Rubutu

Blogs » Kagaggun Labarai » Tsiya Da Wasali: Shafi Na Shida

Tsiya Da Wasali: Shafi Na Shida

 • Ta fi ƙarfin minti goma tana sake karanta saƙon tamkar karatun Mauludi, sai take ganin kamar ba da hannunsa ya rubuta ba ko kuma ba ita zai turowa ba, sai dai fa daga Sururun Qalbyn naki da ya saka ta tabbata shi ne, haka saƙo nata ne ita kaɗai babu wata ma a zuciyarsa sai ita kaɗai ɗin! Wata dariyar farin ciki ta kwace mata ta rungume wayar tana tuna daɗewar da ta yi cikin soyayyarsa.
  A tun ranar da ya fara shigowa cikin ajinsu ya gabatar da kansa ba ta ƙara samun nutsuwa cikin zuciyarta ba.
  A da, kafin lokacin ta tsani karatun, asalima sai da ta shafe shekara guda a gida kafin ta yarda a sama ma mata Admission, sai da Zawwa ta mata jan ido tukunna, haka koda aka sama mata admission ta fara zuwa ba ta je da niyyar karatun ba, ta je ne da niyyar rage zaman gida kawai da hana kunnuwanta sauraron faɗan Mami da take yawan jaddada mata cikin burikan da ta ci na haihuwarta samun iliminta shi ne na farko, so take ta zama babbar likita irin yayanta  Haadiru da a sannan kaf! Kano babu kwararren likitan fiɗa irinsa, so take ta zama likitar zuciya wadda za ta iya tsaga ƙirji ta fiddo mata zuciyar mutum guda ta duba ta gani ko da ƙashi aka yi ta? A lokacin ƙunƙuni take tai ta mita Mami ta faye ƙullata da matsaya ɗan Adam.
  Da ire-iren wannan burin ta shiga jami'ar, ita da ake fatar mata likita ta ɓige da Business Admin, nan ma Mamin murmushi ta yi ta ce duk ɗaya, nan gaba kaɗan akwai dukiyar da ita kaɗai take da burin ta tattala musu ita. To dai ta shiga da burin idan an gaji aka ga ba abinda take sai ɗaukar wanka ta shiga cikin aji Zero kwanya za a fiddata. Sai dai fa dukkan wannan tunanin nata kafin ta haɗu da shi ne, a bayan idanuwanta sun yi tozali da shi kome kuma na ƙudurinta ya canja take jin bata ƙi ta ƙarar da adadin da ya rage mata na rayuwarta cikin makarantar ba idan har shi yana cikinta, za ta iya rantsewa da Allah tafi kowa sammakon shiga jami'ar a yayin da ta san yana da lecture ɗin safe ko da kuwa a maƙotan ajinsu ne. Da ta kula yana da son mutum mai ƙoƙari da hazaƙa nan da nan ta fara nacin karatun dan kawai idan ya shigo musu ta fara rattafo masa tambayoyi. Da wannan ta fara cin kansa har take iya bibiyarsa a duk inda yake cikin makaranta yana yarfata da tsinkata cikin mutanenta ba tare da itan ta damu ba, ta san kome zai ƙare da zarar ta cafki zuciyarsa ta zama ita ce kaɗai ke jagorantar farin cikinsa, haka ma ƙawarta Hanipa ke yawan faɗa mata. To yau dai gashi da kansa yake nemanta da su hadu guri mai muhimmanci. Ta miƙe fuskarta fal murna ta shige toilet a ranta ji take suna haɗuwa ya furta mata yana sonta za ta ce masa ya turo gida kawai a saka musu lokacin aure. Da wannan tunanin ta gama uzurinta ta dawo ta kwanta tana jan blanket ta ƙudundune cikinta.

