Rubutu

Blogs » Kagaggun Labarai » Jini Ba Ya Maganin Kishirwa: Babi na Takwas

Jini Ba Ya Maganin Kishirwa: Babi na Takwas

 • Ku latsa nan don ku karanta babi na bakwai.

  'Da Zaki bi shawarata Sakinah ka da ki yarda Kamal ya aure ki akan shara?in ba za ki yi aiki ba, sabida ko zuwa gaba ina guje miki ranar da za ki bu?aci hakan ya ce a'a, bana tunanin da ilminki da komai za ki iya dauwama a haka takaddu zube ?ura na cika su tsayin shekaru'.

  'Ya Jaheed kenan, insha Allahu babu wata matsala, ni daman bawai son yin aikin na ke ba, kawai dai karatu yana da matu?ar amfani ne a zamanin da muke ciki a yanzu ko dan gudun wata rana, sabida akwai damar da zata iya zuwa ga mutum kwatsam kaga sai ya fito a dama da shi'.

  'Na dai fahimci soyayyar da kike yiwa Kamal ta kai wani mizani mai wahalar aunuwa ba lallai ne ki fahimci abin da nake son ki fahimta ba, babu matsala Allah ya tabbatar da alkhairi Sakinah'.

  Sakinah na zuwa nan a tunanin  ta sake fashewa da wani irin matsanancin kuka mai cin rai kasa jura ta yi, hakan ya sata mi?ewa daga kan gadon ta fito zuwa falon inda Kamal ya yi gado da doguwar kujerar falon ya sanya filo ya kwanta, idonsa a rufe kamar mai bacci, Sakinah da ke tsaye tana kare masa kallo ta yi nufin juya da nufin barin gurin sai taga ya bude ido a hankali, duba ?aya ya yi mata ya ?auke kai tare da juya mata baya.

  Sakinah ta ?araso wajen nasa ta dur?usa daidai kansa tana fa?in.

  "Dan Allah ka yi ha?uri ka barni na yi aikin nan, ka da ka yi yun?urin ?aukan mataki mai tsauri a kaina tun yanzu, na yarda in dai ka ga ina ba daidai ba ka hana ni zuwa aikin, amma yanzu karka ce a'a dan Allah".

  "Kin san dai bana magana biyu ko? Magana ?aya tak na ke yi bana kuma sake wata ko na canja ta".

  Kamal ya bata amsa ba tare da ya juyo ya dubeta ba, Sakina tsaye ta mi?e tana mai share hawayen ta, tare da na?e hannunta duka biyu a ?irjinta ta cije le?anta da ?arfi kamar zata huda su da ?yar ta iya sarrafa bakinta wajen fa?in.

  "Ban ta?a tunanin a ?an wannan ta?aitaccen lokacin zan iya fara da na sanin aurenka ba Kamal, yau ?aya na ji ka fita a raina Kamal tare da tsanar aurenka da na yi gaggawar yi, ba tare da karantar asalin halinka na ?oye ba, ka cutar da ni Kam!"

  Kuka ne ya ci ?arfinta sosai, wanda ya yi sanadiyyar sar?ewar harshenta har maganar da take yi ta samu damar sar?ewa ganin hakan ya sanya ta komawa cikin ?aki da gudu ta fa?a kan gado tana gunjin kuka.

  Duk surutun da ta ke yi Kamal ko juyowa ya dubi inda ta ke bai yi ba, sai bayan ya ji shigewarta ?aki ya mi?e zaune a fusace cikin zafin nama ya dam?o filon da ya kwanta a kai ya yi jifa da shi ?asa tare da dafe kansa hannu biyu yana huci cike da matsanancin jin ciwo da zafin maganganun da Sakinah ta gaya masa, nan ta ke ya ji kaman ya mi?e ya je ya rufe ta da duka ko ya samu sa'ida cikin ransa.

  Sai dai ya yi ?o?arin tausar zuciyarsa kasancewar tunawar da ya yi basu ka dai ba ne a gidan, amma ba dan hakan ba yasan babu abin da zai hanashi sasata.

  "Dan taga ina kyaleta ne yasata samun talala da yawa haka har da zata tsaya tana gaya min maganganu son ranta".

