Rubutu

Blogs » Kagaggun Labarai » Jini Ba Ya Maganin Kishirwa: Babi na Daya

Jini Ba Ya Maganin Kishirwa: Babi na Daya

 • BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

  Falo ne ?an madaidaici mai ?auke da kayan alatu dai-dai karfi, dai-dai misalin rufin asirin mazauna gidan.

  ?arar fanka ce ke ta shi a cikin falon ka?an-ka?an, hakan kuma bai hana tsinkayo maganar wata Dattijuwar mata ba, da ke zaune kan ?aya daga cikin jerin kujerun da suke kewaye a falon, daga wajen ?afafunta a ?asan carpet wani matashin saurayi ne zaune a, duka-duka shekarunsa ba za su haura ashirin da takwas ba, a ido kuwa zaka yi tunanin bai kai hakan ba,  sabida zubi da tsarin tsamurmurin jikinsa dai-dai misali wanda ya da ce da doguwar fuskarsa, ba fari ba ne haka kuma ba zaka kira shi ba?i ba, kallo ?aya za ka yi musu zuwa biyu kamanceceniyar kamar da suke zata wanzu a idanuwan masu kallonsu, hakan zai ?ara tabbatar maka da cewa Uwa ce da yaronta ke zaune.

  Matar tayi gyaran murya irin nasu na manya tana mai cigaba da fa?in.

  "Yanzu Kamal kai gani kake auren Hajiya Shema'u alkhairi ne a gareka? Matar da sai dai ka yi mata kallon Yayarka idan ma bata haifi kamarka ba, ba da ban  haihuwa da bata yi ba ai yanzu da tana da sa'aninka...!".

  Dattijuwar matar da ba zata wuce shekaru arba'in da biyar ba ta katse maganar da take yi cikin takaicin ?an nata, da ke zaune kai ka ce abin da take fa?a yana shiga kunnensa.

  Jin tayi shiru yasa shi ?ago da Kansa ya?an dubi mahaifiyartasa kafin ya mai da kallonsa ?asan carpet yana fa?in.

  "Hajiya bawai inason yin auren nan da wata manufa ba ne, sai dan koyi da abin da manzon Allah (S.A.W.) ya yi ne, shima fa idan bamu mance ba Nanah Khadijah ta girmeshi nesa ba kusa ba, amma hakan bai hana shi aurenta ba, Hajiya ! Ni dai fatana a cikin wannan lamari addu'arki na ke da bu?ata domin raya sunnar ma'aiki zan yi".

  "Hmmm Kamal kenan..! Ba zaka ta?a gane abin da a ke son ganar da kai ba, duka-duka yau fa shekara guda da aurenka da Sakinah ko ka manta ne?".

  "A'a amma Hajiya na ke ganin hakan ba wani abu ba ne..!".

  "Sabida ka kwallafawa kanka ?aukan dala ba gammo ko?".

  "Kamal tun da ka dage akan auren nan bazan yi jayayya ba domin bansan a bin da Ubangiji ya ?oye a cikin auren ba, sai dai ina fargabar halin da zaka shiga kai da matarka ne kawai?".

  "Hajiya kiyi min addu'a insha Allahu babu komai sai alkhairi".

  "To Kamal Allah ya tabbatar da alkhairin amma..! Shikenan dai ta shi ka je Allah ya taimaka".

  "Amin Hajiyata addu'a kawai dama ya kamata ki dinga yi min".

  Ya kai maganar bakinsa a washe kamar gonar auduga, kai ka ce kyautar aljannah aka ce an bashi.

  Kamal ya ta shi ya fita daga falon fuskarsa wasai yana faman doka uban  murmushi, Hajiya Marka mahaifiyar Kamal tabi bayan ?an nata da kallo tana girgiza kai a fili ta furta.

  "Wanda ya yi nisa baya jin kira dai, inban da namiji namiji ne me zaka yi da matar da ta haifeka ko kuma ince yarinta dai, idan auren ya ke so ya duba yarinya dai-dai da shi mana, yanzu maganar mutanen unguwa ma ta ishemu banda ta 'yan uwa".

  "Hajiya ya dai, ke da Ya Kamal ne ko?".

  Cewar wata siririyar budurwa da ta fito daga ?aki, kallo ?aya zaka yi mata kaga yana yi da kama sosai da take da Kamal, hakan ne zai tabbatar maka da cewar ?anwarsa ce.

  Ta zauna gefan Hajiyar tana dubanta.

