Rubutu

Blogs » Kagaggun Labarai » Jini Ba Ya Maganin Kishirwa: Babi na Biyu

Jini Ba Ya Maganin Kishirwa: Babi na Biyu

 • Ku latsa nan don karanta babi na daya.

  Kamal na fita daga cikin gidan kai tsaye Unguwar jan bulo ya nufa, layin farin gida gidan Hajiya shema'u.

  Da zuwansa bugu ?aya ya yi wa ?ofar gate ?in, mai gadi ya bu?e masa ?ofa ya shiga, da ya ke mai gadin ya san shi kuma Hajiya ta garga?e shi akan Kamal, ko da wasa ka da ta ji labarin ya wula?anta mata shi, shi yasa da ya ganshi da tsumar jiki ya ke tsugunnawa ya gaishe da shi, duk kuwa da irin tarin tazarar shekarun da ke tsakaninsu domin a haife tabbas zai haifi Kamal.

  Amma shi gogan naka ko a jikinsa sa asalima ko amsa gaisuwar ba ya yi, ya ke wucewa abinsa yana wani hura hanci sama, a ganinsa ya fi ?arfin ya tsaya amsa gaisuwar talakan ba kauye irin wannan mutumin.

  Mai gadin yabi bayansa da kallo har sai da ya daina hango inuwar hular, sannan ya mi?e daga tsugun nen da ya ke yana mai girgiza kai tare da tausayawa Kamal a kan gudun wuce sa'ar da ya ke shirin yi wa rayuwarsa.

  Gida ne wanda ya amsa sunan gida, domin tun daga wajen gate na gidan zaka san naira na kuka a cikin, labarin ya kan canja ne daga inda mutum ya yi tozali da tsari da tsaruwar cikin gidan, a wannan lokaci kai ne ka dai al?alin da zaka iya lissafin irin dukiyar da aka ?arnatar, amma tawadar al?alamina ta yi ?aran ci wajen iya zayyano maku fasali na gidan.

  Da sallamarsa ya sanya kai cikin  falon, sabida a halin yanzu Kamal ya zamto tamkar ?an gida kamar yanda take fa?a a kullum, baya bu?atar iso a wajenta Kafin isowarsa, duk sanda ya so ya ke kuma da ra'ayin zuwa gare ta tana maraba marhabin da shi.

  Hajiya Shema'u da ke zaune saman ?aya daga cikin jerin kujerun da suka yiwa falon ?awayen ta ?ago kai tana amsa masa sallamar, Masha Allah shi ne abin da dukkan bil'adam da da ya yi to zali da kyakkyawar fuska irinta ta zai iya ambata mace ko namiji.

  Domin ga inda kyawun asali ya ke, Hajiya Shema'u maca ce dirarriya irin matan nan masu matsakaicin tsayi da jiki daidai misali, fara ce sosai tamkar ka ta?a jini ya fito bama ce farinta ba ne zallah, domin zamani ya zo mana da mawuyaci ne ka samu macen da bata harka da mayukan gyaran fata masu ?ara fito da zallar asalin farin mutum da she?i musamman manyan mata irinsu, dogon karan hancinta da ya da ce da doguwar fuskarta tamkar an dasa shi, shi ne abu mafi kusa da ke fara janyo hankalin dukkan namijin da ya yi tozali da ita, ma'abociyar manyan idanuwa ce, mai yalwar suma dake kwance lub saman goshinta har zuwa bayanta, a ta?aice dai ba lallai ne daga kallo ?aya akan wannan mata ba ka iya gano makusarta nan take ba.

  Yarinyar da ke dur?ushe gabanta tana danna mata ?afafuwanta ta mi?e da sauri kai a ?asa ta nufo bakin ?ofar da Kamal ya ke tsaye, ta ?an risina ka?an ta gaishe da shi tana mai cigaba da tafiya har ta fi ce daga falon, Kamal kuwa ?an ta?e baki ya yi ka?an kafin ya ?arasa cikin tsakiyar falon ya nemi guri inda Hajiya Shema'u ke zaune ya zauna a gefanta kafin su kalli juna dukkansu suka yi murmushi a tare.

  "Yalla?aina kai ne tafe haka? Ban yi tsammanin zuwanka da wurwuri haka ba".

  Kamal ya shafo sumar kansa ta baya kafin ya ?an ta?e baki ya ce.

  "Wallahi matar can ce ta ?ata min rai matu?a, shi ne kawai na yi yo ta nan, domin nasan nan ne zan iya samun ishashshan farin ciki".

  Hajiya Shema'u ta ?an yi wata gajeriyar dariyar irin ta manyan mata, ka fin ta bashi amsar.

  "A'a fa Yalla?aina ko dai kai ne ka ?ata mata? Domin nasan halin Sakinah bana jin hakan daga gare ta".

