Makalu

JINI BAYA MAGANIN ƘISHIRWA

 •  *JINI BAYA MAGANIN ƘISHIRWA.*    


  Na

  QURRATUL-AYN.


  NAGARTA WRITERS ASSOCIATIONS.


  BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

                 


                 01


     Falo ne ɗan madaidaici mai ɗauke da kayan alatu dai-dai karfi, dai-dai misalin rufin asirin mazauna gidan.


  Ƙarar fanka ce ke ta shi a cikin falon kaɗan-kaɗan, hakan kuma bai hana tsinkayo maganar wata Dattijuwar mata ba, da ke zaune kan ɗaya daga cikin jerin kujerun da suke kewaye a falon, daga wajen ƙafafunta a ƙasan carpet wani matashin saurayi ne zaune a, duka-duka shekarunsa ba za su haura ashirin da takwas ba, a ido kuwa zaka yi tunanin bai kai hakan ba,  sabida zubi da tsarin tsamurmurin jikinsa dai-dai misali wanda ya da ce da doguwar fuskarsa, ba fari ba ne haka kuma ba zaka kira shi baƙi ba, kallo ɗaya za ka yi musu zuwa biyu kamanceceniyar kamar da suke zata wanzu a idanuwan masu kallonsu, hakan zai ƙara tabbatar maka da cewa Uwa ce da yaronta ke zaune.


  Matar tayi gyaran murya irin nasu na manya tana mai cigaba da faɗin.


     "Yanzu Kamal kai gani kake auren Hajiya Shema'u alkhairi ne a gareka? Matar da sai dai ka yi mata kallon Yayarka idan ma bata haifi kamarka ba, ba da ban  haihuwa da bata yi ba ai yanzu da tana da sa'aninka...!".


  Dattijuwar matar da ba zata wuce shekaru arba'in da biyar ba ta katse maganar da take yi cikin takaicin ɗan nata, da ke zaune kai ka ce abin da take faɗa yana shiga kunnensa.


  Jin tayi shiru yasa shi ɗago da Kansa yaɗan dubi mahaifiyartasa kafin ya mai da kallonsa ƙasan carpet yana faɗin.


    "Hajiya bawai inason yin auren nan da wata manufa ba ne, sai dan koyi da abin da manzon Allah (S.A.W.) ya yi ne, shima fa idan bamu mance ba Nanah Khadijah ta girmeshi nesa ba kusa ba, amma hakan bai hana shi aurenta ba, Hajiya ! Ni dai fatana a cikin wannan lamari addu'arki na ke da buƙata domin raya sunnar ma'aiki zan yi".


    "Hmmm Kamal kenan..! Ba zaka taɓa gane abin da a ke son ganar da kai ba, duka-duka yau fa shekara guda da aurenka da Sakinah ko ka manta ne?".


  "A'a amma Hajiya na ke ganin hakan ba wani abu ba ne..!".


  "Sabida ka kwallafawa kanka ɗaukan dala ba gammo ko?".


  "Kamal tun da ka dage akan auren nan bazan yi jayayya ba domin bansan a bin da Ubangiji ya ɓoye a cikin auren ba, sai dai ina fargabar halin da zaka shiga kai da matarka ne kawai?".


  "Hajiya kiyi min addu'a insha Allahu babu komai sai alkhairi".


  "To Kamal Allah ya tabbatar da alkhairin amma..! Shikenan dai ta shi ka je Allah ya taimaka".


  "Amin Hajiyata addu'a kawai dama ya kamata ki dinga yi min".


  Ya kai maganar bakinsa a washe kamar gonar auduga, kai ka ce kyautar aljannah aka ce an bashi.


  Kamal ya ta shi ya fita daga falon fuskarsa wasai yana faman doka uban  murmushi, Hajiya Marka mahaifiyar Kamal tabi bayan ɗan nata da kallo tana girgiza kai a fili ta furta.


    "Wanda ya yi nisa baya jin kira dai, inban da namiji namiji ne me zaka yi da matar da ta haifeka ko kuma ince yarinta dai, idan auren ya ke so ya duba yarinya dai-dai da shi mana, yanzu maganar mutanen unguwa ma ta ishemu banda ta 'yan uwa".


    

    "Hajiya ya dai, ke da Ya Kamal ne ko?".


  Cewar wata siririyar budurwa da ta fito daga ɗaki, kallo ɗaya zaka yi mata kaga yana yi da kama sosai da take da Kamal, hakan ne zai tabbatar maka da cewar ƙanwarsa ce.


    Ta zauna gefan Hajiyar tana dubanta.


  "Ke ma kinsan dai abin da ya ke sani faɗa a cikin kwanakin nan, Kamal ya kafe baya ji baya gani kan batun auren nan ya da ge dole sai ya yi".


    "To Hajiya banda abinki ki rabu da shi mana shifa ya ji ya gani zai iya sai ki zuba masa ido".


    "Amma Farida kina ganin hakan dai-dai ne?, A ce Kamal duk cikar garin nan ya rasa matar aure sai Hajiya Shema'u !".


    "Hmm Hajiya ni dai da za ki bi shawarata ki sauwaƙewa kanki tunanin auren Kamal a ranki, kada ki jawo wa kanki hawan jinin da ba ki da shi, ba muji ba ba mu gani ba".


  "Shi kenan Farida amma abin ne dole ya dame ni".


  "A dai bar maganar Hajiya".


  Farida ta yi maganar tana mai miƙewa zuwa gaban TV ta kunnawa Hajiyar domin ta ɗebe mata kewa ita kuma ta faɗa kitchen domin yi musu sanwar rana.


  Kamal na fita bakin titin layinsu ya ci karo da abokinsa kuma amini Zayyad suka gaisa ci ke da kewar juna.


  "Ya dai mutumin naga yau cikin  farin ciki ka ke, ko batun aikin ne ya samu?".


  "Kai dai bari Zayyad, Wanne batun aiki kuma, ga babban albishir ɗin da yafi min komai daɗi, Hajiya yau ta amince da batun aurena".


  Lokaci guda annurin kan fuskar Zayyad ya ɗauke, domin jin maganar ya yi tamkar saukar aradu cikin kunnuwansa, baki galala ya ke bin Kamal da kallon mamaki.


    "Hajiya ta amince fa ka ce?".


    "Yes kana mamaki ko?, ni ma wallahi ko a mafarki ban yi tunanin amincewarta da wuri haka ba".


    "Waima na tambayeka, dama maganar auren har yanzu tana nan baka barta ba?".


