Rubutu

Blogs » Kagaggun Labarai » KISHIYAR KATSINA: Babi na Daya

KISHIYAR KATSINA: Babi na Daya

 • Da sunan Allah mai Rahama mai jin ƙai, tsira da amincin Allah su ga tabbata ga masoyinmu kuma masoyin _Sahabi Mus'ab bin Umair_ , Annabi Muhammad S.A.W, Baban Ibrahimul Mu'azzam da Abdallah.

  _Wannan Littafi Ƙirƙira ne, ban yi don cin zarafin wani gari ba. Asali ma littafin na ƴan kowane gari ne, idan kina kano, toh ki ɗauke shi a matsayin KISHIYAR KANO, na sa jihata ne don ni ƴar Katsina ce, ke ma ki kalli labarin da sunan Jiharki, ta haka ne zaki fahimce shi.

  Wannan shafin sadaukarwa ne ga kowa ce _Uwargida_, albarkacin Jikalleta ~Nana Aicha


  Durƙushe take a gaban mijinta mai suna Khamis, wanda ke zaune a gefen gado yana ƙare mata kallo. Idanunta cike da ƙwalla ta dube shi tare da yin magana cikin raunin murya ta ce "Ni fa ban ce zan hana ka ƙara aure ba, kawai dai Ƴar Katsinar ce bana so".

  Ɗago kafaɗunta ya yi tare da faɗin "Tashi ki zauna", ƙasan ransa kuma yana mamakin sauyawarta na lokaci ɗaya, don tunda ya fara zancen ƙara aure take ƙoƙarin danne kishinta, amma da jin ƴar Katsina ce zai aura sai rauninta ya rijayi ƙarfinta.

  Bayan ta zauna a gefenshi ne ya jefo mata tambaya cikin taushin murya "Meye aibun matan Katsina da bakya son in ƙara aure da su?".

  Kara raunana murya ta yi sannan ta ce "Kowa ya shaida *Katsinawa mugun asiri gare su* yanzu kana auro ta sai ta raba mu da kai, ni kuma shi ne bana so".

  Ko da jin hujjar da ta bayar ya gane ƴan zuga ne kawai ke son rikita mata lissafi, saboda ba inda ta san Katsinawa bare ta yi musu wannan muguwar shaidar. Cewa ya yi "Kin taɓa ganin wanda suka yi ma asiri?".

  Shiru ta yi saboda bata taɓa gani ba.

  Ya ce "To Aysha ki dena kula 'yan zuga, don ba inda zasu jefa ki sai cikin rudani".

  "Wallahi ba wani ƴan zuga a nan" ta faɗa tare da sake fashewa da kuka, saboda ta fahimci ƙorafinta bai karɓu ba.

  Yadda take kukan ne ya ba shi tausayi, lallashin ta ya shiga yi da maganganu masu tausasa zuciya. Ya ce "Aysha ki kwantar da hankalinki, bana jin ƙarin aurena zai rage ko da ƙwayar zarra na son da nake maki, kuma yarinyar da zan aura kowa ya shaida bata da matsala, don haka nake da yaƙinin ba zata taɓa zama matsala a gare ki ba".

  Ido ta lumshe tare da
  haɗe gululun da ya tokare mata zuciya, a ɓangare ɗaya kuma tana ganin tunda har zai mata kishiya alhalin haihuwarta biyu, to ba wani sauran sonta a ransa, kawai dai yana faɗin haka ne don ya kare kansa.

  Ba zata iya fitowa kai tsaye ta ƙaryata shi ba, sai dai ta yi mashi hannunka mai sanda ta ce "Ba zan yi maka musun so ba, amma ba sai ka ɓata lokacinka wurin faɗa ba", rufe bakinta ya yi daidai da fitar siraran hawaye a Idanunta, bayan hannu ta sa ta cigaba da gogewa.

  Kai kawai ya girgiza, don ya san kishi ne ke ta ɗawainiya da ita. Bai fasa lallashin ta ba, don ba zai so ta ce ya wulaƙanta ta saboda ƙarin aure ba.

  Jin shi kawai itama take, mafarin yana fita ta kira Aminiyarta mai laƙani da Zuzee a waya, labarta mata yadda suka yi da Khamis ta yi, saboda ita ke tsara mata komai.

