Rubutu

Blogs » Harshe da Adabi » MU GYARA RUBUTUNMU

MU GYARA RUBUTUNMU

 • WURAREN DA AKE AMFANI DA MANYAN BAK'I.

  Assalamu alaikum warahmatullah. Barkanmu da wannan lokaci.
  Barkanmu da saduwa da ku a cikin taskar nan mai farin jini wato BAKANDAMIYA, a cikin fitowa ta farko daga cikin maudu'i mai taken 'MU GYARA RUBUTUNMU' tare da ni Princess Amrah.

  'Ta yaya zan gyara rubutuna?'
  'Wadanne hanyoyi ne zan bi don ganin na inganta rubutuna?'
  'Ya zan yi in gane kalaman hadewa da na rabewa?'

  Wadannan tambayoyi ne da nake yawan cin karo da su, ko ba ni aka yi wa su ba, ina tsintar su a tsakiyar marubuta. Dalilin da ya sa na ga cancantuwar d'auko wannan maudu'in kenan, sai dai ba zai samu ba sai da hadin kawunanku. Zan tabbatar da kuna fahimtar darasin ne ta hanyar ajje mini tambayoyi a duk inda ba ku gane ba, ko kuma ku fad'i ra'ayinku a kan darasi na gaba; inda kuke so mu tsakuro.

  A shirye nake da karbar korafi, shawara, ko kuma gyare-gyare. K'aramar d'aliba ce ni mai son a yi mini gyara komai kankantarsa. Kofa a bude take a koyaushe. Duk inda kuka ga na rubuta ba daidai ba a gyara mini zan karb'a, da izinin Allah, saboda ni ma d'in koyo nake yi.

  A yau za mu fara da wurare, ko in ce muhallan da ya kamata a fara amfani da babban bak'i (capital letter) a wurin rubuta su. Abun nufi, inda dole sai ka saka babban harafi a farkon fara su. Jiya na ci karo da wani rubutu wanda ya ba ni mamaki. Ba a damu da sunan gari ko na mutum ba, ko'ina amfani ake da k'aramin bak'i. Abu mafi mamakin ma shi ne, hatta sunan Allah da k'aramin bak'i ake rubuta shi. Shi ya sa na fara daukar wannan a matsayin fitowa ta farko, domin kuwa ba k'aramin kuskure ba ne amfani da k'ananan bak'i a inda bai cancanta ba.

  1- FARKON JIMLA: Ana amfani da babban bak'i a farkon gina kowacce jimla. Ma'ana, duk abin da za ki fara rubutawa dole sai kin saka babban bak'i a farkonshi sannan jimlarki za ta zama ingantacciya kuma karb'abb'iya.

  Misali;
  Na tafi gidanmu ni dai.\u2714\ufe0f
  na tafi gidanmu ni dai.\u274c

  Ku zo mu je makaranta domin mu koyi karatu.\u2714\ufe0f
  ku zo mu je makaranta domin mu koyi karatu.\u274c

  Ki same ni gida yanzu Hafsa.\u2714\ufe0f
  ki same ni gida yanzu Hafsa.\u274c

  Ku lura da kyau, inda duk na saka alamar kashewa, to hakan na nufin idan kika aikata shi a cikin rubutu, kuskure ne mai girma, rubutunki ba zai zama karbabbe ba ko kadan. Ba ki kuma nuna alamun k'warewa ba a cikinsa.

  2- SUNAN MUTUM, SUNAN ALLAH, SUNAN GARI (POPER NOUN): Duk inda sunan mutum ya zo a cikin jimla, walau farko, tsakiya ko kuma karshe, to ana amfani da babban harafi wurin rubuta farkonshi. Kuskure ne amfani da k'aramin bak'i wurin rubuta sunan mutum ko kuma gari. Sannan a wasu wuraren ma, sunan wuri kan iya d'aukar babban bak'i a farkon rubuta shi. A Turance shi ake kira da Proper noun.