    "Ya kuwa za'a yi na barta Zayyad? Arziki ya tako ya kwankwasa min ƙofa har cikin gidanmu har makwancina ya zo ya sameni, ni kuma sai in sa ƙafa inture shi?, ina..! Ba zai yi yu ba Zayyad, ina haskoni cikin arziƙi madawwami arziƙin da babu yankewa million ashirin da wani abu ba wasa ba".


  Zayyad ya ja dogon tsaki ci ke da takaicin maganar abokin nasa ya dube shi da kyau.


    "Kamal duk wani arziki idan ba alkhairi ba ne kayi addu'a Allah ya yi maka tsari da shi, domin idan har zaka samu arziki mai dorewa ta dalilin auren Hajiya Shema'u to aurenka da ita babu alkhairi a ganina, ka buɗe idonka ka farka daga mummunan mafarkin da ka ke me zaka yi da million ashirin? Ba yan ka ɓata sunanka, ka ɓata sunan danginku, me million ashirin zata yi maka akan auren wata can tsohuwar kilaki..?".


  "Dakata Zayyad..! Ka iya bakinka, ka san hakan na ɗaya daga cikin abinda ya ke haɗamu ko? Idan ka san ba za ka dinga faɗin alkhairi ba to ka yi shiru, Annabi ma ya faɗa".


  "Kamal kenan ! Shikenan Allah ya taimaka ya ba da sa'a, wanda yaƙi ji, baya ƙi gani ba".


    "Amin".


  Kamal ya amsawa Zayyad cikin fushi kowannansu ya wuce ba tare da yiwa ɗan uwansa sallama ba duk da ce war basu ji daɗin rabuwar tasu a haka ba.


  BAYAN SATI DAYA.


     Da sallamarsa ya sanya kai cikin gidan, bayansa yara ne biye da shi ɗauke da akwatuna biyu suka ajiye a filin tsakar gidan Kamal ya zaro naira ɗari  ya basu ladansu suka fi ce.


     Faridah da ke shirin fita daga gidan cikin shigar uniform hijab har ƙasa da alamu islamiyya ta nufa, ta dube shi tare da ɗauke kai ta gaida shi ta yi wucewarta ba tare da ta damu da amsawarsa ba, domin ita yanzu baki ɗaya haushi ya ke bata, mussamman ganin a kwatunan da ta yi a yanzu ya ƙara tabbatar mata har yanzu yana kan bakansa kenan.


  Kamal yabi bayanta da tsaki, cike da tsantsar tsana da takaici, sabida shi duk wanda ba zai goyi bayan aurensa ba a yanzu to sun raba hanya kenan, baki ɗaya yakan ji ya tsani mutum domin gani yake babu wani babban maƙiyinsa a duniya sama da kai.


  Ɗa kansa ya ja akwatunan har cikin falon Hajiyartasu yana mai kwalawa Sakinah matarsa kira ta fito da sauri zuwa falon Hajiya ta zube kan carpet tana jiransa domin tuni ya wuce cikin ɗakin Hajiyar zai kirawota.


  Baifi mintuna biyar da shiga ba suka fito tare tana faɗin.


    "Wai wane kaya ne haka ka kawo? Da za ka sako ni a gaba dole in zo in gani?".


  Ganin akwatuna yasa ta yi turus tana bin Kamal ɗin da kallo, shi kuwa gogan neman guri ya yi ya zauna yana sosa ƙeyarsa.


    Hajiya ta zauna tana duban Kamal domin jin mai zai ce.


    "Hajiya kayan faɗar kishiya ne na Sakinah na kawo mata domin Hajiya Shema'u ta ce bata buƙatar komai illa sadaki, hakan yasa na fita haƙƙin Sakinan na siyo mata nata kayan".


  Ya mai da dubansa gun Sakinah.


    "Ga kayan nan ki duba duk abinda babu kiyimin magana, sannan Hajiya gobe masu fenti za su zo suyiwa gidan fenti za'a gyara duk inda ya kamata".


  Kamal ya sunkuyar da kai yana sosa ƙeya sabida irin kallon da Hajiyar ke binsa da shi, amma hakan bai hana shi dakatawa daga maganar da ya faro ba.


    "Hajiya nan da kwana uku fa za'a ɗaura auren ranar juma'a ken..!".


  "Allah ya kaimu ya nuna mana".


  Hajiyar ta faɗa kafin ya kai ƙarshen maganar ta miƙe tana mai shigewa ɗakinta tabarsu nan zaune, tana shiga ɗakin Sakinah ta miƙe itama zata fi ce.


  "Uban waye zai ɗauke miki kayan?".


  Kamal ya dako mata tsawa, Sakinah ta juyo ta dube shi kawai ba tare data ce komai ba taja akwatunan zuwa ɗakinta.


  Tana shiga yana sanyo kai shima cikin fushi ya fizgo gashin kanta yana faɗin.


    "Duk baƙin cikin da zaki yi da wani munafukin kishi sai dai ki yi ki gama, aure babu fa shi, domin nan da kwanaki Kamal zai koma Alhaji Kamal".


  Ya kai maganar yana mai sanya dariya, Sakinah ta fizge kanta ta yi wucewarta ɗaki ba tare da ta tanka mai ba, Kamal ya ƙara zuciya yabi bayanta .


    "Wato kin mai dani ɗan iska ko dan tsabar rashin mutunci da rainin wayo antaimaka miki ansiyo miki kayan amma babu ko godiya bare addu'a".


    "Angode Allah saka da alkhairi".


  Ta bashi amsa a taƙaice, ba tare da ta yi yunƙurin duban inda ya ke tsaye ba.


  Kamal ya yi kwafa ya cije leɓe  yana mai ƙarewa ɗakin nata kallo.


    "Nan da kwanaki wadannan ko ɗaɗɗun kayan naki sai dai mukai bola ba zai yi yu Alhaji Kamal yana kwanciya akan ruɓaɓɓen gadonnan ba, ko da ya ke gida zan siya mai part uku kawai ke ɗaya amarya ɗaya Hajiya ɗaya komai sabo za'a zuba".


  Ya kai maganar yana mai sauke kallonsa akan kayansu da ta fara ninkewa kafin ya shigo kallo.


  "Hatta kayanku sai dai Ku bayar ko Ku ƙona komai sabo zan siya domin ba za'a zo gidan Alhaji guda aga tsumma ba".


  Sakinah tayi murmushi kawai tana mai ci gaba da ninkin kayan.


  "Au dariya na ke baki ma?".


