Rubutu

Blogs » Kagaggun Labarai » Jini Ba Ya Maganin Kishirwa: Babi na Biyar

Jini Ba Ya Maganin Kishirwa: Babi na Biyar

 • Ku latsa nan don karanta babi na hudu.

  Tsaf Sakinah ta kammala dukkan wani abu da ya da ce ta yi kafin kwanciya baccinta, har ta kwanta Kamal bai shigo ?akin ba, ita kuma har tsawon wannan lokacin bacci ya gagara sauka a idanun ta.

  Sai kusan sha-?aya-da-rabi ya shi go, ko sallama babu a tunaninsa ta yi bacci, kai tsaye rage kayan jikinsa ya yi kafin ya nufi ban ?aki ya watso ruwa, tana jinsa ya kammala dukkan wani shige da fice nasa, ya hawo gefan gadon ya kwanta.

  Ko wannensu gefan da ya ke kallo daban sun jima a haka kafin da ga bisani ta ji yo tashin saukar numfashinsa a hankali, hakan ne ya bata tabbacin ya samu damar barci kenan.

  Ita kuwa baki ?ayan daren barci ya gagareta har kusan ?arfe ?aya na dare ganin lokuta masu daraja suna wanzu agareta a banza ya sanya ta mi?ewa a hankali ta nufi ban ?aki, mintuna ka?an ta fito jikinta duk ruwa da dukkan alamu alwala ta yi, abin sallah ta shinfi?a tare da sanya hijab ta dubi gaban ta tayar da kabbarar sallah domin ganawa da Ubangiji a irin wannan lokacin yana da matu?ar falala da lada, kuma Ubangiji na gaggawar amsa addu'ar wanda ya ro?e shi a wannan lokacin.

  Bayan ta idar ta jima zaune bisa abin sallar tana addu'o'inta, sai kusan uku da wani abu na dare ta koma ta kwanta, shi kuwa Kamal har lokacin barcinsa kawai ya ke shirga abinsa, bata jima da kwanciya ba wani barci mai wanzar da nisha?i ya yi a won gaba da ita. 

  WASHE GARI

  Kiran sallar farko Sakinah ta farka game da salati ta mi?e tana mai bin inda Kamal ke kwance da kallo, a hankali ta kai hannu da nufin tashinsa sai kuma ta fasa  domin gudun masifarsa da baya gajiya da yinta a duk lokacin da ta yi gigin katse masa barcin asararsa, wanda ya gagara ga ne hakan tun kafin yanzu.

  Kai tsaye alwala ta yi yo, kafin ta nufi ?akin  Sajidah ta tayar da ita  sai da ta tabbatar ta tashi sannan na koma nata ?akin domin gabatar da rakatul-fijir, ko da ta koma har lokacin bai farka ba duk kuwa da irin kara?in kiran sallar da ke ta faman ta shi a unguwar sabida kusancinsu da masallaci sosai ake jin kiran sallah a gidan.

  Haka nan ta ji ta kasa tausar zuciyarta kamar kullum wajen jure ha?ora da tashinsa, a hankali ta taka har zuwa gaban gadon tana kiran sunansa, ta kira ya kai sau biyar kafin ya bu?e ido firgigit yana binta da kallo, ta shi ya yi zaune yana faman tsaki ha?e da jefa mata hararar da ta sanya ta yin kasa da kai, domin ta san ta janyowa kanta jangwam ne.

  "Wai ke har tsawon wane lokaci garga?ina da jan kunnen da na ke yi miki a kullum za su fara shiga kunnenki iyeeh?"

  Shiru Sakinah ta yi masa, ba tare kuma da ta kalle shi ba har lokacin kanta na ?asa tana sa?e-sa?en amsar da zata ba shi mai taushi.

  "Au kin ma mai da ni ?an iska ko?"