  Misali;
  Gobe da safe zan je gidan su Amina Kabir.\u2714\ufe0f
  Gobe da safe zan je gidan su amina kabir.\u274c

  Rayuwar Amina Katsina mai kyau ce.\u2714\ufe0f
  Rayuwar amina katsina mai kyau ce.\u274c

  Amina Ma'aji na da kirki sosai.\u2714\ufe0f
  amina ma'aji na da kirki sosai.\u274c

  A misali na farko na kawo sunan Amina da na mahaifinta, inda duk za ku ga da babban bak'i na fara rubuta su.  Sai misali na biyu, na kawo sunan Amina da sunan garinsu, hakan ke nunar da cewa da Amina da garin su Amina duk da babban bak'i ake fara rubuta su. Sai misali na uku, na saka sunan Amina da inkiyar gidansu. Kenan, suk inda inkiyar suna ta zo ita ma da babban bak'i ake fara rubuta ta.

  Akwai sunan mutum Amin. Idan kika zo rubuta jimla da sunan, sai kika yi amfani da k'aramin bak'i, kika rubuta amin, kun ga ya canja ma'ana baki daya, ya zama wani abun na daban, kuma kai tsaye marubuci ba zai dauka mutum ba ne sai ya aje hankalinsa, kenan dai an ba marubuci wahala. A maimakon ya karanta shi a matsayin sunan mutum, sai ya karanta shi da zummar 'amin' ta amsa addu'a.

  Sannan sunan Allah, ko da a wakilin suna ya zo to ana amfani da babban bak'i a wurin rubuta shi.

  Misali;
  Duk abin da mutum zai aikata ya rinka tunawa da Allah Yana ganin shi.\u2714\ufe0f
  Duk abin da mutum zai aikata ya rinka tunawa da allah yana ganin shi.\u274c

  Ka bauta wa Allah tamkar kana ganin Shi.\u2714\ufe0f
  Ka bauta wa allah tamkar kana ganin shi.\u274c

  Haka kuma ana amfani da babban bak'i a farkon rubuta sunan Gari ko kuma K'asa.
  Misali;

  Gobe da sassafe jirginmu zai tashi zuwa America.\u2714\ufe0f
  Gobe da sassafe jirginmu zai tashi zuwa america.\u274c

  Aisha 'yar asalin jigar Katsina ce.\u2714\ufe0f
  Aisha 'yar asalin jihar katsina ce.\u274c

  Na tafi Islamiyya ni dai.\u2714\ufe0f
  Na tafi islamiyya ni dai.\u274c

  Sai dai ana amfani da k'aramin bak'i a farkon rubuta sandararrun abubuwa da dabbobi in dai a tsakiyar jimla suka zo. Kamar; mota, akuya, bishiya, kujera, kaza, da sauransu.

  3- BAYAN ALAMAR ZANCEN WANI ("): Ana amfani da babban bak'i a bayan alamar zancen wani.

  Misali;
  Cikin sanyin murya ta ce, "Ka ji tsoron Allah Ishraq..."\u2714\ufe0f
  Cikin sanyin murya ta ce, "ka ji tsoron Allah Ishraq..."\u274c

  Ishraq ya ba ta amsa da, "To da tsoron ki nake ji?"\u2714\ufe0f
  Ishraq ya ba ta amsa da, "to da tsoron ki nake ji?"\u274c

  Sai dai idan ya kasance d'orawa ne, ma'ana wanda ke kan yin maganar bai gama ba ya d'an yi shiru, sannan ya sake d'ora bayani, to ba za a yi amfani da babban bak'i ba a wurin; ka'rami shi ne a wannan muhallin.

  Misali;
  "Idan aka zo batun abinci mai dad'i,"Aisha ta fad'a, "shinkafa ta zarce komai."\u2714\ufe0f
  "Rayuwa mai kyau suke yi," Maryam ta fad'a, "a gidan aurensu."\u2714\ufe0f

  Idan kuka duba wadannan misalan kai tsaye za ku gane inda na dosa, kafin ma a rufe zancen sai da alamar wak'afi ta zo daidai wurin, alamun dai zancen bai k'are ba kenan. Don haka sai aka sake d'ora bayanin, amma kuma da k'aramin bak'i, tunda da ma ba a kai aya ba. Wak'afi ba ya bukatar a d'ora da babban bak'i sai idan suna ne ya zo gaba.

  4- Rana da wata duk ana amfani da babban bak'i a wurin fara rubuta su, ko da kuwa a tsakiya ko karshen jimla suka zo.