  "A'a Yallaɓai wace ni da yi maka dariya? wani abu na tuna kawai".


  Kamal zuciya ta zo masa wuya, ya yi kwafa tare da cijen leɓansa na ƙasa da ƙarfi, kafin ya fice fuuu daga cikin ɗakin yana mai jin haushin Sakinah akan a abin da take masa cikin kwanakin nan.


  Tama mai da shi wani hotiho ko hamago, kome zai yi mata domin ta ji haushi ba ta ji, ƙarshe ma shike dakon kayan takaicin ba ita ba.

  *JINI BA YA MAGANIN ƘISHIRWA*
  Na

  QURRATUL-AYN.


  NAGARTA WRITERS ASSOCIATION.


  02.


  Kamal na fita daga cikin gidan kai tsaye Unguwar jan bulo ya nufa, layin farin gida gidan Hajiya shema'u.


    Da zuwansa bugu ɗaya ya yi wa ƙofar gate ɗin, mai gadi ya buɗe masa ƙofa ya shiga, da ya ke mai gadin ya san shi kuma Hajiya ta gargaɗe shi akan Kamal, ko da wasa ka da ta ji labarin ya wulaƙanta mata shi, shi yasa da ya ganshi da tsumar jiki ya ke tsugunnawa ya gaishe da shi, duk kuwa da irin tarin tazarar shekarun da ke tsakaninsu domin a haife tabbas zai haifi Kamal.


  Amma shi gogan naka ko a jikinsa sa asalima ko amsa gaisuwar ba ya yi, ya ke wucewa abinsa yana wani hura hanci sama, a ganinsa ya fi ƙarfin ya tsaya amsa gaisuwar talakan ba kauye irin wannan mutumin.


  Mai gadin yabi bayansa da kallo har sai da ya daina hango inuwar hular, sannan ya miƙe daga tsugun nen da ya ke yana mai girgiza kai tare da tausayawa Kamal a kan gudun wuce sa'ar da ya ke shirin yi wa rayuwarsa.


    Gida ne wanda ya amsa sunan gida, domin tun daga wajen gate na gidan zaka san naira na kuka a cikin, labarin ya kan canja ne daga inda mutum ya yi tozali da tsari da tsaruwar cikin gidan, a wannan lokaci kai ne ka dai alƙalin da zaka iya lissafin irin dukiyar da aka ɓarnatar, amma tawadar alƙalamina ta yi ƙaran ci wajen iya zayyano maku fasali na gidan.


    Da sallamarsa ya sanya kai cikin  falon, sabida a halin yanzu Kamal ya zamto tamkar ɗan gida kamar yanda take faɗa a kullum, baya buƙatar iso a wajenta Kafin isowarsa, duk sanda ya so ya ke kuma da ra'ayin zuwa gare ta tana maraba marhabin da shi.


    Hajiya Shema'u da ke zaune saman ɗaya daga cikin jerin kujerun da suka yiwa falon ƙawayen ta ɗago kai tana amsa masa sallamar, Masha Allah shi ne abin da dukkan bil'adam da da ya yi to zali da kyakkyawar fuska irinta ta zai iya ambata mace ko namiji.


  Domin ga inda kyawun asali ya ke, Hajiya Shema'u maca ce dirarriya irin matan nan masu matsakaicin tsayi da jiki daidai misali, fara ce sosai tamkar ka taɓa jini ya fito bama ce farinta ba ne zallah, domin zamani ya zo mana da mawuyaci ne ka samu macen da bata harka da mayukan gyaran fata masu ƙara fito da zallar asalin farin mutum da sheƙi musamman manyan mata irinsu, dogon karan hancinta da ya da ce da doguwar fuskarta tamkar an dasa shi, shi ne abu mafi kusa da ke fara janyo hankalin dukkan namijin da ya yi tozali da ita, ma'abociyar manyan idanuwa ce, mai yalwar suma dake kwance lub saman goshinta har zuwa bayanta, a taƙaice dai ba lallai ne daga kallo ɗaya akan wannan mata ba ka iya gano makusarta nan take ba.


  Yarinyar da ke durƙushe gabanta tana danna mata ƙafafuwanta ta miƙe da sauri kai a ƙasa ta nufo bakin ƙofar da Kamal ya ke tsaye, ta ɗan risina kaɗan ta gaishe da shi tana mai cigaba da tafiya har ta fi ce daga falon, Kamal kuwa ɗan taɓe baki ya yi kaɗan kafin ya ƙarasa cikin tsakiyar falon ya nemi guri inda Hajiya Shema'u ke zaune ya zauna a gefanta kafin su kalli juna dukkansu suka yi murmushi a tare.


    "Yallaɓaina kai ne tafe haka? Ban yi tsammanin zuwanka da wurwuri haka ba".


  Kamal ya shafo sumar kansa ta baya kafin ya ɗan taɓe baki ya ce.


  "Wallahi matar can ce ta ɓata min rai matuƙa, shi ne kawai na yi yo ta nan, domin nasan nan ne zan iya samun ishashshan farin ciki".


  Hajiya Shema'u ta ɗan yi wata gajeriyar dariyar irin ta manyan mata, ka fin ta bashi amsar.


    "A'a fa Yallaɓaina ko dai kai ne ka ɓata mata? Domin nasan halin Sakinah bana jin hakan daga gare ta".


  Kamal ya ja dogon tsaki, yana mai kau da kai gefe ya ɗora idanuwansa akan TV, kafin ya furta.


  "Yardarki akanta harta kai haka?".


    "Fiye da haka ma".


  Ta bashi amsa a taƙaice, Kamal ya dube ta da mamaki kafin ya basar sai ya samu kansa da fiddo mata da tambayar da ba ita ce a cikin zuciyarsa ba.


    "Wai dama a halin yanzu akan samu matan da basa kishin mazajensu?".


  "Kamar ya kenan?".


  Kamal ya juyo da hankalinsa baki ɗaya wajen Hajiya Shema'u, yana mai cigaba da faɗin.


    "E to kawai naga kamar Sakinah bata kishi akan aurenki da zan yi".


     "Kai kishin ka ke so ta nuna maka kenan?".


  Kamal ya yi murmushi kawai yana jujjuya amsar da zai bata cikin ransa tsayin wasu da ƙiƙu kafin ya furta mata.


    "Ba haka ba ne".


  "To ya ya ne?".


  Kamal ya sake ɗago kai ya dubeta yana tantama akan amsar da zai bata, sabida sosai take yi masa kwarjini baya jin zai iya furta mata amsar da ke lulluɓe ƙasan zuciyarsa.