  Tsaki Zuzee ta ja tare da faɗin "Ke rabu da shi, ƙaryar so yake maki, kuma don yana son yarinyar ne yake wani kare ta, amma waye bai san mugun halin Katsinawa ba".

  Tsoro bayyane a fuskar Aysha ta ce "To Zuzee ya zan yi da shi, wallahi tsoron asiri nake".

  "Ki kwantar da hankalinki, muma ai mun iya shige-shigen".

  Ruwan rubutu ta kawo ma Aysha ta ce su riƙa sha ita da yaranta har da Khamis, wai duk kariya ce daga Asirin Katsinawa, tunda dai maganar aure tana nan daram.

  Da yamma liƙis Khamis na zaune a falo ta kawo mashi ruwan rubutun a cup, ɗan yamutse fuska ya yi tare da tambayar ta "Mi ye wannan haka?".

  "Ruwan addu'a ne", ta bashi amsa, sai da ya ƙara kallon cup ɗin sannan ya ce "Kuma baƙi haka?"

  Ta ce "Eh, ka daure ka sha", bayani ta yi mashi wai na kariyar jiki ne. Ba tare da ya tambaye ta inda aka same shi ba ya ɗan kurɓi kaɗan, saboda ya san ƙawayenta ƴan zuga ne suka kawo mata, kuma da sannu zai raba ta da su, don ba zai so su rikita mashi ita ba.

  "Ka shanye mana Abban Haneef", ta faɗa tare da maraicewa.

  "Bana jin ƙishirwa yanzu, amma ki kai shi ɗakina a fridge, anjima zan sha".

  Karɓar cup ɗin ta yi tare da yin abin da ya ce. Aikuwa yana komawa ɗakin ya juye ruwan a flowers ɗin dake bayan windown ɗakinsa, don ba zai iya sha ba.

  Saman fridge ya aje cup ɗin, sannan ya shiga banɗaki ya yi alwalar magarib, yana fitowa ya sanya baƙar jallabiyarsa. Cup ɗin ya ɗauka ya kai mata a kitchen, sannan ya kama hannun Haneef suka tafi masallaci.

  Ganin cup ɗin ya tabbatar mata da ya shanye, aikuwa kusan kullum sai ta kawo mashi, bai taɓa musun karɓa ba, kamar yadda bai taɓa sha ba, saboda yana cewa a'a rigima za tashi.

  A zihiri kam Aysha ta samu nutsuwa, amma a baɗini cikin tashin hankali take, kullum gani take kamar ƙarshen farincikinta ya zo.

  Khamis kuwa ya fahimci bata da nutsuwa a zuciya, mafarin ya ƙara ƙaimi wurin faranta mata, duk sadda ya ga ta yi jugum, toh sai ya san abin da zai mata wanda zai sa ta dariya.

  A lokacin da Auren ya gabato ne ya ɗauke ta suka nufi wani katafaren store, kayan ɗaki na gani na faɗa ya saya mata. A ɓangaren lefe ma duk abin da ke cikin akwatin amarya itama akwai shi a nata, yaranta 2 ma sai da ya haɗa musu nasu lefen, daga ƙarshe kuma ya damƙa mata kuɗi masu yawa ya ce "Idan zan dawo _aza room_ in ji chanji".

  Butulu ne kaɗai bai gode ma Khamis ba a kan Alkhairin da ya yi ma Aysha.

  Sosai itama ta gode mashi, sai dai maimakon ta fara gyaran jiki da kuɗin, sai ta ɗibi kaso mai yawa ta ba Zuzee, wai za'a yi mata addu'ar dangana, saboda tana ji kamar itama zata iya cutar da amaryar idan ta shigo. Ƴan kuɗin da suka rage kuma ta yi gyaran jiki da su.

  A daren ɗaurin auren kuwa kasa bacci ta yi, Khamis da shima baccin ya ƙaurace ma Idanunsa saboda farinciki ya tashi zaune, tsam ya ɗago ta tare da yi mata lafiyayyar runguma.

  Tambayarta ya yi cikin raɗa "Aysha har yanzu baki yi bacci ba?", saboda ya lura tunda ta kwanta take ta juye-juye.

  Sai da ta matse ƙwallan tausayin kanta sannan ta yi magana cikin muryar kuka "Ta ya zan yi bacci a daren da mijina zai damƙa rabin soyayyar da yake mani a hannun wata".