  Washegari ta dinga yin  abu salalo-salalo a tsammaninta na ƙin zuwa makaranta da wuri, so take ya gaji ya kira ta dan kansa shiyasa ko reply ɗin saƙonsa taƙi yi tana jira sai ya kira ta. Tana sane ta tsallake lakcar da take da ita ta safe dan kawai ta ja masa rai da ajinta da ya daɗe da tafiya sai jiya take jin ya dawo.
  Ta sake zoɓarar baki a karo na kusan ashirin a sa'ilin da ta ƙara kallon wayarta babu alamun kiransa zai shigo kai tun safe ma sai ka ce wacce tsiya ta ƙarewa babu wanda ya kirata har shegiyar ƙawarta Hanifa ba ta kirata ta ji yadda aka yi jiyan ba.
  Miƙewa ta yi ta fara shirin tafiyar sai ga Mami ta shigo ta umarce da ta je masallacin ƙofar gida ta kira mata Baba Habu Maigadi. Har ta yi ƙofa sai kuma ta dawo ta ɗauki wayarta tana ma Mamin murmushi ganin ta bita da kallo tana taɓe baki, tasan halin Mamin yanzu za ta ce ta ajiye ita ko gani take yi tana matsawa daga kusa da wayar zai iya kira.
  A sannu ta sauka zuwa ƙasan ta ƙarasa ga gate ɗin ta buɗe, wata ni'imtacciyar iska ta daki fatar fuskarta har sai da lumshe ido tana shaƙarta. Ga mamakinta sai ta ji ƙamshi-ƙamshi irin na turaren Huzaif, irin dai ƙamshin turaren nan da ta ji a yayin da ta tsaya ƙofar gidansa. Ta fara waige-waige idanuwanta suka yi tozali  da wata hamshaƙiyar baƙar mota tana ta walwali cikin hasken rana, sai dai gilasanta baƙaƙe ne ba ka iya ganin wanda ke cikinta. A jikinta ta ji ƙamshin nan daga motar nan yake. Haka nan sai ta ji tana son zuwa taga ko Huzaif ne ke mata wasa, dan haka ta ɗaga ƙafa da azama za ta ƙarasa gun sai kuma wayarta ta yi ƙara, jikinta na rawa ta ɗaga wayar tana ambaton sunansa a zahiri.
  "Ba shi ba ne..."
  Wata murya mai cike da karsashi da ɗaɗin sauraro ta furta cikin kunnuwanta. Ta ɗaga wayar da sauri daga kunnenta ta kalli number taga wata shegiyar special number ce ai sai ta maida kunnenta da azama tana ƙifta idanuwa.
  "Ya Rabbi! You have a golden eyes like her, ki bar juya idanuwan nan dan Allah...
  "Meee?"
  Ta furta tana jin yadda ƙafafunta ke rawa, har yanzu kanta bai tsaya ba tsabar waiwaye, sai kuma ta tsaida idanuwanta kan baƙar motar nan tana jin kamar kowaye yana ciki.
  "Uwa ma bada mama, uwar yarona marigayiya uwar kowa na nake nufi..."
  Ya furta akwai alamun kiɗima cikin muryarsa.
  "Wrong number..."
  "A'a Please... Ba Baby Haƙabiyya ba ce? Ke ce dai, ke nake nema tun jiya da yamma."
  "An mini Miji wallahi..."
  Tana jin yadda ya kwashe da wata matashiyar dariya.
  "Hankali dai, ai bance kome ba, kin ji na ce aurenki zan yi ne? Ko da dai na gode da har kika gane dalilina na kiranki."
  "Wai waye ne?"
  Ta furta tana jingina da ƙofar gate ɗin jin jinin jikinta na shirin daskarewa, in dai zai buɗe baki ya yi magana sai ta ji sautin bugun zuciyarta ya canja.
  "Alherinki ne! Ance mini jami'a kike zuwa ko? Dan Allah alfarma... Kar ki ƙara saka wannan ficicin gyalen naku, haka kar ki yi kwalliya irin ta jiya ki ce za ki tafi makaranta raina ba zai mini daɗi ba, bari na je ki kula mini da kan ki. Am.. Kar fa ki manta ina bibiye da duk abinda nake so, wa billahil azim Baby Sarauniya ba da wasa na samo ki ba."
  Daga haka aka kashe wayar.
  Ta bita da kallo tana riƙe gefen cikinta da ta ji ya tamke tsam, ta yi azamar ɗaga ƙafafunta da ke mazari ta faɗa cikin gidan tana doko ƙofar. Ta toshe bakinta da ƙarfi tana jin wani matsanancin tsoro na ratsa ko'ina na halittarta, wannan mutumin da suka yi waya shi ne dai wannan mai kyan da ta gani jiya a gidan Huzaif, shi ne dai wanda Huzaif ya ce mata ba Babansa ba ne, ƙila Aljanine cikin Aljanun da kwalliyar mata ke burge su. Ai sai ta rushe da kuka da ƙarfi tana cuccusa gashinta da ke waje cikin hula.
  A sannan Baba Maigadi ya shigo ta bishi da kallo fuskar nan kafa-kaca, sai kuma wani tunani ya zo mata ta yi azamar matsawa kusa da shi tana kakkarwa.
  "Baba ka ga wata baƙar mota a waje?"
  Ya girgiza kai, sai kuma ya juya yana buɗe ƙofar ya leƙa.
  "A'a babu mota a waje..., lafiya kike kuka?" Ya ƙarasa cikin walwala.
  Ta kwalalo ido tana jin cikinta na rugugin aradu haka ta ja ƙafa ita ma ta leƙa ai sai ta dafe ƙirji.
  Babu baƙar motar nan, kai ko ƙurarta ba ta hanga ba.
  Ai da gudu ta juya zuwa sama cikin ɗakinta ta fara tattara abubuwan buƙatarta ta yi ɗakin Zawwa, ranar makarantar da bata je ba kenan, haka wayarta kashe ta ta yi ta jefa cikin drawer, duk faɗan Mami da mita a cikin ɗakinta ta kwana a bayanta a kuma tsakiyar gadonta.