    "Mubar maganar kawai, kin kira ni tun safe na zo, ina kasuwa ne bana jinki sosai, shi yasa na bari kawai na zo har gida na ji lafiya?".


  Kamal ya yi ƙoƙarin ajiye zancen da suka faro a gefe ya sanyo wani, Hajiya Shema'u ta ɗanyi guntun murmushi domin ta gane janye zancen ya yi.


    "E haka ne, ɗan jira ni kaɗan".


  Ta kai maganar tana mai miƙewa ta nufi wata ƙofa da ke nan cikin falon, cikin wani irin taku da salon tafiya mai jan hankalin ma'abocin kallonta, Kamal da ya bita da kallo harta shige ɗakin ya sauke ajiyar zuciya yana mai gyara zamansa sosai akan kujerar da yake zaune, a daidai lokacin kuma 'Yar aikinta da ta fita ɗazu ta yi sallama cikin falon hannunta ɗauke da tire ta ajiye akan ɗan ƙaramin table ɗin da ke tsakiyar falon ta juya abinta.


    A daidai lokacin kuma Hajiya Shema'u ta buɗe kofa ta fito daga cikin ɗakin da ta shiga, hannunta ɗauke da wata baƙar jaka mai shegen kyau, anyi mata adon duwatsu farare sai sheƙi da walwali take.


    Zama tayi kusa da Kamal daidai sanda ya ke ƙoƙarin zuba lemo a cikin ɗan ƙaramin kofin ƙarau (glass), Hajiya Shema'u ta yi saurin karɓa ta ƙarasa zuba masa ta miƙo masa ya karɓa fuskokinsu na wanzar da yalwataccen murmushi mai tsada, sai da Kamal ya sha kusan rabin lemon kafin ya ajiye kofin yana mai dawo da kallonsa gunta sosai da alamun sauraronsa ya ke yi akan batun kiran da ta yi masa.


    Tamkar tasan abin da ya ke nufi ta sake gyara zamanta kafin ta buɗe jakartata ta fiddo invitation card ɗauri guda ta ajiye a gabansa, Kamal ya ajiye dubansa akan katunan kafin ya miƙa hannu ya zaro ɗaya yana mai karanta wa.


  Ƙayataccen murmushi ne ya kufce masa na ganin kyawu da tsaruwar katin ɗaurin auren nasu shi da ita, sai da ya karanta sau biyu kafin ya ɗago kai ya dube ta.


    "Dukkan wannan gatan ni ka dai?".


  Hajiya Shema'u ta wanzar da taƙaitacciyar dariyarta kafin ta bashi amsa, wacce da dukkan alamu ta zame mata jiki ne, ko kuma dan tasan tana yi mata kyau ne ya sanya ko da yaushe take yinta oho?.


    "Ka wuce hakan a gare ni Yallaɓaina, tun da ka sanya hannu biyu ka karɓi soyayyata ba tare da gargada ba tabbas zan yi maka dukkan halicci gabanin auren mu..!".


  Hajiya Shema'u ta taƙaice zancen nata tana mai cigaba da jifansa da mayaudarin murmushinta wanda ke wanzar da farin ciki da annashuwa ga dukkan mahalukin da ya yi to zali da shi.


    "Ina godiya matuƙa Hajiyata Allah dai ya tabbatar mana da wannan auren ya yi mana katangar ƙarfe da duk kan wani maƙi gani a gare mu".


    "Amin s amin".


  Ta amsa tana mai kai hannu kan tire ɗin ta ɗauki tufa ta fara ci a hankali suka hau hirarsu cikin annashuwa da jin daɗi.


    

  ***


    Ko da Sakinah ta kammala ninkin kayan da ta ke yi, baki ɗaya hankalinta ya ƙara tashi matuƙa, ga wani abu da ke ƙasan ƙirjinta wanda ke yo iyo zuwa maƙogwaronta ya tokare mata ƙirji, yaƙi gaba yaƙi baya, ta yi jugum tsayin wasu daƙiƙu ba ta yi aune ba sai jin abu ta yi na bin fuskarta ko da ta duba hawaye ne, da saurin ta sanya hannu ta share a lokacin kuma wayarta ƙirar kamfanin Tecno ta fara kukan neman agaji a gare ta.


  Hannu ta kai a hankali ta janyo ta cikin yanayin kasala da damuwa, ganin sunan Ummanta ya sanya ta ƙara ƙarfafa jikinta da muryarta kafin ta ɗaga wayar haɗe da sallama ta kara wayar bisa kunnenta.

        


    Daga can ɓangaren Mahaifiyarta ta amsa sallamar tana mai cigaba da faɗin.


    "Lafiya dai ko Sakinah? Na ji muryarki ta yi wata iri alamun kuka kike yi ko?".


  "A'a Umma, kuna lafiya yasu Sajjad".


  Sakinah ta yi saurin kau da zancen, sabida bata yiwa mahaifiyarta ƙarya, kuma ba tajin zata iya gaya mata damuwar da take ciki a halin yanzu.  


    "Lafiya ƙalau Sakinah, ya nan gidan naku, komai lafiya ƙalau ko?".


    "E Umma, dama yanzu nake shirin kiran ki sai ga shi kin kira".


    "E to naso ma na zo da kaina ne, sai kuma muka wayi gari Sajjad ba lafiya".


    "Ayya Sikilar ce ta motsa".


  "E amma da sauki sosai, barci ma ya ke yi yanzu haka".


    "Allah ya ƙara sauki"


  "Amin".


  Umman ta amsa, Sakinah ta cigaba da faɗin.


  "Umma dama Sajidah na ke so ki bani aro ta ta ya ni aiki, sabida gobe Kamal ya ce za'a zo a ɗan yi mana gyare-gyaren gidan".


    "E daman na ce zan turota, domin jiya ya zo nan ya yi mana batun auren, ya ce a baki Sajidah ta ta ya ki ayyuka, juma'a ne ɗaurin auren ko?".


  Sai da ƙirjin Sakinah ya yi wata irin bugawa har sai da ta kai hannu ta dafe gurin, da ƙyar ta iya bawa Umman amsar.


    "E ɗa zu ya kawo min akwatuna biyu ma, wai na faɗar kishiya".


    "Masha Allah, Sakinah..!".


  Umman ta Kira sunanta, Sakinah ta amsa murya can ƙasa, Umman ta cigaba da faɗin.