  "A'a ka yi ha?uri, gani na yi wannan shi ne lokacin da aka fi so mutum ya gai da Ubangijinsa domin samun ladan rakatul-fijir tare da tarin ladan zuwa Masallaci ga kuma ladan jam'i..!"

  "Ke da Allah ya isa malama..! Wa'azin za ki yi min yau ma kenan? Tuni na haddace wannan babin kinji ko? Bana bu?atar tashinki ki barni na dinga tashi don kaina domin na fison sai ta nuna sosai na yi ta".

  "A kwai nunar Sallah da ta wuce ka yi ta a cikin lokacin ta?"

  Nan ma dai tsaki Kamal ya ja, ba tare da ya bata amsa ba ya mi?e ya nufi ban ?aki domin ba ya son maganar ta yi tsayi sabida ?anwar Sakinah na gidan.

  Sakinah murmushi ta yi tana mai bin bayansa da kallo, domin tuni ta harbo jirginsa na?in tanka mata, domin tasan a kullum in dai har zata tashe shi to kuwa sai ya yi banbami da masifa iya iyawarsa, iya kuma ?arfin muryarsa, kuma hakan nan dole zai je masallacin, hakan ne yasa baki ?aya ta riga ta saba da wannan hali na shi, bata kuma bi ta kansa ba ta tayar da kabbarar sallarta.

  Yanda ya ja ?ofar ?akin na su ya buga da ?arfi shi ya bata tabbacin ya fita masallacin Kenan, tasan har mutanan da ke waje a wannan lokacin za su iya jin ?arar buga ?ofar, wani lokacin idan yana wani abun dariya kawai ya ke bata domin yakan zama tamkar wani yaron goye ne, ko dan ?an fari ne? Oho.

  Gari na fara haske Sakinah ta sallame karatun Alqur'anin da ta ke yi ta shafa addu'a, kafin ta mi?e tsaye tana mai ninke abin sallar ta ajiye a inda ta saba ajiye shi ta fito domin shi ga kitchen, can ta tadda Sajidah tuni ta fara yi mata dukkan abin da ya da ce ta yi a lokacin, hakan ba karamin da?i ya yiwa Sakinah ba, shi yasa sosai ta ke jin da?in zama da ?anwarta ta sabida sanin ya kamata irin nata.

  7:00am.

  ?arfe  akwai daidai agogon ?akin ya buga lokacin tuni sun kammala dukkan abin da ya ce, har sun fara kici-kicin ha?e kayayyakin ?akin waje guda, sai lokacin Kamal ya shigo gidan kai tsaye wajen Hajiya ya nufa ya gaisheta kafin ya dawo na su ?akin, a falo ya taddasu duk sun ha?e kujerun da komai, Sajidah ta dur?usa ta gaishe da shi ya amsa fuska a sake yana mai wucewa cikin ?akin barcinsu.

  Sakinah ta mi?e ta nufi kicin mintuna ka?an ta fito hannunta ?auke da babban tire cike da kulolin abinci ta nufi cikin ?akin.

  Zaune bakin gado ta hangeshi ri?e da waya yana dannawa, a jiye farantin ta yi ?asa ta russuna tana mai gai da shi ya amsa ba yabo ba fallasa, zama ta yi gaban kayan abincin ta fara ?o?arin ha?a masa abin karin kumallonsa, shi kuwa gogan sai wani shan ?amshi da basarwa ya ke yana wani ?ara hakimcewa.

  Sai da ta gama ha?a masa komai sannan ta fito zuwa falo wajen Sajidah domin su cigaba da aikin, tarar da ita ta yi tana waya cike da nisha?i bama ta lura da fitowar ta ba sai daga baya ta ce.

  "Au ga Aunty Sakinan ma".

  Ta ?arashe maganar tana mai mi?a mata wayar, Sakinah ta amsa tare da kara wayar a kunnenta ha?e da sallama ta ke fa?in.