  Washegari sai da hantsi ya dubi ludayi ta iya lalubo wayarta ta kunna.
  A take kiran Huzaif ya shigo ta ɗaga da azama tana sauke ajiyar zuciya.
  "Wai menene haka kike yi? Kinsan sau nawa na kira ki? Kinsan awana nawa jiya a ƙofar gidanku na kasa bugawa?"
  Ta kwalalo ido.
  "Dama ka san gidanmu?"
  "Ban sani ba!"
  "Yi hakuri dan Allah."
  Ya sauke ajiyar ta can ɓangarensa yana jin duk zafin kansa na sanyaya. A rayuwarsa yana son mutum mai bada haƙuri. A jiya da bai jita ba shi kaɗai yasan yadda ya ji. Ɗauko mota ya yi takanas ya zo cikin unguwarsu ko zai ganta, gashi baya so tun yanzu da bai gama fahimtar ta ba mahaifinta ya gansa, ban da haka da kai tsaye zai kutsa cikin gidan nasu.
  "Sururul Qalby baka haƙura ba ko?"
  Sassanyar muryarta ta ƙara ratsa dodon kunnensa.
  Ya ja iska ya fesar yana sanya hannu ya shafo tattausar sumarsa.
  "Na haƙura mana, amma kar ki ƙara rufe waya kinji, kin ɗagan hankali sosai."
  "To ai ban san kana kiran wayata ba har haka."
  "Ban san wata magana fa, ina za mu haɗun?"
  "Sitting room din Abbanmu."
  Ya harari wayar kamar tana gabansa.
  "Ke ai na san da gidan naku na ce miki mu haɗu waje ko?"
  Ta yi ƙasa da murya sosai.
  "Ai na daina fita ne, na bar zuwa ko makaranta ance na killace kaina."
  "What? Wai ni sa'an wasanki kika maidani ko."
  "A'a, ka tsaya ka ji mana..."
  Ta furta tana wawwaigawa, gani take kamar Aljaninta na cikin ɗakin.
  "Me zan ji wai? Kina tunzura ni wallahi."
  "Kai Sir?..."
  Sai kuma ta nisa.
  "Bari dai zan rubuto maka gun a text."
  Ta ƙarasa tamkar mai raɗa, ta kashe wayar ta buɗe gurin rubuta saƙo ta rubuta masa ta tura. Sai kuma ta yi murmushi tasan dai duk maitar Aljan bai san abinda ke zuciyar bawa ba balle ma ya zo mata nan gurin.