    "Ki ƙara haƙuri Sakinah akan wanda na sanki da shi, dukkan macen da ki ka ga ta ci ribar zaman aure kuma ki ka ganta zaune lafiya a cikin gidan ta, to indai kin bibiya ribar haƙuri da gajiyarsa ta ke ci,  sannan ki ninka soyayyar mijinki a ranki fiye da yanda ki ka so shi kafin auren ku, ta hakan ne za ki samu damar kyautata masa tare da yi masa biyayya fiye da zamanku a da, ka da ki yarda da dukkan wata gurguwar shawarar ƙawa ko zancen 'yan unguwa, ki girmama mahaifiyarsa kiyi mata biyayya tamkar yanda za kiyi min".


    "Sakinah..! Haƙuri haske ne mai haska dukkan tsananin duhu, haka kuma juriya a bace mai wanzar da mutum zuwa tafarkin da bai yi tsammani ba, a matsayina na mahaifiyarki na hore ki da abubuwan nan ba dan komai ba sai dai su ne ka ɗai ababe masu ɓullewa, ki sanya a ranki aurenki a yi ke yi, kuma aure ibada ne ga ko wacce 'ya mace ta duniya, kuma shi ne cikar mutunci da kamala ga dukkan wata 'ya mace, ko kaɗan ka da ki nuna fushi ko jin haushi akan auren nan, asalima ki ƙarfafa masa gwiwa idan da dama, hakan ka ɗai zai sanya ki dasa kujera a zuciyar mijinki, kujerar da babu wata wadda ta isa ta tumɓuke ta, sai ma ƙarin daraja da girma da ƙima da hakan zai janyo miki a gare shi".


    "Sannan ki dage da addu'a matuƙa, ki kasance mai raya daran barcinki, ka da ki gajiya, ka da addu'a ta yanke a bakinki duk tsanani, domin ita ce ka ɗai maganin da zata iya warkar miki da ciwon kishi, kishi dole ne ga 'ya mace Sakinah amma na hore ki da yin kishi mafi tsafta akan mijinki, ki yi haƙuri ki danni zuciyarki kinji Sakinah..!".


  Sakinah ta share hawayen da ke zuba kan kuncinta kafin ta ce.

  JINI BA YA MAGANIN ƘISHIRWA*

  Na

  QURRATUL-AYN.


  NAGARTA WRITERS ASSOCIATION.


    03.


     Sakinah ta share hawayen da ke zuba kan kuncinta kafin ta ce.


    "Insha Allahu Umma zan yi aiki da dukkan abin da ki ka umarce ni da shi da yardar Allah, ba zan taɓa baki kunya ba".


    "Yauwa Sakinah Allah ya yi miki albarka".


    "Amin".


  Sakinah ta amsa, ya yin da Umman ta cigaba da faɗin.


    "Kin yi waya da Yayanku kuwa? Ya ce min sun kusa dawowa mu taya shi da addu'a".


    "E ya kira ni jiya, ya ke faɗa min  cikin satin nan zai kammala HND ɗin sa, zasu dawo gida amma bai faɗa min ranar da zasu dawo ba, wai ba zata zai yi mana".


    "To Allah ya ba da sa'a, ya dawo mana dasu lafiya".


    "Amin Ummata, a gaishe min da Abba da su Sajjad idan ya ta shi".


    "Za su ji insha Allah, a cigaba da hakuri dai Sakinah".


    "Insha Allah Umma nagode".


  Kusan a tare suka kashe wayar, Sakinah ta ajiye wayar gefan inda take zaune kan gado, fuskarta wasai da dukkan alamu ta ji daɗi matuƙa kan wayar da su kayi da Ummanta, sosai ka so goma daga cikin ashirin na damuwarta ya kau, hakan ne ya sanya nan ta ke ta ji ƙarfin gwiwar ya zo mata ta miƙewa tare cigaba da ayyukanta. 


  4:30.


  Ƙarfe huɗu da rabi ta kammala dukkan gyaran ɗakunan su har zuwa falo ta sanya turaruka masu daɗin ƙamshi da jan hankalin dukkan wanda ya shaƙesu, kicin ta faɗa domin ɗora musu sanwar dare abincin da Kamal yafi so da ƙauna ta ɗora jallof ɗin shinkafa da bushashshen kifi, ta yi mata haɗi na musamman, ba ta damu da haɗa lemo ba domin ba kasafai yake shan na haɗawa ba yafi son na kwali.


    A gurguje ta kammala ta ɗauko kula ta zuba masa ta zubawa Hajiyarsa, ta gyare gurin tsab sannan ta koma ɗaki domin yin shirin wanka.


  Cikin mintuna talatin da biyar ta kammala ta yi kwalliyarta cikin atamfa Hitarget yaluwa mai ratsin ja da baƙi riga da siket, sun mata kyau sosai duk da cewar ba wata kwalliya ta yi wa fuskarta ba, babu laifi Sakinah kyakkyawar maca ce, dukkan wani cikar halitta na matan hausa Fulani ta haɗa, maca ce son kowa ƙin wanda ya rasa, gata ko da yaushe fuskarta sake shiyasa ba lallai ne ka gane tana cikin damuwa ba in dai ba abin ya yi tsamari ba.


    Kular abincin Hajiya ta ɗauka tare da sanya takalmi mai kamar silifas ta nufi ɗakin Hajiyar, da sallamarta ta sanya kai cikin falon, Hajiya dake zaune kan carpet a falon ta ɗago kai tare da amsa sallamar.


  Sakinah ta ƙara so gareta haɗe da durƙusawa ta ajiye kular abincin a gefe, kafin ta gaishe da ita, Hajiyar ta amsa gaisuwar fuskarta wasai alamun jin dadin ganin Sakinah ya wanzu a kana fuskarta.


  Maganin ciwon ƙafar Hajiya da ke riƙe a hannunta ta kalla tana faɗin.


    "Kawo na shafa miki Hajiya, Farida bata dawo ba kenan?".


     "E ta ce min zata biya dubo Husnah bata da lafiya".


    "Allah sarki Allah ya bata lafiya, yasa kaffara zazzaɓi ne ko?".


    Sakinah ta yi tambayar tana mai amsar maganin ta fara shafawa Hajiyar tare da ɗan danna mata ƙafar dan ta ji daɗi.


    "Kin san ciwon yanzu baya wuce maleria, abin sai addu'a ga zazzaɓin da nacin tsiya sai ya tafi ya dawo".


