Featured Create an Ad

Makalu

Blogs » Kagaggun Labarai » Ma'aurata: Babi na Biyu

Ma'aurata: Babi na Biyu

 • Idan baku karanta babi na daya ba to ku latsa nan don karantawa.

  Ana kiran sallah asuba ta farka daga bacci addu'an tashi daga bacci tayi kafin tayi mi?a tana salati ga Annabi S.A.W kai dubanta tayi a gefen da Fahad yake kwance tayi, har yanzu yana nan yana bacci kamar matacce.

  Ka?aa kanta kawai tayi ta mi?e ta nufi ban ?aki ta ?auro alwala sannan tayi raka'atainil fajar bayan ta idar tajima asujjada tana addu'a da nemawa mijinta shiriya.

  Tana idarwa ta fara karatun ?ur'ani mai girma ganin ankusa atayar da sallah ko motsi baiyi ba yasa ta tashi dan ta tayar dashi.

  Duk da kashedin da yayi mata idan yana bacci ba atashinsa hakan bai hanata tashinsa ba.

  Bu?e idanunsa yayi cike da bacci ya ce; "ke lafiya"?

  Cikin rawar murya ta ce; "uhm um da...ma. lokacin sallah ne naga yayi shine nace ko zaka tashi kar jam'i ya wuce k....

  Marin da ya kaimata ne yasa ta ha?iye sauran maganar ba tare da ta shuryawa hakan ba.

  Cikin masifa ya ce; "wai Fatima meyasa kika raina ni?”

  Idan kika kuskura kika sake tashina bacci Allah sai na lahira ya fiki jin da?i shasha kawai!"

  Daganan ya mi?e fau ya wuce ?akinsa yabarta zaune awajan tamkar mutum mutumi.

  Jin an tayar da jam'i yasa ta mi?ewa jiki asanyaye ta bi jam'i.

  Da safe bayan ta idar da ha?a abun karin kumallo ta sake gyara gidan ko ina tsab sannan ta yi wanka bayan ta shirya ta ?auko abincin ta tana ci tana kallon tashar larabawa.

  Bata ji motsin fitowarsa ba sai ganinsa tayi tsaye akanta fuskar nan ba annuri.

  "Ke kiyi abincin rana da yawa zanyi ba?i".

  Cikin ladabi tace dashi "to ina kwana"?

  Bai amsa mata ba yayi hanyar fita falon  da sauri ta ce; "ga abincinka ko na kawoma ?akin ka"?

  "Barshi acan" yayi maganar yana  mai ?arasa shigewa ?aki.

  Sai wajajen goma ya sake fitowa kai tsaye dani ya wuce ya cika cikinsa sannan ya tashi zai fita ya ?awala mata kira

  "Ke kina ina"? Fatima dake ?akinta kwance ta fito da sauri kamar zatayi tuntu?e ta ce; "ga ni".

  "Sakwara nakeso kiyi anjima koma dakan hannu na keso na kimanin mutum goma bana son na na'ura".

  "To Insha Allahu"

  Fita yayi ba tare da ya amsa addu'an da take masa na Allah ya tsare ba.

  Koda akayi sallah azahar ta kammala komai sai dai kam tasha wahala dakan sakwara.

  Uku dai dai ya shigo tare da ?an mata uku da samari hu?u dukansu ba mai shiga ta kirki,da kagansu kaga ?an bariki.

  Lokacin da suka shigo Fatima tana ?aki tana karatun novel a wayarta sam bataji shigowarsu ba sai muryarsa da tajiyo yana kiranta da sunan da ya saba "ke ke kina ina!?"

  Da rawar jiki ta ajiye wayarta tare dasa hijab har ?asa ta fito turus tayi ganin wa?anda ke zaune a falon sai wata budurwa da tayi shigar banza kwance ajikin mijinta tasani bata son Fahad amma dole taji ba da?i tunda mijinta ne.

  Tsawa ya daka mata "ke baki da hankali ni zaki zo kiyi mana tsaye aka da Allah wuce ki kawo mana abinci!"

  Cikin kirma  tabar wajan kitchen ta nufa tana zubar hawaye tana jin dariyar abokan.

  "Man baka da kyau miye dan Allah matsalar yarinyar nan ba laifi tana da kyau da diri sai dai da gani ?ar ?auye ce".

  ?ayan yace "tasa wani hijab kamar matar Liman".

  "Hahahaha Man kace ustaziya kake aure" cewar budurwarsa.

  Tsaki yayi kafin ya ce; "ai kawai ku bari Dady ya gama dani ya rasa wacce zai had'ani da ita sai wannan bagidajiyar"!

  Share hawayen da ke fuskarta tayi kafin ta ?auko babban  farantin da ta ha?a abincin da sallama ta shigo falon ta ajiye a gabansa sannan ta koma ta ?auko abun sha ta kawo har zata   wuce ya daka mata tsawa,

  "ke zo nan"!

  Da rawar jiki ta dawo ta sunkuya gabansa "ga ni"

  "Ubanwa kika ajiye da zai zuba abincin"?!

  Cikin kirma ta ce; "kayi ha?uri bara na zuba"

  Tana bu?awa da sauri  Sumeey tace kutt! waye zai ci wannan?

