Recent Entries

 • CIKIN ƁAURE:Babi na sha-bakwai

        Sosai maganar Umman Abbas ta saka Aunty cikin rudani, dan kuwa alamu sun nuna cikin tsananin fushi take, "Wata sabuwa kuma", Aunty ta fada cike da jimami, lokaci daya kuma ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, Asma'u da gabanta ke dukan uku-uku ta ce "Aunty me ta ce maki?", sai da A...
  comments
 • CIKIN ƁAURE:Babi na sha-shida

  Ta ɓangaren Abbas kuwa, tamkar farincikinsa ne gaɓaɗaya ya ba Asma'u a cikin takardar sakin, domin tunda suka baro gidan yake jin wani kalar tashin hankali a ransa, don ma ya yi ƙoƙari sosai ta yadda wani ba zai gane irin wutar da ke babbakar masa zuciya ba.    Bai iya gane shayi ruwa ne...
  comments
 • CIKIN BAURE: Babi na Sha-biyar

  Ko da lafiya lau Asma'u take abu ne mai wahala ta iya amsa kiran Abbas, bare kuma yanzu da take rai a hannun Allah. Ɗan bubbuga jikinta ya shiga yi, dan in ma bacci take ta falka, sai dai ko motsi bata yi ba, cike da kaɗuwa ya lumshe idanu, bakinsa kuma na cigaba da karanto "Inna li Llahi wa inna il...
  comments
 • CIKIN BAURE: Babi na Sha-hudu

  >>Previous page  A soro ya kafe mashinɗinsa kana ya shiga gidan. "Abbas ne?" Aunty ta faɗa, lokaci ɗaya kuma tana karantar yanayin fuskarshi, da dariyar yaƙe ya bata amsa da "Eh ni ne Aunty", hakan ne ya yi sanadin faɗuwar gaban Aunty, domin duk wanda ya san Abbas, toh zai iya banbance y...
  comments
 • CIKIN BAURE: Babi na Sha-uku

  >>Previous page Tsammanin Abbas dariyar jin daɗi ce Asma'u ke yi, wanda kuma haka yake fata ya ga ya yi mata abin da zai faranta mata zuciya, tambayarta ya yi "Yau ne sunan; ko yaushe?", ta ce "Gobe ne", d'an nazari ya yi kafin ya ce "Aaa! Ba gobe Thursday za ki koma awo ba?", ce mashi ta yi ...
  comments
 • CIKIN BAURE: Babi na shabiyu

  Ku  latsa nan  dan karanta babi na shaɗaya "Ban damu da duk wani sharad'i naka ba, in dai bu'katata zata biya", cike da gadara ta 'karashe maganar, tare da yi mashi kallo mai cike da tsangwama. Murmushin da ya fi kukan da yake ciwo ya yi, lokaci d'aya kuma ya girgiza kansa da ya yi ...
  comments
 • CIKIN BAURE: Babi na shaɗaya

  Ku latsa nan dan karanta babi na goma   Wani irin masifaffen son shi ne ya cigaba da azalzalarta a zuciya, sake sumbatar hoton ta yi kafin ta yi save. cigaba da gamsar da zuciyarta ta yi da kallonsa, a fili ta ce "Mutumin nan ya had'u", a ranta ta 'karashe fad'in "In dai na mallake shi b...
  comments
 • CIKIN BAURE: Babi na Goma

  Ku latsa nan  dan karanta babi na tara   A wannan karon ma, Asma’u bata ji me ya ce ba saboda komai nata ya d’auke in banda bugun zuciyarta dake ta ‘karuwa. A tsammanin Abbas miskilancinta ne ya motsa, don haka ya zuge bakinsa tare da maida dukkan nutsuwarsa ga tuki. I...
  comments
 • CIKIN BAURE: Babi na Tara

  "Wato titsiye ni zaki yi ko?", bakin Asma'u dauke da dariya ta jefo ma Khadijah wannan tambaya, kai Khadijah ta girgiza "A'a waace ni, kawai dai dan in san irin shawarar da zan baki wadda zata fisshe ki ne." 'Dan rausaya kai Asma'u ta yi "Auho!". Shiru na wucin gadi ta yi tana nazarin hujjar da za...
  comments
 • CIKIN BAURE: Babi na Takwas

  Idanun likitan cikin nata ya bata amsa da "Yeah, kina da juna biyu Madam." Tamkar wadda aka tsikara ta miƙe gami da dafe ƙirjinta dake luguden faɗuwa ta ce "Na shiga uku ni Asma'u", a yadda ta ƙarashe maganar kai ka ce faɗowa ƙwayoyin idanunta zasu yi saboda tsananin firgici. A tarihin rayuw...
  comments
 • CIKIN BAURE: Babi na Bakwai

  Kallon ta Abbas ya cigaba da yi, lokaci ɗaya kuma yana murmushin da shi kansa ya san yaƙe ne, don ko kaɗan bai ji daɗin yadda ta yi ƙerere a gabansa tamkar sandar rake ba, sai dai ya danne rashin jin daɗin saboda ya fahimci ɗanyen kan yarinta na ɗibar ta, uwa uba kuma ga ƙarancin wayewa a tattare da...
  comments
 • CIKIN BAURE: Shafi na Shida

  Zaman da Asma'u ta yi don chat ɗin bai mata daɗi ba, kasantuwar jikinta bai iya ɗaukar sanyin da ke ratsa ƙafufunta yana shiga cikin jikinta, naɗe kafafuwan ta yi a kan kujerar one seater da take zaune, lokaci ɗaya kuma ta lulluɓe kaf jikinta da marron Hijab, farinciki fal a ranta ta yi zaman hakim...
  comments