  "Yayanmu kana lafiya, ya karatu? Ka ?i dai sanarmana yaushe zaka dawo don kar mu tana de ka ko?".

  Daga can ?angaren ya amsa murmushi kwance bisa fuskarsa har ?asan ransa ya ke jin nishadi ainun, domin daga yanda ya ke furta magana zaka fahimci hakan.

  "Duka wa?an nan tambayoyin ni ka ?ai? Za?i wacce ki ke so na amsa miki?".

  "A'a duka ina bu?atar amsarsu".

  A tare suka yi dariya kafin ya cigaba da fa?in.

  "To shi kenan, komai lafiya ?alau ?anwata, batun zuwa kuma cikin satin nan insha Allah, da a ce ma ni wani hamsa?in mai ku?i ne visa zan yi muku ku zo ku tafi da ni, ko ya ki ka gani?".

  "Wallahi kuwa da munji da?i sosai, yau a ce gani a cikin jirgi a ?asar Misra tab..da?i kashe ni".

  Suka kwashe da dariya har Sajidah da ke zaune gefe tana sauraronsu.

  "Dama kira na yi na ji lafiyarku, sannan na gabatar miki da albishir".

  "Albishir ?in samun budurwa zaka min ko?".

  "Allah shirye ki Sakinah, ke damuwarki kenan ko?".

  "Amin, E mana, muna bu?atar ganin ka yi aure ne sosai".

  "Zan yi ne insha Allah, lokaci dai Sakinah na nan zuwa, kinga mubar wannan batun, na turowa Zainuddeen ku?i anjima zai kawo miki furniture, sai ki yi list na kayan kitchen dukkan abin da ki ke bu?ata sai a canja miki".

  "Haba dai, da gaske Yayanmu?"

  "Na ta?a yi miki irin wannan wasan?"

  "A'a Yayanmu, kai masha Allah na ji da?i sosai wallahi Ubangiji Allah ya ?ara bu?i ya saka da alkhairi nagode sosai".

  "Amin, amma dai ki bar godiyar haka ai nauyi na ne, karki damu da ina da ku?i ma zan yi miki wanda ya fi haka kin ji?"

  "Hakan ma nagode sosai, amma kai da ka ke karatu kuma kana irin wannan hidima haka".

  "Ke..! Karki damu kanki fa, ba fa zaune na ke haka ba, ko kinmanta a kwai shagunan mu da Zainu ke juya mana, kuma a nan ma na samu wani aboki na kirki muna business sosai, sai na dawo za ki sha labari ai".

  "To Allah ya dawo mana da kai lafiya".

  "Amin Amin, babu wata damuwa ko?"

  "Komai lafiya ?alau wallahi".

  "Masha Allah, ku huta lafiya ki gaida mutanan gidan".

  "Za su ji insha Allah".

  A tare suka kashe wayar cikin nishadi da annashuwa Sakinah ta rungume Sajidah tana fa?in.

  "Wayyo Sajidah Yayanmu ya canja min kayan ?aki".

  Tsalle Sajidah ta yi dan murna har da juyi tana fa?in.

  "Kai amma na taya ki murna wallahi, to yanzu wa?an nan ina za'a kai su?"

  "Mu bari idan ankawo sababbin sai a tafi da wa?an nan a kaiwa Ummah ko?"

  "E haka ne, ta shi to mu?arasa aikin, ko mu fara karyawa?"

  "Da dai ya fi".

  Sakinah ta yi maganar tana mai ficewa ta nufi kitchen domin ha?o musu abin kari.

  Kamal da ke tsaye jikin window yana jin dukkan abin da su ke yi, ya ?an ta?e baki ka?an a fili ya furta.

  'Aikin ?ur...! Koma mene za'a canja ba zai ta?a burge ni ba ehee'.

  Ya juya tare da komawa gaban kayan abincinsa ya cigaba da ci yana mita.

  *****

  Ku latsa nan don karanta babi na shida.

Comments

0 comments