Featured Create an Ad

Makalu

Blogs » Kagaggun Labarai » Jini Ba Ya Maganin Kishirwa: Babi na Hudu

Jini Ba Ya Maganin Kishirwa: Babi na Hudu

 • Ku latsa nan don karanta babi na uku.

  Yana fitowa daga wankan kai tsaye gaban mudubi ya nufa, tun kafin ya kai ga ?ara sawa idanuwansa suka tsinkayo masa  ?ananan kaya ya she akan gado riga da wando,  da dukkan alamu Sakinah ce ta ajiye masa su, sai faman wani tashin ?amshin dad-da?an turare su ke yi, ?an ta?e baki ya yi ka?an kafin ya ?arasa  gaban gadon ya fara ?o?arin sanya wa.

  Yana kammala shirin kai tsaye falo ya nufo, lokacin Sakinah ta kammala  jere masa abincinsa tsakiyar falon, kai tsaye wajen abincin ya nufa ya zauna, yayin da Sakinah ta yi murmushi tare da tsugunnawa ta fara zuba masa abincin, har ?asan ransa bai yi ni yar cin abincin ba, amma to zali da ya yi da abincin da yafi so da ?auna ga kuma tashin ?amshin abincin na musamman ya ke jinsa a yau, nan ta ke ya ji kamar an yashe masa cikinsa har ya ?agauta da son fara ci, sai faman ha?iyar yawu ya ke.

  Sakinah ta ajiye masa abinci a gabansa, nan da nan ya fara aikawa cikin bankin cikin, ba Sakinah ba shi kansa ya yi matu?ar mamakin irin abincin da ya ci, kai ka ce wunin ranar bai ci komai ba ne, sabida irin tulin tarin abincin da Hajiya Shema'u ta ciyar da shi a yau, bai yi tsammanin zai sake kallon wani kalar abinci ba a ?an ta ?aitaccen lokaci kamar wannan ba, amma sai ga shi lokaci guda ya share abinci faranti guda.

  Sosai Sakinah ta ji da?i a ranta, sabida rabon da ya ci abinci da yawa haka tun kafin ya fara maganar aurensa, farin cikinta kasa ?oyuwa ya yi har sai da ta kai ga furta.

  "Mijinah abincin ya yi maka dadi sosai, da dukkan alamu bakinka ya yi kewar girkin gimbiyarka ko?".

  Kamal ya yi ajiyar zuciyar kawai tare da mi?a hannu ya ?auki ruwan da ta zuba masa cikin kofi ya sha ka?an ya ajiye kafin, tare da ?an yin gajeren murmushi kafin ya ce.

  "Ni ma dai na yi mamakin yanda aka yi na ci abincin da yawa haka, kuma kin san cewar a ?oshe na ke wallahi, amma dad-da?an ?amshin girki ya ja ni na wafce abincin ciki biyu".

  A tare suka yi gajeriyar dariyar, kafin su yi shiru ko wanne daga cikinsu yana sa?e-sa?e cikin ransa, Kamal ya katse shirun da fa?in.

  "Kin duba kayan dana kawo miki kuwa?"

  "Wayyo..! Wallahi shaf na sha'awafa inata faman aiki ne tun sanda ka fita ka barni, ko da ya ke yanzuma bata ?aci ba, bari na ?auko mugani tare kallon ya fi da?i ma".

  Ta kai maganar tana mai kanne masa ido ?aya, ta mi?e tsaye tare da ba shi baya ta nufi cikin ?aki, baki galala ya bita da kallo cike da guntun murmushin da bai san yana yinsa ba, sai daga baya ya yi gajeren tsaki tare da ?an bugun kansa ka?an yana girgiza wa.

  ?aya bayan ?aya ta fito da akwatunan kafin ta zauna tana mai da numfashi a hankali, daga baya kuma ta hau bu?e kayan tana gani, ci ke da tsantsar farin ciki duk wanda ta ?a ga sai ta ce.

  "Masha Allah, kamar kasan kuwa zan so wannan".