  Kamal ya ja dogon tsaki, yana mai kau da kai gefe ya ?ora idanuwansa akan TV, kafin ya furta.

  "Yardarki akanta harta kai haka?".

  "Fiye da haka ma".

  Ta bashi amsa a ta?aice, Kamal ya dube ta da mamaki kafin ya basar sai ya samu kansa da fiddo mata da tambayar da ba ita ce a cikin zuciyarsa ba.

  "Wai dama a halin yanzu akan samu matan da basa kishin mazajensu?".

  "Kamar ya kenan?".

  Kamal ya juyo da hankalinsa baki ?aya wajen Hajiya Shema'u, yana mai cigaba da fa?in.

  "E to kawai naga kamar Sakinah bata kishi akan aurenki da zan yi".

  "Kai kishin ka ke so ta nuna maka kenan?".

  Kamal ya yi murmushi kawai yana jujjuya amsar da zai bata cikin ransa tsayin wasu da ?i?u kafin ya furta mata.

  "Ba haka ba ne".

  "To ya ya ne?".

  Kamal ya sake ?ago kai ya dubeta yana tantama akan amsar da zai bata, sabida sosai take yi masa kwarjini baya jin zai iya furta mata amsar da ke lullu?e ?asan zuciyarsa.

  "Mubar maganar kawai, kin kira ni tun safe na zo, ina kasuwa ne bana jinki sosai, shi yasa na bari kawai na zo har gida na ji lafiya?".

  Kamal ya yi ?o?arin ajiye zancen da suka faro a gefe ya sanyo wani, Hajiya Shema'u ta ?anyi guntun murmushi domin ta gane janye zancen ya yi.

  "E haka ne, ?an jira ni ka?an".

  Ta kai maganar tana mai mi?ewa ta nufi wata ?ofa da ke nan cikin falon, cikin wani irin taku da salon tafiya mai jan hankalin ma'abocin kallonta, Kamal da ya bita da kallo harta shige ?akin ya sauke ajiyar zuciya yana mai gyara zamansa sosai akan kujerar da yake zaune, a daidai lokacin kuma 'Yar aikinta da ta fita ?azu ta yi sallama cikin falon hannunta ?auke da tire ta ajiye akan ?an ?aramin table ?in da ke tsakiyar falon ta juya abinta.

  A daidai lokacin kuma Hajiya Shema'u ta bu?e kofa ta fito daga cikin ?akin da ta shiga, hannunta ?auke da wata ba?ar jaka mai shegen kyau, anyi mata adon duwatsu farare sai she?i da walwali take.

  Zama tayi kusa da Kamal daidai sanda ya ke ?o?arin zuba lemo a cikin ?an ?aramin kofin ?arau (glass), Hajiya Shema'u ta yi saurin kar?a ta ?arasa zuba masa ta mi?o masa ya kar?a fuskokinsu na wanzar da yalwataccen murmushi mai tsada, sai da Kamal ya sha kusan rabin lemon kafin ya ajiye kofin yana mai dawo da kallonsa gunta sosai da alamun sauraronsa ya ke yi akan batun kiran da ta yi masa.

  Tamkar tasan abin da ya ke nufi ta sake gyara zamanta kafin ta bu?e jakartata ta fiddo invitation card ?auri guda ta ajiye a gabansa, Kamal ya ajiye dubansa akan katunan kafin ya mi?a hannu ya zaro ?aya yana mai karanta wa.

  ?ayataccen murmushi ne ya kufce masa na ganin kyawu da tsaruwar katin ?aurin auren nasu shi da ita, sai da ya karanta sau biyu kafin ya ?ago kai ya dube ta.

  "Dukkan wannan gatan ni ka dai?".

  Hajiya Shema'u ta wanzar da ta?aitacciyar dariyarta kafin ta bashi amsa, wacce da dukkan alamu ta zame mata jiki ne, ko kuma dan tasan tana yi mata kyau ne ya sanya ko da yaushe take yinta oho?.

  "Ka wuce hakan a gare ni Yalla?aina, tun da ka sanya hannu biyu ka kar?i soyayyata ba tare da gargada ba tabbas zan yi maka dukkan halicci gabanin auren mu..!".

  Hajiya Shema'u ta ta?aice zancen nata tana mai cigaba da jifansa da mayaudarin murmushinta wanda ke wanzar da farin ciki da annashuwa ga dukkan mahalukin da ya yi to zali da shi.

  "Ina godiya matu?a Hajiyata Allah dai ya tabbatar mana da wannan auren ya yi mana katangar ?arfe da duk kan wani ma?i gani a gare mu".

  "Amin s amin".

  Ta amsa tana mai kai hannu kan tire ?in ta ?auki tufa ta fara ci a hankali suka hau hirarsu cikin annashuwa da jin da?i.

