin?"
  Ta yi firgigit ta tashi zaune tamkar wacce aka watsawa ƙanƙara. Ta ɗago da fuskar wayar ta dai tabbatar shi ne, ai ba shiri ta sake ƙanƙame wayar tana dariya marar sauti.
  "Sururul Qalby ka bari mana."
  "Na bari. Ke wai mene wannan sururun kamar kina zagina?"
  Ta lumshe ido ta buɗe daɗin muryarsa na ratsa kowane tsiron gashi na jikinta.
  "Kai ɗin ne ai ka yi sururu zuwa cikin zuciyata kamar walƙiya, tunfa ranar da na fara ganinka har yau ban ji sukuni ba. Uhum! Amma da ka je gidan ka ganshi ko?"
  "Babu kowa a gidana..."
  Ta sauke ajiyar zuciya tana ƙin gasgata shi.
  "Da gaske nake miki."
  Ya furta tamkar wanda ya karanci zuciyarta.
  "Sir me ya sa ka kira Ni?  Ina ta mamaki fa."
  "Ki daina to."
  "Ta yaya?"
  "Ta hanyar sakawa ranki ni Malaminki ne, haƙƙi nane na ji yadda kika isa gida a wannan yanayin."
  Ta tsuke fuska tana hararar wayar, ba wannan ta so ji ba.
  "To ai abokinka zai faɗa maka."
  "Ba zai isa ba."
  Suka yi shiru na ɗan lokaci, ta can ɓangarensa mamaki yake na yadda yau duk wata maganarta ta ƙare, ita kanta mamakin abinda ya hanata dogon surutu take. A sannu fuskar mutumin ta ƙara wulgawa cikin idanuwanta. Ta runtse ido da ƙarfi tana jan auzubiyya.
  "Hala shaiɗan na zama kike neman tsari da Ni?"
  "Kai! A'a a zuciya na yi fa."
  "Hmm! Kinsan me?"
  "A'a.."
  Ya yi shiru na ɗan lokaci har sai da ta ƙagara.
  "Ina ji fa..."
  "Ɗazun kin yi kyau sosai!"
  Ƙit! Ya kashe wayarrr ta bita da kallo tana jin kamar ta kurma ihun dan murna, sai dai fa tsoron Zawwa ba zai barta ba.
  Ta ƙara ƙanƙame wayar a ƙirjinta tana jin kiris ya rage ta yi bankwana da damuwar mutumin Mami.
  A sannan wayarta ta yi ƙara alamun shigowar saƙo. Hannunta na rawa ta buɗe message ɗin.
  _Ki tuna wani guri mai muhimmanci agurinki, ina son mu haɗu anan domin faɗa miki wani abu mai muhimmanci a gurina._
  _*Urs Sururul Qalby.*_

Comments

0 comments