  Misali;
  Ranar Litinin da sassafe zan tafi gidan su Khadija.\u2714\ufe0f
  Ranar litinin da sassafe zan tafi gidan su Khadija.\u274c

  An haife ni a farkon Yuni.\u2714\ufe0f
  An haife ni a farkon yuni.\u274c

  5- A wurin title (Sunan labari) ko kuma heading duka ana amfani da babban bak'i idan za a rubuta su.

  Misali;
  Sunan sabon labarina Rai Da Fansa.\u2714\ufe0f
  Sunan sabon labarina Rai da fansa.\u274c
  Sunan sabon labarina rai da fansa.\u274c
  Sunan sabon labarina rai Da fansa.\u274c
  Sunan sabon labarina rai da Fansa.\u274c

  Za mu fafata muhawara tare da 'yan kungiyar ALZAZ, a kan; Auren Saurayi Talaka da Auren Attajiri Mai Mata Wane Ya Fi Amfani Ga 'Ya Mace?\u2714\ufe0f

  Za mu fafata muhawara tare da 'yan kungiyar ALZAZ, a kan; auren saurayi talaka da auren attajiri mai mata wane ya fi amfani ga 'ya mace?\u274c

  6- WURIN RUBUTA YARE KO K'ABILA: A duk inda marubuci zai rubuta sunan yare ko wata k'abila, to zai fara su ne da babban bak'i.

  Misali;
  Waccan tana da zubin Inyamurai ko Yarbawa.\u2714\ufe0f
  Waccan tana da zubin inyamurai ko yarbawa.\u274c

  Ba Inyamura ba ce, cikakkiyar Bahaushiya ce.\u2714\ufe0f
  Ba inyamura ba ce, cikakkiyar bahaushiya ce.\u274c

  7-  A WURIN SAKAYA SUNA: Ana amfani da babban harafi a farkon sakaya sunan 'yan uwa ko dangi.

  Misali;
  Jiya da yamma na je gidan Anti Balkisu.\u2714\ufe0f
  Jiya da yamma na je gidan anti Balkisu.\u274c
  Jiya da yamma na je gidan anti balkisu.\u274c

  Abokin Kawu Aliyu ya ba ni alewa d'azu.\u2714\ufe0f
  Abokin kawu Aliyu ya ba ni alewa d'azu.\u274c
  abokin kawu aliyu ya ba ni alewa d'azu.\u274c

  Za ki raka ni gidan Kaka Mero gobe?\u2714\ufe0f
  Za ki raka ni gidan kaka Mero gobe?\u274c
  Za ki raka ni gidan kaka mero gobe?\u274c

  Sai dai, ba a farawa da babban harafi idan ba sunan kowa za a dora a gaba ba.

  Misali;
  Mutumin da ya zo d'azu kawuna ne.\u2714\ufe0f
  Gobe zan je gidan yayata.\u2714\ufe0f
  Aisha don Allah ki raka ni gidan kakata.\u2714\ufe0f

  8- BAYAN ALAMAR AYA, MOTSIN RAI, DA KUMA ALAMAR TAMBAYA: Duk inda wadannan alamomin rubutun suka zo, to alamun zancen da ake kan yi ya k'are kenan. Sai dai a d'ora wata sabuwar maganar. Don haka duk wata kalma da za ta zo bayan wadannan da na lissafa, ana amfani da babban bak'i a farkon rubutawa.

  Misali;
  Ta yaya rayuwar talaka za ta yi kyau? Ya kamata Gwamnati ta tashi tsaye don ganin an raya talakawa.\u2714\ufe0f
  Ta yaya rayuwar talaka za ta yi kyau? ya kamata Gwamnati ta tashi tsaye don ganin an raya talakawa.\u274c

  Abun tsoro! Kura a rumbu.\u2714\ufe0f
  Abun tsoro! kura a rumbu.\u274c

  Ilmin 'ya'ya mata na da matukar muhimmanci. Shin ko kun san cewa ilmin 'ya mace daidai yake da gina rayuwar al'umma baki daya?\u2714\ufe0f
  Ilmin 'ya'ya mata na da matukar muhimmanci. shin ko kun san cewa ilmin 'ya mace daidai yake da gina rayuwar al'umma baki daya?

  Za mu dakata a nan, ba don darasin ya k'are ba. Za mu sake had'uwa da ku a mako mai zuwa idan Allah Ya nuna mana.

  Taku har kullum;
  Amrah A Mashi
  (Princess Amrah).

Comments

8 comments