Rubutu

Blogs » Kagaggun Labarai » Jini Ba Ya Maganin Kishirwa: Babi na Uku

Jini Ba Ya Maganin Kishirwa: Babi na Uku

 • Ku latsa nan don karanta babi na biyu.

  Sakinah ta share hawayen da ke zuba kan kuncinta kafin ta ce.

  "Insha Allahu Umma zan yi aiki da dukkan abin da ki ka umarce ni da shi da yardar Allah, ba zan ta?a baki kunya ba".

  "Yauwa Sakinah Allah ya yi miki albarka".

  "Amin".

  Sakinah ta amsa, ya yin da Umman ta cigaba da fa?in.

  "Kin yi waya da Yayanku kuwa? Ya ce min sun kusa dawowa mu taya shi da addu'a".

  "E ya kira ni jiya, ya ke fa?a min  cikin satin nan zai kammala HND ?in sa, zasu dawo gida amma bai fa?a min ranar da zasu dawo ba, wai ba zata zai yi mana".

  "To Allah ya ba da sa'a, ya dawo mana dasu lafiya".

  "Amin Ummata, a gaishe min da Abba da su Sajjad idan ya ta shi".

  "Za su ji insha Allah, a cigaba da hakuri dai Sakinah".

  "Insha Allah Umma nagode".

  Kusan a tare suka kashe wayar, Sakinah ta ajiye wayar gefan inda take zaune kan gado, fuskarta wasai da dukkan alamu ta ji da?i matu?a kan wayar da su kayi da Ummanta, sosai ka so goma daga cikin ashirin na damuwarta ya kau, hakan ne ya sanya nan ta ke ta ji ?arfin gwiwar ya zo mata ta mi?ewa tare cigaba da ayyukanta.

  4:30pm

  ?arfe hu?u da rabi ta kammala dukkan gyaran ?akunan su har zuwa falo ta sanya turaruka masu da?in ?amshi da jan hankalin dukkan wanda ya sha?esu, kicin ta fa?a domin ?ora musu sanwar dare abincin da Kamal yafi so da ?auna ta ?ora jallof ?in shinkafa da bushashshen kifi, ta yi mata ha?i na musamman, ba ta damu da ha?a lemo ba domin ba kasafai yake shan na ha?awa ba yafi son na kwali.

  A gurguje ta kammala ta ?auko kula ta zuba masa ta zubawa Hajiyarsa, ta gyare gurin tsab sannan ta koma ?aki domin yin shirin wanka.

  Cikin mintuna talatin da biyar ta kammala ta yi kwalliyarta cikin atamfa Hitarget yaluwa mai ratsin ja da ba?i riga da siket, sun mata kyau sosai duk da cewar ba wata kwalliya ta yi wa fuskarta ba, babu laifi Sakinah kyakkyawar maca ce, dukkan wani cikar halitta na matan hausa Fulani ta ha?a, maca ce son kowa ?in wanda ya rasa, gata ko da yaushe fuskarta sake shiyasa ba lallai ne ka gane tana cikin damuwa ba in dai ba abin ya yi tsamari ba.

  Kular abincin Hajiya ta ?auka tare da sanya takalmi mai kamar silifas ta nufi ?akin Hajiyar, da sallamarta ta sanya kai cikin falon, Hajiya dake zaune kan carpet a falon ta ?ago kai tare da amsa sallamar.

  Sakinah ta ?ara so gareta ha?e da dur?usawa ta ajiye kular abincin a gefe, kafin ta gaishe da ita, Hajiyar ta amsa gaisuwar fuskarta wasai alamun jin dadin ganin Sakinah ya wanzu a kana fuskarta.

  Maganin ciwon ?afar Hajiya da ke ri?e a hannunta ta kalla tana fa?in.

  "Kawo na shafa miki Hajiya, Farida bata dawo ba kenan?".

  "E ta ce min zata biya dubo Husnah bata da lafiya".

  "Allah sarki Allah ya bata lafiya, yasa kaffara zazza?i ne ko?".

  Sakinah ta yi tambayar tana mai amsar maganin ta fara shafawa Hajiyar tare da ?an danna mata ?afar dan ta ji da?i.

  "Kin san ciwon yanzu baya wuce maleria, abin sai addu'a ga zazza?in da nacin tsiya sai ya tafi ya dawo".

  "Wallahi kuwa Hajiya, ?azu muka yi waya da Umma ma, ta ce a gaishe da ku, Sajjad ma yana kwance amma ta ce min da sau?i sosai".

  "Allah ba shi lafiya, ciwon ya tashi kenan?".

  "E wallahi?".

  Hajiyar ta ?an gyara zamanta ka?an kafin ta cigaba da fa?in.

  "Ai yaron na fama da jiki wallahi, sikila sai addu'a ciwo mai wuyar sha'ani ga wahalar da mutum".

  Sakinah ta ?an yi murmushi, ba tare da ta ce komai ba, Hajiyar ce ta cigaba da magana.

  "Sakinah ki yi ha?uri akan halayyar Kamal, ni kai na bani da yanda zan yi ne, dole ce ta sanya na amince da auren nan domin gudun abin da gobe zata haifar".

  "Babu komai insah Allahu Hajiya".

  "Da komai fa Sakinah..!, ka da kiyi zargin laifina ne da ban hana shi ba, sanin kanki ne ya sauya matu?a cikin kwanakin nan, ina tsoron ka da kafiyata akan ?in yarda da auren ta sanya ya fa?a wata harkar ta da ban domin biyan bu?atarsa, na amince da auren Kamal ne dan ka da ya jefa kansa ga halaka, akan abin da bai taka kara ya karya ba, gara na amince ya yi auren akan na hana shi ya biyewa sharrin she?an da zugar zuciya ya kaucewa hanyar data da ce".