  "Ke ma kinsan dai abin da ya ke sani fa?a a cikin kwanakin nan, Kamal ya kafe baya ji baya gani kan batun auren nan ya da ge dole sai ya yi".

  "To Hajiya banda abinki ki rabu da shi mana shifa ya ji ya gani zai iya sai ki zuba masa ido".

  "Amma Farida kina ganin hakan dai-dai ne?, A ce Kamal duk cikar garin nan ya rasa matar aure sai Hajiya Shema'u !".

  "Hmm Hajiya ni dai da za ki bi shawarata ki sauwa?ewa kanki tunanin auren Kamal a ranki, kada ki jawo wa kanki hawan jinin da ba ki da shi, ba muji ba ba mu gani ba".

  "Shi kenan Farida amma abin ne dole ya dame ni".

  "A dai bar maganar Hajiya".

  Farida ta yi maganar tana mai mi?ewa zuwa gaban TV ta kunnawa Hajiyar domin ta ?ebe mata kewa ita kuma ta fa?a kitchen domin yi musu sanwar rana.

  Kamal na fita bakin titin layinsu ya ci karo da abokinsa kuma amini Zayyad suka gaisa ci ke da kewar juna.

  "Ya dai mutumin naga yau cikin  farin ciki ka ke, ko batun aikin ne ya samu?".

  "Kai dai bari Zayyad, Wanne batun aiki kuma, ga babban albishir ?in da yafi min komai da?i, Hajiya yau ta amince da batun aurena".

  Lokaci guda annurin kan fuskar Zayyad ya ?auke, domin jin maganar ya yi tamkar saukar aradu cikin kunnuwansa, baki galala ya ke bin Kamal da kallon mamaki.

  "Hajiya ta amince fa ka ce?".

  "Yes kana mamaki ko?, ni ma wallahi ko a mafarki ban yi tunanin amincewarta da wuri haka ba".

  "Waima na tambayeka, dama maganar auren har yanzu tana nan baka barta ba?".

  "Ya kuwa za'a yi na barta Zayyad? Arziki ya tako ya kwankwasa min ?ofa har cikin gidanmu har makwancina ya zo ya sameni, ni kuma sai in sa ?afa inture shi?, ina..! Ba zai yi yu ba Zayyad, ina haskoni cikin arzi?i madawwami arzi?in da babu yankewa million ashirin da wani abu ba wasa ba".

  Zayyad ya ja dogon tsaki ci ke da takaicin maganar abokin nasa ya dube shi da kyau.

  "Kamal duk wani arziki idan ba alkhairi ba ne kayi addu'a Allah ya yi maka tsari da shi, domin idan har zaka samu arziki mai dorewa ta dalilin auren Hajiya Shema'u to aurenka da ita babu alkhairi a ganina, ka bu?e idonka ka farka daga mummunan mafarkin da ka ke me zaka yi da million ashirin? Ba yan ka ?ata sunanka, ka ?ata sunan danginku, me million ashirin zata yi maka akan auren wata can tsohuwar kilaki..?".

  "Dakata Zayyad..! Ka iya bakinka, ka san hakan na ?aya daga cikin abinda ya ke ha?amu ko? Idan ka san ba za ka dinga fa?in alkhairi ba to ka yi shiru, Annabi ma ya fa?a".

  "Kamal kenan ! Shikenan Allah ya taimaka ya ba da sa'a, wanda ya?i ji, baya ?i gani ba".

  "Amin".

  Kamal ya amsawa Zayyad cikin fushi kowannansu ya wuce ba tare da yiwa ?an uwansa sallama ba duk da ce war basu ji da?in rabuwar tasu a haka ba.

  BAYAN SATI DAYA

  Da sallamarsa ya sanya kai cikin gidan, bayansa yara ne biye da shi ?auke da akwatuna biyu suka ajiye a filin tsakar gidan Kamal ya zaro naira ?ari  ya basu ladansu suka fi ce.

  Faridah da ke shirin fita daga gidan cikin shigar uniform hijab har ?asa da alamu islamiyya ta nufa, ta dube shi tare da ?auke kai ta gaida shi ta yi wucewarta ba tare da ta damu da amsawarsa ba, domin ita yanzu baki ?aya haushi ya ke bata, mussamman ganin a kwatunan da ta yi a yanzu ya ?ara tabbatar mata har yanzu yana kan bakansa kenan.

  Kamal yabi bayanta da tsaki, cike da tsantsar tsana da takaici, sabida shi duk wanda ba zai goyi bayan aurensa ba a yanzu to sun raba hanya kenan, baki ?aya yakan ji ya tsani mutum domin gani yake babu wani babban ma?iyinsa a duniya sama da kai.