  Zuwa ƙarfe uku ta gama kintsawa, ta je ga Mami ta ce mata tana da lecture ƙarfe huɗu kar a turo Baba Direba sai shidda. Zawwa ta bita da kallo daga sama har ƙasa, wata doguwar baƙar riga ta zira ta ɗaura wani cukurkuɗaɗɗen niƙaf da alama da ƙyar ta gano shi cikin shirgi, hatta a hannunta sai da ta  saka safa haka ƙafarta tamkar dai wadda za a bawa laƙanin shiga Shi'a.
  "Lafiya ko?"
  Ta furta tana daɗa ƙare mata kallo.
  Ta yatsine fuska ta cikin niƙabinta ta haɗe hannayenta guri guda, cikin rawar murya ta ce.
  "Mami sanyi nake ji."
  "Ko yaushe kika fara jin sanyi? To ki goge niƙaf ɗin mana ji shi fa kamar an kwato shi daga bakin kura."
  "Ba lokaci ne na makara kuma lecture ban so ta wuce ni, Mami na tafi sai na dawo.
  "Au to madalla."
  Da haka ta fice zuwa gurin Huzaif.
  Tun daga nesa ta hange shi zaune, saɗaf-saɗaf ta laɓaɓa gurinsa ta zauna, ya bita da kallo sai kuma ya fara ƙoƙarin miƙewa zai canja waje, da sauri ta ɗaga masa niƙaf ɗin fuskarta tana masa gwalo.
  Ya ja siririn tsaki cike da takaici.
  "Wai saboda Allah menene haka? Wannan da cikin dare ne ai sai ki firgita mutum."
  "Ni ma a firgicen nake, manta kawai."
  Sai kuma ta yi masa murmushi a bayan ta ƙare masa kallo.
  "Sir wallahi ka yi kyau kamar ango, amma wannan shi ne zuwa zancenka na farko?"
  Ya harareta yana yafito wani waiter ya kawo musu smooth. Sai kuma ya maida hankalinsa kanta yana kallon idanuwanta.
  "Menene ke faruwa wai, duk na ganki a wani firgice."
  Ta waiwaiga hagu da damarta, ta ɗaga kai tana ganin yadda motoci sai ku yi jerin gwano a can nesa da su, ai sai ta yi tsam ta miƙe tsaye.
  "Mu shiga daga ciki dan Allah, bansan zaman waje duk ƙura ta buɗe ma abin sha."
  Hannunsa yasa ya jawota ta koma ta zauna.  Sai kuma ya yarfe hannun yana yatsine fuska.
  Ta bishi da kallo Idanuwanta a ƙanƙance tana taɓe masa baki.
  "Ji abinda kake yi sai ka ce ka taɓa ƙazanta."
  "Ban saba taɓa mace ba, gidanmu ma babu mata. Sannan ai nasan da cikin na zauna anan ko, Ni bansan can dan haka ki zauna zan kare ki daga duk wata ƙura."
  Ta masa murmushi a sanyaye.
  Ya sauke ajiyar zuciya yana kallon idanuwanta.
  "Kina ji ko, magana mai muhimmanci nake so mu yi, ina so ki sanni ki san kome nawa kafin musan matsayar mu.
  Ta tattaro hankalinta kansa duk da jefi_ jifi ta kan juya ta kalli inda aka ware dan parking motoci.
  Ya daɗa nisawa tamkar yana jajanta abinda zai faɗa matan.
  "Haƙabiyya, asalina ba ɗan nan ba ne, mun zo ne daga can wani ƙauye da ke cikin Gombe. Mahaifina ya..."
  Ta yi wata irin zabura tana matsowa kusa da shi idanuwanta a warwaje.
  "Huzaif! Maza waiga damarka ka gane mini akwai wani babban mutum jikin wata ƙatuwar Cgreen ɗin mota"
  A hankali ya zare hannunsa daga nata da ta ƙanƙane ya juya. Tana kula da sa'adda idanuwansa suka ƙara girma da zallar mamaki, sai kuma ya miƙe tsaye ita ma ta miƙe ko'ina na jikinta na kakkarwa.
  "Wai baka ga kowa ba ne gashi can fa a tsaye."
  Ta murta tana daɗa nuna masa mutumin da ke tsaye yana kallonsu. A sannan taga mutumin yasa hannu yana yafito Huzaif, shi kuma ya tafi da sauri. Hannunta a ƙirji bakinta a hangame haka ta tsaya tana kallonsu.
  "Ashe kana nan kana hutawa..."
  Mutumin ya furta yana kallonsa cike da fara'a.
  "Kana ji waccar yarinyar da kuke tare ya kuke da ita ne?"
  Huzaif ya yi wani ɓoyayyen murmushi yana sanya hannu ya sosa ƙeyarsa cike da kunya.
  "Abba Ɗaliba ta ce..."
  "Au to to to."
  Abba ya furta yana sanya hannu ya zare hular kansa ya ajeta saman mota.

Comments

3 comments