  "Da a ce yau jinina yana aikata mugun sa?o musamman zina, Gara a ce yau gudan jinina ya auri sa'ar kakarsa Sakinah, domin zina bashi ce, ba kai da ka ke aikatawa ake gujewa ba, ka jajawa wanda bai ji ba bai gani ba shi ake gudu, nasan Kamal na zalintarki domin ina hankalce da dukkan  abin da ke wakana agare ku, amma ba ni da yanda zan yi ne, ba ni da abin da  zan iya yi a halin yanzu wanda ya wuce addu'ar Allah ya dawo da shi hanya, ya sa ya gane gaskiya, kema ina ro?onki da ki da ge da addu'a Sakinah, addu'a makamin mumini ce kuma bata ta?a fa?uwa ?asa banza, wata rana sai labari, nasan kina ha?uri amma ki ?ara akan na da kin ji".

  Sakinah ta yi murmushi daidai sanda take rufe kwalbar maganin Aboniki ?in, ta ?ago kai ta dubi Hajiyar kafin ta sauke su ?asa tana fa?in.

  "In Allah ya yarda Hajiya zan yi aiki da shawararki a gare ni, nagode sosai da tunatar wa".

  Nan dai suka cigaba da hira jefi-jefi, yawancin hiran duk akan  tausar Sakinah ne Hajiyar ke yi tare da bata baki, haka ne yasa sosai Sakinah ke matu?ar son mahaifiyar Kamal da bata girma matu?a, domin ita ba suruka ta dauki Sakinah ba ta ?auke ta ne tamkar 'Yar data haifa a cikin ta.

  ***

  Kamal ba su yi sallama da Hajiya Shema'u ya baro gidan ba sai ana kiraye-kirayen sallar maghriba, a masallacin unguwar ya yi sallah kafin ya nufo gida zuciyar na tunani kala-kala akan yanda zai je ya tadda Sakinan.

  Sakinah bata bar ?akin Hajiya ba  sai da aka kira sallar maghriba a masallacin unguwar, lokacin Farida ta jima da dawo wa sun ?an yi hira kafin daga baya ta yi musu sallama ta nufi ?akinta.

  Tana shiga ban ?aki ta nufa ta ?auro alwala, tana fitowa ta shi ge ?aki ta shimfi?a abin sallah tare da sanya hijab ta tayar da kabbarar sallah.

  Bata jima da idarwa ba tana cikin ninke hijab ta tsinkayo sallamarsa tsakar gidan, mudubi ta nufa ta ?an sake gyara fuskarta tare da sake feshe dukkan sassan jikinta da turare kafin ta fito zuwa falon, ta nemi ?aya daga cikin kujerun falon ta zauna tana jiran shigowarsa.

  Sai da ya fara shiga ?akin Hajiya ya yi mata barka da yanmaci kafin daga baya ya fito zuwa ?akinsu, a can ?asan ma?oshi ya yi sallama cikin falon nasu, Sakinah ta masa tare da mi?ewa tsaye tana fa?in.

  "Sannu da zuwa Habibina".

  "Yauwa".

  Ya amsa mata a ta?aice yana mai zama kan kujerar tare da ajiye ledar katunan bikin a gefansa sai faman wani cika yake da batsewa ha?e da shan ?amari, Sakinah ta yi murmushi ta zauna a gefansa tana mai cigaba da fa?in.

  "Ya jama'a da rana, yau naga an yi rana sosai".

  "Lafiya".

  Ya sake amsa mata, gyara zamanta ta yi, murmushi kan fuskarta har a lokacin bai gushe ba daga gareta.

  "Nasan ka gaji Sweety, da me zaka fara wanka ko cin abinci? Sabida yau abin da ka fi bu?ata na girka maka".

  Bai ko kalleta ba, bare ma ya nuna cewar yasan tana magana, illa ledar katunan bikin da ya bu?e ya ?ebo kusan guda biyar ya ?ora mata akan cinyarta, har a lokacin bai ce da ita komai ba.

  Sakinah ta ?auki katunan tana dubawa yayin da can ?asan zuciyarta na ta yi mata lugude, ga wani irin zugin zafi da zuciyarta ke yi, da ?yar ta yi ?arfin halin ?a?alo murmushin dole tare da daidaita tsayuwar numfashinta kafin ta furta.

  "Kai..! Masha Allah katunan sunyi kyau sosai matu?a wallahi, Allah dai ya kaimu ranar ya nuna mana".

  Sai a lokacin Kamal ya ji yo ya dube ta baki galala cike da tsantsar mamakinta, akan kawaici da basarwa irin nata.

  Kamal ya gayyato murmushi zuwa kan fuskarsa sosai ya nuna matu?ar jin dadin akan maganarta tunaninsa zata ji haushi, hakan ya sa cike da za?uwa ya amsa da.

  "Ya burgeki sosai haka?"

  "Sosai kuwa, ya yi kyau wallahi".

  Sakinah ta kai maganar tare da mi?e wa tana fa?in.

  "Bari dai na je na ha?a maka ruwan wankan, domin nasan zaka fi bu?atar wanka a halin yanzu".

  Bata damu da amsawarsa ba ta yi wucewarta, Kamal ya bi bayanta da kallo a cikin ransa yana fa?in.

  "Wannan kuma wacce irin mata ce haka?"

  Murmushi ya yi tare da jan tsaki ka?an, sosai kwalliyarta ta burgeshi amma girman kai da gadara yasa ba zai nuna mata ba,  yana gudun ka da ya nuna mata raini ya ?ulla har ya samu gurin zama a tsakaninsu.

  *****

  Ku latsa nan don karanta babi na hudu.

Comments

0 comments