  ?ananun kaya saiti biyar ta gani ciki, tare da dogwayen riguna guda uku, nan da nan ta mi?e cike da ?auki ta fara gwadawa, wai ya gani idan zasu yi mata kyau, tun Kamal na basar da ita har dai ya biye mata, har da su dariya da hira kala-kala cike da nisha?i, Sakinah ta ji tamkar su dauwama a haka, nan ta ke wasu al'amuran watannin baya suka fara katantanwa a cikin kwakwalwarta, kwallar da ke ?o?arin zubar da ruwa kan fuskarta ta yi saurin sharewa tare da saurin kau da tunanin da ke shirin bijiro mata, a daidai lokacin kuma suka sinkayo sallama bakin ?ofar falon.

  Sakinah ta amsa sallamar tana mai nufar ?ofar falon, ganin Sajidah tsaye ya sanya ta bu?e baki cike da dariyar jin da?i ta ke fa?in.

  "Shigo mana kamar wata ba?uwa, sai ki tsaya kina faman kwa?a sallama haka".

  Sajidah ma dariyar tayi kafin ta bata amsar.

  "Kin ji kuma Aunty Sakinah, ko ba ba?uwa ba ce ai sallama ta zama dole a gare ni, domin jajjada koyarwar addinin islama".

  "Kin yi gaskiya sarkin zance".

  Kamal ya bata amsa yana mai mi?ewa tsaye daidai lokacin aka fara kiraye-kirayen sallar isha'i.

  "Kin zo a daidai, na mi?e a daidai ga kiran sallah can ana yi, ya ki ka baro Abba da Umma, ya jikin Sajjad kuma?.

  "Alhamdulillahi duk suna gaishe ku, na jima da zuwa fa ina wajen Hajiya muna gaisawa tun ?a zu".

  "Masha Allah da kyau hakan, ni dai zan wuce masallaci to".

  "A dawo lafiya Yayana".

  Cewar Sakinah kenan ta fa?a da murmushi akan fuskarta, a cikin ransa ya amsa tare da fi ce wa da sauri daga falon, Sajidah ta zauna ?asan kafet tana fa?in.

  "Wash Allahna, duk na gaji wallahi Aunty Sakinah".

  "Kamar wacce ta yi tafiyar wuni guda, ban son raki fa".

  Sakinah ta ?arashe maganar tana hararar Sajidah.

  "Ba za ki gane ba ne Aunty Sakinah, wai nan kayan lefe ne ko me?".

  Ta yi tambayar tana mai kai wa kayan cikin akwatunan kallo, kafin ta kai dubanta kan Sakinah.

  "Ba dai ma gwadawa ki ke yi ba?, kai Aunty Sakinah ke ma dai sai a hankali wallahi".

  "To me kuma na yi? Kayan fa?ar kishiya ne ba lefan wata ba, bare ki ce na gwada kayan wata".

  "Tab..duk da hakan kuma ki ke gwadawa? Kai Aunty Sakinah ko kishi babu, sai wani faman harkokinki  ki ke yi, Allah da ni ce ko kallon kayan ba zan yi ba wallahi".

  "Ke dai ki ka sani, ni kuwa babu abin da zai dame ni yarinya, gara ma tun yanzu ki koyawa kanki kyakkyawan kishi, ka da ki biyewa sharrin zuciya da jin da?in sautin bugun gangar she?an ki sanyawa kanki ba?in kishin da zai kai ki ga halaka".

  "Kamar ba auren So ku ka yi da Yaya Kamal ba, ai dole zaki ji kishi fa Aunty Sakinah, ko ya ya ne".

  "Wannan ai shi ne asalin kishi kin ji ko, ki duba kissoshin matayen Manzon Allah (S.A.W), suna yin kishi ne da dukkan gaskiyar soyayyarsu akan mijinsu, ?ara ?aimi suke a kullum wajen rige-rigen kyautata masa da dukkan abin da suka san ya fi so da ?auna, domin samun gurbi a mazaunin zuciyarsa, ina son kwatanta ko da kwatan-kwacin hakan ne, na san ba zan ta?a yin ko da rabi-rabin kaso ?ayan yanda suka yi ba, amma ko daidai da gwayar zarra ne ina son na kwatanta Sajidah".

  "Hmm..to Allah ya ba da iko, ya samu a danshin ku, amma gaskiya Aunty Sakinah ke ta musamman ce a zamanin abu ne mawuyaci samun kamar ki".