    "Wallahi kuwa Hajiya, ɗazu muka yi waya da Umma ma, ta ce a gaishe da ku, Sajjad ma yana kwance amma ta ce min da sauƙi sosai".


    "Allah ba shi lafiya, ciwon ya tashi kenan?".


    "E wallahi?".


  Hajiyar ta ɗan gyara zamanta kaɗan kafin ta cigaba da faɗin.


    "Ai yaron na fama da jiki wallahi, sikila sai addu'a ciwo mai wuyar sha'ani ga wahalar da mutum".


    Sakinah ta ɗan yi murmushi, ba tare da ta ce komai ba, Hajiyar ce ta cigaba da magana.


    "Sakinah ki yi haƙuri akan halayyar Kamal, ni kai na bani da yanda zan yi ne, dole ce ta sanya na amince da auren nan domin gudun abin da gobe zata haifar".


    "Babu komai insah Allahu Hajiya".


    "Da komai fa Sakinah..!, ka da kiyi zargin laifina ne da ban hana shi ba, sanin kanki ne ya sauya matuƙa cikin kwanakin nan, ina tsoron ka da kafiyata akan ƙin yarda da auren ta sanya ya faɗa wata harkar ta da ban domin biyan buƙatarsa, na amince da auren Kamal ne dan ka da ya jefa kansa ga halaka, akan abin da bai taka kara ya karya ba, gara na amince ya yi auren akan na hana shi ya biyewa sharrin sheɗan da zugar zuciya ya kaucewa hanyar data da ce".


    "Da a ce yau jinina yana aikata mugun saɓo musamman zina, Gara a ce yau gudan jinina ya auri sa'ar kakarsa Sakinah, domin zina bashi ce, ba kai da ka ke aikatawa ake gujewa ba, ka jajawa wanda bai ji ba bai gani ba shi ake gudu, nasan Kamal na zalintarki domin ina hankalce da dukkan  abin da ke wakana agare ku, amma ba ni da yanda zan yi ne, ba ni da abin da  zan iya yi a halin yanzu wanda ya wuce addu'ar Allah ya dawo da shi hanya, ya sa ya gane gaskiya, kema ina roƙonki da ki da ge da addu'a Sakinah, addu'a makamin mumini ce kuma bata taɓa faɗuwa ƙasa banza, wata rana sai labari, nasan kina haƙuri amma ki ƙara akan na da kinji".


  Sakinah ta yi murmushi daidai sanda take rufe kwalbar maganin Aboniki ɗin, ta ɗago kai ta dubi Hajiyar kafin ta sauke su ƙasa tana faɗin.


    "In Allah ya yarda Hajiya zan yi aiki da shawararki a gare ni, nagode sosai da tunatar wa".


  Nan dai suka cigaba da hira jefi-jefi, yawancin hiran duk akan  tausar Sakinah ne Hajiyar ke yi tare da bata baki, haka ne yasa sosai Sakinah ke matuƙar son mahaifiyar Kamal da bata girma matuƙa, domin ita ba suruka ta dauki Sakinah ba ta ɗauke ta ne tamkar 'Yar data haifa a cikin ta.


  ***


  Kamal ba su yi sallama da Hajiya Shema'u ya baro gidan ba sai ana kiraye-kirayen sallar maghriba, a masallacin unguwar ya yi sallah kafin ya nufo gida zuciyar na tunani kala-kala akan yanda zai je ya tadda Sakinan.


  Sakinah bata bar ɗakin Hajiya ba  sai da aka kira sallar maghriba a masallacin unguwar, lokacin Farida ta jima da dawo wa sun ɗan yi hira kafin daga baya ta yi musu sallama ta nufi ɗakinta.


  Tana shiga ban ɗaki ta nufa ta ɗauro alwala, tana fitowa ta shi ge ɗaki ta shimfiɗa abin sallah tare da sanya hijab ta tayar da kabbarar sallah.


  Bata jima da idarwa ba tana cikin ninke hijab ta tsinkayo sallamarsa tsakar gidan, mudubi ta nufa ta ɗan sake gyara fuskarta tare da sake feshe dukkan sassan jikinta da turare kafin ta fito zuwa falon, ta nemi ɗaya daga cikin kujerun falon ta zauna tana jiran shigowarsa.


  Sai da ya fara shiga ɗakin Hajiya ya yi mata barka da yanmaci kafin daga baya ya fito zuwa ɗakinsu, a can ƙasan maƙoshi ya yi sallama cikin falon nasu, Sakinah ta masa tare da miƙewa tsaye tana faɗin.


    "Sannu da zuwa Habibina".


  "Yauwa".


  Ya amsa mata a taƙaice yana mai zama kan kujerar tare da ajiye ledar katunan bikin a gefansa sai faman wani cika yake da batsewa haɗe da shan ƙamari, Sakinah ta yi murmushi ta zauna a gefansa tana mai cigaba da faɗin.


    "Ya jama'a da rana, yau naga an yi rana sosai".


    "Lafiya".


  Ya sake amsa mata, gyara zamanta ta yi, murmushi kan fuskarta har a lokacin bai gushe ba daga gareta.


  "Nasan ka gaji Sweety, da me zaka fara wanka ko cin abinci? Sabida yau abin da ka fi buƙata na girka maka".


  Bai ko kalleta ba, bare ma ya nuna cewar yasan tana magana, illa ledar katunan bikin da ya buɗe ya ɗebo kusan guda biyar ya ɗora mata akan cinyarta, har a lokacin bai ce da ita komai ba.


  Sakinah ta ɗauki katunan tana dubawa yayin da can ƙasan zuciyarta na ta yi mata lugude, ga wani irin zugin zafi da zuciyarta ke yi, da ƙyar ta yi ƙarfin halin ƙaƙalo murmushin dole tare da daidaita tsayuwar numfashinta kafin ta furta.


    "Kai..! Masha Allah katunan sunyi kyau sosai matuƙa wallahi, Allah dai ya kaimu ranar ya nuna mana".


  Sai a lokacin Kamal ya ji yo ya dube ta baki galala cike da tsantsar mamakinta, akan kawaici da basarwa irin nata.


     Kamal ya gayyato murmushi zuwa kan fuskarsa sosai ya nuna matuƙar jin dadin akan maganarta tunaninsa zata ji haushi, hakan ya sa cike da zaƙuwa ya amsa da.


    "Ya burgeki sosai haka?".


    "Sosai kuwa, ya yi kyau wallahi".


  Sakinah ta kai maganar tare da miƙe wa tana faɗin.