  Ya ?arashe maganar yana mai yin kwafa ya koma ya kwanta fuskarsa na kallon ceiling tare da na?e hannuwansa a ?irji ya zubawa fankar da ke juyawa a hankali ido tamkar mai lissafin juyawar da ta ke yi.

  Dukkan su bacci a wannan daren sai ?arawo.

  Washe gari

  (Rana bata ?arya...!)

  7:20am

  *****

  Yau take juma'a kuma rana wacce ta kasance babbar rana ga dukkan al'ummar musulmi, amma ga Kamal farin cikinsa a wannan ranar ya zarce dukkan tunanin mai tunani, ya kuma tsalle tsammanin masu tsammani.

  Yauma kamar jiya su Sakinah tun asuba basu koma bacci ba tuni suka hargitse gidan da aikace-aikace har ?arfe bakwai da mintuna, wasu da ga cikin ma?ota suka shigo domin ?an taya su aiki, ka sancewar Hajiya ta ?an aikawa wa?anda tasan sun zama dole a gareta, bare kuma tasan ko bata aike ba za suji sabida yanda maganar auren ta kara?e dangi da unguwa.

  Kamal ango tun shida na safe ya fice da nufin za suyi wasu shirye-shirye kafin zuwa lokacin ?aurin auren, saboda a masallaci za'a daura bayan sallar juma'a kamar yanda aka rubuta a jikin katin.

  Haka gidan Hajiya Shema'u tun jiya ya ?inke da 'yan uwanta da ?awaye dam?am, sa?anin kuma wayewar garin juma'ar ?awayenta tun safe suka fara sallama a gidan kasancewarta mace mai mutane kuma hamsha?iyar mace da ta yi suna ta kowanne fanni dalilin bazuwar maganar auren kenan.

  Hajiya Shema'u ce zaune kan makeken gadonta tare da ?awayenta su biyar wasu a kwance wasu a zaune, a marya tasha jan lalle da ?aki gwanin ban sha'awa da ya ke fara ce ita tas sosai zanan ?unshin ya bayyana ra?au a jikinta, kanta kuwa ya sha kitson attachment har gadon baya ba?i si?ik sai she?i ya ke yi.

  ?aya daga cikin ?wayenta ta dubeta tare da ?an da fa hannun Hajiya Shema'u tana fa?in.

  "Amarsu ta Alhaji Kamal, kinsha ?amshi wallahi mutuniyar".

  Wata ba?a siririya da ke zaune gefe ta amshe da fa?in.

  "Ai Shema'u ba da ga nan ba, ni kuwa ya labarin kishiyar taki?"

  Biyu daga cikin su wa?anda suke farare ne ma'abota zubin manyan mata sosai suka tafa ha?e da shewa tare da yin gu?a ?aya daga ciki na fa?in.

  "Kamilar kishi zaki ce".

  Suka kuma kwashewa da dariya tare da shewa, Hajiya Shema'u ta yi murmushi kafin ta ce.

  "Lallai kuwa Kamilar kishi wai ni zata nunawa barikanci, mu da muka ginu cikin barikin, nan ya zo min yana fa?amin wai bata nuna kishi akan auren mu, da alamu kuma haushin hakan ya ke ji, ki ji min wata tsiya".

  Nan ma dariyar suka sanya duka kafin ?aya ta amsa da fa?in.

  "Ai nasan halinki mutuniyar to ya kuka ?are da shi?"

  "Ni kuma zama zan yi ina ?iban kayan takaici kenan?"

  "To yanzu ke me kika yanke nasan dai ba haka nan kike zaune ba, dole zaki ?au mataki domin ba kisan me ta taka ba".

  Cewar wata mace wadda duk ta fisu jiki sosai a cikin su a girme ma zata iya ?arasu da wasu shekaru, Hajiya Shema'u ta gyara zama da wani yalwataccen murmushi akan fuskarta kafin ta furta.

  "Kamar kin mance da wacece ni Hajiya Turai? Shema'u fa na ke, ka da ki manta da wani abu guda ?aya, shiru ba ya da wata katara, shintatar shiru abu ne mai matu?ar wahala, amma wanda ya yi shiru ba'a san iya tsaurin tana dinsa ba".

  *****

  Ku latsa nan don karanta babi na tara.

Comments

0 comments