  "Amin, ban son iya shege kuma, akwai wa?anda suka fini sosai Sajidah ke kanki idan kin daure wata ?ila ki fini ma".

  "Gara dai da kika ce wata ?ilan".

  Sajidah ta bata amsa cike da tsokana, yayin da Sakinah ta ?an bugi bayanta ka?an , suka sanya dariya dukansu, ka fin su rufe akwatunan Sajidah ta taimaka mata suka mayar da su ?aki.

  Kai tsaye Sajidah ?akin saukar baki ta shige domin yin alwalar sallar isha'i, haka ma Sakinah ?akinta ta nufa zuciyarta fari tas har wani murmushin jinda?in zuwan Sajidah ke kufce mata.

  Bayan sun idar da sallah har ?aki Sakinah ta kaiwa Sajidah abinci da dukkan abin da zata bu?ata tana fa?in.

  "Ki kwanta da wuri ?an Allah, sabida tashin wuri za mu yi gobe don yin aiki".

  "Insha Allah, ni dama kin bar abincin na gaji wallahi bacci kawai na ke da bu?ata yanzu".

  Harara Sakinah ta jefa mata kafin ta ce.

  "Ka da ma ki fara wannan tunanin malama, ki ci abinci ka da ki soma kwanciya haka kinji?".

  "To zan ci amma ka?an".

  "Ke ki ka ji yo kuma wannan, kin ga tafiyata".

  Ta kai maganar tana mai fice wa daga ?akin tare da rufo mata ?ofa, ta koma nata ?akin domin yin shirin bacci, sabida itama yau agajiye ta ke jin jikin nata, ga shi har lokacin Kamal bai dawo ba, ko ya dawo yana gun Hajiya ne bata sani ba? Domin tasan shi bamai hirar waje ba ne, bare ta ce ya tsaya hira wajen abokai ne.

  *****

  Ku latsa nan don karanta babi na biyar.

No Stickers to Show

X

Da Dumi-Dumin Su

 • A karkashin ilimin kimiyyar lissafi wato (physics), yau zamu yi karatu ne akan wata maudu’i mai matukar mahimmanci. Wannan maudu’in kuma ba wata ba ce face heat. Idan muka tuna a makalar da ta gabata mai suna energy mun ce heat nau’i ne daga cikin nau’ukan energy. A yau zamu ...
 • A wannan makala dalibai za su ga yadda za a yi bayani game da work da kuma power dama yadda ake solving mathematical problems. Workdone ko work a physics yana nufin a yi multiplying na force da displacement. Sa’annan aikin yana gudana ne a direction na force. Idan har W ya kasance work, F kum...
 • Vanilla cupcake kalar cupcake ne da yara kar harma manya su ke so sosai. Na san muta ne da dama suna sha'awar koyon yadda za a sarrafa shi. Saboda haka a yau muka kawo muku yadda ake yinsa domin mai sha'awar koyo. Wannan recipe idan kin bi shi yadda ya ke, za ki samu cupcakes guda 20 ne dai dai. Ab...
 • Ku latsa nan don karanta babi na takwas. Ga ɗaurin Zahra Buhari. Ni dai ban iya ɗaurin ba. Yayata ke kafa min in zan je biki. In kuwa fita yawo ne ɗaurin 'yan Hausa na ke yi mai lankwasa a gaban nan. "Mama!" Ta furta cikin mamakin ganin ta. Bata saurareta ba bare ta amsa, cikin hanzari ta isa bak...
 • A kwanakin baya na ga wani tattaunawa a social media game da zuwa aiki ga mata, musammam matan aure da kuma mata masu yara. Abinda na lura shi ne yawanci mazaje ba su fiya son matansu na zuwa aiki ba duk da cewa yawancin mazan na so a ce matansu sun yi karatu sosai kuma sun waye da sanin abubuwan ra...
 • Ku latsa nan don karanta labarin Mai Haƙuri Ya Kan Dafa Dutse. A ƙasashen ƙetare an yi wani ɗan Sarki ana kiran sa Bihizadu. Ya kasance kyakkyawa ne, kuma yana da kirki domin kuwa yana zama tare da talakawa da fatake da attajirai. Mutane suna son sa, sai dai yana da saurin ƙagauta a al'amuran ...
View All