  Ido Khamis ya lumshe, cikin ransa yana jin wani irin tausayin ta da ya fara zame masa jiki "Aysha ban san da wane baki zan tabbatar maki da son da nake maki yana nan daram ba, amma ina son ki ɗauki wannan auren a matsayin wata ƙaddara, wadda muke fatan ta zama mai kyau a garemu baki ɗaya". Cikin sigar lallashi ya cigaba da faɗa mata maganganu masu tausasa zuciya. Ba su suka kwanta ba sai da Khamis ya ga ta samu ƴar nutsuwa.

  Da ƙarfe huɗun Asuba suka tashi, wanka suka gabatar da ƴan nafilfili, bayan gamawarsu kowa ya roƙi Allah buƙatarsa, shi dai Khamis fatansa Allah ya sa su je ɗaurin aure lafiya kuma su dawo lafiya.

  Aysha kuma roƙonta Allah ya sassauta mata wannan azababben kishin dake addabar zuciyarta.

  Da sanyin safiya kuma Khamis da Haneef suka fara shirin tafiya ɗaurin aure. A ɗan lokaci kowannen su ya fito cikin farar getzna da aka ƙawata aikin bababbar rigar da blue ɗin zare, hular da suka sa ma ta dace da aikin rigar.

  Haneefa na ganin su ta kama kuka, wai sai an tafi da ita, dubara Khamis ya yi mata ya ce "Je ki ce ma Aunty Hafsat ta yi maki wanka", kasantuwar a gidan ƙannensa mata suka kwana, da gudu kuwa ta ruga a ɗakin da su Hafsat ɗin suke.

  "Abba mu tafi kafin ta dawo", cikin zaƙuwa Haneef ya faɗi haka, don ya san wayau ne aka yi mata.

  Sai da Khamis ya ɗauke dubansa akan Aysha da itama ta kafe shi da idanu sannan ya ce ma Haneef "Bari Mammy ta fesa mana turare".

  Murmushin yaƙe Aysha ta yi sannan ta ɗauki ƙayataccen turaren dake kan dressing mirror ta shiga fesa musu, cikin zaulaya kuma ta riƙa faɗin "Ango ka sha ƙamshi"

  Dariya kawai Khamis ya yi, sannan ya tura Haneef a waje.

  Jawo ta ya yi dai-dai lokacin da take faɗin "Ka yi kyau mijina, Allah ya sa kuje lafiya, kuma ku dawo lafiya".

  "Amiin Habibty, godiya mai yawa" ya faɗa tare da sumbatar ta a goshi.

  Irin wannan kulawar ce Aysha ta tsani wata mace ta same ta a wurin Khamis, kasantuwar sa mutumin da ya ƙware a wurin cire ma mace damuwa.

  "Aysha ki iya control ɗin damuwarki kin ji, kada ki bari a taron da za'a yi a gane maki, kaɗan zaki kuskure mutane su samu abin faɗi".

  Ɗaga kanta ta yi alamar "Zan kula" lokaci ɗaya kuma ta maida kan a ƙirjinsa. Sun ɗan ɗauki lokaci ba tare da magana ba, daga bisani suka fito falo.

  Sosai Ƙannensa suka yaba kyawun da ya yi, fatan dawowa lafiya suka yi mashi, Haneefa kuwa tana can cikin towel, wai sai ta tsane sannan za'a shirya mata.

  Falo Aysha ta zauna suka cigaba da hira ita da ƙannen Khamis, a zahiri ba zaka taɓa cewa tana da damuwa ba, a baɗini kuwa ji take kamar zuciyarta zata buga.

  Washegari ran walima ne takamaiman abin da take ta ƙoƙorin ɓoyewa a zuciyarya ya fito fili.
  A wurin buɗar kai ana damƙa mata amanar Amarya ta ce "Amana wuya gare ta, don haka ban karɓa ba", wannan magana da ta yi duk shawarar Zuzee ce, domin sun daɗe a jiya suna ƙullawa da kwancewa.

  Sosai ta ba kowa mamaki, musamman danginta da na Khamis, saboda basu taɓa tsammanin haka daga gare ta ba.

  "To ba damuwa, Insha Allahu mu Ƴarmu zata riƙe ki da amana, saura kuma ya rage naki" In ji Gwaggon Amarya.

  Jiki ba ƙwari ta miƙe tare da kama hannun Amarya dake ta mazurai a cikin lifaya ta ce "Mu je Maryam"...

  Maman Mu'azzam

Comments

0 comments