  "Bari dai na je na haɗa maka ruwan wankan, domin nasan zaka fi buƙatar wanka a halin yanzu".


  Bata damu da amsawarsa ba ta yi wucewarta, Kamal ya bi bayanta da kallo a cikin ransa yana faɗin.


    "Wannan kuma wacce irin mata ce haka?".


  Murmushi ya yi tare da jan tsaki kaɗan, sosai kwalliyarta ta burgeshi amma girman kai da gadara yasa ba zai nuna mata ba,  yana gudun ka da ya nuna mata raini ya ɓulla har ya samu gurin zama a tsakaninsu.

  JINI BA YA MAGANIN ƘISHIRWA*

    Na

  QURRATUL-AYN.


  NAGARTA WRITERS ASSOCIATION.


     04.


    Yana fitowa daga wankan kai tsaye gaban mudubi ya nufa, tun kafin ya kai ga ƙara sawa idanuwansa suka tsinkayo masa  ƙananan kaya ya she akan gado riga da wando,  da dukkan alamu Sakinah ce ta ajiye masa su, sai faman wani tashin ƙamshin dad-daɗan turare su ke yi, ɗan taɓe baki ya yi kaɗan kafin ya ƙarasa  gaban gadon ya fara ƙoƙarin sanya wa.


    Yana kammala shirin kai tsaye falo ya nufo, lokacin Sakinah ta kammala  jere masa abincinsa tsakiyar falon, kai tsaye wajen abincin ya nufa ya zauna, yayin da Sakinah ta yi murmushi tare da tsugunnawa ta fara zuba masa abincin, har ƙasan ransa bai yi ni yar cin abincin ba, amma to zali da ya yi da abincin da yafi so da ƙauna ga kuma tashin ƙamshin abincin na musamman ya ke jinsa a yau, nan ta ke ya ji kamar an yashe masa cikinsa har ya ƙagauta da son fara ci, sai faman haɗiyar yawu ya ke.


    Sakinah ta ajiye masa abinci a gabansa, nan da nan ya fara aikawa cikin bankin cikin, ba Sakinah ba shi kansa ya yi matuƙar mamakin irin abincin da ya ci, kai ka ce wunin ranar bai ci komai ba ne, sabida irin tulin tarin abincin da Hajiya Shema'u ta ciyar da shi a yau, bai yi tsammanin zai sake kallon wani kalar abinci ba a ɗan ta ƙaitaccen lokaci kamar wannan ba, amma sai ga shi lokaci guda ya share abinci faranti guda.


    Sosai Sakinah ta ji daɗi a ranta, sabida rabon da ya ci abinci da yawa haka tun kafin ya fara maganar aurensa, farin cikinta kasa ɓoyuwa ya yi har sai da ta kai ga furta.


    "Mijinah abincin ya yi maka dadi sosai, da dukkan alamu bakinka ya yi kewar girkin gimbiyarka ko?".


    Kamal ya yi ajiyar zuciyar kawai tare da miƙa hannu ya ɗauki ruwan da ta zuba masa cikin kofi ya sha kaɗan ya ajiye kafin, tare da ɗan yin gajeren murmushi kafin ya ce.


    "Ni ma dai na yi mamakin yanda aka yi na ci abincin da yawa haka, kuma kin san cewar a ƙoshe na ke wallahi, amma dad-daɗan ƙamshin girki ya ja ni na wafce abincin ciki biyu".


  A tare suka yi gajeriyar dariyar, kafin su yi shiru ko wanne daga cikinsu yana saƙe-saƙe cikin ransa, Kamal ya katse shirun da faɗin.


    "Kin duba kayan dana kawo miki kuwa?".


    "Wayyo..! Wallahi shaf na sha'awafa inata faman aiki ne tun sanda ka fita ka barni, ko da ya ke yanzuma bata ɓaci ba, bari na ɗauko mugani tare kallon ya fi daɗi ma".


    Ta kai maganar tana mai kanne masa ido ɗaya, ta miƙe tsaye tare da ba shi baya ta nufi cikin ɗaki, baki galala ya bita da kallo cike da guntun murmushin da bai san yana yinsa ba, sai daga baya ya yi gajeren tsaki tare da ɗan bugun kansa kaɗan yana girgiza wa.


    Ɗaya bayan ɗaya ta fito da akwatunan kafin ta zauna tana mai da numfashi a hankali, daga baya kuma ta hau buɗe kayan tana gani, ci ke da tsantsar farin ciki duk wanda ta ɗa ga sai ta ce.


    "Masha Allah, kamar kasan kuwa zan so wannan".


  Ƙananun kaya saiti biyar ta gani ciki, tare da dogwayen riguna guda uku, nan da nan ta miƙe cike da ɗauki ta fara gwadawa, wai ya gani idan zasu yi mata kyau, tun Kamal na basar da ita har dai ya biye mata, har da su dariya da hira kala-kala cike da nishaɗi, Sakinah ta ji tamkar su dauwama a haka, nan ta ke wasu al'amuran watannin baya suka fara katantanwa a cikin kwakwalwarta, kwallar da ke ƙoƙarin zubar da ruwa kan fuskarta ta yi saurin sharewa tare da saurin kau da tunanin da ke shirin bijiro mata, a daidai lokacin kuma suka sinkayo sallama bakin ƙofar falon.


    Sakinah ta amsa sallamar tana mai nufar ƙofar falon, ganin Sajidah tsaye ya sanya ta buɗe baki cike da dariyar jin daɗi ta ke faɗin.


    "Shigo mana kamar wata baƙuwa, sai ki tsaya kina faman kwaɗa sallama haka".


    Sajidah ma dariyar tayi kafin ta bata amsar.


    "Kin ji kuma Aunty Sakinah, ko ba baƙuwa ba ce ai sallama ta zama dole a gare ni, domin jajjada koyarwar addinin islama".


  "Kin yi gaskiya sarkin zance".


  Kamal ya bata amsa yana mai miƙewa tsaye daidai lokacin aka fara kiraye-kirayen sallar isha'i.


    "Kin zo a daidai, na miƙe a daidai ga kiran sallah can ana yi, ya ki ka baro Abba da Umma, ya jikin Sajjad kuma?.


    "Alhamdulillahi duk suna gaishe ku, na jima da zuwa fa ina wajen Hajiya muna gaisawa tun ɗa zu".


    "Masha Allah da kyau hakan, ni dai zan wuce masallaci to".


    "A dawo lafiya Yayana".


