Makalu

Blogs » Kagaggun Labarai » TALLAH

TALLAH

 • Ta ƙurawa hoton idanu ba ta ko fahimtar abinda lakcaran ke magana a kai, ranta ya dinga wani irin tafarfasa. Babbar mace ce a hoton sanye cikin shiga ta alfarma, ta sha lulluɓi, a gefenta kuwa wata budurwa ce da ba ta fi shekaru goma sha hudu ba rungume da ita ta dora lebbanta saman kumatun matar. Hakan ya sa matar dariya har wushiryarta ta bayyana muraran. Hoton ba'a fi awanni biyu da ɗorashi ba, yarinyar, mai suna Zulaihat, ita ta ɗora a shafinta na fesbuk tana taya uwar murnar cika shekaru goma da aure. Hotuna ne kala-kala har da wanda take tare da Uban, duk ba su tsayamata a rai kamar wannan ba. Buga kafaɗarta da akai da ƙarfi ya sa ta dawowa hayyacinta, a razane ta kalli aminiyarta kafin ta kalli Lakcaran da ya murtuke fuska babu digon annuri, mutumin da hatta da yanmatan da ba ƴan ajin ba, suke halartar ajinsa da niyyar su burgeshi ko su ja ra'ayinsa garesu. Ba'a kawomasa wargi kamar yanda babu wani ko wata da ta isa ta taka ofishinsa bai ci mutuncinta ba. Ba ƙaramin kwarjini ne da shi ba kamar yanda suffar halittarsa ke girgiza zuƙatan ƴanmata da ma matan aure marasa kamun kai da tsoron Allah. Babu abin burgewa kamar yanda ya zaɓi yin Degree dinsa ɓangaren Hausa, ya ke kuma koyarwa duk a wannan ɓangaren a jami'ar. Mutum mai kishin harshensa.

  Umarni ya ba ta akan ta fito, ba musu ta miƙe tana goge kwallar da ta cikamata idanu a faƙaice, ba don abinda Malamin ke kokarin yi mata ba sai don bakin cikin da hotonnan ya jazamata. Yanda ta ke jin ranta a ɓace, za ta iya karɓar kowane hukunci daga gareshi.

  Ta karasa har inda yake, ba tare da ya kara dubanta ba ya ce.

  "Ajiye wayarki ki ficemin daga aji, kar ki yarda naga ƙafarki a ofis dina da zummar ba da hakuri, idan kuwa ba haka ba zai shafi karatunki. Wayarki sai ƙarshen Semester."

  Maganar ba ta yiwa ƴan aji dadi ba, ko ba komai ba ta da abokin faɗa, kowa suka haɗu zaa gaisa a mutunce a wuce. Wannan yasa suka shiga tayata bada hakuri, yayinda a gefenta ta ji zuciyarta na kara zafi. Kawai ta dire wayar kusa da nashi wayoyin dake ajiye saman desk ta juya ta fice daga ajin. Wannan abu ya ƙara tunzura zuciyar Sir Rufa'i, ya tsani girman kai da gadara, ya dakawa ƴan ajin tsawa akan su yi shiru sannan ya ci gaba da koyarwarsa.

  MIJIN MAHAIFIYATA......Muharram in sha Allah....\ud83c\udfca\ud83c\udfca\ud83c\udfca\ud83c\udfca\ud83c\udfca\ud83c\udfca\ud83c\udfca

Comments

4 comments