  ***

  Ko da Sakinah ta kammala ninkin kayan da ta ke yi, baki ?aya hankalinta ya ?ara tashi matu?a, ga wani abu da ke ?asan ?irjinta wanda ke yo iyo zuwa ma?ogwaronta ya tokare mata ?irji, ya?i gaba ya?i baya, ta yi jugum tsayin wasu da?i?u ba ta yi aune ba sai jin abu ta yi na bin fuskarta ko da ta duba hawaye ne, da saurin ta sanya hannu ta share a lokacin kuma wayarta ?irar kamfanin Tecno ta fara kukan neman agaji a gare ta.

  Hannu ta kai a hankali ta janyo ta cikin yanayin kasala da damuwa, ganin sunan Ummanta ya sanya ta ?ara ?arfafa jikinta da muryarta kafin ta ?aga wayar ha?e da sallama ta kara wayar bisa kunnenta.

  Daga can ?angaren Mahaifiyarta ta amsa sallamar tana mai cigaba da fa?in.

  "Lafiya dai ko Sakinah? Na ji muryarki ta yi wata iri alamun kuka kike yi ko?".

  "A'a Umma, kuna lafiya yasu Sajjad".

  Sakinah ta yi saurin kau da zancen, sabida bata yiwa mahaifiyarta ?arya, kuma ba tajin zata iya gaya mata damuwar da take ciki a halin yanzu.  

  "Lafiya ?alau Sakinah, ya nan gidan naku, komai lafiya ?alau ko?".

  "E Umma, dama yanzu nake shirin kiran ki sai ga shi kin kira".

  "E to naso ma na zo da kaina ne, sai kuma muka wayi gari Sajjad ba lafiya".

  "Ayya Sikilar ce ta motsa".

  "E amma da sauki sosai, barci ma ya ke yi yanzu haka".

  "Allah ya ?ara sauki"

  "Amin".

  Umman ta amsa, Sakinah ta cigaba da fa?in.

  "Umma dama Sajidah na ke so ki bani aro ta ta ya ni aiki, sabida gobe Kamal ya ce za'a zo a ?an yi mana gyare-gyaren gidan".

  "E daman na ce zan turota, domin jiya ya zo nan ya yi mana batun auren, ya ce a baki Sajidah ta ta ya ki ayyuka, juma'a ne ?aurin auren ko?".

  Sai da ?irjin Sakinah ya yi wata irin bugawa har sai da ta kai hannu ta dafe gurin, da ?yar ta iya bawa Umman amsar.

  "E ?a zu ya kawo min akwatuna biyu ma, wai na fa?ar kishiya".

  "Masha Allah, Sakinah..!".

  Umman ta Kira sunanta, Sakinah ta amsa murya can ?asa, Umman ta cigaba da fa?in.

  "Ki ?ara ha?uri Sakinah akan wanda na sanki da shi, dukkan macen da ki ka ga ta ci ribar zaman aure kuma ki ka ganta zaune lafiya a cikin gidan ta, to indai kin bibiya ribar ha?uri da gajiyarsa ta ke ci,  sannan ki ninka soyayyar mijinki a ranki fiye da yanda ki ka so shi kafin auren ku, ta hakan ne za ki samu damar kyautata masa tare da yi masa biyayya fiye da zamanku a da, ka da ki yarda da dukkan wata gurguwar shawarar ?awa ko zancen 'yan unguwa, ki girmama mahaifiyarsa kiyi mata biyayya tamkar yanda za kiyi min".

  "Sakinah..! Ha?uri haske ne mai haska dukkan tsananin duhu, haka kuma juriya a bace mai wanzar da mutum zuwa tafarkin da bai yi tsammani ba, a matsayina na mahaifiyarki na hore ki da abubuwan nan ba dan komai ba sai dai su ne ka ?ai ababe masu ?ullewa, ki sanya a ranki aurenki a yi ke yi, kuma aure ibada ne ga ko wacce 'ya mace ta duniya, kuma shi ne cikar mutunci da kamala ga dukkan wata 'ya mace, ko ka?an ka da ki nuna fushi ko jin haushi akan auren nan, asalima ki ?arfafa masa gwiwa idan da dama, hakan ka ?ai zai sanya ki dasa kujera a zuciyar mijinki, kujerar da babu wata wadda ta isa ta tum?uke ta, sai ma ?arin daraja da girma da ?ima da hakan zai janyo miki a gare shi".

  "Sannan ki dage da addu'a matu?a, ki kasance mai raya daran barcinki, ka da ki gajiya, ka da addu'a ta yanke a bakinki duk tsanani, domin ita ce ka ?ai maganin da zata iya warkar miki da ciwon kishi, kishi dole ne ga 'ya mace Sakinah amma na hore ki da yin kishi mafi tsafta akan mijinki, ki yi ha?uri ki danni zuciyarki kinji Sakinah..!"

  *****

  Don ci gaba da karanta babi na uku sai ku latsa nan.

Comments

0 comments