  ?a kansa ya ja akwatunan har cikin falon Hajiyartasu yana mai kwalawa Sakinah matarsa kira ta fito da sauri zuwa falon Hajiya ta zube kan carpet tana jiransa domin tuni ya wuce cikin ?akin Hajiyar zai kirawota.

  Baifi mintuna biyar da shiga ba suka fito tare tana fa?in.

  "Wai wane kaya ne haka ka kawo? Da za ka sako ni a gaba dole in zo in gani?".

  Ganin akwatuna yasa ta yi turus tana bin Kamal ?in da kallo, shi kuwa gogan neman guri ya yi ya zauna yana sosa ?eyarsa.

  Hajiya ta zauna tana duban Kamal domin jin mai zai ce.

  "Hajiya kayan fa?ar kishiya ne na Sakinah na kawo mata domin Hajiya Shema'u ta ce bata bu?atar komai illa sadaki, hakan yasa na fita ha??in Sakinan na siyo mata nata kayan".

  Ya mai da dubansa gun Sakinah.

  "Ga kayan nan ki duba duk abinda babu kiyimin magana, sannan Hajiya gobe masu fenti za su zo suyiwa gidan fenti za'a gyara duk inda ya kamata".

  Kamal ya sunkuyar da kai yana sosa ?eya sabida irin kallon da Hajiyar ke binsa da shi, amma hakan bai hana shi dakatawa daga maganar da ya faro ba.

  "Hajiya nan da kwana uku fa za'a ?aura auren ranar juma'a ken..!".

  "Allah ya kaimu ya nuna mana".

  Hajiyar ta fa?a kafin ya kai ?arshen maganar ta mi?e tana mai shigewa ?akinta tabarsu nan zaune, tana shiga ?akin Sakinah ta mi?e itama zata fi ce.

  "Uban waye zai ?auke miki kayan?".

  Kamal ya dako mata tsawa, Sakinah ta juyo ta dube shi kawai ba tare data ce komai ba taja akwatunan zuwa ?akinta.

  Tana shiga yana sanyo kai shima cikin fushi ya fizgo gashin kanta yana fa?in.

  "Duk ba?in cikin da zaki yi da wani munafukin kishi sai dai ki yi ki gama, aure babu fa shi, domin nan da kwanaki Kamal zai koma Alhaji Kamal".

  Ya kai maganar yana mai sanya dariya, Sakinah ta fizge kanta ta yi wucewarta ?aki ba tare da ta tanka mai ba, Kamal ya ?ara zuciya yabi bayanta .

  "Wato kin mai dani ?an iska ko dan tsabar rashin mutunci da rainin wayo antaimaka miki ansiyo miki kayan amma babu ko godiya bare addu'a".

  "An gode Allah saka da alkhairi".

  Ta bashi amsa a ta?aice, ba tare da ta yi yun?urin duban inda ya ke tsaye ba.

  Kamal ya yi kwafa ya cije le?e  yana mai ?arewa ?akin nata kallo.

  "Nan da kwanaki wadannan ko ?a??un kayan naki sai dai mukai bola ba zai yi yu Alhaji Kamal yana kwanciya akan ru?a??en gadonnan ba, ko da ya ke gida zan siya mai part uku kawai ke ?aya amarya ?aya Hajiya ?aya komai sabo za'a zuba".

  Ya kai maganar yana mai sauke kallonsa akan kayansu da ta fara ninkewa kafin ya shigo kallo.

  "Hatta kayanku sai dai Ku bayar ko Ku ?ona komai sabo zan siya domin ba za'a zo gidan Alhaji guda aga tsumma ba".

  Sakinah tayi murmushi kawai tana mai ci gaba da ninkin kayan.

  "Au dariya na ke baki ma?".

  "A'a Yalla?ai wace ni da yi maka dariya? wani abu na tuna kawai".

  Kamal zuciya ta zo masa wuya, ya yi kwafa tare da cijen le?ansa na ?asa da ?arfi, kafin ya fice fuuu daga cikin ?akin yana mai jin haushin Sakinah akan a abin da take masa cikin kwanakin nan.

  Tama mai da shi wani hotiho ko hamago, kome zai yi mata domin ta ji haushi ba ta ji, ?arshe ma shike dakon kayan takaicin ba ita ba.

  *****

  Ku latsa nan don karanta babi na biyu.

Comments

5 comments