  Gaskiya Man bana cin wannan abar kuma yunwa nakeji"

  Sauran ma duk sukace ba zasu ci ba dan ba cimarsu bace,  Ali wanda tun shigowarsu tausayin Fatima ya cikashi daganin yanayinta mai sanyi

  sam bata dace da mutum kamar Fahad ba.

  Kallonta yayi cikin tausayi ya ce; "Fatima zubo mun"

  "Toh" ta amsa jiki asanyayi bayan tazuba ta kaimasa Man ya ce; "gayu me kuke bu?ata ta girka maku"?

  Wannan ta ce; tuwon samu wannan taliya wannan jalof d'in shinkafa

  "To kinji maza kije ki girka masu kuma karki kuskura ki ?ata mana lokaci"

  Haka ta shiga kitchen tana aiki tana mamakin almubazzaranci irin na Fahad sabida Allah abinci kala hu?u awuni Allah ya kyauta.

  Haka ranar ta wuni cikin bautawa Fahad  da abokanan sa sai Isha suka bar gidan bayan sun gama jin ka?i-ka?insu sallah kuwa ko sau ?aya bataji waninsu yayi ba.

  Ranar kam jam'i ko ?aya bata samu ba saboda ?aran ki?an da suka sa sai ita ka?ai tayi sallah,

  Tana jin fitarsu ta fito falon ko ina kaca kaca abinci kowa gashinan ba awani ci abincin kirki ba dama da hijab ajikinta fitowa tayi  tabawa mai gadi abincin tace idan wanda ta kawo masa bai ishe shi ba ya ?ara sauran ya kai makarantar almajiran da ke bayansu.

  ?arfe bakwai na safe  yagama shirinsa zai wuce wajan aikinsa ta shigo ?akin ba ko sallama 

  "Habib ina so zanje gida"

  "Kije makarantar koyan sallama idan kin koyo mayi magana"

  Yayi maganar batare da ya kalleta ba ya ?auki jikka laptop ?insa zai wuce tayi saurin shan gabansa cikin masifa ta ce;

  "wallahi Habib kana da matsala to naji salamu alaikum"

  Girgiza kai yayi kafin ya amsa da "amin alaiki salam"

  "To tunda nayi sallama sai abani amsa kuma ina son ku?i dubu goma zan biya  kasuwa"

  Murmushi yayi aransa yana mamakin halin Ru?ayya wai ta manta abun da tamasa jiya

  "Kayi shiru"

  "Bazaki ba, k?'i kuma bazan ce babu ba bayarwa ne dai bazanyi ba"

  Daganan yasa kai ya fita yana jinta tana magana cikin ?aga murya

  "kada Allah yasa kabayar ?in ma?o kawai"!

  Haka tabar ?akinsa zuciyarta na suya.

  Ranar kam a office yasa sakatirinsa ya sayo masa abinci ya karya.

  Ku latsa nan don karanta babi na uku.

  Ta ku Aisha A. Yabo (Fulani)

No Stickers to Show

X

Da Dumi-Dumin Su

 • Ku latsa nan don karanta labarin Saurin Fushi Na Kawo Da Na Sani. A wani ƙauye akwai wani mutum  ana kiran sa Abu Sabiru, ya kasance mai tsananin haƙuri da kawar da kai akan wasu al’amura. Dalilin da ya sa ma ake kiransa Abu Sabiru kenan. Yana zaune tare da matarsa kyakkyawar gaske ...
 • Ku latsa nan don karanta darasin rana ta uku. DARASI NA 1 Matakan rubutun gajeren labari A jiya mun yi bayani akan matakan da ake bi wajen tsara labari, yau kuma za mu bayani a takaice kan matakan da ake bi wajen rubuta ingantaccen labari. Waɗannan matakai ba tabbatattu ba ne, ma'ana ba wajibi ne...
 • Ku latsa nan don karanta babi na shida. Habeeb na kwance a kan doguwar kujera ya ji an murɗa handle ɗin ɗakinshi tare da turo ƙofar a hankali. A hankali ya buɗe idanunsa da suka yi nauyi sakamakon ciwon kan da yake fama da shi. "Fateemah" ya faɗa a ransa, lokacin da ya kai duba ga Jummai da ke ts...
 • Mon at 1:39 PM
  Posted by Bakandamiya
  Uwargida ba za ki yi dana sanin koyan yadda ake yoghurt in fruits ba. Domin kuwa kayan dadi ne sosai da sosai kuma cikin mituna kalilan za ki hada. Ba a ba yaro mai kiwiya!!! Wannan recipe yana daya daga cikin recipes da muka koyar a zauren Free Ramadhan Classes with Umyuman a nan Bakandamiya. Abu...
 • Hadin special salad nawa na musamman ne! Ga sauki ga dadi, uwargida sai kin gwada za ki bani labari! Wannan ma yana daya daga cikin recipes da muka koyar a Ramadan a shirin girke-girkenmu wadda aka gabatar a zauren Free Ramadhan Classes with Umyuman. Shin ko kin tuna gashin tsokar kaza da muka koya...
 • Red velvet cake, cake ne da mutane da dama suke so kuma kuma suke son ci. Saboda haka, akwai hanyoyi daban-daban na yin red velvet cake, ga yadda na ke nawa cake din na kawo muku. Wannan yana daya daga cikin recipes da muka koyar lokacin Ramadan anan Bakandimya. Domin ganin duk jerin recipes din da...
View All