  Cewar Sakinah kenan ta faɗa da murmushi akan fuskarta, a cikin ransa ya amsa tare da fi ce wa da sauri daga falon, Sajidah ta zauna ƙasan kafet tana faɗin.


    "Wash Allahna, duk na gaji wallahi Aunty Sakinah".


  "Kamar wacce ta yi tafiyar wuni guda, ban son raki fa".


  Sakinah ta ƙarashe maganar tana hararar Sajidah.


    "Ba za ki gane ba ne Aunty Sakinah, wai nan kayan lefe ne ko me?".


    Ta yi tambayar tana mai kai wa kayan cikin akwatunan kallo, kafin ta kai dubanta kan Sakinah.


    "Ba dai ma gwadawa ki ke yi ba?, kai Aunty Sakinah ke ma dai sai a hankali wallahi".


    "To me kuma na yi? Kayan faɗar kishiya ne ba lefan wata ba, bare ki ce na gwada kayan wata".


    "Tab..duk da hakan kuma ki ke gwadawa? Kai Aunty Sakinah ko kishi babu, sai wani faman harkokinki  ki ke yi, Allah da ni ce ko kallon kayan ba zan yi ba wallahi".


    "Ke dai ki ka sani, ni kuwa babu abin da zai dame ni yarinya, gara ma tun yanzu ki koyawa kanki kyakkyawan kishi, ka da ki biyewa sharrin zuciya da jin daɗin sautin bugun gangar sheɗan ki sanyawa kanki baƙin kishin da zai kai ki ga halaka".


    "Kamar ba auren So ku ka yi da Yaya Kamal ba, ai dole zaki ji kishi fa Aunty Sakinah, ko ya ya ne".


     "Wannan ai shi ne asalin kishi kin ji ko, ki duba kissoshin matayen Manzon Allah (S.A.W), suna yin kishi ne da dukkan gaskiyar soyayyarsu akan mijinsu, ƙara ƙaimi suke a kullum wajen rige-rigen kyautata masa da dukkan abin da suka san ya fi so da ƙauna, domin samun gurbi a mazaunin zuciyarsa, ina son kwatanta ko da kwatan-kwacin hakan ne, na san ba zan taɓa yin ko da rabi-rabin kaso ɗayan yanda suka yi ba, amma ko daidai da gwayar zarra ne ina son na kwatanta Sajidah".


  "Hmm..to Allah ya ba da iko, ya samu a danshin ku, amma gaskiya Aunty Sakinah ke ta musamman ce a zamanin abu ne mawuyaci samun kamar ki".


    "Amin, ban son iya shege kuma, akwai waɗanda suka fini sosai Sajidah ke kanki idan kin daure wata ƙila ki fini ma".


    "Gara dai da kika ce wata ƙilan".


  Sajidah ta bata amsa cike da tsokana, yayin da Sakinah ta ɗan bugi bayanta kaɗan , suka sanya dariya dukansu, ka fin su rufe akwatunan Sajidah ta taimaka mata suka mayar da su ɗaki.


    Kai tsaye Sajidah ɗakin saukar baki ta shige domin yin alwalar sallar isha'i, haka ma Sakinah ɗakinta ta nufa zuciyarta fari tas har wani murmushin jindaɗin zuwan Sajidah ke kufce mata.


    Bayan sun idar da sallah har ɗaki Sakinah ta kaiwa Sajidah abinci da dukkan abin da zata buƙata tana faɗin.


    "Ki kwanta da wuri ɗan Allah, sabida tashin wuri za mu yi gobe don yin aiki".


    "Insha Allah, ni dama kin bar abincin na gaji wallahi bacci kawai na ke da buƙata yanzu".


  Harara Sakinah ta jefa mata kafin ta ce.


    "Ka da ma ki fara wannan tunanin malama, ki ci abinci ka da ki soma kwanciya haka kinji?".


  "To zanci amma kaɗan".


    "Ke ki ka ji yo kuma wannan, kin ga tafiyata".


  Ta kai maganar tana mai fice wa daga ɗakin tare da rufo mata ƙofa, ta koma nata ɗakin domin yin shirin bacci, sabida itama yau agajiye ta ke jin jikin nata, ga shi har lokacin Kamal bai dawo ba, ko ya dawo yana gun Hajiya ne bata sani ba? Domin tasan shi bamai hirar waje ba ne, bare ta ce ya tsaya hira wajen abokai ne.
  YAU DAI BA YAWA KU YI HAƘURI DA NI.

    


   

No Stickers to Show

X

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Duk mace na bukatar sanin wadannan abubuwa guda 6 kafin ta yi aure

  Posted Nov 29

  Aure abu ne mai matukar muhimmanci a rayuwar mutum don ya zamo cikar mutuntaka ta dan adam. Allah madaukakin sarki ya halicci mata daga jikin mazaje domin su matan su zama natsuwa a gare su, ya kuma sanya soyayya da shakuwa a tsakanin wadannan jinsin guda biyu.  A...

 • Ko kun san adadin yawan nutrients da jikinku ke bukata?

  Posted Nov 24

  Samun abinci mai kyau da kara lafiya, wato good nutrition, ya dace ya zamo daya daga cikin burin kowani dan adam da ke raye.  Ya kasance mun san adadin yawan abinci mai kyau da jikkunanmu ke bukata, sannan mun san addadin yadda ya kamata mu rinka motsa jikinmu, kum...

 • Yadda ake hada buttered chicken

  Posted Nov 22

  Assalamu alaikum barka da sake saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau insha Allahu zamu gabatar da shirin yadda za ki hada buttered chicken. Abubuwan hadawa Kaza Ginger and garlic paste (citta da tafarnuwa)  Albasa Yoghurt Butter Fresh cream ...

 • Yadda ake hada papaya drink

  Posted Nov 22

  Assalamu alaikum barka da sake saduwa a cikin shirin Bakandamiya a yau insha Allahu zamu gabatar da shirin yadda za ki hada natural papaya drink Abubuwan hadawa Papaya (gwanda) Sugar Ruwa Zuma (optional) Yadda ake hadawa Farko za ki yanka gwanda ki cire ma...

 • Alamomi 8 da za ki gane cewa namiji da gaske yake

  Posted Nov 22

  So wani irin yanayi ne da kan sa mutum ya tsinci kansa a cikin wani hali na daban. Sai dai mi? Abu ne shi mai dadi a kuma gefe guda abu ne mai matukar ban tsoro. Duk da kasancewar sa hakan bai zama abin ƙyama ga mutane ba. Da yawa kan rungume shi da hannun biyu. A gefe...

View All